← Book details Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 38

Sashe 28

Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har nakai wajen da aka tanada don jiran baki banji Alamar ya biyoni ba, koda na juya na waiga yana can cikin mota abun sa,dage kafada nayi na samu waje nai zamana ina duba time lokaci zuwa lokaci,banzo da wata shaida da zata sa ya iya ganoni cikin sauki ba,don haka idona akan hanya yake har sadda lokacin ya cika,munajin dirar jirgin dan danan naji zuciyata ta soma bugawa nai nadamar tahowa ni kadai inama Ruky ta biyoni kila da nasamu courage,ahankali mutane suka fara bayyana kowa yana zuwa don tarbo wanda yazo domin sa,zuciyata nata bugawa inata zuba ido amma banga mai kama dashi ba,har na sare da tsayuwa zan koma na zauna kawai naji anyi mun d'ass da yatsa a fuskana, a firgice na jiyo don na tsorata...........caraf mukai kyakkyawan four eyes dashi,mugun daskarewa nayi a inda nake saboda kwata-kwata ya rik'ide mun ya canza muguwar canza wa, wani irin had'ad'd'an murmushi ne yake saki mai dan karen kyau a fuskar sa, yayin da kamshin sa ya cika mun cikina tab tsabar dad'insa, kafin na dawo hayyacina naji dadda'ar muryar nan tashi ta ratsa kunnena yana fad'ar,
"Easy mana Rooh,karki cinye ni tun anan bamuje gida ba"

Muguwar kunya ta ratsani na boye fuskata cikin tafin hannuna,Ina murmushin farin ciki da annashuwa wani irin kaunar sa na sake samun waje a zuciyata, cikin shagwaba na ce masa "nifa bangane ka bane,halan ma an canza mun yayana"

Yar dariya yayi mai kyayatarwa,ya dan matso kusadani yana kallon fuskata kamar me rad'a ya ce "Nima Love d'ina kamar an canza mun ita,u look so cute and more beautiful"

Wani iri naji sosai na sadda kaina kasa murmushi sosai, na kasa cewa komi ganin duk kunya ta isheni yasa ya ce, "ke da wa kuka zo?"

Na nuna masa hanya Ina cewa, "muje ka gani da idonka ma na"

Yana jaye da trolling dinsa ni kuma na daukar masa bag d'in muna tafiya zuwa parking space din motoci,sai tsokana ta yake daman ba kuma gwanine wajen tsokanar mutane,munzo wajen motar kenan suka had'a ido da shi,kallon juna na seconds sukai ma junan su ba wanda yace ci kanka, Yah Rafeeq ya zaga ya bud'e But da kansa ya saka akwatin jikkar kuma ya saka ta a gaban motar,ya bud'e mun baya na shiga sannan shima ya shigo yana rufewa, fira ya fara mun Ina biye masa muna dariya, jira muke muji motar tatashi amma shiru har saida na ce, "lafiya kuwa?"

Kafadar sa ya dage sama alamun bai sani ba,kuma ga Yah Ramadan din nan zaune wayarsa yake dannawa, na hadiye miyau na daure na ce "Yah lafiya bamu tafi ba?"

Kusan minty uku baice komi ba,saida ya mulmule sannan ya ce "waye drivern ku?"

Sai na gane cewar zaman mu duka a bayan ya jawo rashin tafiyar,duk da raina ya sosu sai na danne na ce , "ayya to bari na dawo gaban.......rik'e mun hannu Yah Rafeeq yai dan danan har ransa ya baci gashinan a fuskar sa ma, "ba inda zaki,in bazai ja ba ya fita yatai"

Bazan so ai wanan rigimar ba daga isowar sa KO ruwa bai sha ba,na ce "miye aciki Yah Rafeeq just 40minutes ne fa sun kaimu gida kayakuri kaji"

Dole ya kyaleni na koma bayan,amma sai tsaki yake da karfi nidai kagare nake mu isa gida saboda a rabu lafiya, na rasa wace irin rashin jituwa ce tsakanin su,duk nima ba wani shiri muke ba amma takun sakar yafi karfi tsakanin su,duk yadda naso jansa da fira muje gida kiyawa yayi,dole naja bakina nai shiru abun yai mun ciwo sosai,kamar sabbin kurame haka muka iso gida.

A fusace ya buga kofar motar ya fice,ko waigena baiba abun ya sake bata mun rai watau kaina zai huce aiko wallahi zai gane kurensa,ko jikkar tasa van dauka ba nabi ta hanyar bangaren Abba Habibu na wuce dakinmu, ban samu Rukee ba nasan tana can falo ana jiran shigowar mu,gyalena ya yakice na jefar na kwanta rubda ciki bisa gadon kurin, raina inyai dubu ya baci toni miye nawa aciki?don kawai na bi hanyar da zata hana rigima da tashin hankali tsakanin su?

Ban san iya lokacin dana dauka a haka ba,sai ga Rukee ta shigo "Aaha,ke kuma nan kika yo ana ta cigiyarki?lafiyarki kalau kuwa?"

Sai kurin na sakar mata kuka saboda iyakar k'ulewa na k'ule da abunda yai min, mamaki ya kama Rukee tai saurin zama gefena tana cewa, "kece ke kuka yah Roohe?abun yai zafi haka?"

Ni kaina nayi mamaki yadda kuka ke min wahala amma yanzu abu kadan kuka, "wallahi saiya biya wannan bacin ran,duk irin kokarin da nake akansa shine zai saka mun da haka.............daidai sadda mukaji shigowar mutum,dago kan da zanyi nagansa tsaye hannuwan sa cikin aljihun jeans dinsa, saurin kawar da Kai nayi Rukee kuka tatashi ta fita, kamar daman jiran fitar ta yake yai saurin isowa bakin gadon ya zauna saman bedside, nai saurin tashi zan matsa don a hangule nake, amma sai ya rik'eni gammm yak'i sakin hannun, sai na sanya kuka mai karya zuciyar duk wani lafiyayyan namiji, dan danan ya fara rawar jiki "Rooh sorry pls I'm very sorry,I don't mean to hurt u naji ba dadi ne yadda kika biye masa akan ra'ayinsa, amma banyi don bacin ranki ba,nayi laifi kimin afuwa wallahi kukan ki yana kassarani,zan iya kamuwa da rashin lafiya please Love pls pardon me"

Shashshekar Kukana kurin nake lallashin da yake min yasa nafara sabkowa,ba abunda nake so idan Ina kuka sama da lallashi da tattausan lafaxi, haka yaita gaya min dad'ad'en kalamai har naji nad'an huce, na daina kukan sai jan majina nake, "ki yafe mun na sanya kin zubar da kwallarki akaina,"

Kaina na jinjina kurin bance komi ba, "muje ki zuba mun abunda kika hadamun,bazan iya cin komi ba in bakya gefena"

Makale kafad'ana nayi ya sassauta muryasa sosai ya ce, "Ayya my love I'm feeling hungry"

Harara na masa na dauke kaina,sai ya saki wani kafirin murmushi mai kid'imani, "naji komi zaki mun zan dauka nidai zaki tashi muje,bazan iya asarar wannan delicious d'in naki ba pls Rooh dina"

Da wadannan kalaman ya siye mun zuciya,daman kuma ban iya dogon fushi dashi ba,soyayyarsa bata barina nayi hakan.
Ana ganin mun fito tare aka saki baki don sunyi zaton tunda nayi fushi to fa bazan fito ba, dariya aka kama yi mana wai duk wanda yashiga fadanmu zaiji kunya, sai gashi inata murmushi yana mun fira yana zolayata sai santin duk abunda na zuba mishi yake, saida kowa ya watse yabar mu anan, fira mukai tayi ko ince kauna don kamar mu kad'aine a duniyar haka muka ringajin kanmu, naita narkewa kamar wata kankara,saida Allah ya jeho Abba Nura ya ce "firar ta isa duk kutashi kuje ku kwanta"

Lokacin daya da rabi tama wuce sosai,badan rai ya soba saida ya biyoni zuwa hanyar dakin mu Abba ya ce, "kai! Ina zaka?"

Sosa Kai yayi yana cewa, "raka ta zanyi Abba"

Dak'uwa yai masa yana nuna masa hanyar dakin sa, "ban son sakarci kajiko"

Dole ya kyaleni amma har yakusa kullewa yana waigo ni, ranar Ina bacci amma murmushi nake ina jinjina irin kauna da soyayyar dake cikin zukatan mu,Ina tunanin to in har Auren mu bai yuwu bafa?cikin sauri nake kauda wannan tunanin don lokaci guda zanji hankalina yai kololuwar tashi,daker nai addua na kwanta.

Mom muhseen&Asaad
_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_

*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*

By
Mom muhsen&
Asaad.

Wattpad name
Humaira3461.

🅿️.....19

Washe gari dana tashi kamar wacce mijinta yai tafi tsayin lokaci ya dawo,haka na kasance nice shirya wannan gyara wannan haka nai tayi na hada masa lafiyayyan breakfast da kaina,wanda ko yai mamakin ganina a kitchen tunda ba sana'a ta bace,na gama naje nai wanka na d'an d'asa kwalliya kamar zanje biki,Rukee dai har ta daina mamakina ma saidai tayi murmushi kawai ta kauda kai,yanzu ma abunda tayi kenan na jiyo ina ce mata,

"Na miki uziri baki san gard'in soyayya ba,dakin sani ba zaki ga laifin abunda nake ba amma muje zuwa akwai ranar da zaki zo kina neman shawarata akan kin afaka rijiyar kaunar wani..........dariya ce ta kwace mata ta ce "Allah ya kyauta mun,bana fatan shiga soyayya irin wannan, don cutuwar ta tafi dad'inta yawa,ni hasalima kin ganni nan bana son duk abunda zai hanani sukuni a zuciyata, bance miki bazan yi soyayya ba,tabbas zanyi watarana tunda dole muyi aure amma irin wannan da kike ma Yah Rafeeq uhhh aa gaskiya tayi yawa,ace baka iya ganin laifin mutum inyai maka?kuma baka iya dogon fushi dashi?sannan bakajin kunyar kowa indai akanshi ne?uhhh Aa ba irin wannan ba sai sa sai sa dai mastad'aa"

Dariya ma na kama yi mata nace, "we shall see"

Na gama kwalliyata na fita zuwa bangaren su Mami,amma saida na biya na gaida Abba na iske Hajja tazo wurin sa suna magana, duk kallona suke kamar wata sabuwar Halitta. Abban ya ce "Ina zuwa mamana?"

Na sunkuyar dakai Ina murmushi "Ba ko Ina Abba,gaidaka nazo inyi kawai?"

Murmushi yayi ya ce, "Aa gaya mun gaskiya dai?"

Na soke kai Ina dariya,Hajja ta ce "zai wuce wajen Rafeeq zataje"

Abban ya ce "wai haka?"

Na d'aga kai alamar ehy,murmushi yayi sannan ya ce "to a rage rawar k'afar nan kinji ko?kuma a rage shigema juna"

Na jinjina kai na kasa magana saboda naji kunya sosai, "jeki abunki,kice da Abbanku Nura Hajja na jiransa anan"

Sadda na isa bangaren Mami na iske falo tana shirya dining na gaidata,Ina ansar kayan na soma shirya mata, na ce "Mami Abbanmu yace agaya ma Abba Hajja na jiransa"
Chapter 28 · 0% Book details