← Book details Aljanar Ruwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 55

Sashe 15

Aljanar Ruwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

amriya Akwai fah gagaruman Matsala . Share hawayenta Amriya tayi tace wane matsala. Uwar shedanu zata sa yaranta su sace kabir gobe .

Amriya tace Toni ina ruwana sukasheshi mah bazan kara taimakonsa bah Wlh.

Kitaimaka Amriya kekadai zaki iya dakatardasu daga Darian hakan. Amriya tace taya, taya zan iya dakatarda su. Zan yiwa mom dinshi dabara sainace mata banyarda da maganan kibah nacewa hakuri yabaki daya futardake.

Sainace mata tasa gobe kutafi wajan company sa tare yanda zamu tabbatar da cewa yabaki hakuri. Daganan kuma nasan dole yayarda kar hagane ba hakuri yabaki bah.

Ni bazanje bah. Su kasheshi din sukawo min zobena natafi duniyata.

Meee wanee zobee Aunty Amarya ta tambaya cikeda rashin fahimta Damm gaban Amriya yafadi .

*************************

MUJEDAI ZUWA FAN'S DOMIN JIN YANDA ZATA KAYA 馃尯馃尯馃尯
DA ALJANAR RUWA CE 馃鈥嶁檧锔忦煂婐煂?
COMENT & SHARE PLEASE 馃憦馃徏馃憦馃徏
DAGA ALKALAMIN 馃枈锔忦煐婏笍
BABY ISHA 馃尮馃尮馃尮
2/28/24, 22:05 - AISHA M.B (Baby isha): 馃尮BISSMILAHI RAHANI RAHIM 馃尮
ALJANAR RUWA CE 馃鈥嶁檧锔忦煂婐煂?
PAGE 1锔忊儯3锔忊儯.

WRITTEN & DIRECTED馃枈锔忦煐婏笍 BY BABY ISHA 鉁ㄢ湪

-------------------------------------------

Tashi Aunty Amarya tayi taje kusada Amriya Wanda tayi zuru zuru tana Kallonta.

Aunty Amarya tace wane duniya amriya zaki koma, kuma wane zobe kabir zai baki.

Hmmm dama emm a gaskiya ni da kal....

Sallamar Kalisat sukaji waigowa sukayi gabadaya.

Aunty Amarya tace banace kubani guri zamuyi magana bah. Turo baki Kalisat tayi tace Aunty Amarya su yaya Khaleed ne fah suka ce nakira musu Amriya.

Mike wah Amriya tayi, da sauri tanufi hanyar futa.

Aunty Amarya tace Amriya ina zakije bayan bamu gama magana bah.

Kass Aun..ty Amar..ya ki ...ba.. Ri.. Wata.. Ran.. Na.. Fa.. Da.. Miki.

Tana kaiwa nan taja hannun Kalisat suka fuce daga part din tah.

Mamaki Aunty Amarya tashiga ganin da kafun Kalisat tashigo normal take magana. Amma tana shigowa kuma tadawo yin kikina. Lallai yarinyar nan miskilace.

Bangaren su Kalisat kam suna futa direct part din su kabir sukashiga.

Sallama sukayi. Daga ciki su khaleed suka Asma banda kabir Wanda gabadaya hankalinshi yanakan computer da Alama Abu Mai mahimmanci yake yi Aciki.

Nuni khaleed yayi Kalisat data futa. Turo baki Kalisat tayi tace. Ni Wlh bazan tafi hakuma cin zalin Yar uwata bah.

Kee dani kike. Tashi khaleed yayi yanufi inda Kalisat take. Kalisat naganin haka kafa Mai naci ban baka bah.

Matsoraciya kawai khaleed yafada.

Harde hannuwanta Amriya tayi a kirjinta. Tareda yin kallan tsayuwan kabir.

Tace ga.. Ga.. Ni.. Ance.... Kana... Ki... Ra.. Na..

Ajiyan zuciya khaleed da sadiq suka sauke.

Khaleed yace Dan Allah Amriya zauna.

Harara Amriya ta galla Mai tace da....ba...dan ka..ce Dan All.ah ....bah da...ba..zan zau.. Na.. Bah..

Zama tayi tace ga.. Ni..
Khaleed yace dama Amriya inason nabaki hakuri ne hakan halin tsana dana dunga nuna miki tun muna Lagos.

AMRIYA Tace shi.. Ke.. Nan.... Na... Ha...ku... Rah..

Sadiq yace yauwa kanwar mu.

Sadiq yakumacewa shima oga kabir din yace zai baki hakuri.

Dago kansa kabir yayi yawatsawa sadiq wani banza kallo.

Yace sadiq are you normal. Hope dai bawani abu kasha bah. Imagine mee giving this dog hakuri.

Kee kabir ya daka WA Amriya tsawa . Karki yi tunanin cewa zan iya baki hakuri impossible.

Abunda bazai taba yuhuwa kenen.

Cikin kasa da murya sadiq yaceda khaleed inaga fah Oganan kishi yake. Dan yasan ko A mafarki bazai iya samun kyakyawa irin wannan bah.

cikin huci kabir yace sadiq don't dare mee this afternoon. Wlh. inka karacewa kishi nake ranka zai yi mumunan baci.

in rasa wanda zanji kishi sai wannan abar Mai kama da Aljana. god for bid. ku kyau yadama banibah. Kada kusake hada koda inuwata da wannan karyar.

Khaleed yace kenen dama sanda kuka futa ba hakuri kabata bah.

Daukan computer shi kabir yayi yace bani zaka yiwa wannan maganan bah. Ita zaka tambaya tunda itah takware a harkar karya harta iya fadin abunda bai farubah tace yafaru.

Yana kaiwa nan yayi hanyar daki daga sama sukaji muryan Amriya tace da...ka..ta.. Kalb.

tsayawa kabir yayi domin yaji wane raini hankalin tazomai dashi. Zuwa Amriya tayi hargaban kabir.

Kallon zoben hannunshi Amriya tayi takuma maida kallonta kansa tace. Ban...yi tsam....ma....nin zaka iya gaya.....min ma.... GA.... Nah.. Har.. Haka.. Bah.

nayi... tsa... mmani... koda... kowa.. zai.. gujeni... bazaka.. kujeni.. bah... sabida... taimakon ... Rayuwarka dana... dungayi... .

keee what are you saying.. guys inaga yarinyar nan tah kwalbe ne Amma.

Murmushi Amriya tayi. Tareda rikee hannun kabir da zobenta ke sanye ajiki ... Yarrr, yarrr. Jikinshi yayi.

saurin fuzge hannunshi yayi daga nata. Tareda nunata da yatsa yace kada koda kuskuren ne yasa ka ki kara tabamin hannu. Domin jikina banaki banebah na adanawa masoyiyata ne harsai naganta. Kuma bazan gaji da nemanta bah.

Dan haka bace min daga gani.

Wani hawaye Mai zafine yafara zubowa Amriya. Murmushi Amriya tayi tareda fadin.. Ina.. Fa... Tan.. Kah... Gane... Gas.. Kiya..

kuma... Zanso .. Inga ... Ranar... Daza kah... Gah... Masoyiyar.... Taka... Wacce.. Ta mallaka... Maka... Wannan... Zoben.... Dake... sanye... A hannunkah.... Domin..... Farin.... Cikin... Kah.... Kuma... Itah... Ta zauna... Ciki... Bakin... Ciki..

Kee malama.. Na rantse inbaki futabah.. Daga dakinan bah. Zakisha mamaki. Nah.

Cikeda kunan rai Amriya tace.. Wai... Meyasa... Baka.. Gane... Wah... Ne...

tassss kakeji kabir yazubawa Amriya lafiyanyan mari.. Dago idanuwanshi yayi wanda suka kada sukayi jaa. Yace . Nine bana fahimta how dare you.

Kara daukan hannushi yayi zai karamata wani marin..

sadiq naganin haka ya funcikoh Amriya.

Yace is OK kabir. Kayi hakuri kashiga daki

kaii malam gafara. kabir yafada . gabdayan su khaleed sun tsorata da halin kabir tunda suke basu taba ganin ran abokin nasu yakai kololuwar baci bah
kamar yau.

Cikin lion Voice dinshi kabir yace leave now kafun ranki ya baci.

cikeda rawar jiki Amriya tayi saurin barin dakin.

Direct dakin su nadirah tanufah. Da gudu ta shige dakin .

A firgice su fateema dake firah suka dago Kai. Kafun suce Kala. Amriya tashige toilet tareda kulle wa.

numfashinta na sama sama. Ta cika bafff da ruwa.. Tareda shigee cikin ruwan tana Jan numfashi hatake kyakyawan bindinta ya baiyyanah Hawaye ne sukafara bin fuskanta

A furgice su nadirah sukayi hanyar toilet. Din sukashiga Bubuga kofan . Amma sukaji shiru.

Kalisat ce tafara kuka. tareda fadin dama nasani shiyasa nace bazan tafi bah gashi inaga sunkarayimata wani abun.

Cikin rashin fahimtar magana tah nadirah tace kiyi mana dalla dalla mana ni bangane abunda kike fadi bah.

Tundaga abunda yafaru harkarshe Tafada musu.

saida macemata kada takara shiga harkar su amma gashinan abunda yakarar faruwa.
bubuga kofan sukacigaba da yi. bude kofan Amriya tayi. fadawa jikinta sukayi tareda fashewa da kuka. banbare jikinta Amriya tayi tareda kwanciya kan gado hawaye nabin fuskanta.

4 :30 am

kada kadamu zan ceci rauyuwarka bazan Bari kamutu bah.
a furgice yafarka daga mafarkin dayake. Dafe kanshi yayi Tereda fadin meyasa kike wahalar dazuciyata ne yaushe zaki dawo cikin rayuwata yaushe zaki baiyyana. Damm gabanshi yafadi zuciyanshi yafaramai zafi zoben hannunshi yakalla yaga yachanza Kala.
dafe zuciyanshi yayi tareda fadin meyasa kuma zoben ya chanza Kala.

鉁ㄢ湪鉁ㄢ湪鉁ㄢ湪鉁ㄢ湪鉁ㄢ湪鉁?
2/28/24, 22:05 - AISHA M.B (Baby isha): 馃尮BISSMILLAHI RAHANI RAHIM 馃尮
ALJANAR RUWA CE 馃鈥嶁檧锔忦煂婐煂?
PAGE 1锔忊儯4锔忊儯

WRITTEN & DIRECTED BY BABY ISHA (AISHA M. B馃尯)

-------------------------------------------

Meyasa mu wannan zoben tukunamah wai me wanccan yarinyar take magana hakai ne dafashi yaji hanyi. Dago Kai kabir yayi yazubawa Sadiq.

Lfy kabir naga kana magana Kai kadai. Ajiyan zuciya kabir yasauke tareda fadin bakomai kawai wani Abu na tuna.

OK toh tashi kadauroh Alwalah Kai kadai muke jira khaleed yana waje .

Tashi kabir yayi yanufi toilet yayi Alwalah sannan suka wucce masjid.

Bayan sun dawo daga masjid suka wuce dakin su dad domin gaishe dasu dama Alhadan gidan kenen da safiya kowane da na gidan saiyaje yagaise da iyaye

Aunty Amarya na hango tana tafiya sadaff, sadaff harta Isah dakinsu nadirah. Murda hannun kofan tayi sai ta Tatar a bude.

Shiga tayi tanufi inda Amriya ke kwance. Amriya, Amriya tashi. Bude idonta Amriya tayi tace Aunty Amarya kece Awanan lokacin. Shiii kiyi shiru Amriya kisameni A part dina yanzu.

Tana kaiwanan tabarar dakin tashi Amriya tayi tabi bayan Aunty Amarya.

Shiga part din Aunty Amarya Amriya tayi ta Tatar da ita a zaune kan kujera.

Gani Amriya tafada. Aunty Amarya tace kin manta maganan da mukayi dake. Amriya tace wane magana kuma mukayi.

Kai Amriya yanzu so kike kifadamin cewa kin manta maganan mu hakan kabir .

Niba zanje bah cewar Amriya Aunty Amarya tace dan Allah Amriya kije ke kadai ce kawai zaki iya tseratar da rayuwansa daga WA encan shedanun mutane.

Amriya tace toh wane tabbaci kikedashi nacewa zan iya taimakonshi tun jiya kikecewa ni kadai zan iya.

Taya nidin harnaki matsayin wah dazan ceci rayuwansa.
Murmushi Aunty Amarya tayi tana Mai fadin nafa ganki ranan nan.

Damm ganan Amriya yafadi tace a ina kika ganni yaushe kuma.

Aunty Amarya tace naganki sanda kika zo kika tada guguwa. A lokacin fuskanki sanye da gyale ina takallonki gabadaya a ranar kinyi matukar burgeni. Harnakecewa ina mazanga fuskanki.

Kina cillah guguwan kuma gyalen fuskanki ya cire. Saikuma naga fuskanki ya baiyyana.

A lokacin danaji su nadirah nafadin kin bata banyi tsammani kebace saida naganki tukunan. Sannan zuciyata yasamu salama sbd nasan idan kina tareda kabir bazaki bari a cutardashi bah.

Duda bansan kedin mutum bace koh Aa amma Wlh zuciyata ta aminta dake fiye da yayan dana Haifa da cikina.

Ajiyan zuciya Amriya tasauke tareda fadin a gaskiya nidin mutum ce kuma nibansan suwaye ahalina bah.

Tun ina yarinya natashine da wannan baiwar ajikina.

Amma dai zaki taimakeshi koh aunty Amarya Ta tambaya .

Kwarai zan taimakeshi indai ina numfashi a wannan duniyan bazan Bari shedanun mutane nan su taba koda farcensa bah. Koda kuwa zan rasa Raina.

Yauwa koke fah haka, haka San jaruma da cika magana. Yanzu kije kiyi wanka kiyi sallah nizan je na fadawa su dad dinsu kabir. Maganan mu najiya.

Ni nayi sallah dazu tareda su nadirah. OK toh kishiga kiyi wanka.

Toilet Amriya tanufah idanuwan Aunty Amarya ne yasauka hakan bayan Amriya wanda yayi kaca kaca da jini. A firgice aunty Amarya tayi kan Amriya. Tareda fadin Amriya meyasa meki haka naga jini a bayanki.
Chapter 15 · 0% Book details