← Book details Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 38

Sashe 32

Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya kashe wayar yasa aljihunsa, ban san sadda wani dogon tsaki ya kubce min ba,saboda haushin mufeey intana wannan zazzak'ewar akanshi wallahi bata min rai take sosae,munzo dai dai bakin get din kasuwar yaci burki,na sake jan wani tsakin na bud'e na fito ina buga k'ofar motar,ashe rigata ta datse sadda naja zan tafi naji rigar ta mak'ale daker na fizgota,saboda naja murfin naji kamar yasa lock ta ciki,Ina d'aga k'afata kenan naji an fizgoni da karfin gaske an had'a ni da jikin motar,wani rasssss kirjina ya ansa saukina wajen ba kowa saika shiga cikin get din zaka ga mutane,idon sa cikin nawa dana fiddosu waje saboda tsorata,nashi idon jajawur da bacin rai nima raina ya b'acin,yadda ya damke min hannu da karfi yasa na fizga da karfi Ina cewa "Dalla malan sakeni..........takalmina mai tsini ya tusgud'e na tafi zan kifa a k'asa,yai saurin saka hannunsa ta wajen k'uguna ya taroni,kamar jira ruwan sama keyi aiko jikake shaaaaaaaaa ya balle da d'an karfi,dagani har shi kamar wad'anda aka d'aure mun daskare a wajen,sai ya zama kamar yana rungume dani ne,hannunsa ya zagayo dashi ta bayana saman k'uguna ya rik'eni,nima hannuwana suna bisan wuyansa na rik'esa gam sadda nazo fad'uwa,tun ina kalon idonsa da suka washe daga jaan bacin rai,har ruwan yasa dola na sauke idona k'asa na runtse su,cikin sand'o na sauke hannuwana dake bisa wuyansa,jikina yana yar rawa saboda abune da bai tab'a faruwa ba sai saudaya radda na fad'i a basketball,amma wannan karon kusancin yafi yawa sosai nake jikinsa har inajin sautin bugun zuciyarsa a kirjina da muka manne,sannan hancina yana shak'o wani sassanyen kamshi daddad'an kamshi mai ratsa hanci da kwalwa daga jikinsa,ruwan nan ya mana shar kaff har d'iga muke kayanmu amma motsin kirki ba wanda ya iyayi acikin mu,zuciyata nima kamar zata fashe saboda yadda take bugawa sosae,bazan iya gane tsawon lokacin da muka d'auka a hakan ba,har ruwan ya rage karfe sosae.
Sai lokacin naji ya d'an saki jikina kamar jira nake nai sauri ida fita daga jikinsa,santsin kasar wajen ya kwasheni na tafi zanci k'asa da sauri ya sake rik'oni again muka sake had'ewa waje guda,fuskata cikin kirjinsa Ina sauke numfashi,gaba d'aya na rikice ma hankalina ya tashi natsuwa na neman gagarata,muna a hakan ya bud'e motar ya zaunar dani sannan ya rufe jikina sharkaf har pant dina kanshi a jik'e yake,dunkulewa nai waje guda Ina kermar sanyi nama rasa wane kalar tunani zanyi,haushin kaina zanji komi?
"Ina list d'in abun da za'a siyo"
Naji sassanyar muryar sa yana tambayata,ai bazan ma iya gane ina na sake shi ba,girgiza kaina nayi kawae bance komi ba,sai ya zagayo inda nake ya bud'e k'ofar yana dubawa,kaina na cikin guiwata shi kuma ya duk'o ya dauko takaddar dake wajen k'afata,jin sa a wurin nai saurin ciro kaina dai-dai shima ya sawo kai a wurin,fuskokin mu suka had'u har hancin mu yana haduwa dana juna........YA SALAM!!!

Abunda ya bak'uncin ilahirin jikina tunda nazo duniya ban tab'a jinsa ba,a zabure naja baya da kaina shi kuma cikin sanyin jiki ya dauki takaddar ya fita, bansan ya akai ba nadai ga ya shigo ya kwantar da kujerar sa ya dora hannunsa bisa fuskarsa,ban san hawaye sun balle mun ba na rashin abunyi,nidai nasan harga Allah bada niyyar kaina hakan ke faruwa ba, shima kuma nayi imanin baida wata manufa akaina,to miyasa hakan ke faruwa?ban sani ba,ban San ansar ba shashshekar kukana ta fito fili har yaji da kamar bazai tanka ba,sai zuwa can naji ya ce mun "Sanyi kikeji ne?"
Ba tare daya cire hannun sa daga fuskar ba,banza nayi masa tunda banda abun cewa,daga inda yake ya sanya hannu ya kunna heater yadda zamuji gumi don sosai nakejin sanyin.
Bayan wani lokaci akai knocking ta glass ya tashi ya bud'e glasse din wani mutum ne yake ce masa, "an had'a komi yallab'ai"
Jinjina Kai yayi yace "bud'e kaya ka sanya"
Ya bude bayan motar yana loda kayan,sannan ya ce an gama ya biya kudin sannan yace "please kawo mun kwa-kwa da dabino"
"To yallab'ai"
Har mutumin ya juya sai ya tsayar dashi,yana jiyowa kaina yace "ba kyason komi?"

Mamaki ma tambayar ta bani,ce masa nai inason wani abun? Amma banyi magana ba na girgiza kai alamar aa, sai yace dashi "ka had'o da inibi please" sannan mutumin ya tafi,haushi duk ya isan nama rasa abunyi nace, ciki-ciki "Ni bana shan inibi ai"

Ya koma ya kwanta yana ce mun, "na sani ai,daman kuma ba naki bane mufeeda na siya mawa"

Yadda naji haushin mgnr ban San sadda naja wani tsakin ba mai tsawo tsuuuuuuu,a zabure ya taso kamar wani kubuwa "keeeee!"

Na jiyo gabana na fad'uwa,Idona cikin nashi yai mun kuriiii nima ina kallon sa, "idan Kika sake mun tsaki wallahi sai kin gane baki da wayau"
Na juyar dakaina Ina murgud'a baki kawae,.........yai k'uta yana cewa, "sai karyar iskanci"

Ina gunguni nace, ciki-ciki "wallahi ni ba yar iska bace.........mikika ce?zagina kike?" Ya taso da sauri yana kawo hannu kamar zai buge mun baki,nai saurin ja baya ina turo baki, "Wlh ni ban zageka ba,cewa nai niba yar iska bace........idanunsa a warwaje yake kallona ni kuma na makale jikin k'ofar kamar zan shige cikinta, kanshi ya nuna yana wani kala da idonsa "nine d'an iskan kenan.........Aa wallahi ba haka nake nufi ba nidae" ya sake yin k'uta yana koma wa ya kwanta, har sannan ruwa ake sosae ya dawo kan dazun daya dan rage,munyi shiruu bakajin komi sai karar ruwa zuciyata ansawa kawae take,Allah yasa ma na baro wayata gida da kiran da yah Rafeeq zai mun yawane dashi,kiran salla da akai yasa na jiyo ina kallon sa shima a takuren yake alamun sanyin yakeji,don ma heater daya kunna aida mun gane kurenmu......."ba zamu tafi gida ba?"

"Anan zamu dawwama,har saikin gaya mun waye d'an iskan naki"

"Ya salam,wallahi ba da kai nake ba, ka yarda wallahi bance ma haka ba"

Banza yai ya kyaleni har sannan ruwa ake daman ankwana biyu ba ayi ba zafi ya addabemu, "Wallahi sanyin kayan nan y daman,inaso na canza ka tada motar mutafi.........."kizo kija to,ni kam yanzu bazan iya tuki ba ana ruwan nan"

"Ni zanyi,"

Ya jiyo yana kallona cikin hasken kwan cikin motar,duk na marairaice na ce "ehy zan ja motar wlh na matsu naje na canjaa"
Kamar bazai daina kallona ba,ya wani lumshe idonsa ya d'age kafadar sa yace "bismillah bude ki zagayo"

"Ruwan dukana zai sakeyi fa"

Wani kalar kallo yai mun yana cewa "ohk,lemme exchange"

Ya mik'o mun hannunsa in kama in taso daga inda nake zuwa mazauninsa, (uhmmm wadannan sun raina mutane😂🫣)kasa musu nayi da dai in fita ruwan ya sake dukana, rike hannunsa gam nayi na sanyo kafata daya inda tashi take,na dafa kujerar da d'ayan hannun nawa sai ya zamana kamar nai masa rumfa,wajen in ida sanya dayar kafar ne kawae naji na fad'a masa a rashin sani,daman kujerar kwance take sai kawae naji mun tafi gaba d'aya na fada bisa kirjinsa shi kuma bayan sa ya bugu da kujerar har saida yace "Ausshhh"

Mom muhseen&Asaad
_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_

*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*

By
Mom muhsen&
Asaad.

Wattpad name
Humaira3461.

🅿️.....23

Fuskata na bisan dokin wuyansa,wanda naji zafi kamar alamun baida lafiya,wata irin kunya da ban tab'aji ba ta lullun'eni,motsin kirki na kasayi kamar yadda shima ya kasa motsawa daga yadda yake,Hannuwansa duka biyun suna bisa bayana,ban san ma ta yadda zan sauka ajikinsa ba,ban san iyakar lokacin da muka dauka a haka ba,saidai naji mgnrsa a kunnena cikin sanyin muryarsa da ta kara zama cool, "*LAYLA please a d'agani haka nan ko*"

Wani iri naji kamar in b'ace daga inda nake sai kawae na sanya kukan rashin abunyi,da borin kunya don wallahi sosai naji kunya dubeni duk irin k'iyayyar da nake masa,da k'yank'yamin da nake ji akansa amma gani d'are-d'are ajikinsa kamar zan shiga cikinsa,kasa motsi nai duk haushi ya kamani.
Ganin na kasa motsin kirki sai ya d'ago kujerar daga kwantar da itan da yai dazun,d'aff ya cironi ya maida ni mazauni na,zuwa sannan yayyafi ne akeyi ruwan ya rage sosai,tada motar yayi cikin sanyin jiki ya fara sarrafa sikiyarin har muka bar wajen,muka sake zama kurame sosae ko motsin kirki banyi ba,na dunkule kamar curin tunkuza ga wani zazzabi naji ya sauko mun,sannan ba abunda nakeji illa wannan sassanyan kamshin nasa har cikin bakina,ilahirin jikina shine nakeji,zuciyata kamar zata fad'o k'asa so nake na bud'e ido na ganni gidama gaba d'aya ba gidan Anty sha'awa ba,hon din da naji yayi anbud'e get yasa na d'ago kaina har mun iso gidan Antin,magadi yazo zai bud'e ya kirasa yazo
Yace"don Allah ka shirgar musu da kayan nan,kace ina sauri na wuce zan sauke wannan yarinyar gida bata lfy"
Mamaki ya kasheni ya akai yasan banda lfyr?kamar ya shiga raina ya gano cewar banda lafiyar, daker na ciro kaina nace ma maigadin "don Allah ka ce Rukee ta baka wayata ta kawo mun" cikin girmamawa ya ansa da "to hajiya"
Ya kwashe kayan yai cikin gidan dasu,yana shigewa yaja motar yabar kofar gidan,jiyowa nai ina cewa "wayata fa?"
Uffan baice mun ba sai na kama kaina nima,in miskilanci ne gidan ka tarar mun kusa isa gida aka kirasa, yai picking yana sa wayar speaker, yanzun ma Mufeey ce take cewa "Favorite lafiya baku iso ba?"
Muryar sa ta d'an dishe kad'an yace "Bakiga anyi ruwa ba,shine ya tsayar dani sakon ki na nan cikin kayayyakin kiduba"
Cikin murna ta ce "thank you very much Favorite,to ina sister ka barota?"
Kai tsaye ya ansa da cewar "gida"
"Ohk sai munyi mgn bye"
Ya kashe wayar yasa aljihunsa,yana yinsa ya nuna shima baida lafiyar kamar ma yafini jinjiki mgnr daker yake yinta,mun iso gida cikin yardar Allah na bude na fito wani sanyi ya ratsani tsikar jikina tatashi,daker da daker nake tafiya har na shige k'ofar entrance d'in.
Falon mu ba kowa haka main falon gidan,alamun dai duk suna cikin dakunan su.

********

"Ramadan Ina kashiga haka?kar dai duk ruwan nan kanka ya k'are subhanallahi"
Cewar Mama bayan shigowar sa bangaren su ya zube cikin kujera yana rawar sanyi har bai jin abunda take fad'a sosae, daker yai mgn "Mmn kausar ta aikeni kasuwa nida waccen yarinyar to a can ruwan ya iske mu"
Chapter 32 · 0% Book details