← Book details Aljanar Ruwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 55

Sashe 17

Aljanar Ruwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zaro ido gabadaya sukayi tareda kallon saman ten stories din. Amriyaaaa. Khaleed yafada kada ki tsaya kada ki saki gamunan zuwa. Rintse idanuwan tah Amriya tayi hawaye nabin fuskanta. Jin hannunta tayi yana mata zafi da radadi. Gashi inta Saki zata iya mutuwa.

Kabir kam ibanda tsaki ba abunda yakeyi. wai mema yakaita ten stories kabir yafada. su sadiq da sauran ma'aikatan company sukayi hanyar hawa na goma lifter suka danna zasu shiga amma yakiyi hakan yasa suakabi upstairs.

Amriya kam jin hannunta take kamar zai cire tama kasa yin ihuun. sbd Azaban datakeji.

Cikin sheshekan kuka. Tace Allah sarki. Kiyi hakuri Aunty Amarya bazan iya cika miki Alkawarin Dana miki bah nasan ina cikawa mutuwa zanyi. Ban cika muradainah bah.

kallon kabir tayi Wanda kokadan damuwa bata baiyyana a Fuskansa bah. Kayi hakuri Kalb bazan iya taimakonka bah ni nasan yanzu tawa taruga data Kare. Murmushi tayi tareda fadin zanyi kewarkah. Daidai su khaleed suka hauroh kan ten stories. Din.

ina maka fatan Alkhairi Kalb. tana kaiwanan ta rufe idonta tareda sakin karfeen.

Amriyaaaaaaaaaaa.

鉁ㄢ湪鉁ㄢ湪鉁ㄢ湪

SHIN AMRIYA NA FADOWA NE KOH AA, HANYAKUWA ZA'A SAMU WANDA ZAI CECI AMRIYA DATA FADO, SHIN MUTUWA TAKEYI DAGA FADOWAR KOH KUMA HAKASIN HAKAN

MUJE ZUWA DOMIN JIN YANDA ZATA KAYA. ACIKIN LITAFIN MU MAI SUNA ALJANAR RUWA CE 馃鈥嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔忦煂婐煂?

COMENT & SHARE PALEASE 馃憦馃徏馃憦馃徏

ALKALAMIN 馃枈锔忦煐婏笍
BABY ISHA 馃尯馃尯
2/28/24, 22:05 - AISHA M.B (Baby isha): 馃尮BISSMILAHI RAHMANI RAHEEM 馃尮
ALJANAR RUWA CE 馃鈥嶁檧锔忦煂婐煂? PAGE 1锔忊儯5锔忊儯

WRITTEN & DIRECTED馃枈锔忦煐婏笍 BY BABY ISHA (AISHA*M* B鉁?
)

''''''''''''''''''''''''''鈥?''''''''''''''''''''''''''''鈥?'''''''''''''''''''''''''''鈥?

Kabir naganin haka yatafi daidai inda yaga Amriya zata fada da gudu. Da mugun karfi ya chafko tah tafada jikinshi
sumammiya. Wani irin yarr yarr yaji sanda tafada ajikinshi

Ajiyan zuciya su khaleed dake sama suka sauke. Da sauri suka saukoh daga upstairs din

Tafi ma'aikatan suka farayi. Tsaki kabir yaja Tereda cewa duk Wanda yakaramin tafi toh daga yau zai bar aiki a company nah Tsit kake ji.

Sadiq yace kabir amma fah wannan ranar kayi Abun kirki. Cikeda takaici kabir yace Kai dallah baka ganta a hannuna bah a rikee kuzo ku amsheta kokuma na jefarda ita Wlh.

Zaro ido khaleed yayi yana Mai fadin kabir, sadiq Amriya bata numfashi fah.

Rass's gaban Kabir yabada tareda fadin kamar ya bata numfashi. Ajiyeta kabir yayi a bayan mota. Tareda Kare mata kallo. A firgice sadiq yace bamu ruwa khaleed

Gaban mota khaleed yanufah tareda daukoh ruwan faro. Mikawa kabir ruwan khaleed yayi.

Kabir yace mezanyi kuma da ruwa. Tsaki khaleed yaja tareda fadin wayake takai hana ta rai kaikuma kana shakiyanci.

Karbe ruwan khaleed yayi yafara watsa mata kadan kadan a fuska. Koh giftawa amriya batayi bah.

Innalilahi Wa inahilaihi rajihun. Sadiq kirama daddy kah muna bukatar Ambulance 馃殤 yanzu.

Mukaita Asibitin da motan mu cewar sadiq. Baza akaita a motana bah saidai ku tari napep.

Wlh kabir bakada baka da hankali cewar khaleed. Cikeda zafin rai kabir yace ni kakecewa banida hankali sbd mace kuma agaban ma'aikatana

Yess kabir kana Abu uwa mara lisafi. Kokuma nace kamar wanda baiyi karatun adini musluncibah.

How dare you khaleed.
Ganin abun nasu bana zubawa ido bane yasa sadiq fadin plaease kabir kudaina wannan bah girmanku bane. Kuna kuna musayar yawu da juna.

Barana kira dad dina idan yana kan duty.

Ringing biyu haka dauka sallama sadiq yayi daga dayan bangaren mommy ta amsa.

Mommy ina wuni, lfy kalau sadiq ya aiki, sadiq yace Alhamdulillah.

Toh haka hakeso. Amma bawani matsala daiko naga ka kira daddy kah.

Eh Wlh mommy nah bawani matsala yau baije wajan aiki bane.

Mommy tace eh Wlh baije bah sbd yau mami tadawo abuja. . Sadiq yace mami tadawo OK toh kibawa daddy wayan inason zanyi magana dashi.

Mommy tace ok sadiq barana bashi Wayan.
Direct dakin daddyn su sadiq ta nufah. Da Sallama tashiga daki daga ciki daddy ya Amsa. Mika wah daddy wayan mommy tayi.

Karba daddy yayi tareda yin sallama. Amazes sadiq yayi tareda fadin daddy Dan Allah inason kayiwa nursings dinka magana suzo company mu da Ambulance Dan Allah.

Ambulance kuma badai wani abune ya faruba. Eh wlh daddy bakomai kawaidai Amriya ce ta sabulo tafado daga kan ten stories.

Innalilahi wahinahilaihi rajihun daddy fada tareda mikewa tsaye tareda fadin ganinan zuwa company yanzu.

Noo daddy you don't need to stress yourself kawai Ambulance muke bursts sbd missing abata taimakon gaggawa. Amma Dan Allah daddy kada kafadawa su mom sbd kan hankalinsu yatashi.

Shikenan sadiq barana kira nusings din sai sutawo da Ambulance .

OK daddy muna godiya Agaishe mundasu Aisha. OK toh zasuji.

Katse wayan sadiq yayi tareda sauke nannauyan ajiyan zuciya.

Kallon ma'aikatan kabir yayi tareda fadin kowa yatafi gida nabaku holiday na 1 week kuma kowane mutum acikinku zaiji alert na dubu Dari wanda zai isheku na ci da sha har na tsawon 1 week.

Godiya sosai ma'akatan sukashiga Mai daganan kowa yayi hanyarsa.

Gefen naga zainab takoma tareda daukan wayanta tafara kira. Nikainah banji abunda take cewa bah sbd yanda take magana ciki ciki.

ba'a fi 15 minutes bah Ambulance yakaraso cikin company .da sauri kabir yadauki Amriya tareda saka tah cikin Ambulance din

suma su khaleed ba'a barsu a baya bah. Zainab naganin za'a rufe kofan Ambulance din tanufesu da gudu.

Kutaya, kutsaya, Dan Allah cewar zainab. Cikin zafin rai kabir yace kee malama Murray's mu miki uban mee.

ZAINAB tace nima zan iya binku Dan Allah .

kibimu kimana mee cewar kabir. Koh ke zaki Samar mata da lfy.

Dan Allah kabir bamuda ishashen lck kabari kawai ta tawo tareda mu cewar sadiq.

Kinga shigo mutafi shiga ciki zainab tayi tana Mai murmushin gefen baki.

Bayan wasu lck daya gabata.

Hawaye nabin fuskanta tashige parlour . Alhj usman yace lfy yata waya tabamin kee yanzu nasa Asamin shi bakonci lahira.

Aa Baba basaika sa han kashe shibah. Sir kabir nee.
What wane kabir din,, zainab tace sir kabir Mai company K.B FISHES PRODUCTION.

what meya hadaki dashi Gsk Baba I love him kuma inajin idan badashi bazan iya rayuwa bah. Wlh Baba jinake duk wanda ya hanani strands saina aikashi lahira koda kuwa kaine.

Aa memazaisa na hanaki auransa. Auranki dake dashi bah fashi amma ta anya daya zaki iyasamun soyayyar sa.

Wata anya kafadamin komenene Zanbi koda kuwa zan rasa Raina.

dole kinemi aiki a company sa what ZAINAB tafada tareda fadin Baba amma aikasan ba fishery na karanta bah taya kuma zan iya aikin fishery. Kee Dan dallah bakya kwashewa Wlh ai daganan ai zaki samu soyayyar sa kuma inason zaki daukoh min kadararsa dake cikin company a boye..

Kayy amma Baba sosai ka hadu. Alhj waigowa gabadaya sukayi suka dora hakanta. Turo baki zainab tayi tareda fadin ya muna mgn kuma kizo kiyimana gatso.

Kee zainab ni mahaifiyarki kike fadawa haka. Aba Alhj maimakon kadorata hakan hanya Mai kyau shine kuma kake dorata a gurba tacciyar hanya.

kee malama ina ruwanki cewar Alhj. Da ruwana mana Alhj tunda nice nadau cikinta na wata tara. Nakuma haifo ta da cikina rai a hannun Allah na Raine ta hartakai wannan lckn. Toh taya zakace ina matsayin mahaifiya kace bazan San ciwon kaina bah.

Alhj kasani karshe Azzalumai bata kyau. Wannan hanyar dakuka dauka ba hanya bace Mai kyau. Wlh ka chanza hali.
Wannan kenen

ke dallah rufewa mutane kofa khaleed yafada . A firgice zainab ta farfado daga tunanin data shiga.

kulle kofan tayi tareda ya mutse fuska.

Tafiya suka farayi. Lck daya kuma haka karya kwana.

Kabir yace Kai ya haka Bayan mikewa zakayi kuma zaka Karya kwana.

Shiru sukaji ba amsa. Cikeda baccin rai kabir yace ehh who are you dazanyi maka mgn kayimin banza.

Juyowa hakayi hatake na razana ganin bah nursings bane monster ne da yaransa. Wani kwalba Mai kama dana Turare monster ya daukoh tareda fesa musu.

Ba'a fi 30 second's bah bacci Mai nauyi yayi awon gaba dasu.

1hours later
Su kabir na hango a daddaure ajikin bishiya.

Ruwa acikin bokiti naga monster yadauka tareda watsa musu da mugun karfi.

A firgice dukkansu suka farfado banda Amriya da haryanzu bata farfado bah.

cikeda zafin rai kabir yace ehh who are you guys. wato kidnapping mu kukayi koh.

kwarai kidnapping din ku mukayi kuma kaikadai kumayi niyan kidnap saikuma tsautsayi yasa suma sukashigo tarkon mu. waya monster yadauka tareda dialling numbern dad. Daga WA dad yayi.

hello monster ne ke magana muna bukatan dukiyan kabir dake jigawa. Nan da 24 hour dakuma 1 billion inba Hf haka bah zaku zo kutarar da mushen su. Bai jira cewar dad bah ya katse wayan.

a firgice dad ya Mike tsaya. Cikin tashin hankali Mom tace meyafaru dad kabir.

Sun sace su kabir. Karima yan garkuwa da mutanene suka kirani. Salati gabadaya su sukayi. Harsu nadirah dake saukowa daga kan bene.

Nashiga uku Aunty Amarya tafada cikin zuciyanta.

Grandma tace waiyoo nashiga uku na lalace shiyasa nace su dunga tafiya da hody guds amma sunki.

Muhammadu ka kara kiransu Dan Allah.
A firgice mom tace dad kabir yanzu meye abun yi. Wlh in habu yasami dana zan iya mutuwa. Dashes gabadayansu sukayi dakuka. Banda Dad daya dake yace suyi shiru.

cikeda kunan rai kabir yace kayi maza ka kunce mu inba haka bah ranka ya bace.

Dariya monster yayi tareda fadin nasaba jin irin wannan kananun maganganun a irin bakin mutane irinku.

Dan haka kayimana shiru kokuma ka bakunci lahira.

murmushi kabir yayi yace fada kawai kayi baka aikataba idan ba tsoro bah kah aikata mana. Ka aikani lahiran indai da gsk gyatumarka namiji ta haifo bah Dan daudu bah. Toh kanunamin mazan takan kah mana yafada a tsawace.

cikeda baccin rai monster yayi kan kabir tareda kunceshi hadeda shake Mai wuya.

Kabirrr su khaleed suka fada .

Cikin zafin rai kabir ya kwace wuyanshi daga wajan monster.

Kokawa sukafarayi tsakaninsu Inda kabir yayi nasaran buga monster a kasa.

wajan su sadiq kabir yanufah domin ya kuncesu.

Kwarbo kafan kabir monster yayi. Kabir baiyi ko inabah sai jikin amriya. Hatake zoben dake hannun damansa yataba goshin Amriya. Wani kara da walkiya ne ya wanzu. Tareda bakin hadari. Wanda ya kauraye gabadaya ilahirin dajin.

Yarrrrr jikin Amriya yayi. Tafara bude idonta kadan kadan. Daga bisani ta saukesu hakan kabir. Dake yashe hakasa.
Chapter 17 · 0% Book details