← Book details Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 38

Sashe 23

Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi yayi mun yace, "shikenan,na yarda na san watarana shi zai zama favorite d'inki........Aa Abba ai Mufeey ke ce masa haka,nidai mu tsaya a gaisawar ma yayi suje can suyi ta favorite dinsu"

Yar dariya yayi ta manya ya ce, "naji,tashi kije kinga har ten tayi.......da sauri na suri jakata ina cewa, "Abba test gareni ten thirty saina dawo ai mun addua pls"

Girgiza kai kurin yayi yana adduar Allah ya kara shirya masa zuria,tare da fatan wani buri nasa ya tabbata ba tare da saka hannun sa ba,Allah yake fatan yai masa jagora acikin burin nashi.

(Tofa Abba wane burine wannan🤔)

********

Rayuwar ta cigaba da tafiya abubuwa suna caccanzawa yau fari gobe bak'i,mun shirya da Rukee kamar ba abunda ya faru saidai kuma ko yaka junan mu bama firar Yah Ramadan balle yan uwansa, iyakar mu dashi mu gaidashi in hanya ta matse mana,ko wata magana wadda ta zama dole sai munyi dashi,ba shiri amma babu gaba ko kad'an,sabgar gabansa yake muma ita mukeyi,yana yawan kwanciya asibiti lokaci zuwa lokaci wanda hakan ya fara damun su Abbanmu,har ya shirya masa tafiya zuwa india a duba lafiyar tashi sosai tunda nan sun ce ulcer ce ke yawan kwantar dashi,su kuma su Abba sun kasa yadda da hakan shiyasa yafara masa shirin tafiya can,amma kiri-kiri yace bazaije ba shi yana jin sauki jikin sa sosai ba sai anje har india ba,dole aka kyalesa aka sa masa ido.

Kwanci tashi ba wuya wajen ubangiji sai gashi biki yazo,zuwa lokacin munyi hutun session zamu koma aji uku,murnar da nake saura shekara d'aya Yah Rafeeq d'ina ya dawo,nida shi kullin ba lissafin da muke inba na dawowar sa ba,ban san waye yake cikin tsananin d'oki da son zuwan wannan lokacin ba,kowa ji yake yafi dan uwan sa son zuwan wannan ranar,yadda nakeji a raina inama yana nan za'ai wannan bikin da abun sai yafi armashi,duk events din da za'ai sai yafi burgewa in muna tare,amma duk da haka bamu fasa shiri ba,tunda muka taso ba ai biki da wayan mu ba sai wannan karon,kuma gagarumin biki na y'ay'a biyu.

Kudi Abbanmu yake saki kamar bai san darajarsu ba,su dukan su sune yai musu kayan d'aki na burgewa duk kushen mai kushe bai isa ya kushe kayam nan ba,shi kuma Abba Nura ya dauki dawainiyar duk wani nau'i na abinci da za'aci tun daga satin biki har a wanye,Abba Habibu kuma shine ya dauki nauyin duk wani nau'in lemo da ruwa da za'a sha a bikin,ba laifi yayi k'ok'ori don tunda aka soma hidimar kullin mota guda ke sauke lemuka da ruwa tatafi,kuma shine da wannan aikin.

Rannan naje kan batun kudin d'inkunan mu na anko wajen Abbanmu,na ji yana ce masa Haba Yaya don Allah kabari ba abunda zai gagara ahidimar nan,mu so muke ka huta kwandalar ka bamu son tayi ciwon kai,kayi mana a baya yanzu ne lokacin da ya kama ta kaji dad'i,don Allah karka ce zaka dauki nauyin wani abu."

Naji yace, "sai Ace ana bikin y'ay'ana Taheer kace kar nayi komi?na zuba ido kurin kuyi saboda kuna dashi,sai dai idan kun raina arzik'ina.........Subhanallahi!miya kawo wannan mgnr Yaya fisabilillahi"

Cewar Abba Nura, Abba Habibun Ya ce, "to Nura ba dole ince haka ba,tunda kun kawo karfi yanzu ai dole kuce ku zakuyi komi"

Duk jikin su yai sanyi, "kayi Hakuri Yaya ba nufin mu haka ba,wallahi da zuciya d'a mukai maganar nan nan"

Murmushi yayi ya ce"na sani ai,don haka kubarni nayi abunda nayi niyya,ba donku zanyi ba y'ay'ana ne zan aurar"

"Shikenan Yaya Allah ya saka da alkairi ya k'ara girma ya kuma ja da rai"

Sai na koma kurin don kar suce ina musu lab'e, ina mamakin irin kaunar da suke ma junan su irin haka,kullin kara son juna suke bam tab'ajin koda da wasa sunyi musayar yawu ba,ko ja in ja basa yi,sunfi amfani da ra'ayin wanda yake babba karami sai yayi hakuri,hakika zumuncin su yana burgeni in bacin halin mu na mata ko ince in basu su Umma ai da bakaramin jin dadin wanan hadin kan za'ai ba,da ba wani fada ko tashin hankali.

Ankuna kala hudu akai ni kam nida Rukee da Mufeey dinkuna kala bakwai mukayi,zamu fara saka wa tun daga monday d'in biki,don baifi saura kwana goma ba bikin shiri kawai ake ta faman yi,wani abu da naji yaso ya tsaya mun a rai naje Bangaren Mami neman Rukee ina daf da shiga bedroom din Mamin naji suna magana ita da wata kanwar ta, Mamin Ke cewa "shiyasa tun farko banso ta dashi ba mutumin nan sailuba,saboda banga wani abu da zai iya tsinana mana ba,ki duba kiga babban mutumin da Rafeea zata aura,wallahi tunda aka fara hidimar nan yake sakin kudi kamar hauka,ko jiya a bakin uwar nakejin yai ma amaryar alert din five hundred thousand kudin kama hall din da zasu kamu kawai,to nasan yau ma ya turo wasu kudin da zasu kwalliya,kina tunanin kafin a gama bikin basu tara dukiya ba,amma sha'awa ta bijire mun saboda tana son aga gazawar mu,ga Abbansu ya makale bakin aljihu ni kam ai na shiga tara wallahi,Allah ya sani inajin kishin mijin Rafeea sosai...........sai nai kwana na koma don ban san me zan sake jiyoma kunnena ba kuma,na jima abun yana damuna to miye matsalarta da kudin mijin Anti Rafeea,ba dole bane Allah ya baka abunda yaba wancen, in ta dauro wanda ya bakan shine alkairi a wajenka da wanda duk yake tare dakai,haka dai na share ban yi maganar da kowa ba muka shiga sabgogin mu.

Yau ya kama alhamis saura tara biki,zamuje ansar d'inkunan mu cikin gari gashi Abba baya nan,inata kiran sa baya picking nasan kila abune mai muhimmanci ya hana ya d'auka,gashi dole sai da kudin zamu tafi duk munyi jigum jigum kowa da tunanin inda kudin zasu fito muke,daman Abbanmu yai alkawarin bamu to bainan,don kud'aden da dama gaskiya,ko na mutum d'aya kad'ai zasu kai 35k,naje ga Umma ta koroni wai in rabu da ita itama jiransa take ya cika mata zasu siyo wasu abubuwan,Abba Nura ma bai nan kuma ko hauka muke ba muzuwa ga Abba Habibu,duk damun san zai bamu in har mukaje.

"Ga shawara mana"

Cewar Mufeey,duk muka zuba mata ido nida Rukee, ta cigaba da cewa "favorite na nan mai zai hana muce ya kaimu,tunda daman taxi zamu shiga,kunga in mukaje sai daya ya shiga shagon yafito irin cikin damuwa kun gane,nasan zai tambaya sai muce sun hana kayan dole saida kud'i,kila ya bamu wani abun koda ba duka ba................ban san sadda dariya ta k'wace mun ba har ina fadowa daga gado,Rukee kan ta saida tayi murmushi mufeey ta soma k'ulewa ta ce,"bana son wannan abun kin sani,miye na dariya shawarar ce ba tai ba komi?"

Daker na tsagaita na ce, "ke wai tunanin ki ko 30k yana da ita a account ne?to wallahi har gara ni ma inada 25k shi kau daker ne,ni banji shawara anan ba wallahi"

Rukee tace, "ba batun raini bane Mufeey,wallahi Yah Ramadan baida wannan kud'in,in kuma kina ganin kamar mun son wulakanta shine muje kiyi masa magana ya kaimu,sai abi shawarar taki bamu san mizai faru ba koko Rohee?"

Inta dariyar kasa-kasa na ce "sosai ma,ba asan inda rana zata fad'i ba"

Tatashi ta fita duk jikinta yai sanyi,Rukee ta ce "bata san bai wani aiki babba ba,kila kallon k'udi take masa"

Ina kyaran muryata data shak'e nace,"yau zata sani ai,inbam da kankanba sai kawai muce ya biya mana kudin dinki,uhmm bada Rohee ba nan gaba ai maka gori shiyasa Abba kawai nake rok'o kudi ko yai mun gorin banjin komi"

Muna nan zaune ta shigo ta ce, "ku shirya shaf-shaf ni dai a shirye nake ina jiranku a mota........ai ke kam indai tafiya ce da shi to baki bata lokaci"

Murmushi tayi tafice,doguwar rigace jikina ta Atamfa dinkin rafa tai bala'in yi mun kyau,ko ina ta hau jikina ba kamar daga kasa data bud'e kuguna yai daidai da rigar,haka daga sama ma ma sha Allah,d'an gyalena baki nai rolling kawai na d'an saka turare kadan na saka lipstick fari mai dank'o na zizara kwalli,amma a hakan inka kallan saika ce ma sha Allah.

Rukee abaya ta saka bak'a tayi rolling gyalenta ni na daukar mana handbag muka fito,motar dai da yake fita da ita ce kamar kullin,don kamar ta zama tashi ma tunda duk inda zaya da ita yake fita,Abba yabar mishi key hannun sa.

Baya muka zauna nida Rukee ita gwanar tana gaba sai d'umi take masa, saida muka fita cikin gidan sannan Rukee ta ce "Yah Ramadan ina wuni duk yau van ganka ba"

D'an smile yayi ya ce cikin lallausan lafazin sa mai dad'i, "Ruk'ayya wallahi nima dawowa ta kenan"

"Ayya kuma mun tado ka baka huta ba"

"No,karki damu mufeeda tafi karfin na tsallake bukatar ta"

Inajin su nidai bance komi ba hankalina na kan wayata,duk ina jinsu dai saida sukai shiru sannan na d'an ciro kaina in gaida shi silently na ce, "good evening" ta center mirror muka had'a ido mai makon inji ya ansa mun,sai ya lumshe idonsa kawai bai sake kallona ba,su kuma da basu san miyai ba sai mufeey tace, "Favorite ana gaidaka Roheen Abba na gaida ka"

Yana karkata kan motar wajen shiga wata hanyar yace, "ohhh mufeeda na ansa fa"

Ta ce, "Allah baka ansa ba,Rukee kinji sadda ya ansa ne?"

"Aa gaskiya Yah baka ansa ba"

Gajeren murmushi yai yace, "to ku tambayeta mana"

"Wai haka sister?"inji Mufeey ta waigo tana kallona,toni mizan ce musu cewa zan ya ansa mun da ido?to yaushe ya ansa da idon shida ke tuk'i,in nace musu ta mirror ya zasu dauki maganar?sai na zab'i cewa "kila ya ansa banji ba"

"To kaji abunda ta ce,kodai ta kurame kayi Yah"

Jinjina mata kai kurin yayi don magana wuya take masa,nayi mugun mamaki ma yau da yake fira haka ni ban tab'ajin maganar sa data wuce seconds ba,har muka iso shagon mufeey keta masa fira parking yayi sai Mufeey da Rukee suka fita zuwa shagon,jira nake inga karshen wannan game d'in.
Chapter 23 · 0% Book details