Sashe 15
Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ai Rafeeq d'an cikin gida ne Rafeea,sannan d'an uwanta na jini yadda ba za aima Roohe Aure yanzu ba shima babu mai yi masa Aure sai ya kammala karatun sa ya samu aikin yi,kinga kenan zasu iya jiran juna har sadda ya dace suyi auren,sannan dukan su idonmu akaan su sab'anin wani na waje da ba ganin sa zamu ba musan abunda ke faruwa,ki kyalesu su so junan su ni abun yayi mun,daman kullin burin mu kenan nida Safiya Allah ya had'a kansu to gashi kuma,don haka kiyi musu Addua"
Bata ji dad'in maganar ba Amma bata isa sake cewa komi ba akai,jin hakan da umma ta fada sai bance komi ba,na tashi na bar falon na wuce dakin mu sai eleven na gama karatun,muka dasa video call dashi har Rukee ta shigo.
"Allah dai ya sassauta muku wannan k'unatar junan,haba ko gajiya bakwayi"
Harara na wurga mata na ce masa, cikin shagwab'a "Yah kayi ma qanwarka magana,nidai yanxu ba tsarar ta bace ato"
Daga inda Rukeen take ta hangame baki tana kallon,shi kuma ya ce mata "Ruk'ayya zamu yi mummunan sab'awa dake,ki fita idona Allah ko baki saj Antyn ki bace yanzu"?
Nai mata gwalo ina fari da idona, ta ce "Sorry Yah"
"Sorry for your self"
Ficewa tayi don naga ranta ya b'aci,ni kuma ba dan haka nayi ba nasan zamu shirya,na cigaba da video call d'ina sai d'ayan dare muka rabu,asuba nayi mukai waya dashi sai six muka rabu saboda shirin makaranta da zanyi,shi kuma yana da aji karfe bakwai zai test.
Sallama nayi cikin main falon na Abba Habibu,babu kowa tsit kakeji sai k'amshin turaren wuta dake tashi a boner,cikin shirina makaranta uniform ne jikina sun sha guga sosai, don kullin sai munyi wanki da guga saboda karma a raina mu,falon Mama nayi ma tsinke don nasan duk suna can,ba ka cika samun su a babban falon ba inba dare bane,har na d'ora hannuna akan k'ofar naji maganganun su,Mama ke cewa "nidai inhar na isa dake Rahma kar ki sake ki fara tunkarar wani da wannan maganar,ba ruwanki naki ido ne ance abunda ba ruwanka yafi dad'in kallo,inma kinje kin tofa wata magana takice zatai zafi,ni duk abunda zai kawi cecekuce bana so tunda dai ga yadda mutanan nan suka dauke mu"
"Yawwa Mama gara hakan,Allah ko Ammi ki fita maganar nan inba ke bama wallahi mudai nan babu mai zuwa yayi ta,har kuwa Yah Ramadan"
Cewar Najeeba da alama breakfast take a sadda take maganar, Anti Rahma ta ce "Mama ni bana son irin wannan wallahi,ai na dauka mu da muke manya mun isa mu fad'a aji?taya za'a zuba ido yarinya kamar Roohe ace tana soyayya mai zafi irin wannan,kuma ma ba aure aka tashi yi mata ba,sannan shi kanshi yaron ba aure ne ke gabansa ba karatune saiya gama ya samu aabunyi kafin nan,ai su Rafeea ne ya dace ace suna wannan soyayyar suma da sunan aure za'ai next"
"Nidai na haneki,tunda dai iyayen maza ba wanda ya sani kifita maganar nan,inma sun sani su zasu yanke hukunci bake ba"
"Shikenan Mama nayi shiru tunda bakyaso nai maganar"
Jinjina kai kurin nayi watau duk akaina ake wannan muk'abalar,uhmm walahi ko sama da k'asa zata had'e bazan rabu da Yah Rafeeq ba,naja tsaki na tura k'ofar a hankali tare da sallama,
Duk suka ansa ni kuma fuska babu walwala a cinkushe na gaida Mamar, "lafiya lau Roohe har an shirya kenan?"
"Ehy"
"Ammi ina kwana,daman Abba yace yazo mutafi time yana wuce wa"
Yadda nai maganar zaka d'auka wanda akace yazo d'in baya wajen,amma ban kalli inda yake ba balle na tanka masa,Ammin ce ta ce "lafiya lau Roohee y'an mata,amma ai naga bani ce zan kai kun ba ko?sannan kila kin san sunan sa don haka kije ki nemo shi inda yake saiki isar da sak'on naki"
Tayi maganar ne cikin sakin fuska,amma kuma cikin maganar akwai bacin rai aciki,kamar zan ja tsaki sai na fasa nai shiru bance komi ba,kuma ban tafi ba na kuma kasa yin abunda ta ce,tunda nufinta inyi masa magana da bakina..........."Kinga jeki abunki gaya nan zuwa"
"Aa MAMA karki shiga maganar nan don Allah,ki kyale ni da ita kawai"
Sai naji kwalla ta cika idona saboda bacin rai,mamar bata sake magana ba ta kyale mu wani k'ullutu yazo mun wuya bakina na rawa na ce, "Kazo ka kaimu inji Abba time na wuce wa"
Da rawar murya nayi maganar wadda kiris nake jira na fashe da kuka,kamar ma baya wajen nayi maganar mama ta sake cewa "Ramadan kanaji ai"
Uffan baice ba Ammin ce ta sake cewa, "kila ba a rad'a masa suna ba,kila duk gidan nan shine wanda baida suna............"Rahma!"
"Aa Mama ki bari kawai"
Ta sake katse mamar da fadin hakan,hawaye suka ringa silalo mun na bakin ciki labbana na rawa na ce "Yah Ramadan Abba yana........sai kuka ya kwace mun na fita aguje ina kukan sosai don bakin ciki kamar zai kasheni.
"Miyasa kike haka Mama?bayan ni duk gidan nan sama yake dasu,akan ke ba zasu bashi girma ba?sai ki bada goyon bayan a raina shi?kaima hadda kai daka zuba ido kana kyale duk ubanda yai maka iskanci,har nawa Roohee take da zata kasa risina ma Ramadan,?sanyin halinka yai yawa wallahi ni bazan dauki wannan abun ba"
Ya gama kalacin sa ya mik'e ya ce, "Na tafi Mama,daga can zan wuce wurin Abulkhair kila yau zan fara aikin nan"
Mamar ta ce, "Ma sha Allah,ubangiji yasa albarka ya kuma tsare ka ya bada sa'a sai a rik'e amana duk da bana jin ka RAMADAN saidai inyi maka tuni"
Ammin Kausar ta ce "wane aiki ne haka Ramadan?"
D'an murmushi yayi wanda yana jima wa baiyi ba,sai ya kara masa wani irin kyau sosai yace "mama tai miki bayani,Najee muje ko"
Yai gaba ita kuma ta ruga ta sanyo hijab d'in kayanta Uniform iyakar guiwar hannu take tsaya musu,saboda rigunan har guiwa suke,bayan tafiyar Ramadan Ammin kausar Ta ce "Wane irin aiki ne haka mama,ni da ina can nida Baban yara muna kokarin bud'e masa boutique yafara dashi,don har ya tura kudin kayan shi dubai"
"Nidai Addua nake masa kullin,duk inda arzikin sa yake Allah ya kaishi can,ya kuma zab'a masa mafi alkairi saboda zaman sa haka yana damuna,shiba ga koma wa makaranta ba shiba ga wani aiki ba,kina gani karatun ma daker aka gama Rahma,ki barsa yaje nan d'in in munga ana samun wani abu ba sai yatafi kebbin ba,in kuma sama-sama ne sai ya tafi Allah ya kiyaye"
Tana maganar ne duk rauni da damuwa sun bayyana tattare da ita, Ammin kanta duk damuwa ta nuna a fuskarta, taja ajiyar zuciya cikin sanyin jiki ta ce "Abun nan yana bani mamaki Mama,duk cikin gidannan bana jin ko Roohee da Rafeeq zasu nuna ma Ramadan kwalwa da basira,kina gani duk abunda ya shigema Abban yara duhu kan kasuwancin sa shine yake bude masa komi,kina gani duk semester baida c.o ba a tab'a kama shi da wani abu na rashin kokari ba,amma kuma akai ta maida shi baya,kullin abun nan yana raina"
"Bakomi Rahma,jarabawa ce kowa da kalar tashi in sha Allah komi zai wuce"
"Allah yasa,Allah ya nuna mana lokacin lafiya"
"Amin"
*********
Da Abba mukai karo na fito da gudu ina wannan kukan bakin cikin,suna tare da umma hankalin su ya tashi ya rik'oni yana tambayata ko lafiya,
"Minene Roohee?lafiyarki kalau,daga ina kike haka?kiyi shiru kimun bayani mana,ina shashsheka da jan numfashi daker nake maganar,umma ta rungumeni tana shafa kaina.
Falo muka zauna tare dasu nan main falon mu,umma ke cewa "nasha gaya maka mutanan nan ba kaunar mu suke ba,karma ace Roohee kamar su kunna wuta su jefata ciki saboda ganin yadda Allah ya kyautata halittarta,bayan haka kuma kafi sonta kafi yimata hidima fiye da kowa,shiyasa suka kafa mata k'ahon zuk'a to gaskiya ni nagaji idan ba zaka sama mana wani gidan mu koma ba ni zan tashi nida y'ata..........y'arki kika ce?ashe da ita kika zo gidan ban sani ba?"
Tai shiru bata tanka ba,nidai ina kwance kan cinyarta nai lamo,har sannan ban daina hawayen ba zuwa can ya ce mun, "Roohee"
Na tashi ina ansawa murya a shak'e, "tashi kije ki kira Rukee ku wuce mota kafin ya fito,ban son koke-koke kiyi shiru ya wuce hakanan,anshi nan kud'in break dinku yau na kara muku ma"
Ya zaro kudi ya kirga yana bani, "kiba Najeeba budu biyar,Rukee ma haka saiki dauki goma ke"
Sai naji sanyi yadda yaketa lallashina saina sauko daga fushin,nai masa godiya na tafi sannan ya koma ga ummar,fuska ba annuri ya ce "idan kika sake furta irin wadannan maganganun gaban yarinyar nan wallahi maijidda ranki zai b'aci,ashe bakida hankali ban sani ba,wace irin dauka kike so tai musu?kina so ki dakile zumunci tsakaninta dasu?nai imanin cewa izgilanci da iya shege tai musu wanda na tabbata Rahma ba zata dauki hakan ba shiyasa tai mata haka,don haka ki kiyaye kalamin ki,kuma gida ba zan nemo ba inanan tare da yan uwana har mutuwa ta rabamu,inkinji zaki zauna bismilla in kinji baki iya zama k'ofa abud'e take kije duk inda kike so,saidai bada y'ata ba wallahi"
Daidai nan muka fito ni da Rukee,tai masa godiya sannan muka wuce wajen motar,umma ranta ya b'aci sosai ta ce "ni zaka wulakanta akan yan uwanka Taheer?duk irin karamci da mutuncin da nai maka a rayuwa...........duk abunda kike k'ok'arin cewa kinyi mun baiyi rabin rabin abunda Yaya Habibu yai mana ba shida Matarsa, don haka zan iya zabarsu akanki............alamun shigowa yasa yai shiru har sadda mai shigowar yai sallama, "Ah Ramadan ne?"
Inji Abban yana sakin fuskar shi sosai, Ramadan d'in calmly ya na shafa kanshi ya risina ya gaida shi,sannan ya ce "umma ina kwana"
Tsaki taja tatashi fuuuu tabar wajen kamar kububuwa, binta sukai da kallo harta bace, Abban cikin jin kunya da takaici ya ce "kayi hak.......haba Abba miye na bani hakuri anan,bakomi ai ansaba"
Abban yaja iska ya fesar ya ce, "Allah ya kyauta"
Ramadan ya amsa da "Amin,daman yau ne zan fara zaman shagon da mukai magana dakai rannan"
Abba yad'an dafe kanshi cikin damuwa, kafin ya nisa ya ce "Kayi hakuri Ramadan,Allah shine shaida ta ina bakin kokarina akan neman aikin ka,ban tab'a neman abu mai wahala irin aikin ka ba Ramadan,damar tak'i zuwa"