← Book details Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 38

Sashe 36

Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina fita suma Suka biyoni muka nufi wajen mota, Rukee ke cewa "ki daina irin abunda kike,koma mi kikeji a ranki game dashi ki ringa dannewa,Rohee baki yana yanka wuya kuma watarana baka san illar da maganar ka zatayi ma ba,in kikai shiru ma ya isa ansan an b'ata miki ba dole saikin yi rashin kunya da rashin kirki ba,Abunda kikai baki kyauta ba koba komi Mama na wajen........Rukee ya isan haka don Allah,na riga na gama gane kin daina kishin iyayen mu kin daina kishin kanki balle ni,wad'anan mutanan da suka hana iyayen mu mata zaman lafiya da mazajen su kikeso na risina mawa?kina gani saboda su da Mufeey tsakanina da Abba ya lalace ko gaisuwata sama-sama yake ansawa,aka mari uwata akansu aka saketa duk kina nufin na risina na nuna rashin damuwata kenan?"
Iska naja inajin tsananin takaicin hakan, ta ce "ni ban daina kishin su umma da Mami ba,haka kema ban daina kishinki ba nima kuma haka,saidai duk Abunda zamuyi da zaija ran iyayenmu ya b'aci suyi fushi damu muyi kokarin kiyayewa,kina da tabbuna wajen Abba Rohee kiyi fatan kirabu lafiya dashi,kina sane da cewar irin illar sab'ama iyaye kin sani sarai amma kike take sanin kina yin son ranki,ni nasan wallahi hadda zugar Yah Rafeeq sannan ki sassauta k'iyayyarki ga Yah Ramadan saboda watarana"
Jikina ya d'anyi sanyi bance mata komi ba mukai ta jiran Abban ya dawo daga cikin asibitin muka dawo gida,washe gari muka shiga camping cikin sa'a da nasara.

********

Akwana a tashi ba wuya wajen ubangiji har gashi mun shiga camping mun fito cikin yar dar Allah,wasu kwanaki muka soma zuwa wajen service dinmu nan cikin garin Abuja, har sannan dai ba wata rigima da ta sake tashi a gidan,amma kuma shirin dai da ake nema ayi babushi har hanxun,kawunan sunk'i haduwa waje guda jiya iyau saidai hkr kurin dasu Abba keyi da iyayen mu mata,don matsalar duk ta tare a wajensu,kwatsam wata ranar lahadi ba aiki da safe muna gyaran dakinmu nidai Rukee,ita tana gugar kayanmu ni ina sanitation na dakin,saiga Umma ta shigo dakin da sallama muka ansa mata, tayi tsaye tana kallona sai na aje tsintsiyar hannuna na ce "umma lafiya"
D'an murmushi tayi tace "kizo Abbanku na kiranki"
Gabana saida ya fad'i don yanzu kiran Abba tada mun hankali yake,tunda muka daina d'asawa dashi shikenan ya zamar mun dodo........"Ke dallah can ba laifi kikai ba"
Naja ajiyar zuciya nabita muka tafi,Ina shiga Falon idanun su sukai mun caaa har naji na sake shiga rud'u,Abba habibu da Abba Nura sai shi Abbanmu da Yah Rafeeq,na samu waje can na zauna Ina gaidasu cikin jam'i

Abba Habibu ne ya fara mun magana "Y'ata Rohee natsu kinji ba wani babban abu bane,mun kiraku ne don muji halin da kuke ciki keda d'an uwanki Rafeeq,saboda a halin yanzu wani malamin ku a makaranta yazo neman aurenki ga mahaifinki,to sanin cewar akwai d'an uwanki dake sonki yasan ya mukace ya d'an jira tukunna, idan mukaji ta bakin ku cewar har yanzu kuna kan bakan ku na son juna shikenan,sai a bashi hakuri ku kuma mu tsayar da lokacin da ya kamata,kafin kizo munji ta bakin Yayanki cewar yana sonki kuma shirye yake da Auren ki,yanzu ke muke jira?"

Kunya ta lillib'eni,na sadda kaina k'asa y'an yatsuna kurin nake wasa dasu na rasa abun cewa,sunyi mun yawa kunyar ansa musu nake,ganin hakan sai Abban ya ce "wannan shirun naki yana nufin kin amunce da d'an uwanki kenan,to ai Alhamdulillah mu daman haka muke so *GIDA BATA K'OSHI BA AI BA ANKAI DAWA BA* Ku tashi kuje Allah yai muku albarka,zamuje ma Hajja da wannan labarin mai dad'i don daman munfi son muji ta bakin Ku kafin taji komi wajenmu,Allah ya tabbatar da alkairi ya kuma nuna mana lokacin auren da rai da lafiya"

Mom muhseen&Assad

_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_

*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*

By
Mom muhsen&
Asaad.

Wattpad name
Humaira3461.

🅿️.....26

LAST FREE PAGE.......👏🏻

*BAYAN KWANA BIYU*

Daga Ranar da akai mana wannan kiran nida Yah Rafeeq wani irin farin ciki ya wanzu a cikin zukatanmu,domin kuwa kallon kanmu muke matsayin ango da amarya don munyi imanin cewar Hajja itace mutum ta farko da wannan had'in zaiyi ma dad'i nesa ba kusa ba,tunda a kullin ba abunda take buri illa auren zumunci tsakanin mu da y'an uwan mu maza,saboda a ganinta hakan zai taimaka wajen gyaruwar zumuncin dake neman b'alb'alcewa,nidashi mun saki jiki sosae kaunar mu muke sha kamar an riga an saka mana rana,Sau tari Rukee kan ce mun "Ki ringa sassauta soyayyar nan Rohee,ance in zakai so kayi shi sai-sa,sai sa haka nan in zakai k'i kayisa shima sama-sama,saboda baka san abunda Allah zai nan gaba ba,shiyasa zakiga ko akan Yah Ramadan Ina miki mgn ki sassauta,ba dan cewar nima baya bani haushin ba Aa ina dai dannema raina ne kurin,to shima Yah Rafeeq d'in ki sassauta hakanan..........kasa danne bacin raina nayi nace mata "inajin raina yana b'aci sosae idan kina nuna mun kamar wani abu marar kyau zai faru dani akan kaunar da nake ma d'an uwanki,miyasa bakya kyautata zato akodayaushe tsakanina dashi Rukee?miyasa bakin ki baya fadar kalmar da zanji dad'i tsakanina da Yah Rafeeq,?kamar ba d'an uwanki ciki guda ba?"

Girgiza Kai tayi tana cewa, "wallahi kaunar da nake miki ce tasanya nake jiye miki gaba,namiji ko ya kake dashi anso ka ringa jan ajinka saboda watarana,amma kiyi hkr tunda mgnta tana b'ata miki rai,banyi da wata manufa ba kuma ko kusa bana k'inki dashi,hasalima Ina matuk'ar farin ciki da hakan kiyi hkr bazan sake miki mgnr ba"

Nafi kowa sanin Rukee,kuma nafi kowa sanin cewar tana kaunata duk abunda zai cutar dani bata kaunarsa,kuma zatai bakin iyawarta ta shigar mun fad'an,hakan danai tunani sai jikina yai sanyi sosae,na iso inda take na rungumeta jikina sosae ina cewa cikin sanyin murya, "Kiyi hkr Rukee wlh son da nake ma Yah rafeeq yasa bana iya jurar a kushe soyayyar mu,ciwo abun kemun amma na fahimce ki kuma zanyi kokari in gyara"
Shikenan muka dai-daita bamu yarda wani abu yajamu ga doguwar gaba muna kokarin kiyaye hakan.
Bamu sake ji daga su Abba ba,muna dai saurarensu.

Yah Ramadan saida yai kusan kwana biyar asibiti kafin aka sallamosa,mudai daga ranar bamu sake zuwa ba har ya dawo gida,Ko agidan ma bazuwa bangaren nasu muke ba inba abinci za'aci ba,saifa in munga Abba na gari muje mu gaida Abba Habibun shikenan,ko mamar bama zuwa mu gaida inba suna tare ba.

***********

*💥TUSHEN K'ADDARATA*💥

Abba Habibu,Abba Nura,Abbanmu su duka sun zagaye Hajja a falon ta sunzo da niyyar bayanin Auren Rohee da Rafeeq bayan sun gama dukkan bayanin da suke son yi mata, ta gama nazartar su da fahimtar dukkan abunda sukazo domin sa,tayi shiruuu na wajen minty ashirin da d'oriya batai magana ba,su kuma sukai zuru suna kallonta yayin da dan danan suka ga wani yana yi akan fuskarta, su duka ba wanda ya iya tambayarta dalilin shiga wannan yana yin da take ciki,sai Abba Habibu ne yayi jarumtar yin magana cikin tausasa halshen sa,saboda yaga wani abu dayake neman rikirkita masa natsuwa a tattare da Hajja, "Hajja munzo da batu mai muhimmancin da muka d'auka cewar zaki fi kowa farin ciki da hakan,amma kuma daga yana yin fuskar ki ya nuna mana kamar bakiyi na'am da zancen ba,ko kina ganin akwai wata matsala da kika hango mu bamu hangeta ba,don Allah ki magantu ko zamu fita daga rud'un da muke ciki"

Shirun ta sake wanzuwa acikin falon Hajja,sai karar Ac da k'yaftawar agogo kurin kakeji yana tashi a falon,har sun riga sun sare da yadda Hajja tayi shiru ta kasa magana,kuma fuskar ta babu wani alamar lamarin yai mata dad'i.........kwatsam suka tsinci maganarta tana cewa cikin kakkausan lafazi,

*"AURE TSAKANIN RAFEEQ DA ROHEE BAZAI TAB'A YUWUWA BA"*

kamar saukar aradu haka sukaji maganar ta ratsa kunnuwan su,cikin razani da mamaki da neman ba'asin wannan maganar mai matukar rikitarwa suke kallonta, ta jinjina kanta cikin sake basu tabbaci mai kyau,

"Wannan maganar haka take,kuma babu abunda zai iya canza ta daga yanzu daga gobe daganan har abadan,"

Wata irin zuface ta keto masu su dukan su,saboda abun yai mugun zuwar musu a bazata wannan shine ANA WATA GA WATA, ana zaton wuta a mak'era gata a masak'a,duk suka sauko k'asa cikin nuna k'ask'antar da kansu da neman alfarma da magiya, Abba Nura ne ya fara magana cikin k'ask'antar da kanshi yake cewa, "Hajja kiyi ma Allah da manzon sa,ki fidda mu daga cikin wannan rud'anin kiyi mana bayanin da zamu iya fahimtar wannan dalilin naki,wallahi kin jefamu cikin wani irin tunani mai rikitarwa"

Abba Taheer ya ansa da cewar "Wallahi mun san kinfi mu son Auren zumuncin nan ga yaran nan,saidai bamu tunanin jin haka daga gareki ba muna bukatar karin bayani dole kina da Hujjar ki domin baki yin abu haka nan"

Abba Habibu ma yace, "Tun da har kika fad'i cewar Aure tsakanin su babu shi har Abada,wallahi Hajja cikin mu ba wanda ya isa ya bijirewa umurnin ki..........."wannan ba umurnina bane Habibu,umurnin Allah ne shine ya haramta ba ni Layla ba"

Kallon junan su suke cikin sake kullewar kai,duk sadda tayi wata maganar sai tashin hankalin su da kullewar kansu ta k'aru,shin ko dai Hajja ta fara rikicin Tsufa ne?to Amma Hajja batai kama da tsohuwar da zatai irin wannan rikicin ba,ras take cikin hankalinta babu wani rikicewa tare da ita garau take............."Ku tashi kuje idan Allah ya kaimu safe Ku tara mun kaf iyalanku na kusa dana nesa zanyi magana gaban kowa,Amma tabbas wannan Auren babu shi har Abadan,na sallameku kuna iya tashi"
Tatashi tayi cikin d'akinta tabarsu kamar masu zaman gaisuwa,kowa da tarin tunani cikin kanshi da zuciyarsa wanda yake kamar xai faso kirjinsu ya fito.

********

*RANAR DA BAZAN TAB'A MANTAWA DA ITA BA A RAYUWATA*
Chapter 36 · 0% Book details