Sashe 31
Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bamu samu kanmu ba sai karfe shidda da rabi na yamma,jikina kamar an bubbugeni su Rukee sai dariya suke min,suna tsokanta wai azo kallona gidan mijina saboda dole zan sha wuya,jinsu kawae nake nidai saida nayi baccin gajiya ina tashi muka hau waya da Yah Rafeeq yana bani lbrin aikinsa,yace in yai sa'a ma bazai wuce kwana goma ba zai dawo,naita murna ina ce masa "gidan duk babu dad'i da baka nan,nasan da ace kana nan akai haihuwar nan kullin tare zamu fita mu dawo," yai saurin cewa "waye yake kaiku?"
"Wannan ne mana,ai kasan dae in yana nan Abba baya sanya kowa akan wata hidima saishi kamar yafi kowa"
"Rooh"
Yai mgnr cikin wani yana yi marar misaltuwa,jikina yai sanyi jinsa kamar cikin damuwa sosai na amsa masa tare da tambayar ko lafiya?
"Naji ka so cool,akwai wani abunne?"
"Wallahi da ina da hanyar da zan hanaki zama duk inda yake da nayi,kwata-kwata bana kaunar ganinki tare dashi koda hanya ce kau,.........."yah Rafeeq ni kam inaso yau ka gaya min dalilin ka na yawan fadar hakan" na katsesa da fadin haka cikin damuwa,sabda ni nagaji daji tunda yasan dai nid'in tashice ba wani d'a namiji da zan iya ma kallon rahma sama dashi indai akan mgnr soyayya ne da aure..........."Rooh wannan da kike ganin sa munafukine,ni kad'ai nasan irin kallon da yake miki,ke ba zaki gane ba da zai samu dama wallahi zai iya cewa".........."karka karasa Yah Rafeeq!!!"
Numfashina har wani sama da k'asa yake saboda yadda naji bugun zuciyata ya karu sosai,kwata-kwata ban tab'a kawo wannan tunanin a raina ba saboda ma duk abunda zai tada min hankali game day aurena Dashi bana kaunarsa......."come down Rooh,Ina so na nuna miki ne yadda zaki nesa dashi,.......Yah Rafeeq ko maza sun kare walahi gara min na dawwama babu aure,Dana auresa gara na mutu wallahi.....sai kawae na sanya kuka sosai sbd yadda hankalina yai kololuwar tashi,kuka sosai nai tayi da yake dakin ni kadai ce yana ta kiran sunana da niyyar lallashi hankalin sa ya tashi sai kawae na kashe wayata.
Naci kuka sosae wanda na dad'e banyi ma irinsa ba,bansan dalilin da yasa nakejij tashin hankalin mgnr ba, ni koda wasa bana kawo ma irin haka a zuciyata,sabda nasan nafi karfinsa nesa ba kusa ba,kuma a ganina ko ga kafa aka daura masa ni dagudu zai kunce saboda yasan wutsiyar rak'umi tayi nesa da k'asa,sadda su Mufeey suka shigo da fara shirin tafiya gida suka sameni cikin wannan yana yin,Anti Rafeea ta kalleni ta ce "miya sameki?kinga fuskarki kamar jan kosai?"
Mufeey ta ce "Haba Anti,maimakon lallashi saiki ce mata haka?,yakuri sister miyafaru?"
Bance komi ba nidai ina kwance abuna har sannan zuciyata bana jinta dai-dai, Rukee tace "bai wuce ita da Yah Rafeeq ba,kila shine ya sata kukan"
"To miya shafeki ne idan shine?,sunfi kusa ai inma shiga kikai kunya zasu baki"
Cewar Anti Rafeea mufeey na cewa, "yanzu dai abar mgnr,sister ki tashi ga Favorite can yazo ganin baby daga nan mu wuce gida"
Kai kurin na d'aga mata bance komi ba,suna ta firar su nidai kallo ne nawa,har suka gama komi sannan na sauki na shiga toilet,gyara jikina nayi na wanke fuskana na tsane da towel na maida kayana danazo dasu na fesa turare na daura veil dina,kana kallon idona da fuskar zaka san nayi kuka ainun,lipstick na saka ma bakina na dauki phone dina nabiyo su,duk suna babban falon Anti sha'awa,mu kadai ne ba wasu yan barka,anata fira shi kuma rik'e da Babyn mufeey na kusa dashi cikin two siter,Ina saukowa daga stairs naji kawae na soma hard'ewa gabana ya fad'i sosae ban d'ago kaina ba har sauko na zauna gefen maijegon........"Roheen Abba lafiya kuwa?kinga fuskarki,ku fararen nan matsalar da kunyi kuka sai angane maku"
Uffan bance ba ban kuma tanka ma kowa ba sai suka kyaleni,har sannan inajin alamun ana kallona naki duban ma inda raina ke ban nan ake kallon nawa,.........idona rufe naji Antin tana cewa "Yah Ramadan hadda wata hidima kuma?to Angode Allah yasaka da alkairi"
Bud'e idona nayi naga wata leda ce babba da kayan jarirai na tab'e bakina,na maida idona na rufe saida ya fita sannan Muka tashi mukai musu saida safe,Anti Rafeea mijin take jira yazo ita muka baro da mai jegon........
*********
Tunda muka taho a hanya bakin mufeey baiyi shiru ba,ita dai bata gajiya da magana ko kad'an sai in bacci take amma inhar ido biyune tofa bata hutawa, tunda na zauna mazaunina ban d'ago kaina ba saboda bana kaunar koda wasa idona ya shiga cikin nashi,caan naji anja uban burki duk saida muka tsorata ba shiri na ciro kaina da sauri,hakan yai dai-dai da haduwar idanun mu cikin madubin center mirror, jinai zuciyata ta tsinke gabana ya fad'i rasssss da karfi, da sauri na kauda kaina Ban ma tsaya kallon kiya faru ba nasan iskanci ne kawae,ya tada motar muka iso gida muna tsayawa nice farkon shigewa saboda a k'agare nake na ganni a dakinmu.
Mom Muhseen&Asaad
_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_
*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*
By
Mom muhsen&
Asaad.
Wattpad name
Humaira3461.
🅿️.....22
Mun cigaba da zuwa gidan zaman jegon Anti sha'awa har kwana hudu,duk wata hidima mukeyin ta anyi sa'a Ammi tazo ita da kausar mun samu saukin hidimar duk dasu ake tayi,wata ranar Najeeba zata zo ayi da ita duk da bama sake mata itama kuma batamu take ba,Ammi Rahma kuwa bama ruwanta da wani kin sakewar da muke da ita, sabgar gabanta kurin take zata samu aiki dole muyi tunda gaba damu take sosae,in maganarta tazo kanmu zata tanka mana dole mu bata ansa,tun muna kakkauce mata ala dole saimun nuna bama yi da yan bangarensu,dole muka sake da ita anata hidima.
Don itace tayi uwa tayi makarb'iya a hidimar sunan,kuma hakan yai mana dad'i har ita maijegon,saboda babu wani babba sosai dazai shige gaba a hidimar,Su ummanmu Abba yace subar mana mune ya dace muyi,to tunda suka zo barka basu sake zuwa ba.
Daren suna aiki ya kacame Ammi ta kirani ta bani list d'in abubuwan da za'a siyo kasuwa,su Rukee da Mufeey na can sunata aiki nice na gudu na b'oye ashe rabon ni zanje kasuwar, idona yai narai-narai zan hawaye na ce "wallahi Ammi ban san kasuwar da zanje ba,kuma Abba ya hana shiga taxi ba kamar in yamma tayi sosae"
Ni duk dan in zillema aiken,sai kawae naga ta dauko wayarta tana kira,zu wacan naji tace "yanzu nake son ganin ka pls,magariba nayi bana so ace tayi ba asiyo kayan ba,ohk ina jiranka"
Na sauke ajiyar zuciya nasan na tsira, sai naji ta ce dani "kijara RAMADAN farfajiyar gida zaizo kuje tare,"
Ta juya kurin ta kyaleni nan tsaye nabita da ido,na ma rasa mi zanyi inama na ansa mata kurin naje da kaina?inama banyi musu da ita ba balle ta had'ani tafiya dashi,wallahi ba abunda nake gujema wa irin haduwa wuri daya dashi,bana so har raina bana so.........."mikike baki tafi kinjira sa ba,Roohe wallahi ki kiyayeni"........."yanzu zan tafi" na wuce dakin da muka aje kayanmu na dauko veil d'ina,doguwar rigace rafa jikina ta atamfa ta kamani daga sama boobs dina sun fito ma sha Allah,daga k'asa tabi k'uguna ta baje sosai tayi masifar fidda shape dina,yane kaina nayi da veil din inata jan tsaki kurin na fesa turarena da duk inda zani da kayana,da lipstick dina.
Ina bud'e kofar mukai kicib'is da ita, "wallahi dana cinmaki baki niyyar fitowa ba dakin sha tafi,ki wuce yana waje yana jiranki,sai hadarin ya taso ruwa ya sauka kuyi mana salalar tsiya"
Ina tafiya inajin zuciyata kamar ta fito don bakin ciki,raina b'ace haka na tafi farfajiyar gidan yana tsaye bakin motar yana danna wayarsa keypad,naja tsaki Ina cewa a raina "KO uwar meye acikin keypad din da zaka samesa kodayaushe yana dannawa?............tsaye nayi daga nesa kad'an dashi nace cikin shan murr, "gani nazo"
Saida ya gama shan k'amshin sa bai dubi inda nake ba ya zaga ya shiga motar, na ja wani tsakin kurin,na mance ba abunda ya tsana sama da tsaki ni ina ruwana........na bud'e motar na shiga yaja muka tafi KO radio bai kunna ba balle ta dauke mana shirun,inda saboda ma ai mun saba tafiya ba mai cema d'ayan sa ci kanka,ba muyi nisa ba iskan tasowar hadari ya soma kad'awa gwanin dad'i ga sanyi ga k'amshin ruwa,har lumshe idona nayi.
Haka mukaita tafiya zuwa can aka kirasa a waya, ya ciro ya saka speaker ya aje daga saman motar naji muryar Mufeey, "Favorite don Allah Ina son kwa-kwa in ka gani kaji"
Yadda take maganar cikin wata shagwab'a da salo yaban mamaki,anya mufeey ba son wannan mutumin take ba kuwa?........."ohk Mufeeda,bayan ita bakya son komi"
Ta sake narke murya cikin salon daukar hankali, "Ina son dabino to favorite,"
Ya sake ce mata yana murmushi wanda ya daskarar dani inda nake,Ina satar kallon sa ta gefen ido.
Ya sake cewa "To mufeeda bayan shi sai mi kike so?"
Dariya tayi mai kyau tana lauya murya "Aa Fa favorite shikenan,bayan wadannan abu d'aya nakeso"
Juyo da kaina nai na kallesa sau d'aya shima akai sa'a ya jiyo muka had'a ido,bazan iya fassara kallon sa ba nima bansan miyasa na kallesa ba, ansa yake ba Mufeey amma idonsa ni yake kallo, "miye kikeso fad'a min"
Saurin juyar da kaina nayi ga taga kawae,Ina kallon yadda aka d'an soma yayyafi jefi-jefi........"inaso ka dawo lafiya,ka kuma kula da titi"
"Ohk angama sai na dawo"
"Ohk bye"