← Book details Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 38

Sashe 8

Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda muka taso a cikin gidanmu mun ga ummanmu da Mami basa shiri da Mama mahaifiyar su Yah Ramadan,wata irin k'iyayya ce suke mata wanda ko ganinta basa so,kuma suka katange mu daga yin huld'a da ita da y'ay'anta,to kun sani a duk sadda uwa bata son wancen to lashakka y'ay'anta zasu bi bayanta ne ba tare da sanin miye dalili ba,su dai tunda bata son wancen to suma basa son sa,
A haka muka taso muna nuna halin ko in kula da Mama,bama yi mata rashin kunya amma kwata-kwata babu ruwanmu da shiga sabgarta kai har shi Abba Habibun in ba hanya ce ta matse mana ba bamu zuwa takanas muce munzo gaidashi, hakan kuma bai dame mu ba mudai tunda basa shiri da uwayen mu muma hakance, koda akai bikin Anti Rahma babu wanda yai anko cikin mu, kuma bamu shiga cikin sabgar bikin ba kamar ma ba biki ake gidanmu ba, duk mun san ba dai-dai muke ba amma kuma bazamu iya gyarawa ba gudun fad'an uwayen mu mata, kuma duk Hajja ce tajawo wannan k'iyayyar a cewar Mami saboda tana nuna tsananin banbanci tsakanin Mama da su,duk abunda ya taso to Mama ce kan gaba kafin su, kuma tafi janta ajikinta fiye dasu hasalima da ita kawai take fira bandasu Mami,wannan abun ya kara taka rawa wajen sake jefa kiyayyar Mama da Ahalinta a zukatan su.

Wannan kenan........

Yadda muke kusanci da mami da y'ay'anta abun ba'a cewa komi,don Rukee tamkar Ummanmu ta haifeta haka muke tare,ko ina zamu tare ko a school sit d'inmu guda haka ma islamiyya,Anti shaawa ma ita da Anti Rafeea kamar tip da taya suma haka suke, haka zalika Yah Rafeeq da Yah Fahad suma sosai suke abota da juna,komi ya shafi d'aya to ya shafi d'aya, ummi ce kawai bata da partner, hakan ba kadan yai ma uwayen mu dad'i ba yadda muka had'e kanmu muka ware su YAH RAMADAN,.

Zan fara daga sadda muka shiga Ss3 don daga nan ne zakufi fahimtar komi.

Tunda mukai wayau da sanin kanmu yar tsama ce ke tsakanina da Yah rafeeq,tun ban da wayau inhar yana waje to ban da sak'at haka zai tisani gaba da tsokana yana jana fad'a, duk da tarin shekarun daya bani hakan bai hana shi tsokana ta ba,don shida yah fahad xasu bamu shekara bakwai-bakwai nida Rukee,amma in kaga yadda yake mun zaka d'auka wata tsarar sa ce, ba irin tsakanin da Abba Nura bai mana ba amma ta inda ta shiga ta nan take fita, kowa yasan a da niba mai fad'a bace balle wata hayaniya, hasalima zaka iya jana inyi kamar ban gani ba,zaka jima kana mun abu ko kallon ka banayi,amma silar Yah Rafeeq na zama mafad'aciyar karfi da yaji,sannan na zama soda uwar magana,har ta kai ga indai babu ni a gidan kowa zai gane,a hankali abun ya soma.

Kasancewar duk cikin yan matan gidanmu gaskiya babu wacce ta kawo ni a komi na dirin jikin y'a mace da kyau,don komi na Hajja na kwaso kuma Hajja farace sosai sol da ita kuma ko yanzu ka kalli jikinta kasan sadda tana da kuruciyarta tayi kyau na ban mamaki,to nima haka don shiyasa ma dokar saka Hijab in za'a fita ta zama wajibi garemu duka, duk da wani sa'ilin a sace nake saka gyale ajaka in mun fita mu saka nida Rukee,ban tab'a jin wanda ya kushe ni ba sai akan Yah rafeeq, komi na saka saiya kushe bama akan sitira ba har k'ok'arin da nake dashi a makaranta inhar na anso abun yabo shine nafarko da zai kushe yace satar ansa ce, abun yana mun ciwo inyita kuka idan na kasa maida masa,shi kuma daman haka yakeso yaita dariya yana cemun rab'o ashe haka nake ma qawaye kuka suma,irin haka dai tasha faruwa ba iyaka ko inyi kwaalliya zamuje wani waje yai dalilin da zai saka a hana fitar ko ya dizgani inji na tsani kaina, karshe bazan je ko ina ba.

Muna falon Mami watau bangaren su Rukee assignment muke na physic,duk kaina yai zafi daman kuma nice karfin assignment d'in, to yawa ne dashi kuma ga kaina dake ciwo,Rukee daman in inayi take kallo don ta iya saboda ba subject din da bata ganewa irin sa,daker take sha a exam.

Jinai kurin an fige book din ta baya na a zabure na d'ago don ganin waye, "Aikin banza, wai wannan abun ya gagare ku fiddawa ohh ni Rafeeq, ashe daman k'ok'arin a baka yake malaman da alama cin hanci ake basu don su baki overall,yo inba haka ba ta ina zaki iya kawai dai an cuci overall"

Ya fad'a yana jifata da book d'in,tsare sa nai da idanuna da suka rage girma saboda ciwon kai, haushi da bakin ciki kamar suyi mun me?

Kwalla ta taru cikin idona na ce, "koma dai ya ya ne bai shafe ka ba Yah Rafeeq, nidai ka daina shiga sabgata............ked'in banza Roohe,saina shiga sabgarki inyaso kiyi duk abunda zaki"

Sai kawai na fara tattara kayana ina hawayen bakin ciki, "ai don kana ganina a bangarenku shiyasa kake mun duk abun da ka ga dama, ni kuma daga yau bani babu nan b'angar...........Miyai zafi Roohee karki yadda yai nasara akanki,daman ai haka yake so inajin sa yana cewa ganin ki bangaren nan ne baya so,ke kuma saiki biye sa"

Mami ta katseni da fad'ar hakan, Uffan bance komi ba,kuma ban fasa tattara kayayyakina ba ina hawayen bak'in ciki,ganin da gaske tafiyar zan kuma ya sani sarai in na bar Abu na barsa kenan.......keeee doluwa wai tafiyar zaki?amma anyi shashasha,baki san wasa ba ke wai?wallahi ke kam hamago ce, d'an wasan nan na abokin wasa ma baki iya ba,tirr da halinki"

Nai masa banza na nufi k'ofa Rukee da Mami ba wanda yace k'ala dariya suke ma abun su, "kin san waye d'aya?wallahi ba zaki fita anan ba salan kija mun masifa ga Abba ko?"

Na watsa masa idanuna manya tubarkalla masha Allah, nace "Ehy d'in,kuma saina fita tun da ba anan aka haifan ba"

Dariya yai tayi yana sake tare hanya, yana cewa "yawwa ko kefa, haka nake sonki ai,amma mutum kullin dunkum kamar dankali.......duk'ewar da nai ta kasan kafafun sa zan wuce yai wuff ya rik'oni ya zaunar cikin kujera, "kifa kiyayeni Roohe ba inda zaki saikin gama abunda kike, ni zolayarki nake"

Fafur yak'i barina in tafi na fara kuka na gaske ina cewa, "kabar ni natafi kaina ke ciwo zan sha magani ko"

Sauri yayi yaje ya dauki box d'in magungunan gidan yana ajewa gabana, "yawwa gashi nan, gaya mun ta ina kike ciwon kan in san kalar maganin da zan baki kisha,"

Na nuna gaban goshina inata hawaye sosai, "to share wad'anan hawayen tukun, stress ne ke damunki ki ringa hutawa alhuda huda"

Ya bani paracitomal tare da ruwa na sha
"Rukee ki rakata ta kwanta ta huta,in so samu ne kiyi bacci ma dakin tashi zakiji ya sauka"

Nace cikin laushin jiki da sanyin muryata "ni banajin bacci,assignment d'ina zan ida...........wai ke wace irin jarababba ce ehy?assignment din banza da wofi dalla malama kije kiyi bacci zan ida miki"

Ban sake cewa komi ba na mik'e Rukee ta kamani muka nufi dakinmu dake cikin part d'inmu, kwanciyar nayi nai lamo kamar mai baccin, Rukee tai tsaye kaina har saida na gaji nai magana idona a rufen,

"Wai miye ne?"

Murmushi Rukee tayi ta ce, "kawai wata extraordinary caring nagani daga Yah Rafeeq,kin san nafara lura da hakan kwana kin nan.........ya isa don Allah mi kike son cewa?"

Na katse ta dafar hakan ina lullumshe idona, xama tayi bakin gadon tana cewa "kawai ina ga ya fara canza wa daga yar tsama,lamarin sa yayi kama daaa........kinga don Allah kyaleni da maganarsa bana so,kije kawai bacci zan"

Shikenan ta kyaleni,shiyasa bama fad'a da Rukee duk abun da na nuna bana so tofa tabar yi mun shi ba kuma zata sake tada maganar ba.
Shiyasa muka shak'u sosai da sosai nida ita muna kaffa kaffa da bacin ran juna, kamar wasa kuwa sai gashi nayi baccin ban tashi ba sai ana kiran sallar magariba, kuma naji dad'in baccin ainun na sauko na shiga nai alwalla naxo nai salla,na gama na fita zuwa wajen ummanmu anan falon ta na iske su Anti Rafeea da Yah Rafeeq dasu Yah fahad suna fira,hadda anti sha'awa da Rukee...........jikin umma na lafe ina gaida su cikin jam'i muna had'a ido dashi yaja tsaki yana ci gaba da maganarsa kamar bai sanni ba, nima sai na fita sabgarsa nace ma umma yunwa nakeji,

"Rafeea samo ma Roohe abinci mana"

Yah Rafeeq yace, "wai Wannan katuwar za'a sanya ma abinci?haba Umma ke kike lalata ta wallahi,"

Nai banza dashi,Anti Rafeea daman jira take don ta tsani a sata tai mun aiki, "yawwa Yah gaya mata,sai kace dai Roohe ke sama dani don Allah don' Annabi.......to kawai kice baki zuwa mana ba shikenan ba"
Cewar umma,ni kam nai murmushi ina kallon ta tana banko mun harara lodi lodi, na b'ata rai "Umma kice ta daina hararata wallahi"

"Kyaleta Ai bata k'ari,"

Haka tatafi tana jin haushin aikin da aka sata akaina, daman kuma kowa yasan nice yar gaban goshin umma ba ummi ba,don duk da take da sunan mahaifiyarta to tafi ji dani,kuma hakan bai dameta ba tunda itama ana bata kulawa daidai yadda ya kamata, sai gata ta dawo bata zubo abincin ba tana ta fara'a tace "Sak'o mak'ok'o daga Abba,yace kowa yafito aje b'angaren Abba Habibu ayi dinner kamar yadda aka saba"

Haushi ya cika ni ganin yadda kowa ke mun dariya, alamun dai dole ai zan taka naje can naci sab'anin a biyoni dashi har daki.
Chapter 8 · 0% Book details