← Book details Aljanar Ruwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 55

Sashe 44

Aljanar Ruwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon Dad doct khadija tayi tace, tabbas abunda Amriya ta fada muku gaskiya ne, babu karya, first wife dinka , wato Fatima Tana raye bata mutu bah, Kuma tana kulle ne acikin wannan gidan na tsawon shekaru, batareda ansani bah, Amriya ce kawai ta iya gano, inda Matarka take.

Kallon ta Dad yayi, yace Dama wanda ya ruga ya rasu yana dawowa ne, wato zuwa kikayi domin ki cusa mun bakin ciki a zuciyata koh, leave now, banason jin komai dazai futo daga bakin ki.

Doct khadija tace, zant tafi, amma bazan bar gidanan Ba Tareda na tona asirin wannan shedaniyar bah.

COMMENT & SHARE PLS
ALAKALAMIN
AISHA M.B(BABY ISHA)

BISSMILLAHI RAHAMANI RAHEEM.
ALJANAR RUWA CE PAGE 46 ?47
WRITTEN & DIRECTED BY AISHA M.B (BABY ISHA)

-----------------------------------------
Murmushin k'eta Mom tasaki sa'anan tace,
Yanzu khadija wane laifi na aikata da kike son wargaza gidana, mene na aikata miki? Wane abu na tsare miki a rayuwar ki .

Meyasa kike son ganin baya na ta karfi da yaji, Grandma tace, Karima ki rabudani ita, so take ta lalata miki aure, toh ta Allah na Tata bah, maza zoki futa kafun na sakar miki karnukan gidanan, suyi hawan gaba da ke.

Wani kukan bakin ciki ne ya ziyarci Doctor Khadija, doct khadija tace, ku yarda dani wannan matar shedaniya.

Mom tace DAD Kabeer Dan Allah ka roke ta, ta bar mana gida, saboda wannan matar munafuka ce.

kece dai babbar munafuka!" sukaji kalisat tafada! ,ta cigaba da fadin kwarai kuwa, kece munafukar,

Tsinka mata mari doct khadija tayi tace, Duk abunda zai faru, karki kuskure kikara ce mata munafuka, saboda a haifa ta haifi sama dake. Kuma itadin a matsayin mahaifiyar ki take.

Allah ya kiyaye, Allah ya mun katangar karfe da wannan shedaniyar algunguma, mara imani. Wannan matar bata cancan ci akirata da Kalman uwa bah, domin kuwa yin akan kuskure ne.

Dad yace, ke Kalisat," kinsan abunda kike fada kuwa, kina da hankali, bakisan cewar, Tana a matsayin mahaifiyar ki bane, ya karashe maganar ranshi a matukar bace

kalisat tace, Dad am sorry to say", gaskiya, ita ba'a matsayin mahaiyata take bah, saboda mahaifiyata ta fita daraja da kima, kuma ita wannan azzaluma ce, mara zuciyar tausayi.

Magannanun tane suka sauka akan dodon kunuwan Khalid dakuma su Kabir dake sauk'owa daga upstairs, bata hankara bah taji sauk'an mari akan kuncinta, Dafe kuncinta kalisat tayi,

Idan ran Khalid ya Kai dubu toh ya baci, yace kalisat, kina cikin hayyacin ki kuwa, wacce ta raine mu, ta kula damu tamkar yaran ta, ta nuna mana soyayya kamar yadda itama Mami iya karkarin abunda zata iya kenen, shine yau kike kallon tsabagen Idanuwanta kina fada mata magana son ranki, kamar itadin sa'ar kice.

Kalisat tace wallahi matar nan, bata son mu Illah son cutar da mu da take kokarin yi, Amriya ce kawai take dakatar da ita, amma na tunan ta gama da yahya kabeer ya kashe kowa na wannan family.

Fashewa Mom tayi da kuka!, tace, Yau a gaban idona ake min karya cewar ina kokarin cutar da ahalin nan, meyasa zanyi muku aka, kalisat. Duda irin alkhairy da nayi muku amma da irin wannan abun zaku saka min dashi Dama ance Dan adam butulu ne, Hatake ta Fara tarin karya, tana zubda hawaye

Hakuri su Kabir da Dad suka Shiga bata, cikin fusata Kabir ya nufi inda kalisat ke tsaye, Ba tareda bata lokaci bah ya fuzgo ta, sa'anan ya shake mata wuya yace, ke mahaifiyata sa'ar ki ce, wallahi Kuma idan wani abu yasami mahaifiyata saikin dandana kudarki,

Murmushi kalisat tayi tace, mahaiyar ka, ko mahaifiya yar basaja, ta dolantar daku, tasaka ku cikin duhu, babu abunda idanuwan ku ke gani sai duhu, Amriya tayi kokarin fidda ku cikin aske, amma kuka ki ku fahimce tah.

Da wacce kake Kira mahaiyar na sonka baza tayi kokarin cutar da rayuwar ka bah, idan akane meyasa ta kashe Ummi.

Da sauri Kabir ya sake ta, ya dago da idanuwansa wanda suka kad'a sukayi ja.
yace, what nonsense are you talking about.

Kalisat tace am not saying nonsense, amma ni nasan tabbas Mom itace ta kashe Ummi, kuma sa'anan ta batar da Salma.

Gabadaya suka hada Baki wajan fadin what! Dad yace toh menene hujjar ki na fadin akan, gayamin Wacece hujja.

Nice hujja . Sukaji an fada, juyawar su keda wuya suka ga, Salma duk ta bi ta rame, tayi baki. Da sauri su nadira sukaje suka rungume ta, fashewa Salma tayi da matsanan cin kuka mai taba zuciya.

Nadira tace, Salma Wacece tayi miki aka, ina kikaje cikin wadanan kwana kin, ba Tareda kin dawo bah,

Salma tace babu inda naje, asali mah Mom ita ta bayar dani, ba Tareda kowa ya sani bah, kuma tabbas itace makashiya, wacce ta raba Ummi da rayuwar ta, saboda son kanta da son abun duniya.

Dafa kanshi Kabir yayi Wanda yake mugun saramai, Kallon Mom wacce tayi zuru zuru, Kabir yayi yace, Mom" shin abunda Salma ta fada gaskiya ne koh kuwa karya take miki? Shiru Mom tayi, ta rasa wane karya zata Kuma yi a wannan karan.

Grandma tace, ba shiru aka ce kiyi bah Karima, tambaya ce mai sauk'i, shin kece kika kashe Ummi, kuma kika batar da Salamatu,

Mom" tace wallahi karya take yi, saboda me zan kashe Ummi, me ta, tare mun, menene riba ta idan na kasheta, wallahi wannan abun kawai hadamin akayi domin kawai aga an rabani da gidan aurena.

Kabir" yace toh Salma kindai ji abunda Mom ta fada, tace ita batasan wani batun kisa bah,

Salma tace Aba Mom, ramin fah karya kurarre ne, say the truth and shame the devil, kiji tsoron Allah Mom, duda cewar ta sanadiyan ki nazo duniya amma akan bazai sa na rufa miki asiri bah,

Kiyi hakuri Mom, ke mahaifiya ta ce, amma dole yau sai gaskiya tayi halinta, tabbas babu karya ke kika kashe Ummi, a gaban idona, ta dunga baki hak.. Bata karasa bah kuka ya kufce mata, sosai take kuka idanuwanta suka koma ciki sukayi jajirr.

Cikin sheshekar kuka, Salma tace, babu abunda Salma bata ce bah, don kawai ki rabu da ita, babu koh d'igon tausayi kika samu, kwalba kika fasa mata Kai, akan baisa ta daina rokon ki bah, na dafa kafanki, nace kidau raina a madadin nata, amma kika ki, saboda son zuciyar ki, aka kika samu wuka kika kashe wacce bataji bah, bata gani bah. Ta karashe maganar tareda fashewa da wani kukan.

Jikin kowa na parlour ne ya dau zafi, wani iriyar kasala ya ziyarci kowannen su.
Kalisat tace, koh yanzun mah Baku yarda bah, toh inada wani prove din, zira hannu tayi cikin aljihun rigarta ta dauko waya,

Sannan tayi connecting da TV, tasa play, Mom ce bayyane akan screen din TV , inda Ummi ke bata hakuri, amma samm tsabar rashin imani, ta kashe ta.

Cikin kowa ne ya duri ruwa, a Hatake Mom ta hade rai. Cikin dak'a tsawa Dad yace Karima! Shin wannan kece da gaske.

Mom ta Bashi amsa da fadin kwarai kuwa nice, tabbas nice nan bah kowa bah, kuma ba iya ita kadai bah, sai na hallakar da kowa na wannan family kamar yadda na tsara,

Kabir kamm ji yake kamar mafarki yake, Dad yace Karima why? Dama Allah ya Barnum raina ne domin na ga wannan bakar ranar, Dama cin amanar ahalin nan kike da koh Y'ay'an ciki kin ki, baki Bari bah, why Karima? Why?

Mom ta Bashi amsa da fadin, FANSA, tabbas na shigo wannan ahalin ne badan komai sai dan na dauki fansar abunda aka aikata min na wajan shekara da shekaru,

Kuma tabbas saina dauki fansa akan wannan ahalin, Tana kaiwa nan ta kwashe da dariya, Tana mai fadin, wallahi Baku ga komai bah,

Kai kuma Kabir, tabbas bani ce mahaifiyar ka bah kamar yadda Amriya ta fada tun farko, ni kawai na rike Kane a matsayin d'ana domin idan lokacin salwantar da rayuwar ka yayi wa qungiya ta, saina kashe ka.

hawaye ne suka Fara bin kuncin Kabir yace, Mom please na roke ki kice min karya kike, wasa kawai kike yi. Hade rai Mom tayi tace, kwarai kuwa bah karya na ke fada bah, gaskiya na fada nidin, bah mahaifiyar ka bace,

Jiri ne ya fara diban shi, faduwa Kabir yayi sumamme. Hankali tashe su Dad sukayi kansa, da sauri, Tareda fara jijigashi, babu abunda kakeji a gidan sai kukan su nadira.

Ruwa Khalid ya dauko, sannan ya watsa masa, amma still bai koh Motsa bah, hankalinsu bah karamin Kara tashi yayi bah,

Cikin baccin rai Dad ya shake wuyan Mom yace, Dama da tantiriya, nake rayuwar aure ban sani bah, ban taba zaton aka daga gareki bah, tabbas dole ki girbi abunda kika shuka.

Ture Dad Mom tayi, ya fadi, da sauri su Sadiq suka nufi inda yake, d'aga shi sukayi.
Tareda zaunar dashi. Babu bata lokaci high blood pressure din Dad wato BP, ya tashi,

Hankalin kowa na gidan bah karamin tashi ya karayi bah, fashewa da dariya Mom tayi, tace ina farin cikin ganin wannan ahalin cikin kunci da damuwa, kamar yadda kuka sakani kunci, nima saina ga bayan ku,

Cincibar Dad da Kuma Kabir sukayi, suka nufi hanyar waje dashi, cikin mota suka nufa da su, Khalid ya tada motan, sannan yayi wa su body guard magana dasu bude kofan.

Ganin koh yunkurin bude kofan basuyi ba, yasa ran Sadiq baci, futowa Sadiq yayi daga cikin motan, yace bakuda hankali ne, Baku ga rayukansu na cikin had'ari bane, maza ku bude kofan kafun, ranku ya baci.

Daya daga cikin body guard din yace, ba'a bamu umarnin mu bude muku kofa ba. Aka zalika, wannan gidan mallakin uwar shedanu ne, babu wani ma'aluki da ya isa yayi kokarin futa daga gidan nan, domin wannan gidan makabartar ku ce.

Mutuwar tsaye Sadiq da Khalid sukayi! Ya rasa abun cewa, jiyayi gabadaya duniyar ta isheshi.

Dariya gabadayansu suka kwashe dashi, daya daga cikin su yace kuna mamaki ne, toh mudin bah body guard dinku bane, kamar yadda kuka tsammani, mudin yan qungiyan asiri ne, uwar shedanu kawai muke wa aiki, Baku bah, mun zo gidan nan ne badan komai bah, sai don mu taimaka mata, ta cika burinta, akan ku.
Chapter 44 · 0% Book details