← Book details Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 38

Sashe 35

Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mun fito mukai karo da Umma a fujajan tataho zuwa part din,bata tsaya wajena ba ta isa garesa tana huci muna iya jiyota daga inda muke, take cewa cikin karaji........."Wallahi Tallahi TAHIR idan ka sabauta mun yarinya kotuce zata rabani dakai,!akan me?akan wasu shashashu wofi dasu zaka dakar mun yarinya da wannan dorinar ta bugu jakkai..........MAIJIDDA!!!"
Tsawar da Abban ya daka mata harmu ta tsorata,durkushewa nai na saki wani irin kuka na bakin ciki,inajin yadda yake maida mata cikin kakkausan halshe tare da cewa, "wallahi idan kika sake aibata yan uwana saikin tafi gidanku,don ki gane yan uwana sun fiye mun ke muhimmanci nesa ba kusa ba...........to in na tafi gidan mun sai me?ai daman acan kaje ka ganni ka auro,don girman Allah Tahir ka sawwake mun yanzu ba sai anjima ba,daman nagaji da kwankwad'ar bakin ciki agidan nan"
Abun yayi k'amarin da Hajja ta kasa tsawatar musu suji,sai magana take sun kasa yin shiru kafin sadda Abba Habibu zai zo Abba ya cire hannu ya zabga ma Ummanmu mari,sannan yace tatafi gidansu ya sawwake mata igiyarsa guda.
Tashin hankalin da nake ciki ma ba a magana saboda ko kusa bamuyi zaton abun yakai haka ba,ji nayi duk duniya ba wanda na tsana irin RAMADAN da Mufeey saboda duk ta dalilin su ne Abba yake neman rasa hankalin sa har ya mari umma ni kuma yai mun bugun kawo wuk'a, mizan dasu kuma ahalin yanzu...........tuni Umma har ta had'a kayanta tana kuka,kuka sosae irin wanda ban tab'a ganin tana yinsa ba a rayuwata,alamar yau turarta takai bango kenan
Bamu San ya akai ba tun fitowar Abba Habibu zuwa wajen Abba sai ga Abbanmu ya fito fuskar sa murtik,bazan iya tuna iyakar lokacin da naganshi haka ba,Ina rik'e da umma nak'i sakinta nida Ummi muna ta kuka ya shigo bedroom d'in,ya tsaya kurin bakin k'ofa rungume da hannunsa,sakin umman mukai munata sharb'en majina,ta dauko akwatin ta nufo k'ofar zata fita sha gabanta duk da bai sake fuskar ba har sannan,........."Ki koma ki aje akwatin na maidaki......ban maidu ba!nace ban maiduba a yau gidan ubana zani,koda bashida rai haka uwata ma na gwammace naje na zauna a kango.....da......dai in......in sake zama dakai"
Kuka ya kwace mata ta durkushe tana yi sosae,muma muna taya ta saboda muna son uwarmu duk abunsa zai sata kuka muna k'insa.........durkushin yayi gabanta cikin sassaucin fushin sa yasake cewa, "yanzu ma gaban yaran zaki daga mun murya Maijidda?........naje na d'aga ni ai a gabansu ka cire hannu ka maran,na d'aga muryar zan kuma sake d'aga maka,ka tashi gabana TAHEER!"...........gani mukai kurin ya d'agota ya rungume jikinsa,ai har rige-rigen ficewa muke nida ummi,muka baro bangaren nata gaba d'aya.
Daga haka mukaga umma ta fasa tafiyar amma kuma babu walwala fuskarta kwata-kwata,gidanma gaba d'aya ya canza kowa rai babu dad'i,mufeey ta kasa dawowa dakinmu kuma bamu ma juna magana kwata-kwata,sai ma naga sun fara shirin tafiya gida.
Ranar da zasu tafi ma sai nai tafiyata gidan Anti Rafeea don har raina haushinta nakeji,karma ace RAMADAN tsanar da nake masa ta linka sosai,wannan ne dalilin rabuwar mu da mufeey ko a waya balle gani da ido,bata sake zuwa Abuja ba sai da akace an saka bikin mu,shima kuma Ramadan d'in wannan na daga cikin dalilin da yasa na kara tsanarsa.

Mom Muhseen&Asaad

_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_

*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*

By
Mom muhsen&
Asaad.

Wattpad name
Humaira3461.

🅿️.....25

Ana cikin hakan Yah Rafeeq ya dawo daga course din da yaje,koda yaga yana yin yan gidan kowa ba karsashi yasan akwae dalili,bai tambaye ni ba sai bayan kwana biyu,Ina kuka nake bashi labarin komi hadda dukan da yai mun da sakin ummanmu, ranar naga zallar b'acin rai ainun tattare dashi idanun sa kamar wuta saboda jaan da sukai,lokacin ne yake ce mun "Rohee lokacin da yadace in rabaki da gidan nan yayi,daman ina da niyyar in nadawo nayi ma Abba Maganar auren mu,inba haka ba komi zai iya faruwa tsakanina da Wannan mutumin (RAMADAN),don haka inaso kiban dama da sahalewarki afara batun auren mu,"

Kaina k'asa muna cikin motarsa sabuwa daya siya kwanan nan,Ina jan majina yayin da zuciyata ta shiga bugu ba k'ak'k'autawa ban san dalili ba, shiru kamar bazan ce komi ba saida na gama tunanin da nake nace masa "banda haufi akan Auren ka Yah,kuma ko yaushe aka saka banda matsala kawae inaso mu fara service kafin hakan,banso sai munyi aure in raba hankalina biyu"

"Service ba matsala bane,karki damu da hakan nidae insan cewar kin zama tawa zan iya iko dake akodayaushe shine kwanciyar hankalina,in yaso daga baya koma miye sai kiyi banda matsala indai kin zama halalina,to ya kike gani inyima Abban mgnr?"

Na kasa kallon sa kaina still a k'asa na d'aga masa kai,cikin jin dad'i ya daki sikiyarin motar yana cewa "Ohhh yess"
Murmushi kurin nayi Ina juyar da kaina wajen window kunya na kamani,kamar wani wanda aka yima babbar kyauta.

Bamu sake mgnr dashi ba bayan hakan,mun dai cigaba da muamalar mu kamar kullin koma fiye da kullin,don duk safiya karajin kaunar juna muke kodan shine mutum na farko da zuciyata tafara so oho?
D'an tsakanin ne Result d'inmu ya fito munyi farin ciki sosae ganin yadda yai kyau sosae,kowa yai mana murna Abba Nura yai mana gift na sabbin wayoyi latest phones da aka yayi yanzu,hakan ba kad'an yai mana dad'i ba don rayuwata Ina son waya sosai,Abbanmu kau ko hanky bai bamu ba har sannan bamu dawo dai-dai dashi ba,haka ummanmu itama banga alamun hucewa daga gareta ba abundai ya tab'amu sosae shiyasa mun kasa yafewa Su mama,don duk ma miye sune da alhakin hakan.

List dinmu ya fito na tafiya bautar k'asa mukai sa'a an ajemu waje guda Rukee,ganin hakan ya kwantar mun da hankali don bana kaunar zuwa wajen da babu Rukee jinta nake kamar raina,ina son Rukee fiyema da son da nake ma Ummi da Anti Rafeea,shak'uwar mu takai kololuwar shak'uwar da duk inda d'aya yaje bazai ji wani dad'i ba in ba d'ayan,muka fara shirye-shiryen shiga camping 3weeks da zamuyo komi munyi sa tare da taimakon Yah Rafeeq duk wata siyayya shine yai mana da aljihun sa,ya hutar dasu Abbanmu hakan kuma yai masu dad'i sosae,Ana saura kwana biyu tafiyar mu aka kwantar da Yah Ramadan Asibiti wai ulcer shi tatashi,wallah ko ajikina ban tausaya masa ba don dai ciwone aida cewa zan Allah ya k'ara,har Ana gobe zamu shiga camp bamuje ganin sa ba duk da mun san Abba ido ya sanya mana akan rashin zuwan namu,kowa yaje Hadda umma amma bamuje ba.
duk da mun san ita da Mami ba da son ransu sukaje d'in ba,muna falon Umma zaune muna kallo yai sallama ya shigo,duk muka sauko muka gaidashi ya ansa ba walwala,Umma tace masa "sannu" bata dago kanta ba ta cigaba da danna wayarta, ya dubeta ransa b'ace "kin gaya ma su Rohee suje sugano Ramadan?"
Yanzun ma bata kallai ba ta bashi ansa, "Kai nike jira ka sanar dasu"
Mu kanmu bamuji dad'in maganar ba muka sadda kanmu k'asa cikin jin rashin dad'i, "nagode Maijidda,"
Yajuya zai fita har yakai k'ofa ya jiyo yana kallona, "keda Ruk'ayya da ummi Ku sameni a mota"

Kasa motsawa mukai bayan fitar sa saida ta ciro kanta daga wayar ta dalla mana harara sannan kowa ya tashi cikin azama muka suri hijabban sallar mu muka rufa masa baya,yau da kanshi yake tuk'in daka kalli fuskar sa kasan ransa ab'ace yake ainun,uffan baice mana ba har muka iso Asibitin wani babban asibiti ne aka kawo sa ba wanda ya saba kwanciya ba, yana gaba muna biye dashi a baya jinake wani bakin ciki yana cika raina,bana kaunar sake had'a wuri da Ramadan,tsanar ganin sa nake yanzu ma da damar dazan b'ace ma zuwa inda yake wallahi sai nayi, muna isowa bakin k'ofar dakin aka kirasa a waya yace mu isa ga dakin nan bari yaje yayi bak'o can wajen parking.
Dad'i ya kama ni yana juyawa ya b'ace naja tunga bakin k'ofar nak'i shiga, Ummi da Rukee suka kalleni kafin ma suce komi na rigasu ta hanyar cewa cikin masifa, "wallahi da dai inje inganshi inyi masa sannu gara ace Abba ya kasheni,yadda na tsani wannan mutumin ko mutuwa banajin na tsana hakan,don haka kudai da kukaji zaku iya ga hanya"
Ummi ta shige bata sake bi takaina ba don tasan inta tanka ubanta zanci,Rukee ta ce "Rohee baki daddara Hukuncin Abba ba ko?miyasa kin faye kafiya ne?shin idan kinje kin masa sannun lafiya zaki basa?sannu ai ta fatar bakice basai kinyi masa addua ba,nima ita zanje inyi masa sannun ai daga ita dai bawani uwar zamuyi masa ba ko?"
Sai kuma naji maganarta gaskiya ce dole na shiga daga shi sai Najeeba d'akin,yana kwance drip na shiga jikinsa singlet ce fara sol da ita jikinsa sai dogon wando na pajamas,idonsa a rufe ruff zaka d'auka bacci yake amma kuma idonsa biyu.
Kallon farko da nayi masa naga ya rame sosai da sosae,zuwa can Mama ta fito daga bayin dakin,ummi da Rukee suka gaidata ni kuma nai kamar banga kowa ba.

Duk sukai masa sannu da jiki ya amsa a takaice,daga haka ba wanda yasake magana nidae daman tunda na shigo wayata nake dannawa ina kallon status d'in mutane wani yagama wani yashigo,videos hadda na wakoki kala kala ba abunda ya daman kamar ina cikin dakin mu........"malama kina damun marar Lafiya pls"
Cewar Najeeba tana mun kallon wulakanci,na ciro na watsa mata nawa kallon na ce "Dagaske?"
Na cigaba da abunda nake, silently gently da muryar irin ta marasa lfy naji ance mun, "idan ba zaki iya adjusting kunna wannan hayaniyar ba pls workout"
Dago kaina nayi na dubi inda yake kwance kamar bashine yai mgnr ba,naja siririn tsaki kurin nai hanyar fita ina cewa, "daman bisa k'aya nake ai"
Ba wanda baijini ba don na fada da sautin da zasuji,ban damu da idon Mama ba don itama d'in natsane ta tunda sune ummul'aba isin komi na fitinar cikin gidanmu.
Chapter 35 · 0% Book details