← Book details Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 38

Sashe 34

Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sallar magriba ina kan gado mun gama waya da Yah Rafeeq cewar jibi yana hanya in hada masa something special, Rukee na chat take ce min "Wae bakiga wani abu ba game da Mufeey?"
Na diro daga gadon zan shiga toilet ina cewa, "ni kau na gani,wahala ce ke neman samunta ba sh akka"

Nayo alwallar sallar isha'i na fito Rukeen ke cewa, "Ban tunanin ta san ma halin da take ciki,ita a haukarta duk shak'uwa ce"
Tsaki naja kawae ina shimfid'a sallaya na ce "zata gane Annabi isa ba d'an Allah bane,don wannan baida kwabon aurenta..........turo k'ofar da tayi ne yasa nai shiru,daga yadda take kallona nasan taji mi nafad'a sai kurin na tada sallar bance komi ba, zama tayi har na kare sallar na sallame na tada shafa'q da wutri suma nayi na gama duk tana zaune batace k'ala ba, inata tazbihi na naji tace min, "LAYLA miya shafeki da nuna damuwata akan Yah Ramadan?ko ince miya shafeku akan hakan?shin kamar yadda kuke bangarar dashi kuke nuna halin ko inkula dashi haka kuke so dole inyi?damuwar da nayi dashi shine yasa har kuke mgnr ban ma san halin dana ke ciki ba akansa ko?to duk abunda nake ina sane,kuma cikin hayyacina nake ba hauka nake ba,tabbas na damu dashi sosae fiye da tunani na ina sonshi son yan uwan taka koma fiye da haka,to miye damuwar ku?bari kuji rashin aikin sa bai daman ba,nasan komi lokaci garai.
Haka zalika rashin gayunsa bai daman ba saboda yana da kyawawan halayen kirki,sannan yana da ilimin sa boko da islama,ba kazanta yake ba Aa gayun da baiyyi ne kamar saurayinki Rafeeq a yake baku haushi,to kowa da ra'ayinsa hakan ba aibu bane,idan ku wajenku don na nuna kulawa ta da kaunarta ta yan uwantaka garesa illa ce ni wajena abune mai kyau,kuma ba abunda zan fasa daman ba danku nake ba ra'ayin kaina ne,tunda shi da nake ma wa bai tab'a nuna min wani hali ba,to bazan damu ba ,sannan mgn ta karshe itace kudaina gulmata haka nan akan Favorite,koma mi nake ciki akansa bai dameku ba"
Tatashi ta fice a fusace idonta cike da kwalla,nasan hali ai kukan zataje tayi kuma zuwa gobe zatai kamar komi bai faru ba,dogon tsaki naja kurin ina cewa "Sakarai da bata san inda ke mata ciwo ba"

Rukee tace "tayi nisa bata jin kira ai"

"Kar Allah yasa taji kiran bai daman ba."

Washe gari nasha mamakin fushinta don irin haka bai tab'a faruwa ba mufeey bata dogon fushi, mutum ce mai saurin hucewa duk da bata da saurin fushi,Rukee kanta tayi mamakin yadda kwata-kwata bata shiga sabgarmu ba yinin ranar,saima fara shirya kayayyakinta tai dake dakinmu, bamu sha mamaki ba saida mukaga ta koma bangaren Mama dakin Najeeba,abun ya matukar bamu mamaki har su Ummanmu da akai gabansu, Mami ta kasa shiru ta ce "waccen kuma lafiya?Ina zata da kaya haka? Naga ai lokacin tafiyarsu bai ba"
Ummanmu da daman kamar jira take wani abun ya faru tsakaninmu da Mufeeyn, don kwata-kwata bata son alakarmu da ita saboda goggo Habi intazo bangaren Abba Habibu take sauka, ta ce cikin ginshira "inajin uwata zata bi can bangaren, ai gara haka azo a takura mana yara suna zaman su suna walawa"
Naji banji dad'in mgnr ba duk da cewa fad'a mukai da ita, Mamin ta ce "Au kuma fa,amma Rukayya miya had'aku kamar kunyi fada tsakaninku?"
Duk shiru mukai ba wanda yai magana saboda dai bamu son suna aibata Mufeey da Goggo Habi, Ummanmu ta ce "Don ubanku zaku Mana bayani ko kuwa?"
Turo baki nayi Ina kauda kai gefe alamun bazance komi ba, Mami ta ma Rukee tsawar da dole saida ta fad'a mata abunda ya had'amu............"To daga yau na yanke kusancin dake tsakanin ku,daman kuma ai kune bakwa jin mgnr mu inbacin haka miye na hudda da ita tunda bata cikin jam'iyyarmu ita da uwarta,don haka koma mi zatai masa shi Ramadan d'in ba ruwanku,na raba tsakaninku ni Allah yasa ma ta aure sa zasu ci ubansu in ta rasa lomar kaiwa bakin salati wataran,"
Duk mukai shiru muna saurarenta ita Ummanmu,don wani lokacin tafi Mami zafi da daukar abu babba koda baikai babban ba,d'ago kan da zamuyi mukai ido hud'u da Abbanmu bayan sa kuma Ramadan ne,wata irin fad'uwar gaba naji ta rufto mun,nai imanin suma sunji kalar abunda naji,da alamar kuma sunji komi tun d'azun.

Tsitt kaji falon yayi su Ummanmu suka sadda kanun su k'asa sun kasa magana,Mami tatashi cike da borin kunya tai bangarenta mukam ai kasa motsawa mukai,baice mana komi ba ya wuce hanyar part d'insa nayi imanin ba kyalemu yayi ba,yanzu dai baida lokacin mune don tafiya yayi tun ranar sunan Anti Sha'awa sai yau Allah ya dawo dashi.........Bin bayan sa ummanmu tayi mu kuma mukai zuru,Rukee ta ce "shikenan zamu gaya masu wajen Abba,kin san wannan shine karo wajen na uku cas d'inmu wajensa akan Yah Ramadan"

Kasa magana nayi saboda nasan halin Abba sarai,nice zanfi kowa hukuntuwa saboda dae nafi kaud'in baki,kuma duk nina jawo abun tunda ni nai maganar data hangula Mufeey d'in,har akai sallar magariba jikinmu a mace ko dinner bamu samu damar zuwa munyi ba,amma naga umma cikin tsananin damuwa tabbas ita ya juye mata kwandon masifar,kuma nasan Abba bazai mata ta sauki ba shi bai had'a yan uwansa da kowa ba,kuma bai kaunar wariyar da akeyi acikin gidan.

Abba bai neme mu ba sai da safe an gama breakfast ranar mun kasa zuwa gaida shi,fitowa ma muyi hidimar mu mun kasa aiko saiga Ummi ta shigo, "Yaya Rohee keda Yaya Rukee Abbanmu na kira"

Duk saida muka tsorata wallahi da zullumin hakan muka kwana,bamai yima d'an uwansa mgn kamar kurame, jiki a sanyaye muka fito zuwa kiran da yake mana.,,
Mufeey muka fara cin karo da ita zaune k'asa,sai shi Abban suna gefe guda Da Yah Ramadan suna magana,kamar wani ake zai masa ko miye oho dae,zaman mukai duk a kasan muna jiran ya sallamesa mu gaida Abban,mu duka ba wanda yace da mufeey k'ala ita ma batace mana ba,saida suka gama sannan muka gai Yah Ramadan d'in,ya ansa atakaice sannan muka gaida Abbanmu,bai ansa ba yafara cewa "Ku rik'e gaisuwar Ku bana so Rukayya da Layla,ashe kun daukan sakarai wofi.........don girman Allah Abba ka daina cewa haka wallahi bamu dauke ka haka ba"
Na fad'a inajin kwalla na son zubo mun, kallon banza ya watso mun ya ce "ke ai yau mai ansarki hannuna sai Allah,wallahi zanar ki zan kamar Allah ya aikoni,yau zaki san cewar baki gama girma ba don duk girmanki dukanki bazai gagareni ba,dawo nan bazan ji duk wata mgnr ki ba"

Sai hawaye suka balle mun,abunda na guda kenan nasan halin kayana,kuma yadda ya fad'a babu fashi yau mai ansata sai Allah, ya kalli Mufeey ya ce "gaya mun miya had'aki da yan uwanki mufeeda"
Kanta k'asa tana share hawaye take masa bayanin abunda taji muna fad'a akanta a daki, sannan ta d'ora da cewa "Abba ba wannan ne karon farko da suke hantara ta akan Favorite ba,duk don me zan ringa kulasa ina nuna damuwata akansa,so suke na ringa banzatar dashi irin yadda sukeyi ni kuma bazan iya ba Abba, jinina ya had'u da nashi sosae,hakuri kawae nake dasu saboda ina son su ina son mu'amalar mu saboda kasancewar sune tsararrakina banda yaya mace banda qanwa,su nake kallo matsayin yan uwana abun soyuwa agareni,amma sun kasa ganewa sun kasa daina abunda suke mun akan sa,sai naji na hakura da shige masu zanja baya dasu kawae Abba..........."
Falon yai shiruu sai shashshekar kukanta akeji da jan majinar ta,Duk Ramadan din na nan baije ko ina ba Abban ya nisa cikin sigar lallashi yake cewa "Mufeeda kiyi hakuri kinji ko,shi zumunci daman haka yake kana son yinsa amma su yan uwan basu baka had'in kai,kiyi hkr karkice zaki janye daga garesu ai kece mai hankalin cikin su,kin fisu wayau da hankali da sanin ya kamata kuma kece karamar su,amma kin cinye girman a haka don haka ki yafe musu kibarni dasu zan dauki mataki zasu gyara kinajina"
Tana goge fuskarta ta d'aga kai ta ce "shikenan Abba sunci darajar ka na yafe musu,suma ina mai basu hk.........Aa karki fara basu hakuri sune zasu baki,don haka Ku bata hkr yanzun nan"

Rukee ta fara magana tana hawaye, "kiyi hkr Mufeey hakan ba zata sake faruwa ba"

Ta ce "ya wuce Allah ya yafe mana gaba d'aya"

Abba ya kalloni kallon banza da wulakanci,muryata na rawa abu ya tsaya mun a makoshina ba abunda na tsana irin a turkeni,kuma ace inba mutum hakuri bakina na rawar kuka nace "I'm sorry"

Abban yai k'uta yana cewa, "tashi kije abunki kinji ko,ki kuma kwaso kayanki ki dawo dasu dakin ku"
"Shikenan Abba zanyi yadda kace"

"Allah yai miki albarka"
Tashi kurin naga yayi ya zaro shafceciyar dorina kamar ta zanar dawaki saboda girmanta, kamar sabuwa ma don ban tab'a ganin sa da ita ba, kafin kowa ya ankara ciki hadda ni ya shammaceni ya zabga mun ita ga ilahirin jikin,ban san sadda na zabura ba ina fasa wata k'ara kamar ana zarar raina,tunda na girma nai wayau ban taba ganin Abba ya dakeni ba,ko dunguri bai taba mun ba lallashine tsakanin mu da nasiha sai gashi yau ya cire hannu da dorina yana dukana akan wad'ansu da basu kaini daraja a wajensa ba,wannan bakin cikin ya danne zafin bulalar da yake mun duk da yadda yake dukana cicin karfinsa, mufeey keta bashi hakuri da Rukee amma Ramadan ficewar sa yayi kamar baisan mike faruwa ba,ban sake motsawa daga inda nake ba saboda zallar bakin cikin wannan abun,saida Allah ya kawo Hajja ta shiga tsakanin mu,sannan ya hakura sai sauke numfashin bacin rai yake........."Attahir kana lafiya kuwa?ka saka babbar budurwa kamar Layla kana duka da dorina?"

Ransa b'ace yace "karki tambayeni Hajja,kin san duk abunda zai jawo na daketa ba karami bane,kuma akan k'in bin umurnina wallahi yanzu na fara dukanki koda gidan aure kikaje kai ko singa da sabon gari kika haifa kuwa,Ku tashi kuban waje ke kuma Rukayya na baki last warning idan na sake kamaki da kamancin wannan kinga hukuncinki kema,mutanan banza da wofi."
Chapter 34 · 0% Book details