Sashe 25
Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bai tsaya bashi wata damar zillewa ba ya ce, "Anshi key din motar tun dazu na dawo masallaci na shiga, kaje ka sauke Rohee wajen partyn nan..........daskarewa yai dajin batun Abban,amma sai bai ce komi ba ya ansa key din shi Ku ma Abban ya wuce ciki, dagowa nai na kallai yayin da shima ni yake kallo,fuskar na ba fara'a kamar kullin..........."ni drivern ki ne?"
Na ya mutsa fuska bance komi ba,don burina nidai ya kaini bazan rigima dashi ba yau duk tsiyarsa, ya waiga yaga Abba ya shige,sannan ya tako kad'an gabana "ki nemi wanda zai kaiki"
Cikin sauri na d'ago manyan idanuna ma sha Allah na zuba mashi su,nai narai-narai zan kuka na d'aga murya zan kwala kiran Abba, na ce "Abba.........cikin yan seconds naji hannun sa bakina,da muryar da tunda nazo duniya ban san shi da ita ba yake cewa, "shut up,are u mad?"
Ganin yadda na zuba mai ido yasa yai saurin dauke hannun sa ya matsa daga inda yake, yaja tsaki yai hanyar wajen mafarin na sauke ajiyar zuciya nabi bayan sa, mamaki nata kamani ashe ya iya gayu amma yake zama da k'azanta,yanzu inkaji yadda yake k'amshi sai kai mamaki kuma k'amshin mai dad'i mai shiga rai, na tab'e baki a fili na ce "duk da haka bai kama k'afar Yah Rafeeq ba,"
Sadda na isa har ya shiga motar kamar munafuka na bude gaban na zauna,ina ta duba wayata lokaci nata tafiya yak'i tada motar, har hakurina ya kare na ce "kaji lokacin nata tafiya"
Kamar da dutsi nake magana,yai banza dani na danne fushina ban sake tanka masa ba,sai da ya mula ya mulmule sannan ya kunna motar muka dauki hanya, kin yin gudu yai sai ya ringa nawa kamar baida lafiya,a lalace yake sarrafa sikiyarin motar had'iyar bakin cikin kawai nake,har Allah ya kawo mu Hall d'in,saidai muna tsayawa na tuna gate pass d'ina........."innalillahi na shiga uku,don Allah ka maidani na dauko gate pass dina,wallahi ba za a barni na shiga ba in babu shi"
Wani lalataccen kallo ya watsa mun,ya kashe motar ya kwantar da sit yai kwanciyar sa,tun ina iya sarrafa kaina har na kasa na soma hasala,amma na danne zafin raina ina rok'onsa.........."karen gidan ku kika maidani?karki cika mun kunne pls"
Abunda yace dani kenan,nai shiru ina kai kawon numfashi sai na ja k'ofar in fita ko zan samu nasarar shiga da rok'onsu,sai me?.........ya gark'ameta na jiyo ina kallon sa idona ya cika da hawaye,ba kasafai nake kuka ba sai abu ya kai kololuwar bata mun rai,..........."wai miyasa baka kaunar farin ciki na,yanzu miye na rufe kofar"
Kamar bazai tanka ba har na juyar dakaina gefe naji ya ce, "miye amfanin fitar tunda baki da gate pass din"
Ban sake tanka masa ba nai shiru inata share hawayena akai-akai,bakin ciki kam ai ina shan shi akan wannan mutumin,baifi saura yan mintoci ba a tashi naji ya fita amotar,can wajen masu gadi yaje bansan meyaje yai ba zuwa can ya dawo ya ce "kije kishiga"
Kallon sa nai kurin kullin abubuwan sa mamaki suke ban,bai dubeni ba ya ce "kifita nace,ni ina da wajen zuwa"
"Ka mai dani gida"
Na fad'a cikin dacin rai wani k'ullutun bakin ciki na mamayata a zuciyata, had'iyar kuka kurin nake ban cika son nayi kuka gabansa ba,rainin zai yawa wanda zai mun...........saboda kin daukan d'an iska,kin sanya an tadoni ina hutawa ta,na kawo ki wuri sanan kice baki shiga in maidaki,watau ga drivern ki ko?"
Nai shiru saboda ina bud'e bakina kuka zan saki,kirjina ke kai kawo kurin..........."darajar ubana kikaci in bacin haka" yaja k'uta kawai bai sake magana ba bai tada motar ba saida yaga an fara fitowa daga cikin Hall d'in taron,sannan ya gyara kujerar sa ya ja muka bar wurin,kamar jira kukana yake mubar wajen ya kubce mun mai rikirkita zuciya,zallar bakin ciki ne kurin cikin sa har jijjiga nake saboda yadda kukan ya taho mun,tafukan hannuna na saka fuskata aciki ina kukan,tun yana yin kamar baiji har kukan ya ishe shi yaja burki gefen titi,wanda ba mota ko d'aya dake wucewa kuma akwai duhu,hasken fitilar kotar kad'ai ne sai wanda ya kunna na cikin motar,jiyowa yai yana kallonta yajingina bayan sa da allon kujerar, yai shiru kurin.
Ban fasa kukan ba saima cigaba da nayi don ji nake inba kukan nayi bazan huce haushin dake dankare a cikin kirjina ba,Naji dai motar ta tsaya amma ban ciro kaina daga cikin tafukan hannuna ba,..........*"LAYLA PLEASE"*
sautin ya ratsa kunnena sosai har ya sanya mun wani irin duka a kirjina,diff naji kukan ya tsaya mun don tsananin mamaki da rud'anin abunda naji,tunda nake rayuwata ban tab'ajin bakin sa ya ambaci sunana ba,sannan bacin sunan yadda ya ambace shi shine ya kid'imani,har hakan ya tilasta mun d'ago fuskata da tayi jaga-jaga da hawaye idanuna sun canza launin su saboda kuka na zuba mashi su,ido cikin ido muka tsare juna da kallo,gabana wani irin mugun fad'uwa naji yana yi,nai saurin kawar da kaina na rasa abunyi,na juyar da fuskata wajen window sai lokacin na ga inda muke.
Shiru ya ratsa motar kamar babu bil adama aciki,natsuwa ta fara shigata na duba wayata naga network ya dauke d'af,kuma lokaci yaja sosai na had'iye wani miyau na ce, cikin sanyin "it's almost eleven thirty yanzu,.........zaki iya jan motar?"
Saurin kallon sa nayi da mamaki,ba dan ban iya na kawai dai miyasa zaice mun haka?kuma Abba ya hanani tuki tunda na tab'a buge wani mai adaidaita, "Aa bazan iya ba"
Na sake juyar da kaina kurin,Inajin mugun son barin wajen bama wajen ba motar nake so inga bana ciki,......."ki gyara kujerar ki kwanta don ban san ranar barin mu nan ba"
A zabure na jiyo ina kallon sa, ko kadan na tsani mu had'a ido idanuwan sa wasu irin idanuwa ne, sai na dauke idona daga cikin nashi kamar zan sake kecewa da kukan na ce, "don Allah mu tafi gida,inma horani zakai da haka don Allah kayakuri nidai mutafi"
Shiru yai kuma inajin kallona yake ta faman yi,kafin ya ce "to ai bazan iya tuk'in bane kizo kija..........idona ya tara kwalla na ce "Abba ya hanani driving"
Ya rausayar dakai yana lullumshe idonsa da sukai jaa,kamar bai da lafiyar dagaske kuma sannan ya ce cikin gajiyawa da magana, "ai yau ne kawai,kuma bazan fad'a masa ba.........Don Allah *YAH RAMDAN*"
Wani irin kallo yajiyo yana mun,mai kama da na mamaki da al'ajabi,nai saurin maida kaina k'asa ina jin nadamar fad'in sunan sa,nasan shi yake ma mamakin jinake nai mugun takura da wannan zaman,haushi ya isan kamar nayi fiffike na ganni gida,nasan bacin daukewar network da yanzu an kirani yakai sau ba iyaka.........."mika ce?"
Naji ya katseni da fad'ar haka,har sannan kallona yake ban dube sa ba na ce "ba komi"
"Ohh na dauka magana kikai sai mu tafi.........cewa nai don Allah ka tada motar"
"In Kika maimaita abunda kika ce zan tada mu tafi"
Ya juyar da fuskar sa can side d'in,na rasa yadda zanyi na goge guntun kwallata ina wasa da zoben dake sanye ga ya tsana, kirjina na kai kawo na ce,
"Don Allah YAH RAMDAN"
Jiyo da fuskar sa yayi yana zuba mun mayun idanun sa,na juyar da kaina wurin taga kurin don na tsani mu hada ido,ni na ma rasa abunda ke damun sa a yau d'in nan............"mu tafi?"
Na d'aga kai na ban dubesa ba,wani numfashi ya sauke kamar wanda yasha kuka ya k'oshi,sannan ya tada motar muka cigaba da tafiyar shiru-shiru har muka k'araso gida.
Mom Muhseen&Asaad
_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_
*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*
By
Mom muhsen&
Asaad.
Wattpad name
Humaira3461.
🅿️.....17
Gaba d'aya main falon gidan kowa na nan harda yan biki anyi jigun jigun,Abbanmu da Abba Habibu da Abba Nura duk tsaye Ummanmu kau sai share hawaye take,Mami ce ke ta lallashi da ban baki.
Rukee da Mufeey suma sai kuka suke,cak muka tsaya nida shi bakin k'ofar entrance d'in.........."Laaaa Abba gasu nan wallahi"
Cewar mufeey da muka fara had'a ido da ita, sai kowa ya mimmik'e tsaye ana ta kace na ce na tambayar mu,mun ma kasa ansawa kowa saida aka natsu Abba Habibu ya ce "Ramadan lafiya kau?ina kuka shiga har karfe shabiyu?kun san irin tashin hankalin da kuka samu ciki?"
Kallon juna mukai nidai na wuce wajen Ummanmu na kwanta cinyarta, kafin naji ya lafta k'arya karon farko da naji yai karya tunda nake agidan nan........"Abba wallahi motar ce ta tsaya mana a titi,gashi ba kowa wajen daker na isa na samo wasu suka tura mun ita inda ake gyara,kuma muna ta gwada kiran ku network ya d'auke kuyi hakuri mun saku cikin tashin hankali"
Yadda nake kallon sa galala haka naga Abban yana masa,sai ya sadda kai kurin bai sake magana ba,anan dai aka wawwatse shima ya mik'e yai hanyar bangaren su,har ya kulle ina kallon sa.
********
Washe gari Friday da yamma ranar ne xa'ai Arabian night,ana ta shige da fice ni dai ina d'aki abuna mun gama video call da Yah Rafeeq Rukee ta shigo ta ce, "ni kam tun jiya nake so muyi magana banga fuska ba,gaya mun gaskiya miya faru jiyan nan da daddare?"
Tsaki naja kurin na diro na shiga toilet na fito,sannan ne nake cewa "wallahi duk duniya ban ga d'an rainin hankali irin wancen guy d'in ba,ke ni ban ma san yana magana ba sai jiya ashe iskan cine daman sai yai zuru kamar wani kurma hmmmm kigan shi kawai wannan mutumin..........Dariya Rukee tayi ta ce "to ai ni har yanzu banji abunda ya faru ba sai bayani kike mun"
Na zauna bakin gado ina bata lbarin abunda ya faru, ta ce "uhmmm anya kuwa?"
Na kalleta cikin rashin Fahimta, "ban gane ba?"
"Aa mubar maganar yanzu ba zaki gane ba ai"
Tatashi tana cewa bari naje wajen Mami indawo,ta fice ta barni da binta da kallo ina nanata maganarta har nagaji na mik'e na fita nima.