← Book details Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 38

Sashe 37

Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun Daren jiya na kwana da wani irin firgici na tunani da rashin sanin mike damuna,yinin jiyan ban iya tab'uka komi ba kwance kurin nake,ko abinci saidai liquid abu nakesha niba rashin lafiya nake ba,haka dae gani nan bazan iya sanin taka mai-mai abunda ke damuna ba,Rukee duk ta damu bini-bini zata shigo ta dubani har ta kasa hkr ta gaya ma ummanmu,itama tazo tai ta tambayata mike damuna saidai ince ba komi,data matsa mun sai na sanya kuka kawae,saboda ban san mizance mata ba.
Kuka nayi sosai ko zan samu saukin zuciyata,da hakan dae bacci ya sace ni sai bayan la'asar na tashi,koda yah Rafeeq ya kirani a waya shima irin wannan yana yin yake ciki don dai shi namijine yafini jarumta,yace mun ko zamu fita yawo musha iska nace Aa ya kyaleni kila zuwa gobe zan warware,dole ya kyaleni.
Amma bayan wani lokaci zai sake kirana yana tambayata ya nakeji,kuma bana iya hkr saina dauka inhar yakira inka gammu dole zamu baka tausayi ainun,kamar mun san akwae wata mummunar k'addara dake jiranmu safiyar Asabar d'in.

Ina dakin Ummanmu Ina breakfast Abbanmu ya shigo da sallama,daga yana yin sa zaka fahimci baida kuzari,baida wani natsuwa tattare dashi na d'ago ina gaida shi ya kalleni wani irin kallo da ban tab'a ganin Abba yayi mun shi ba sai yau,cikin lafazi mai taushi ya ansa mun da kulawa har yana tambayata, "Lafiya lau Rohee,mike damunki duk jiya ban ganki ba,kuma gashinan naga ni duk kinyi wani iri"
Kwalla ta ciko idona nace cikin son yin kuka, "Abba ban San mike damuna ba,bana jin dad'in komi wallahi tun jiya nake haka har yanzu,"
Sadda kanshi k'asa yayi cikin kulawa ya data kaina, "I'm sorry,karki damu kanki da damuwa everything will be fine ohk?"
Na jinjina kaina kurin sannan yasake cewa "kuma kin iya addua why not ba zaki ta lazimtar addua ba har kiji sauki a zuciyarki"
Jinjina kaina nayi Ina cewa, "Ina yi Abba,zan kara kan wacce nake yi d'in"
"Good girl,Allah ya sawak'e ki maza ki gama zamuyi meeting babban falon Hajja nan da karfe shad'aya na safe,Fahad ma na hanya tun asuba na kirasa na sanar dashi"

Ya nufi cikin bedroom d'in Ummanmu,na shiga cikin wani irin matukar faduwar gaba,duk da ba yau akafara meeting ba irin wannan amma naji jikina ya bani kamar akwae wani abu dazai shafeni marar dad'i,haka dai naita cakalkalar cheeps din na sha rabin tea din dake gabana na tashi na nufi dakin mu, na iske Rukee na shafa tayi wanka na ce mata,"kinji wai meeting za'ai"

"Nima yanzu Mami ta shigo tana gaya mun,wai kowa da kowa zaizo hadda su Anti sha'awa suna hanya suma,Ammi ce kurin ba zata zo ba saboda nisa kuma abun yazo suddenly"
Jikina sanyaye na zauna inata loliyar wayata nama rasa wane irin tunani zanyi,yah Rafeeq ya kirani a waya.........cikin sauri na d'auka "Rooh"
Wani irin lumshe idona nayi inajin kiran har cikin jikina,kamar ranar ya fara kiran sunana, naji kwalla ga idona nace masa "Love kana jin ko abunda nakeji?wallahi ji nake kamar za'a rabani da wani abu mai muhimmanci a rayuwata, wata irin kewa nakejin kaina ciki kamar ina rayuwa ni kad'ai..........sai kawae na kashe wayar na kama kuka mai tsuma zuciya, Rukee tayo kaina cikin damuwa "Rohee wai miye haka,kwana biyu duk kin firgice kin sanya mun cikin damuwa,don girman Allah kiyi hkr ki ringa ambatar hazbunallahu wani imalwakeel,ba abunda yafi karfin addua don Allah,na kasa daina kukan saida naji itama tana kukan sannan na hakura,muna nan zazzaune saiga Anti Rafeea ita da iklas da tsohon cikinta daker take tafiya ma,ba dad'ewa Yah Fahad ya iso shima Anty Sha'awa da Farhan suka iso,gida ya kammala muka tattaru duka a falon Hajja inda ake meeting.............

Kowa ya gama Hallara a wannan falon Hajja na cikin kujerar ta ta hakince, fuskar ta babu wani annuri a gimtse take baka isa kawa wani wargi ba, daman kuwa kowa na shakkarta yana shayin fushinta, don yanzu aljannunta sun ci uban mutum basu da mutunci,don ma suna dad'ewa basu motsa ba.
Tunda na shigo na samu waje na zauna jikina yake wata irin rawa-rawa,addua ce kurin bakina saboda zan iya kasa control din kaina,Addua aka umurci Yah Ramadan ya bude taron da ita,yana can gefe guda cikin natsuwar sa ta kodayaushe ya gyara zama sannan yace sallu ala Nabiyyul kareem,akai salati ga Annabi sannan ya karato addua marar tsayi muka shafa.......... Shiru ya d'an ratsa na wani lokaci kafin Hajja ta tashi daga jinginar datai da kujera tana fara magana cikin kakkausan lafazi,

"Na sanya a tara mun ku ne saboda inaso nafad'a gaban kowa,kuma in k'ulla wani zumunci da nake fatan ya d'ore har bayan raina, nasan kowa dake cikin wanan gidan yasan da cewar ROHEE DA RAFEEQ SUNA SON JUNA,KUMA AURE SUKE NIYYAR YI KO?"aka ansa mata da cewar hakane ba wanda bai san da wannan mgnr ba.

Ta jin jina kai tare da cigaba da cewa, "to babbar maganar da nakeso kusa sani itace AURE TSAKANIN SU BAZAI TAB'A YUWU WA BA HAR ABADAN...........Innalillahi wa inna ilahir raju'un!Hajja wace irin magana kike fad'a haka?"
Mami ta rabka wannan innalillahi cikin karaji da kid'ima da ta shin hankali,Ummanmu ta anshe da cewa "Hajja wace irin magana ce wannan?ya kike so yaran suyi tsawon shekara da shekaru suna tare sai yanzu ki b'ullo da wannan matsalar?"
Su dukan su hankalin su ya tashi matuk'a ba wanda ya iya tanka musu cikin su Abba,saboda sun san dolene maganar ta gigitasu ta kid'imasu kamar yadda tayi masu,a wannan lokacin bazan iya misalta halin da zuciyata take ciki ba,abunda na sani shine tana bugawa fiye da kima tana bugawa ne kamar tana neman hanyar fitowa,na daskare inda nake zaune yayin da falon ya dauki wata irin hayaniya da surutu tsakanin juna,Hajja ta zuba ma kowa ido tana kallon sa, yadda bakeji nasan Yah Rafeeq fiye da hakan yakeji na kasa kallon inda yake zuface keta keto min kamar an jik'ani da ruwa,Rukee ta rik'e hannuna sosai cikin son bani kwarin guiwa wanda ban dashi a halin yanzu,Ummanmu hawaye ta fara yi tana cewa "inhar bakida wani dalili na yanke wannan alakar kin cutar da y'ay'an nan,ba karamar cutar wa b.........MAIJIDDA!!"

Abbanmu ya daka mata tsawar data gigita kowa a wajen,falon yai tsit bakaji motsin kowa sai kukan ummanmu tace "kayi mun fiye da haka Taheer,amma wlh inhar babu Hujja wannan auren sai anyishi wallahi,"

"Kyaleta Taheer,barta tayi mai isarta Aure ne dai Ya HARAMTA tsakanin y'ay'an da suka dora ma dogon buri,kuma ba kowane da wannan abun ba sai ni nan,Nice nayi komi duk don inyi maganin ku akan k'iyayyar da kuke nuna ma ZEENAH Allah ya bani wannan damar na aikata hakan agaresu daku,saboda akan kunnena kukai maganar ranar da aka haifi Rohee cewar zaku had'asu Aure ita da Rafeeq idan Allah ya rayaku nan gaba,kuna son kaunar y'ay'anku ta d'ore har abadan kamar yadda zumuncin ku keda Maijidda zai dore har abada ta hanyar had'a zuri'a,akan kunnena kukai wannan alkawarin,ni kuma naci alwashin sai idan ba raina hakan zata tabbata"

"Wata rana ke maijidda kina goyon Rohee a lokacin ba zata gaza wata hud'u ba,na tusa ku gaba muka tafi kauyen mu dake can hanyar katsina,domin muje bikin d'an kanena saboda tunda aka aureku baku tab'a zuwa garinmu ba,saboda a cewar ku baku san zuwa kauye ku kwaso kirci,ita kuma Safiya tana goyon Rukee watan ta Shidda tunda wata biyune tsakanin su,na tafi da k'udirina a raina Ina adduar Allah ya bani damar cikawa,munje Rimi lafiya aka tarbemu cikin mutunci da mutuntawa aka bani d'aki d'aya daku muka sauke kayanmu anan,muka shiga hidimar biki kunata sabgoginku ni kuma duk kallon ku nake,Ina neman hanyar da zan aiwatar da kudirina har aka kwana daya aka kwana biyu ban samu damar hakan ba,sai wata dubara ta fad'o mun na aiki yaro ya siyo min maganin bacci mai karfin gaske,na zuba a cikin zobon biki na sake leda na daure na kawo muku bayan kunci abincin dare kuka d'ora dashi,dan danan bacci ya zo maku kowacce ta tafi shimfid'arta ta kwanta tare da yarta,ranar banyi bacci ba har saida na tabbatar burina ya cika.
Bayan bacci ya sace ku yaran ku nata wasa idonsu biyu,na dauki Rohee daga jikin ki maijidda,naje na ajeta jikin Safiya bayan na dauke Rukee na goyeta,Bayan wani lokaci Rohee ta fara kukan nono na banza da ita, naga dagaske ba kujin kukan sai nai amfani da wannan damar na ciro nono na bata ajikin safiya,yarinya ta anshi tana sha kamar ba gobe,sosai take shan nonon don daman Rohee lokacin Allah yayita da tsotso,Saida tasha tayi tatul har bacci ya sace ta,ban dauketa ba saida asuba tayi da tasake sanya kukan tana son sake shan nonon,na sake kanga mata ta kama zuk'a,ita ko Rukee na tare dani data motsa akwai koko sai in danna mata tasha ta koma bacci,dana tabbatar burina ya cika Rohee tasha nonon Safiya yadda aure ba zai tab'a tabbata tsakanin ta da d'anta ba sai na maida ma kowa d'anshi gabanshi naje nayi alwallar asuba nayi salla nayi kwanciyata,koda kuka tashi ba wacce ta fahinci miya faru,ni kuma ba wanda na sanar ma wa sai Habi ta itace kawae tasan da wannan sirrin,shima saboda halin rayuwa koda ban kawo yanzu ba,kunji dalilin da yasa nace Aure tsakanin su ya Haramta............

_INA FTN MASOYANA ZASU FITO SU NUNA MUN IRIN KAUNAR DA SUKE MUN,TA HANYAR SIYEN WANNAN LBRIN NASAN BA ZAKU BANI KUNYA BA,INA MATUK'AR ALFAHARI DAKU AKODAYAUSHE NI TAKUCE KU NAWA NE,LOVE U FISABILILLAH_

Last free pages.

Ga duk wanda ke buk'atar sa complete zai iya biyan 500 ya samu nashi.

3150952555
First Bank
Aisha Abubakar

My phone no. 09034722970 itace no. Dinda zaka turo kati in kati ne zaka turo,pls banda kira only chat inka turo kudinka ka min mgn ta WHATS APP saina saka grp.

Ngd sosae masoyana Ina alfahari daku sai najiku.

Mom muhseen&Asaad

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Chapter 37 · 0% Book details