← Book details Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 38

Sashe 7

Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma tai jimmm kafin ta ce, "safiya nifa duk abunda za'a had'a da shirka bana son shi wallahi,malam man nan wasun su basa tsoron Allah bokaye ne wallahi"

"Ko d'aya maijidda,wallahi shi ba haka yake ba in munje ai zaki ganema idonki,rubutu ne zai bada ba wani abu ba fa"

Jin inda suke son kai kansu saboda k'iyayyar auren mu yasa na taso na fito daga d'akin na d'aga labule ina cewa, "Mami,ummah,inhar don farin cikin mu zakuyi don Allah karku fara kai kan ku halaka,inhar kun yadda dani ba sai kunje wajen wani boka marar tsoron Allah za'a samu mafita ba,ni da kaina zan kashe auren bayan an d'aura nai maku wannan alk'awarin, shi kuma yah rafeeq ku barsa da Najeeba don naga alamar shi ya mik'a wuya,don Allah kar kuje wajen wani boka pls"

Mami ta ce, "shikenan Roohe Allah ya baki sa'a,don auren dole babbar masifa ce"

Na juya na koma dakin cikin tunani mai tsawo,taya zan iya kashe auren bayan anyi?nan danan zuciya ta shiga sak'a mun abubuwa baji ba gani,hadda wanda ban sanma ya akai ta hasaso mun shi ba,kuma na yadda da kaina dari bisa d'ari inhar nice zan kashe auren in sha Allah,burin su ai a daura ko?to kuwa bayan na tare bazan yadda koda yatsana ya tab'a ba zan bud'e masa shafe shafi na bala'i da masifa, ko baya kaunat uwatai saiya sawwake mun.

(Tofah🤔, bari dai mugani Roohe)

********

Bamu sake haduwa da yah rafeeq ba tun zuwan sa gidan anti,ban nemai ba shima haka inda nasan zan ganshi ma bana zuwa kwata-kwata,bangaren nasu ma nai mashi yajin aiki Rukee har ta gaji da mun korafi,duk ita dakin mu guda bacci ke kawota tafi wuni bangaren su.

Rannan ranar wani weekend ina ta game a laptop d'ina Ummi ta shigo dakin mu tana cewa, "Yah Roohe Abba na kiran ki"

Dagowa nai ina kallon ta bance komi ba,illa nasan da dalilin kiran tunda rabon daa muyi magana nidashi kamar yadda muka saba tun kafin batun auren nan,saukowa bai daga gadon ina sanye da riga da wando kanana rigar iya cinyata wandon pencil ne, sunbi jikina sosai suyi kyau hijab d'in sallata na zira na nufi falon sa.

Da sallama na shiga dai-dai sadda ya d'ago manyan idanun sa tubarkalla mukai four eye's,ras ras naji gabana ya fad'i nai saurin kawar da kaina naja tsaki dai-dai yadda xaiji ba tare da Abba shi yaji ba,na wuce da na isa inda Abban yake na zauna k'asa ina gaida shi.........."Abba ina wuni?"

"Bazan tab'a ansa gaisuwarki ba Roohe har sai kin gaida Ramadan,"

Cikin fishi da bacin rai yai maganar,kaina k'asa ban dubi inda yake ba na gaida shi ciki-ciki, "ina wuni"

"Lafiya lau"

Ya amsa a takaice muryar sa clearly ba wani abu a cikinta,ma'ana haushi ko farin ciki babu ko d'aya, duk mukai shiru na wani lokaci kafin Abban ya ce dani, "LAYLA nasiha zan miki matsayin mahaifin ki daya isa dake,tun da aka fara batun auren ki bance miki komi ba akai,na bari ne inga iya hankalin ki da kuma samun natsuwarki tun da baki da lafiya,a yau daya rage auren ku baifi sati shidda ba shiyasa na tara ku don nai muku nasiha da kwatanci,Aure dai da kuke ganin sa ba abun wasa bane ba abun rainawa bane,kar kuga cewar bakwa son juna akai auren kuje kuyita yin abunda kuka ga dama akai,kowannen ku yana da ilimin addini dai-dai gwargwado,kunsan abunda yake haramun da wanda yake halas ne,kunsan hakkokin miji akan matarsa,haka nan kunsan hakkokin mata akan mijinta,don haka kuji tsoron Allah kuje ku xauna da juna lafiya don Allah,kuyi mun wannan alfarmar bama kamar ke Roohe nafijin ki kece mai taurin kai,kece wadda kowa yasanki da fitina to inhar kikaje kika ringa fitina dashi wallahi zan manta dana haifeki,inhar kina so albarkata tabiki har lahira to kije kiyi biyayya kiyi hakuri a dakin ki,inaso ace sai mutuwa zata rabaki da gidan auren ki,nasan cewa Auren nan ku duka babu maiso amma ku sani bamu da ikon bijirewa umurnin Hajja,yi kata biyayya shine xai saka mushiga aljanna,haka nan kuma in kukai mana zaku ga haske a rayuwar ku,ahankali Allah xai kimsa maku soyayyar juna wadda baku tab'a tsammata ba,sauran yan uwanku duk nai masu fad'a kuma nasan zasuji maganata kamar yadda kuma nasan ba zaki bijirewa maganata ba,don haka ina muku addua Allah yai muku albarka,yasa aalkairi a zaman auren ku ya kuma sanya muku son junan,ya baku zuri'a mai albarka da zasuyi muku biyayya kuma,zan tsaya haka ina fatan kunji kuma zakuyi aiki da abunda nace"

"In sha Allah Abba ba zaka a samu wata matsala daga gareni ba"

Cewar Ramadan cikin biyayya da ladabi, kaina k'asa zuciyata bugawa kawai take,kalaman Abba sun daure ni matuk'a jikina yai nauyi haka ma bakina, saida naji ya ce "kefa Roohe"

Kwalla ta silalo mun ban dago kaina ba nace, "nima haka Abba"

"Ma sha Allah,ubangiji yai muku albarka bari na barku ku zanta"

Ya tashi ya shige cikin bed room d'insa ya barmu nan xaune kamar wasu kurame kuma makafi,ba wanda ya iya dagowa ya kalli d'an uwan sa,kowa da kalar tunanin da yake yi a cikin ransa,munfi minty goma haka zaune ba mai uhm bare uhm uhm,kafin naji tashin sa da muryar sa yana ce mun, "sai da safe"

D'ago kaina nayi ina kallon sa da mamaki,bai dube ni ba ya sa kai yai ficewar sa binsa nai da kallo har ya fice, jinjina kai nayi ina sake jinjina tsabar d'agawar sa da girman kansa,shiba wani shege ba sai fad'in rai,naja tsaki nima na tashi nai tafiyata dakin mu.

Abba Nura ne zaune da iyalin sa duka da yaran da matar tashi mami, Rafeeq,Sha'awa da tazo daga gidan auren ta sai Rukee, saida ya gama masu nasiha sosai akan had'in auren da akai yajawo hankalin su da nuna masu muhimmancin yin hakan, da kuma biyayya da iyaye akan abunda baka so.

"Wai Abban su kun sani sarai Auren dole haramun ne amma kuka bada goyon bayan yima yaran nan shi..........Safiya kimun shiru!"

Ya fad'a cikin yar tsawa,ba shiri taja bakin ta ta tsuke gudun rikici gaban yaran su, ya cigaba da ce mata "idan har ba zaki taimaka mun wajen ganin sunje sun zauna lafiya a gidajen su ba,to Safiya karki kuskure ki bada goyon bayan hana su zaman lafiya da juna,wannan shine kashedi na karshe tsakanina dake,in kuma wani tsaitsayi yasa kikai abunda har yasa wani cikin su ya kashe auren sa wallahi tallahi kema naki zai mutu"

Su duka yaran saida suka razana, wajen dagowa suna kallon shi, Rafeeq ya ce "Please Abba"

"Ba batun Please bane Rafeeq, na fad'a agaban kune yadda inhar hakan tafaru ba zakuyi blaming dina ba"

Sha'awa ta ce "kayi hakuri Abba, Mami ba zata aikata haka ba in sha Allahu"

"Allah yasa,"

Ya fad'a,sannan ya cigaba da cewa "magana ta gaba akan Yayah Habibu ne da matar sa, inaso kusan wani abu guda da baku sani ba akan su, Yaya da matar sa sunyi mana abunda bamu iya biyan su har abada,dani da Abban ku Taheer labarin mai tsayine amma abunda zan iya sanar daku shine Yaya Habibu da matar su da bazar su muka kawo wannan lokacin,sune komin mu tun daga sadda maka taso har kawo yanxu,sunyi hidima damu da jikinsu da aljihun su tun duniya na kwance, shine karatun mu na boko da islamiya har muka zama abunda muka zama,wuyar da Yaya yasha akan mu shida matar sa baki ma bazai iya misaltawa ba,har takai zasu iya rasa abun da zasuci inhar mu zamu samu kuma zamuje makaranta, wannan dalilin yasa Hajja bata had'a kowa dasu ba, duk abun da zai taso bata yadda wani ya raina su ba to balle mu, don haka ina sanar daku da babbar murya inhar kuna so mu shirya daku mu daidaita to ku kyautata masu,yadda kuke zumunci da y'ay'an Taheer suma su ramadan da su Rahma kuyi dasu,hakan shi zai samun cewar eh lallai kun yadda nidin mahaifin kune,sab'anin hakan kuma zai nuna mun cewar ban isa daku ba alamun ban haife ku ba,wallahi rashin bin yaya da matar sa kamar kun tsake kan ku daga cikin zuri'ata ne,don haka yadda zakuyi mun biyayya ku kyautata mun suma haka zakuyi masu,fatan kun jini kuma kun fahimce ni"

"In sha Allahu Abba zaka samemu masu yi maka biyayya akan hakan,Allah ya bamu ikon binsu bisa dai-dai"

Cewar Rafeeq, Abban ya ce "madallah,Allah yai muku albarka kuna iya tashi na sallame ku"

Mom muhseen&Asaad🥰
_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_

*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*

By
Mom muhsen&
Asaad.

Wattpad name
Humaira3461.

🅿️.....6

*WAI WAYE...ADON TAFIYA*

Hajja kakata ce itace ta haifi ubannin mu maza, su hudu rak gareta Allah ya bata su uku maza sai mace daya mai suna goggo Habi,kuma itace autar su tana aure a lagos tana jimawa ma bata zoba yaranta uku itama, babbar sa'ar muce mufida sai sauran maza kamis da jamil.
Abba Habibu shine babba cikin su Babanmu,shida matarsa MAMA suna da yara hud'u Anty Rahma sai Yah RAMADAN sai Yah Najib sai Najiba auta, Abba Nura da matarsa umma Safiya suna da yara uku rak, Yah RAFEEQ Anty sha'awa sai Rukee
Abba Tahir shine mahaifina da nakeji dashi duk duniyata,ina alfahari da Abba na ubana da babu kamar sa a wajena,soyayyarsa mai girma ce agareni,shida mahaiifiya ta mai suna Maijidda sun haifi yara hud'u Yah Fahad,Anty Rafia saini LAYLA da naci sunan mahaifiyar Abba watau Tsohuwa mai ran k'arfe HAJJA ake mun lak'abi da ROOHEE,sai auta ummi mai sunan mahaifiyar ummanmu.
Chapter 7 · 0% Book details