← Book details Aljanar Ruwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 55

Sashe 14

Aljanar Ruwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Monster. Yes lord lady. Inason ka sa yaranka suyimin kidnapping kabir gobe. Katambaye iyayenshi kadarorinsa na gidan marayu daya bude. Inkuma sukaki ka arbeshi har lahirah. Angama ranki shidade

Gaban Aunty Amarya ne yafadi jin za'ayi kiddnapp din kabir.

Alhj usnam yace. Ranki shi dade. Karkice na bujire magananki. Mai zai hana kawai idan. Sunki. A kyaleshi. Nikuma inada yarinya ZAINAB. Innace mata tadauki aiki a company sa tazama hannun damansa.baza ta bujire bah tunda nasan ta Dade Tana sonsa. Kinga abun zaizo mana da sauki. Yanda zata dunga kawomin bayanai hakan kudadensa da kadarorinsa.

Kinga daganan saimu kwashe komai.
Wannan shawarar nakawo amma inkinga baiyibah toh za'a iya kasheshin.

Shikenen na yarda da maganarkah. Amma zan tunatarda Kai kada tamana shirme. Inba haka bah. Zan hallakata.

Da yardan Allah komai zai tafi daidai.

Alhj usman yakara fadin Uwar shedanu gsk inajin tsoro hakan wannan budurwan datazo jiya tace zata hallaka mu.

Inbamuyi wasa bah kada Aje da gsk take zata hallaka mu idan bamu daina bibiyan rayuwan kabir bah.

A hassale uwar shedanu tatashi. Sauran yan qungiya naganin hakan suka durkushe taresa yimata sujjada. Suna bata hakuri.

Karya take, bata isah hallakani bah. Tabbas ba mutum bace . Dole saina gano a ina take. Kuma yanzu wasan yafara.

wannan shine. tanagama fadin haka tayi tafiyarta. suma sauran yan qungiyan suka watse.

Bangaren kabir kam. Saida yamata staff ya gyara mata fuska Dan kar aga shatin Mari a fuskanta. Tashi mutafi gida cewar kabir.

Kisameni a waje Dan bazan jira kibah.
Yana kaiwa nan yayi fucewarsa.

tabe baki Amriya tayi tareda fadin kaika sani mugu kawai. da A lokacinda zobena yana tareda nine dabaka Isah katabamin koda yatsata bah.

Tashi tayi. Wani mugun ciwon Mara taji yazomata. A daddafe tafara tafiya hannunta rikee da maranta Wanda yakemata mugun ciwo .

Saida taje daff dashi. Kawai tatafi luuuuu zata fadi. Saurin riketa kabir yayi yana Jan tsaki.

hadida zaunan da ita a gaban mota. whattt yafada. ganin yanda jikin shi yayi tsenin a jini. what's this rubbish. oh my god. Cikeda bakin ciki da takaici yace

keee bakida hankaline zaki batani da jini. kekinsan kina period bazaki iya killace kanki bah. this is embarrassing Wlh.

Cikeda rashin fahinta Amriya tace. Ni... Ban... Gane... Me.. Me.. Ka.. Ke.. Nu.. Fi.. Bah.

gigiza kanshi Kabir yayi yace wato raina min hankali zakiyi koh.

tsaki yaja yashige ciki. gidan. Yana shiga yanufi toilet. Saida ya yi wanka yakai so goma. Shinshina kanshi yayi yaji haryanzu yana karnin jini. . Saida ya hada sabulai. Wajan biyar. Sannan yacigaba da durza jikinsa kamar fatansa zata bare.

Yanagama wah. Yanufi wardrobe yasaka kananun kaya. Tareda gyara suman kanshi. Yasaka oiling lotion Mai kyau da kamshi.

Wajan turarema saida ya fesa wajan kala biyar. Sannan yafuto yanufi parkin space. Kallonta yayi jiyake kamar wani yana kara huramai wata wutan tsanar Amriya .

dauke kansa yayi daga kallonta. Tada motan yayi suka fuce daga gidan direct hospital yanufa.

parking yayi. yafuto daga cikin motan. ZAINAB dake tareda friends dinta zunzo wucewa ta hangoshi. Jikinta karkarwa tace kunga Sir kabir dream guy dina. Dole mah naje nayimai tayi soyayyata kafun lokaci yakure.

Daya daga cikin friends dinta tace amma bakya ganin Hf akan bai dace bah. Kinsan tsaff ,zai iya duzgaki agaban mutane.

murumushi zainab tayi tace ni yar Alhj usman za'a duzga. God for bid kudai kuzubah ido kugani.

gyara zaman mayafinta tayi Wanda Dashi gwara babu Dan komai najikinta anagani.

Tafara tafiya Tana lankwasa. Hartaje gabanshi. Excuse me handsome. Dago kanshi kabir yayi ya zubamata. Kallon sama dakasa yayi mata.tsaki yaja yace daman haryanzu hana samun lower class ladies bansani bah.

Magananshi bakaramin batawa zainab rai yayibah. Basarwa tayi tace. Sir kabir. Nice Yar gidan Alhj usman.

and so nace saime inke Yar gidansa ce hajiyeni yayi. Dazaki ce ke yargidan Alhj usman.

Am sorry for my words Sir amma wacece wannan. Kallon Amriya yayi. Yakuma maida kallonsa kanta yace me kika gani.

Zainab tace naga kuna tarene kamar ma'aurata. Is she your wife.

Exactly yesss she iss. And how is that your problem .

Wani kishi ne ya mamaye zuciyan zainab tace. Sorry butt.

Eh you banason nakarajin wannan banzan murya naki. Karki tunzurani aikata abunda raina baiso bah. Dan haka leave before i count three.

sir please kasaurareni dama daya kacal. Sir. kallonta yayi yace amma fah kinyi mugun raina min hankali. nayi miki kama da mazan da zan tsaya da ballagaza irinki ina mgn dasu.

Sir but you kn...... Batakarasa bah taji saukan Mari.

Amriya kam inbanda kallo ba abunda takeyi. Ita batasu takebah ta ciwo da radadin da maranta yake mata take.

how dare you am talking you are talking. did i resemble your mate.

dafe kuncinta zainab tayi zuciyanta namata kuna. Wani irin tsanan Amriya ya baibaye zuciyanta. Cikin ranta tace dukk sbd kee ya mareni na rantse hakanki zan fanshe marina.

Barnan yafada a tsawace. Saurin barin wajan zainab tayi. Tanufi inda kawayenta ke tsatsaye sai kwasan dariya suke.

maida kallonsa yayi kam Amriya yace kekuma tashi mushiga ciki. ba.. zan... iya... bah..

Cikeda baccin rai kabir yace baza ki iya bah toh sokike na goyaki kenan tsswm yaja tsaki. Dallah malama tashi duk kinbatamin seat da jini.

Tashi tayi suka nufi cikin hospital din.

wata nurse yasamu yayi mata bayani komai. rikee Amriya nurse dintayi tace kaje kawai zan kulada ita abunda hake bukata yanzu kaje pharmacy kasiyo pad dazatayi anfani.

What you mean mee. Naje nadiyo pad a big person like me. Impossible.

mikawa nurse kudi yayi wajan five thousand yace kekije kisiyo mata. Saurin karba nurse dintayi hannunta na karkarwa . Tace ok Sir. Fucewa yayi daga wajan. Yakai motan wajan wanke mota. Dan bazai iya cigaba da ganin wannan kazantan bah

shigar da Amriya nurse din tayi cikin room 2. Tace barana kiramiki doctor Amina saita dubaki. Daganan kidan gyara jikin ki kafun tazo. Toh Amriya tace. Futa nurse din tayi. Toilet Amriya tashiga tafara gyara jikinta. Saida tadau fifteen minutes kafun tadawo mutum daga Aljanar ruwa datake.

Doctor Amina ce tashigo hannunta rikee da kaya. Futowa Amriya tayi. Sharaff sukayi ido hudu da doctor Amina. Wani mugun faduwa gabane ya ziryarcesu gabadaya.

Amriya tace cikin ranta. Wannan bawanan matar bace da na buge bansanibah awajan kitso.

Tattaro nutsuwanta dct Amina tayi tace sannu yata yajikin Naki.

Da... Sau.. Ki.. Yauwa Ganshi inji mijin ki yace nabaki kisaka wannan kayan.. Amriya tace ba.. Mi.. Jina.. Bane.. kaninane... zaro ido Dct Amina tayi tace kani kuma ba yaya bah.

Amriya tace... bai.. Kai.. nakira.. shi... yaya.. bane.. shi.. yasa... nace kanina... murmushi dct Amina tayi. lck daya taji Amriya tashiga ranta sosai.

dct Amina tace inyaciki fah.. Tabe baki Amriya tayi tace.. Yaji... Din.. Mai... Zai... Iyayi.. Min.. Wanan.. Mug.... Batakarasa bah idanuwata suka sauka hakan na kabir Wanda ya tsaya fuska a murtuke hannusa rungume a kirjinsa.

Kurrrr kara cikinta yashigayi. Hannu na karkarwa ta karbi rigan hannu dct Amina tashige toilet.

murmushi Dct Amina tayi tace da Alama kanacin zalin wannan sister taka. Kalifah tana ganinkah ta rude.

Zama yayi kusada itah yace kyaleta dct zamu gamuda itane.

Ringing wayanta yafarayi dayawa tayi tareda yin sallama. Tace yusuf kafiye takura Wlh nacema idan ina duty kadaina kirana koh ban fadama bah.

Bangaren yusuf kam ya shagwabe fuska yace aba ammi kinsan bazan iyayin 1 hour banji muryanki bah.

Toh saikayi nika rabudani Wlh shiyasa mah nakeson babanka ya aurarda Kai kowa ya huta.
Hau ammi korata kikeyi kenan. Ba dolebah duk kabi ka addabi mutane kodan kasan kai kadai mukeda shiyasa kakeson samun hawan jini koh.

Noo ammi magana bazata kaimu har haka shikenan zandaina kiranki idan kina duty byeee adawo lfy.

Katse wayan tayi tareda fadin this boy bayaji Wlh .

Futowa amriya tayi cikin abaya pink wanda yayi matukar yimata kyau.

Yamushe fuska yayi tareda fadin inkingama kisameni awaje.

Yana kaiwanan yayi fucewarsa.

yauwa yata kinsa pad din. ehh... nasa... yauwa.. toh ka wannan diklophenic din kishashi da safe dakuma dare.

Godiya Amriya tayi mata daganan tafuce daga dakin.

Murmushi dct Amina tayi tace gsk she is beautiful.

Amriya na futa tanufi hanyar Motan tareda bude murfin no motan baya tashiga. Wani kallon bakida hankali yazuba mata yace. Wato ka drivern ki koh. Dallah futo kikoma gaba kafun nabata miki rai. Futowa Amriya tayi tashiga Hanan motan. Fucewa sukayi daga harabar hospital din suka nufi hanyar gida.

horn yayi hatake body guard sukashiga bude kofa. . su mom najin karan mota sukayo hanyar waje.

Parking yayi. Yafuto daga cikin motan futowa itama Amriya tayi. Su nadirah. Naganinta sukatafi da gudu suka rungumeta.

Kusada grandma zaibi yawuce tace zonan Mai kan giginya wato Kai harnakai intsaya agabanka kaki gaisheni toh fadamun ina kakai mun yar jikata.

Wajan su mom Amriya tanufah tareda gaishesu. Mom tace lfy mushiga ciki koh. Shiga ciki gabadayansu sukayi shiko gogon naku inbanda hura hanci ba abunda yakeyi...

Mom tace fadamin yata Mai kabir yayi miki dakuka futa dazu.

dago kanta Amriya tayi tadora hakan kabir harara ya watsa mata sauri dauke idonta tayi daga gareshi tace bako....mai. mun fu..tane yawo. shi...ne yake fada...min Abunda yayi...min ba...dai...dai ba..ne ku..ma inya...femai. shi...ne nace....mai naya...femai. Ya....kaini gu...rin siya...yya yasi...yamin wanan ka...yan.

Zaro ido gabadaya su Kalisat sukayi. Dan tabbas sunsa gabadaya abunda tafada karyane.

Grandma tace karyane Wlh wannan botoramin ne zai baki a hakuri AI Wlh koda AL qur'ani zaki daukoh ki min ratsuwa dashi bazan yardabah.

wannan yaron da bakin zuciyansa gareshi zai baki akuri karewanta man harda siyan kaya.

Su khaleed mah sunyi mamaki wai kabir yabawa mace hakuri

shima kabir yayi mamaki yanda ta rufamai asiri.

Murmushi Amriya tayi tace ku.. Yar.. Da.. Dani... Da.. Gsk.. Nake.

mom tace shikenan wuce daki. daddy su sadiq mah yayi fucewarsa daga gidan . Dad yace kowa zai iya tafiya.

su nadirah kam Bin Amriya sukayi hardakin Aunty Amarya. Kallonsu nadirah Aunty Amarya tayi tace kudan bamu guri zamuyi magana. Tashi gabadaya sukayi suka fuce daga dakin.

Amriya meyasa kikayi karya. Fashewa Amriya tayi da matsanancin kuka tace bazan iya fadabah Aunty Wlh bansan meyasa bah zuciyata bata iya laminta Inga hanayiwa Kalb fada. Shiyasa.

OK shikenen na fahimta ki kwatarda hankalinki.
Chapter 14 · 0% Book details