← Book details Aljanar Ruwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 55

Sashe 47

Aljanar Ruwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yayin da aka ce itama Karima ta futo da miji. Jin akan da Karima tayi yasa ta bayyana wa kowa abunda ke cikin ranta, jin akan kuwa bah karamin bata ran mahaifiyar su mai suna Jamila yayi bah, da Kuma y'ay'an su Suleiman bah.

Amina tace tayi hakuri domin kuwa bazata iya sadaukar da soyayyar ta bah, ita kuwa Karima ta nuna mana cewar, komai ya wuce babu komai a zuciyar ta, ashe itadin munafuka ce.

Bayan wasu kwanaki Habib ya turo magabatan sa , yayinda aka tsaida auren Amina da Kuma Habib.

Ni kuma a lokacin an kusa bikin mu nida Maryam. A lokacin kuwa, Karima ta bijiro da kule kulen samarin, harta kawo min wani saurayi mai suna Harun, wai yana sona, ta karfi da yaji, Karima tasa na fada a soyayyar Harun,

Yayinda muke soyayya Cikeda burgewa, Harun, ya kasance masu matsakaicin karfine, amma akan bai hana ni k'in sonshi bah,

Ranar aure na kuwa, ta zuga ni wai mu gudu da Harun, ni kuwa nace mata gaskiya bazan iya butulci bah, kunyi mun abubuwa da dama, amma in rasa da abunda zan saka muku sai wannan.

Aka dai taita zuga ni, nace indai saboda soyayya zaisa na gudu toh saidai na hakura, data ga nak'i sauraron ta, ta shakamin abu a hanci na, cikin kankanin lokaci bacci yayi hawan gaba dani. Aka suka cincibe ni suka kaini daji batareda nasan inda kaina yake bah,

Bayan farfado wata, take fadamin cewar saita dau fansar abunda muka aikata mata nida Amina, lokacin ne Harun ke fadamin cewar bah sona yakeyi bah ita ta biyashi danya cimin zarafi Kuma nasa ahalin da suka yarda dani, su tsaneni, Suji kaff duniya babu ma yaudariya maciya amana sama dani,

Kuka kamm nasha shi Harna godewa Allah, Hana tsaka da aka, Harun ya bayyana mun soyayyar sa agareni, tareda cewar shin zan auresa, Babu bata lokaci na yarda muka daura aure nidashi, yayin da ya gina mana gida na masu rufin asiri,

Ashe a lokacin Karima ta dai photo na da Kuma Harun ran auren mu, ta tura muku, akan yasa kuka nuna baccin ranku akaina, rana bazata tashi ta fadi ba Tareda nayi kuka bah,

Hana aka naji labarin itama Amina an daura mata aure da Habib, murna sosai nayi shi, domin kuwa har naso zuwa inda gidan ta yake amma kuma bansan gidan ta bah. Ba yadda na iya, aka na hakura na fauwala wa Allah komai, domin shine Mai jikan bayinsa.

Babu bata lokaci, Harun ya neman mu makarantar Jami'a, na fara zuwa Harna karanci medicine, yayin da itama Amina abunda ta karanta kenen.

Hana aka mukaji labarin cewar Abba ya mutu bisa hatsarin mota daya gamu dashi, kuka mai cike da danasani nayi, saboda a ganina nice sanadiyar mutuwarsa .

Bayan lokaci ne Kuma naji labarin kayi aure ka auri Fatima. saboda kunya abunda na aikata bah Lallai ku yarda dani bah yasa nak'i zuwa auren.

Hana aka kwatsam watarana na fara amai mukaji asibity, hanan likitoci suke sanar mana da cewar ina dauke da cikin wata biyu.

Sosai mukayi murnan wannan cikin yayin da Haruna ya dora son duniya akaina har cikin yakai wata Tara.
Ganin muna rayuwa cikin farin ciki da qaunan juna, yasa Karima ta kuma dawowa cikin rayuwar mu, a wannan karan bah ita daya bane, su dayawa ne domin kuwa tayi joining yan kungiyan asiri .

Lokacin ta umarci mijina Harun da ya dunga mata aiki, shikuwa yace bazai taba aikata akan bah. Kuma yace da ita sai ya tona asirin ta a idon jama'a, ya dau Wayanshi Tareda kira police.

Karima na ganin akan ta harbe shi da buduga, ya fadi a wajan mutacce, daidai lokacin kuwa na kuda ya kamani.

Babu bata lokaci police zuka zo, suka kamata, aka kaita police station.

Ni Kuma a lokacin na Haifi dana, kuka nashashi Harna gode Allah, yayinda aka suturta harun aka kaishi gidansa na gaskiya.

Bayan shekaru biyu na gama makaranta na nayi NYSC na a garin Kano, yayinda akayi posting dina'a hospital, na Fara aiki

bayan wasu lokaci naji labarin ta futo daga cell, akan bah karamin tayar min da hankali yayi bah, domin kuwa bansani bah ko wannan futowar tata ya kasance wani gagarumar matsalan, cikin sa'a kuwa ta daina bibiyar rayuwa ta.

Hana aka na shirya Domin naje na nemi gafarar ku, zuwa na keda wuya naganta acikin gidan nan wai a matsayin matar aure, ganin aka bah karamin tayar min da hankali yayi bah, domin kuwa nasan da cewar bah alkhairy ne ya kawo ta wannan gidan bah.

Akan yasa na juya na tafi gida na cigaba da lallaba rayuwata da Kuma na dana. Ina nan duty na a hospital naji kira ya shigo bah bata lokaci, na d'aga Kiran tareda karawa a kunne na,

Muryar dana ji ne yayi matukar girgiza ni, muryar dana ji kuwa bata kowa bace illa na Amina, sosai Nayi murna Mara misaltuwa a ranar, mu ka taba hira, Kuma tace min zata dawo asibity da nake aiki.

Nadira tace kina nufin Doct Amina itace yar uwar Mom, Doct khadija ta bata amsa da fadin kwarai kuwa itace yar uwata, amma kuma har yau har gobe babu wani a tsakanin su dayasan cewa sudin yan uwa bane, domin kuwa, duk saida na bi hanyan danasan cewar Karima baza ta ga Amina bah, domin karta ganta.

Kamar yadda nake fada, bayan kwanaki aka kawo matar yahya, asibity zata haihu, yayinda iyaka Karima take na kuda, a taredai naga kun kawo su asibityn, ganin akan dana yi yasa nasa face mask ta yadda baza ku gane ni bace,

Na karbi haihuwar Fatima da Kuma na Karima, cikin rashin sa'a Kuwa, dan da Karima ya haifa ya ruga mu gidan gaskiya,

Shine sai Karima tamin barazana da d'ana, tace idan ban sauya yaron bah, na bata na Fatima saita kashe d'ana, jin akan yasa na dauki video a memory na, sannan na chanza danta da Kuma dan Fatima, yayinda ta kuma cemin, nace Fatima ta mutu, koh Kuma ta kashe dana, jin akan danayi bah karamin tsorata ni bah, amma ba yadda na iya aka na dauk'i wannan babbar kasadar, nace muku dan ku dakuma Fatima sun rasu.

A lokacin naga hankulan ku bah karamin tashi yayi bah, bayan na isa gida nai ta kuka da danasanin abunda na aikata a gareku. Tabbas ban muku adalci bah, Kuma banyi wa Fatima adalci bah, domin kuwa babu abunda Fatima tayi wa Karima amma saboda rashin imani irin na Karima ta sa na raba da da mahaifiya. Kuma har yau har gobe, ban sake hada ido da dana bah, bansani koh yana raye koh Kuma ta kashe shi bah.

Tana kaiwa nan ta fashe da wani matsanan cin kuka mai cin rai. Hada hannayen ta guri guda tayi tace, iya abunda nasani kenen dan Allah ina neman gafarku daku yafe min, dan Allah ku yafemin tabbas na aikata muku kuskure,

Jikin kowannen su ne yayi sanyi, Hawaye yafara gangaro wa a idanuwan Fatima, fatima tace ni na ruga dana yafe miki duniya da lahira.

Tashi su Nadira sukayi ,tareda rungume ta, Dad yace mun ruga damun yafe miki yanzu babu komai a zuciyoyin mu kinji kanwata.

Kuma insha Allahu Karima saita gurbi abunda ta shuka. Domin kuwa bata ci bullus bah. Amma shin meyasa take cewa mun ci mata dukiya, fansa zata dauka, doct khadija tace wannan Kuma ita zata bada amsa Domin ni kaina bansan me take nufi bah.

Dad yace toh amma shin Amina bata haihu bane har yau, Doct khadija tace ta haife danta Kuma saikuma karamar yarta amma bata kai shekara bah ta rasu.
Allah ya jikan ta, gabadaya suka amsa da Ameen.

Khalid yace yanzu ya zamuyi mu futa muje wajan Amriya Domin ta tashi Kabeer, Aunty amarya tace, inada wata hanya wanda bah kowa yasan da hanyar bah a gidan nan, domin ta hanyar nake bi nake zuwa kungiya,
Kamar hadin baki suka ce, kungiya Kuma!

????????????????

WANNAN NA KUNE FAN'S, ASHA RUWA LAFIYA.

COMMENT & SHARE PLS ?
ALKALAMIN ??
AISHA M.B
(BABY ISHA) ???

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JYYV16dbYaX1dykLX7EE91

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*??
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.??

ALJANAR RUWA CE ??♀???
PAGE 4??8????4??9??
WRITTEN & DIRECTED ?? BY
AISHA M.B??
(Baby isha)

--------------------------------------
Kwarai kuwa kungiya, nima ina daya daga cikin yan kungiyan asiri ,amma bah nashiga bane don cutar da al'umma, nashiga ne kawai Domin tseratar da rayukan ahalin nan, da Kuma na Kabir, so da dama tayi yinkurin kashe Kabir, amma Allah bai bata ikon yin akan bah.

Dan Allah karku yimin gurguwar fahimta, yanzu zaku iya bin nan hanyar Ba tareda kowa ya ganku bah, tashi su Khalid sukayi Tareda daukan mukullin mota,

Doct khadija tace me Kuma zakuyi da makullin mota, Khalid ya bata amsa da fadin, ai da mota zamuje, doct khadija tace toh kenen dai Baku shirya zuwa neman Amriyan bah gaskiya,

Kamar ya Khalid yafada, kamar dai yadda kaji, Baku shirya zuwa bah, ya za'a yi ace zakuje da mota, bayan kasan body guard dinnan na wakan sun zagaye gate baki daya, toh yanzu fadamin ta ina zaku futa da motan.

Sai a yanzu Khalid ya tuna da cewar tabbas akwai yan kungiyan Mom a wajan, sadiq yace toh yanzu a ina zamu je kenen?

Aunty amarya tace, abunda zakuyi shine ku tafi a napep, shine kwanciyar hankalin mu.

Tom shikenen bara mutafi, amma doct khadija zaki biyomu, koh saboda bamusan gidan bah, yes of course doct khadija ta Bashi amsa, tashi gabadayansu sukayi, inda sukayi musu fatan nasara daga bisani su ukun suka fuce daga cikin gidan.

Tafiyar su keda wuya, Mom ta banko cikin dak'in, a razane gabadayansu suka mike tareda ja da baya.

Kallon su Mom tayi tareda watsa musu banzan kallo tace, me kuke shirya wane, koh Kuma shirya yadda zaku tseratar da rayukan kune,

Nadira ta bata amsa da fadin, kwarai kuwa, idan mun tseratar da ran mu laifi ne? Koh kuwa akan ya shafe ki, buge mata baki Aunty amarya Tayi, tana mai fadin Nadira ki kiyaye ni, kada ki kuskure na karajin ki hanan,
Chapter 47 · 0% Book details