← Book details Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 38

Sashe 11

Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga wannan ranar tsakanina da Yah Rafeeq ya kara tsananta, idan ya ganni kamar yaga kashi iskar data kaso ni baya kallo balle ya tanka mun,ni kuam ba nuna masa ban san ma yana yi ba,abu guda ke had'amu shine gaisuwa amma baya ansawa,ni kuma ban fasa gaidashi ban damu da rashin ansawar ba saboda Abba yace kar muyi gaba,kuma inaso sallata ta ansu to akan me Zan yi gaba dashi.

Muna cikin wannan yana yin Abbanmu ya dawo daga Uk,watan sa guda da sati biyu da tafiya,daddare aka had'u babban falon dake bangaren Abba Habibu,bayan anyi dinner aka taru anan ana fira hadda Hajja kuwa,anata raha dasu Abban damu amma bamai sanya MAMa da Ahalinta,inaba su Abban ba da Hajja,itace ma keta janta da fira sai ta saki jiki suna yi tare,amma Mami da Ummanmu bamai ce mata ci kanki,Haka Najeeba da Yah Ramadan ba mai magana dasu inba Su Abban ba,yah Najeeb yana makatanta boadin yake a kano BUK, Abba ya dauko tsarabar kowa ya bashi da hannun sa murna kamar muyi me?saboda abunda mukace muna so ya siyo mana,sabbin abayas ne new design masu kyau hadda jikuna,ba wanda bai ba tsarabar ba su Umma ba yadda suka iya don hadda su MAMA ya yo mawa,don ta Abba Habibu tafi ta kowa yawa.

Ya ce"baka gajiya da d'awainiya Taheer,kaida kaje aiki kuma ka b'ige da kashe kud'ad'e har haka"

Abbanmu ya ce,"Haba Yaya!ina abun yake anan,kuma ai kunfi karfin komi a wajena don nai maku wannan hidimar wallahi ba komi bace, ba zan iya biyanka abunda kai mana ba nida Yah Nura (Abban su Rukee kenan)"

"Shikenan Allah yakara bud'i da arziki,ya kuma kara lafiya"

Kowa ya ansa da amin,Abban su Rukee ya ce "yawwa gara da Allah yasa na tuna,saida na ganku gaba d'aya sannan abun ya fad'o mun arai,kai Rafeeq rannan da zaka kai su Roohe makaranta nace yo ina Ramadan d'in mikace mun a lokacin?"

Wani mugun fad'uwar gaba ta same ni,muka had'a ido da Rukee kowa cikin zullumi,shi kam ko ajikin sa ya hau bashi Ansa,

"Abba ce maka nayi ya aje aiki bai yi,key d'in ma umma yaje yaba wai aba Abba Taheer Hakuri ya aje motar"

Tsit kakejin Falon kowa da kalar tunanin sa,kafin Hajja ta katse shirun da cewa, "kar ka soma lafta masa sharri Rafeequ,na san ka nasan waye kai da shegiyar k'arya,waye bai san halin Ramadan ba,ai haka kawai bazai kawo mukulli yace bazai sake tuk'a motar ba,sai inda dalili"

Jinjina kai Abbanmu yake alamun maganar Hajja ta shigeshi,Abban su Rukee ya ce "haka maganarki take Hajja,dole ma akwai dalilin ai haka kurin Ramadan bazai wannan abun ba"

"Aa ku daina goyon bayan shi Nura,ku barshi yai magana ba lallai yana da gaskiya ba,kila rashin hakuri ya gwada ko?"

Kamar jira kuwa ummanmu keyi ai wannan maganar ta anshe da cewa, "gara da ka fad'a da kanka cewa rashin hakurin sa ya nuna,tunda ranar har so yai yamun rashin kunya daga na ce bazai yuwu ace sai su Roohe sun bashi hakuri ba,tunda ba zaginsa sukai ba"

D'ago kai yayi yana kallon ta da idanun sa masu kamar an zuba oil a ciki,kallon tuhuma da nuna baki da gaskiya tunda tasa ba haka ta fad'a ba.........."Ramadan"

Abba Nura ya Kira sunan sa, ya dago cikin natsuwa yana kalonsa sannan ya amsa,

"Gaya mun miya faru?..........watau baka yadda da maganata ba kenan Abban Rukee"

Umma ta katse sa fad'ar hakan, cikin tsawa Abbanmu ya ce "maijidda idan kika sake magana anan ba tare da an sanyo ki ba ranki zai mummunan b'aci wallahi"

Ranta ya b'aci ainun,ta hau huci kamar kasa magana na cinta ta kasa furta wa,don duk abunta tana tsoron fushin sa,

Hajja tayi k'uta tana cewa, "duk iskancin mutum dai akwai na sama dashi,kuma wallahi ka k'i yin abunda akeso kaga karyar iya shege"

Mami ta tab'e baki bata ce komi ba,su dukan kowa ta ciki na ciki ne kawai,Abba Nura ya sake tambayar Yah Ramadan yadda abun ya faru,

Kanshi k'asa cikin wannan munafukar muryar tashi yake cewa, "ya riga ya wuce Abba,abar duk wani tone-tone daman Abba Taheer ne ya yanke Hukuncin cewa bazan sake kaisu Ruk'ayya school ba saboda sunyi laifi yace har sai sun bada hkr,to shine dai kamar abun baima Umma dad'i ba ta wasu maganganu da raina ya sosu har na gaza hakuri na aje mata key d'in nace taba Abba hkr ga key d'in motarsa nan"

Abba Habibu ya ce "kaji ko?kaji dai ai nagaya maku rashin hakuri ya nuna,miye anan to har da zaka aje mukulli?koma miye ta fad'a ai tana sama da kai...........yi hakuri Yaya na katse ka,amma Ramadan bai laifi ba anan duk da bai fad'i maganganun da tayi har ya hasala shi ba,nasan wallahi ba kananun maganganu bane zasu sa ya hasala,ai duk mai zuciya ba zai juri a wulakanta shi ba,kuma ni ya mun dai-dai wallahi sannan hallau hukuncina akan su Roohe yana nan daram,wallahi muddin basu bashi hkr ya ya hakura ba,daga nan har su kammala secondary d'insu a k'afa za suje,in ba zasuje a k'afa ba kuma saidai su fasa zuwa makarantar"

"Kash!ban so kai rantse ba, Taheer kullin ina gaya maka su Roohe yara ne,kwatanci da nasiha suke buk'ata ba zafin rai ba,kuma Ramadan yayansu ne da baka shiga cikin maganar nan ba,nasan ma shi bai k'ullace su ba kaine ka zafafa abun.........ai da yake kaine zai yadda,in wani ne ya isa ya furta cewa laifin bai kai laifi ba"

Mami ta furta cikin fushi sosai,wani kallo da Abba Nura ya auna mata saida tayi dana sanin maganar da tayi, a kausashe fiye da yadda Abbanmu yayi yake ce mata, "waya sanyo ki anan?Safiya ki fita idona wallahi na kusa sallamarki saboda wannan d'abi'ar"

"Yanzu Abban Rukee ni zaka ce zaka sallama akan..........idan kika sa ke kika sake wata magana anan na rantse da Allah saikin je gidanku"

Ya sake fad'a cikin tsananin fushi wanda muka jima bamuga irin sa tattare dashi ba, Abba Habibu ya ce "Auzubillahi minna shaid'anir rajim,Nura miye haka?miyai zafi karka soma karka sake furta mummunan kalami irin wannan,agaban yaran zaka ringa wannan maganar"

Ransa sosai ya b'aci har Huci yake yake cewa, "saboda raini da iskanci zata sanya baki kana magana yaya?wane irin abune suke son yi haka?kullin basa son a zauna lafiya Maijidda da Safiya,wallahi yaya duk wacce zata raina ka ta nemi wulakanta ka ba dai agidan nan ba,don haka in ana son zaman lafiya a girmamaka akuma mutuntaka,wannan shine"

Jinjina kai kurin Abbanmu keyi,alamun hakaan yai masa dai-dai,Hajja ta ce "Allah yai maku albarka,ashe dai kun cika y'an halak wad'anda basa mance alkairi,ina goyon bayanku akan wannan hukuncin duk wacce ta nemi raina HABIBU ta wulakanta shi babu girmamawa wallahi saitabar gidan nan,don da bazar Habibun kuke taka rawa,in bacin Habibun bana jin d'ayan ku zata iya kallon Nura ko Taheer tace tana so zata aureshi,don haka duk wacce bata kiyaye ba k'ofa abud'e take"

Hankulan mu sunyi tashin gauron zabi,don irin haka bata cika faruwa ba mudai bamu saba gani ba,yawan cinmu kuka muke Rukee ta rarrafa gaban Yah Ramadan tana cewa "Don girman Allah Yah Ramadan ka ya kuri,ba zamu sake ba in sha Allahu"

Tana ta kuka take maganar, kamar bazai magana ba ya ce "ya wuce Ruk'ayya na yafe miki"

Wani abune ya k'ulle mun ga mak'oshi,kenan ni ma saina bashi hkr wata tsanarsa ta dirar mun a zuciyata,saboda duk shine ummul aba isin komi har ake kirarin za'a kora uwayen mu gidajen su saboda su,naji duk duniya ba wad'anda na tsana sama dasu Abba Habibu da iyalin sa.......kallon da Abba ke mun yasa na tashi naje daga kusa dashi muryata da kuka na ce, "I'm sorry"

A ginshire ya ansa da cewa, "it's ok"

Sallamarmu akai su iyayen suka zauna tattaunawa,har iyayen mata muka fito tare dasu,muna fitowa umma ta fashe da kuka gabanmu wanda ya tada mana hankali, ta ce mana "wallahi duk wanda yai huld'd'a da iyalin Habibu ban yafe masa ba nono na daya sha"

Ta shige dakinta Mami kam ta kasa magana,sai hawa numfashin ta yake Anti sha'awa ta jata suka wuce bangaren su,haka muka kwana nida Rukee kowa rai babu dad'i saboda abunda ya faru.

Mom Muhseen&Asaad

_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_

*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*

By
Mom muhsen&
Asaad.

Wattpad name
Humaira3461.

🅿️.....8

Duk yadda Abba yai mana nasiha da kashe di akan su Yah Ramadan mun kasa masa biyayya muyi abunda yake so saboda furucin Umma,kuma muna kishin ta sosai don a ganin mu saboda su duk Abba ke mata abun da yake mata.

Yah Ramadan ya koma kai mu school kamar baya,amma ko hak'orin mu baya gani gaisuwar ma mun daina sadda zai fito saidai ya same mu cikin mota,Haka zamu isa baka jin ko tarin mu wanda shi banga alamar hakan yana damun sa ba,daman kuma ko da can hakan muke dashi,ummi ke zaka gaba Nida Rukee da Najeeba a baya wadda Ban san ya akai ta dawo tana binmu ba,kila Abba ne yai mata fad'a.

Wannan ya wuce ba kuma don an samu dai-daito ba anyi shiru ne saboda kashedin su Abbanmu,amma badan mun yadda zamu bisu Mama da ahalinta ba,kuma bamu da gamsashiyar hujja da zamu bada da zamu ce ba zamuyi zumunci dasu ba,kawai dai munbi ne tunda ra'a'ayin uwayenmu ne.

Hutun yah Rafeeq yazo ya k'ara ya soma shirin koma wa,har sannan babu wata alak'a mai dad'i tsakanin mu,ko zamu bi ta k'ofar allura baya tanka mun,nice dai har yau ban fasa gaidashi ba rannan dana kaishi bango ya hayyak'o mun kamar zai cinyeni d'aya, a falon mami ne muna kallo shi kuma ya dawo daga ball ya shiga yai wanka ya fito ya zauna yana cema Rukee ta kawo masa black tea, tatashi kenan daga ni sai shi na ce "Yah Rafeeq ina wuni?"

Zaka rantse ma baisan sani a wajen ba,banyi fushi ba na sake cewa "Yah Rafeeq ina fa maka magana"

Wani k'azamin kallo ya watsa min dayai mun ciwo, raina ya sosu na ce "in bacin Abba yace kar nayi gaba dakai wallah.............Roohe kike ko ubanwa?wallahi tallahi kika sake mun magana saina b'allaki,saidai Abban ya kashe ni,ke wace irin mayya ce ne iye?bana son gaisuwar dole ne?"
Chapter 11 · 0% Book details