← Book details Aljanar Ruwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 55

Sashe 41

Aljanar Ruwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aunty amarya lafiya na ganki acikin wannan lokacin, murmushi Aunty Amarya tayi tace, kwarai kuwa lafiya,

Shawara nazo na baka, badan ko bana sonka bah, sai don soyayya da nake maka da Kuma, yan gidan nan.

Okay Tom ina jinki Aunty. Aunty Amarya tace , Kabir inason ka saura reni da kyau, inason fada maka abu dake cin rai na na wajan shekara da shekaru,

Kabir! Dago wa yayi ya kalle ta sannan yace na'am aunty, Aunty Amarya tace, ina son na fada maka cewar, Duk abunda Amriya ta fada dazu babu karya acikin ta, tabbas abunda ta fada gaskiya ne. Mom itace ta kashe Ummi Kuma.... Bata karasa bah taji yace,

Aba Aunty, aba Aunty, koda kowa zai biyi bayan aci dun duniyar mom ai bazaki ciba .

Na tabbatar miki da cewar karya Amriya tayi wa mom, so take ta hada mu nida mom dina, Kuma bata San Allah yafi karfin tah bah.

Murmushi Aunty Amarya tayi, sannan tace, Allah sarki Amriya baiwar Allah, kina taimako, kina sa rayuwar ki a hatsari amma basu San kina yi bah,

Kace ka tabbatar cewa karya Amriya take koh! Kabir yace yes of course, am 100% sure that, karya take yiwa mom.

Aunty Amarya tace tunda ka tabbatar, toh menene hujjar kah.

Kabir yace ni Banida hujja amma nasan mom can never do such thing, idan mah tayi ribar mee zata ci, Amriya kawai yar leken asiri ce, maybe wani ne ya turo ta gidan nan.

Wai kai Kabir Meyasa baza ka yi nadamar abunda kakeyi bah?
Saboda mahaifiya ta, ta tsaya min, Kuma Duk mahaifiyar da ta iya tsaya wa domin Kare rayuwan danta, babu wata ma'alukiya da zata iya cin galaba akan tah.

Kenen kana nufin Amriya bah mutuniyar kirki bace,

Dai dai lokacinda Amriya ta karaso cikin gidan. Jin muryar Kabir tayi, taji yace kwarai kuwa, Amriya bah mutuniyar kirki bace,

Chakk Amriya ta tsaya, Tareda jigina ajikin kofan Tana jin abunda yake fadin.

Kabir yace tunda yarinyar nan ta dora kafa fuwanta a gidan nan, toh tun lokacin masifa da baka'i suke ta faruwa, tabbas yarinyar nan bah mutuniyar arziki bace.

Da nafara dana sani abunda na aikata mata, amma shigowar ki yanzu, yasa na tuna da cewar tabbas mashekiya ce , muguwa Kuma, Mara imani. Baby macen da nafi tsana a duniyar nan sama Da itah. Na tsane ta, na tsane ta, tsana mafi muni, kinga Kare war Ta mah, bana son na kara hada ido hudu da ita, banason na Kara Ganin ta har abadan abada.

Hawaye ne suka Fara gangaro wa daga idanuwan Amriya, hannunta ne suka Fara Kar kar wa, kuka ne ke shirin subuce mata Saurin rufe bakin ta tayi, Tareda rintse idanuwanta jin zuciyar take kamar zata futo..

Tashi tayi daga jikin dakin, inda kuka ya ci karfinta.

Juyawa gabadayan su sukayi, inda Kabir yace waye a nan.

Saurin rufe bakin ta tayi, Tareda Saurin barin gidan.

bude kofan Kabir yayi yaga babu kowa, futowa Aunty Amarya tayi tace shikenen, ni zan wuce, ina fatan ka gane gaskiya. Tana kaiwa nan tayi fucewar tah.

Ya mutse fuska kabir yayi tareda rufe kofan ya koma kan gado ya kwanta.

Tafiya Amriya ta farayi batare da tana cikin hayyacin ta bah. Dafa kanta tayi wanda ke mugun Sara mata. Jiri ne yafara di banta, a daddafe ta karasa wajan junction. Tareda samun guri ta zauna.

Kallon kanta tayi, ta fashe da matsancin kuka mai cin rai.

Meyasa, Meyasa, wannan wace iri yar jarabbta ce, wannan wace iriyar bakar kaddara ce, Meyasa na ka sance a raye har yanzu. Dama na kasan ce a raye ne don kawai naga wannan ranar bakin ciki, ranar da bata da gobe.

Meyasa tun tuni ban mutu bah, na tsane ka Kabir, na tsane ka, bana son sake hada ido dakai, bana kaunar kah,

Kuma wannan ajiyar da ka bani, zan Adana tah har karshen rayuwa ta. Zan kula da abun ciki na har numfashi na, na karshe.

Tabbas zan Nisan ceka, kamar yadda ka bukata , bazaka sake haduwa da koh inuwa ta bah. Karuga da ka Gina min tsanan ka acikin zuciya ta. Rayuwa tah da komai nawa, nasa a hadari don kawai naga, baka cutu bah, amma akan baisa ka gani bah.

Ta karashe maganar tana mai fashewa da kuka, mai ratsa zuciya.

馃ス馃ス馃ス馃ス馃ス馃ス馃ス馃ス
COMMENT & SHARE PLS 馃檹馃檹馃檹

ALKALAMIN 馃枈锔忦煐婏笍馃枈锔?
BABY ISHA 馃挒馃挒馃挒
(AISHA M.B)

2/28/24, 22:12 - AISHA M.B (Baby isha): https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

JAJIRTATTAU WRITER'S ASSOCIATION 馃枈锔?
(J.A.W)
Rubutu baiwa ce daga Allah,jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan kasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauk'i鉁忥

ALJANAR RUWA CE PAGE 44?45
WRITTEN & DIRECTED BY BABY ISHA (AISHA M.B).

-----------------------------------------
Kallon wajan gidan Amriya tayi tace, ya Allah, kada ka kawo abunda zaisa na Kara sanya kafafuwa na acikin wannan gidan, insha Allah baza ka Kara ganina bah na har abada, har abadan abada.

Mike wa tayi, ta Fara tafiya, Chan cikin dajin wajan ta nufa ta tarar da doct khadija a Zaune, Kallon ta doct "khadija tayi cikin rudewa tace,

yata Amriya, me yafaru?, Meyasa kike kuka? shin Kabir ya Kara bata miki rai nee? tambayar da doct khadija ta Shiga yi wa Amriya kenen.

kuka Amriya ta Kara fashe wa dashin cikin, kuna da bakin ciki, tace doct khadija na aikata wani kuskure mara goguwa a rayuwa ta, wai shin yaushe kuka na da bakin ciki zai zo karshe,

Nayi dana sani futowa daga ruwa nazo duniyar mutane, Meyasa banyi za mana a ruwa bah, Kalb ne yayi sanadin futowa ta daga ruwa , abunda na futo karba daban, abunda na tarar daban, Meyasa

na tsane shi, banason sa, tunda aka yake so zaiga asalin tsana Daga Aljanar ruwa, wallahi, yanzu ji nake kamar na kashe shi nima na kashe kaina.

Saurin rufe mata baki doct khadija tayi tace, Aa Amriya kada ki Bari zuciyar ki ta kaiki nesa, kada ki Bari shedan ya rin jaye ki, komai yayi farko zaiyi karshe, ma hakuri mawada ci, idan kikayi hakuri zaki dace.

Amriya tace, hakuri na me, hakuri na nawa, wane hakuri ne nan banyi bah a wannan rayuwa, ya wulakan ta ni, yaci min mutunci, zagi ba dare bah rana, yace min kaskantaciya, Duka zagi Ba bu abunda baiyi bah.

toh fadamin shin Nayi hakuri koh banyi bah, na tabbata da wata ce bani bah, wallahi saita iya kaishi ga hallaka..

kinga Dan aka yaje na bar masa zoben, Dama rayuwa tah bata da amfani, Kuma cikin kwanan na zan mutu, kamar yadda gumurzu ya fadamin. inaso zanga abunda zan haifa a duniya kafun Allah ya dauki raina.

insha Allah babu abunda zai same ki cewar doct khadija, ta cigaba da fadin, kada kidamu, duda cewar Ahalin Muhammad sun tsane nii, saka makon sharrin da Karima ta min, amma akan bazai hana ni na je na bayyana musu gaskiya bah, dole Su san abunda Karima ta shuka.

Karima tayi min abubuwa da Dama Mara misaltuwa. ta raba ni da yan uwana, ta rabani da yar uwata mafi soyuwa a gareni, ta kashe min dana, Wanda iya shi Allah ubangiji ya bani, ta sanya na raba da da mahaifiyar sa, ta kuntata wa rayuwa ta.

tasa na aikata babban zunubi amma akan baisa ta rabu dani bah, dole ne na dauki mataki akan tah, shiru bazai yi magani bah, saidai abu ya Kara baci.

Amriya tace, Dan Allah inason kikaini wajan mahaifiyata, inason zan ganta.

Kallon ta doct khadija tayi tace, zan kaiki kamar yadda kika bukata amma yanzu lokacin kaiki baiyi bah, dole sai mun kashe wutar dake ci a gidan Muhammad kafun na kaiki,

Amriya tace bazan karya rantsuwa ta bah, nice miki bazan sake dora kafana akan wannan gidan bah.

murmushi doct khadija tayi tace, bazan ga laifin ki bah, saboda kina da hujja tayin akan, Kuma akan bazai sa naji bah dadi bah,

Amriya tace zan cigaba da zama na a nan dajin har sai lokacin da zan sauka lafiya. Aa Amriya" bai kama ta ki zauna a nan bah, kama ta Ai ace kin samu gida, Wanda za'a dunga kula dake.

ki tawo Tareda ni, zan kaiki gidan ka wata doct Amina, na tabbata zata kula dake harda abun cikin ki.

Aa doct khadija, ki barni na cigaba da zama a nan shine zai fiye min sauk'i, saboda idan ina cikin jama'a, zan dunga jin zuciya tah na kuna, inaso na zauna ni kadai.

Aa Amriya kiyi hakuri, ki tawo dani muje, Banaso na kaiki gida na, saboda har yanzu Karima bata San ina Raye bah, Kuma idan ta gano baza ta bar ni har ke bah, Dan aka ki tawo na kaiki gidan kawa ta Dan Allah.

shikenen, zanje amma da sharadi, Doct khadija tace inaji ko menene ki fadamin .

Amriya tace, zaki je gidan su Kalb, kamar mahaukaciya, Kuma sannan kice musu, mahaiyar Kalb Tana Raye, what doct khadija tace, Tana mai fadin kinsan ko me zanyi bazasu taba yarda bah, Amriya tace kawai kiyi abunda na fada miki .

shikenen, Doct khadija ta fada, Tareda fadin, zanje Kuma zan fada musu. insha Allah gobe goben nan.

ki taso muje gidan doct Amina,cewar doct khadija. Amriya tace, Aa ki Bari gobe. Tom shikenen, Allah ya kaimu goben.....

Washe gari da sassafe Amriya da doct khadija suka wuce gidan doct Amina.

Kwan kwasa gate din gidan sukayi, inda mai gadi ya bude musu Ganin doct khadija ce, yasa mai gadi ya bar su suka Shiga, yayi musu rakiya har wajan corridor din, parlour. Shiga ciki doct khadija tayi bakin ta rike da sallama.

Kabir inason muyi wata magana mai mahimman ci da Kai, dago kai Kabir yayi ya dora idanuwansa akan mom yace mom inajin ki.

mom ta cigaba da fadin, kasan wannan yarinyar kirkin wato zainab yar gidan Alhj usman, Kabir yace Eh nasan zainab, naga yarinyar Tana da tarbiya, Kuma tana da hankali, mezai hana ka aure ta domin d'aga darajar Ahalin mu.

Dan jimmm, Kabir yayi, yace naji dadin wannan Shawarar mom, amma am sorry to say, i can't marry zainab, she's not my type. bata Kai tsarar da zanso tah bah.
Chapter 41 · 0% Book details