← Book details Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 38

Sashe 29

Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta amsa da cewar bari taje ta sanar dashi,tana tafiya nai wuff na wuce dakin sa,kwance yake yanata bacci na fizge bargon daya rufa aiko yai firgigi ya tashi, aiko na kama masa dariya yai k'urii yana kallona da idanun sa cike da Bacci,sai suka kara kasa kyau sosai naji wani abu ya tsarga mun,na hade hannuwa na alamun ban hakuri "afuwan Yah,ka koma ka cigaba da baccin ka bazan sake tashinka ba"
"Ai wallahi karya kike yarinya, ni zaki tada kuma kice na noma nacigaba da baccin,bacin kinfi kowa sanin in natashi bana iya koma wa,bayani zaki.......ya diro daga bisa gadon yana niyyar biyo ni,aguje na yo hanyar waje Ina tsuwwa caraf ya cafke hanuna daidai budewar k'ofar, mukai ido hud'u da Yah Ramadan,kallon mu yake muna kallon sa kafin Yah Rafeeq yaja wani dogon tsaki yana yin kamar bai ganshi na,,ni kuma sai kokarin anshe hannuna nake yaki sakina, "waye yace ki tadani,don haka koki biyani baccina ko kuma bake ba fita dakin nan,anan zamu yini baci ba sha.............Kazo Abba yana kiranka"

Abunda Ya fad'a kenan ya juya yai gaba,shi kuma kamar anyi mgn da dutsi bai ma nuna dashi ake mgr ba,magiya naita masa ina cewa "wallahi ba da niyya nayi ba,zuwa nai na ce maka kazo nayi maka breakfast mai dad'i sai muci tare"

Kokarin had'e ni yake da jikinsa,nikuma inata ja baya gabana na fad'uwa,duk karfina saida yai nasarar sani cikin kirjinsa,wata nannauyar ajiyar zuciya muka sauke muduka,sai kuma mukai shiruuu,zukata nata biting sosai ahankali na zare jikina gabana na fad'uwa na fice daga dakin,

Breakfast din saidai yazo ya dauka da kanshi,kasa sakewa nayi bare muyi tare,kunyar sa ta cika mun ciki shikau ko ajikinsa yakeji, ranar lectures din yamma garemu nida Rukee shine kuma ya kaimu ranar,karfe bakwai na dare muke tashi ya koma ya dauko mu,ya biya damu shopping muka siyo kayan zak'i sannan muka tsaya wani bakery muka siyo cake ice cream da sauran su,ya kashe mana kudi sosai muka dawo gida.

Daga wannan rana shi ya zama yana kaimu sch inda baya komi, sannan yaje ya dawo damu hidima yake mun kamar dai anriga an bashi ni, bayajin komi abu duk tsadarsa ya siya mun,kayan kwalliya dana gayu baya gajiya da siya mun,haka kayan shafa masu masifar gyara fata don zan iya cewa shiya lalatani da bana iya amfani da wasu maya-mayai inba dove da Nevia ba,ko wane set dinsa yake siya mun banda su shampoo na wankin gashi turarukan jiki dana kaya,Dana gashi kai yah Rafeeq har turarukan Hq da sabulan tsarki siya mun yake,tun Ina nuna haushi dakunya har na daina,don fara House man ship dinsa abun yakaru,don duk wata yanajin alert na dubu dari biyu asibitin da yake aiki, baya komi dasu sai hidimata da tashi sai Rukee.

Yaje gidajen su Anti Rafeea da Anti sha'awa ya kai musu abun arziki,kuma duk tare muke zuwa inka ganmu zaka dauka sabbin amare ne tsabar yadda jikinmu yake glowing yana wani fresh tsabar jin dad'i da kuma kud'i da ake kashe ma jikin,sannan sitira yinsu yake kamar me duk sati saiya je boutique donshi yana son kananun kaya, nima kuma zaisiyo mun duk abunda ya siya ma kanshi.

Idan bamu zuwa ko Ina to tabbas muna lambu ko farfajiyar gida muna fira,ko wasanni volleyball ko basketball irin wannan lokutan muka fi haduwa da Yah Ramadan,kallo bamu isheshi ba nice ma nakan iya cemasa Ina wuni,zai ce lafiya kawai ya wuce.

Yah Rafeeq ya ce, "ke banga kwakwar dakike ta gaida mutumin da bai damu dake ba,nifa gaskiya vana so ma inga ko kallonsa kinayi"

"Arzikin Abbanmu yakeci kai ma kasan ai bai daman ba,akwai alkawarin da Abba yasani na dauka shiyasa,amma badan wai na huce daga jin haushin Saba"

Ire iren wadannan maganganun muke yawan yi inmun ganshi,tun Ina gaidashin har na daina saboda hudubar Yah Rafeeq d'in,rayuwar gwanin dad'i yanzu nakan mance da wani b'acin rai ko damuwa,kuka kam tun ranar da Yah Rafeeq ya dawo ban sake yinsa ba,baya bari na nuna damuwata sosai.

Akwai abunda yake daure mun kai,sau uku hakan na faruwa ban dai sanar da kowa ba,watarana munyo saloon nida Rukee to tarigani tahowa sabo kiran da Mami tai mata na gaggawa,sai nayo dare ban iso gida ba sai bayan sallar isha'i Yah Rafeeq na wajen aikin sa balle ya dauko ni,muna daf da isowa naga napep ya tsaya wata mata ta fito da dogon hijab jikinta da nik'abi a fuska,ta shiga gidanmu.

Amma koda nashiga banga alamun wata bakuwa agidan ba,ba bangaren da ban shiga ba don ganin ko bakuwar ce, amma babu alamun ta har shabiyun dare Ina falo amma banga wata tafito ba,haka naje na kwanta ina kokwanto a raina.

Na biyu kuma let evening ne gab magriba,mun rabu da Yah Rafeeq zai je masallaci na zagayo daga baya wajen lambu zan shigo ta kofar entrance d'inmu,na hangi again matar tana ta sauri kamar zata kifa ta shige cikin gida,aiko na ruga da gudu don inaso inga yau wacece ke shigo mana cikin b'adda kama haka,saidai duk shige da ficena na rasa ta sama ko k'asa, zuciyata ta soma tsorata anya ba aljannu keson budemun ido ba,na rasa dawa zan mgnr kar ace na samu tab'in hankali,haka dai nabar abun a raina badan ya daina bani tsoro ba,

Na karshen wanda ya kid'imani,karfe d'ayan dare na fito zuwa main kitchen d'in babban falo insha ruwa,na manta ban shiga dashi ba ranar Ina cikin kitchen naji wani kauri haka ga hanci na,nai saurin juyawa naga wulgin mutum ya shige corridor na hanyar bangaren Mami,duk yadda zuciyata take bugawa da tsoro hakan bai hanani bin hanyar ba cikin tashin hankali,don jinake kozan yi miye saina ga wacece wannan?

_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_

*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*

By
Mom muhsen&
Asaad.

Wattpad name
Humaira3461.

🅿️.....20

Jikina wani irin tsuma yake ainun,saboda dai Ina cikin tsoro matsanan ci saboda al'amarin yana matuk'ar bani tsoro da mamaki,jiki na rawa nabi hanyar da tabi duk da wannan warin yana bugar hancina yana sani jin jiri kamar juwa na neman kadani,kamar walkiya banga kowa ba saidai k'ofar shiga bangaren Mami abud'e zuciyata keta bugawa,na kasa shiga zuwa can naji duhu ya mamaye idona daga haka ban sake sanin Inda kaina yake ba,

Sai farka wa nayi da sanyin asuba na ganni bisa gadonmu,mamaki da al'ajabin abun yai mugun kamani dan danan abubuwan da suka faru a daren jiyan suka soma dawo mun tiryan tiryan, nai saurin tashi zaune cikin wani irin firgici har saida Rukee tatashi tana tambayata lfy "Rohee?"

Jikina kamar an zuba mun ruwa,saboda zufar data kwaranyo mun, na kasa bata ansa kaina ya kulle.

tashi tayi taje ta d'ebo mun ruwa ta kawo mun, "kisha ruwa, ko mafarki kikayi na tsoro?"

Kallon ta nai kamar yau na fara ganinta daker nasha ruwan,na jingina da allon gado ina kallon ko ina nad'akina,kafin na iya bud'e bakina nace mata,

"Waya kawoni nan Rukee?, jiya da daddare na farka naji kishirwa,nafita insha ruwa........ Sai na kasa bata labarin abunda ya farun, nai shiru dai.

"Sai miya faru? Tsoro aka baki ne?"

Ajiyar zuciya naja mai karfi kafin ince mata,"Ehy, to nidai nasan dana fita ban dawo nan ba,yanzu kuma na farka na ganni anan"

"Kodai mafarki kikai kin tashi kin fita,inba haka ba ya za'ai haka ta faru, to waya dawo dake nan d'in?"

Idona cike da kwallar tashin hankali nace mata"wallahi ban sani ba,kuma ni cikin hankalina nake ba mafarki nayi ba"

Cikin son ta kwantar mun da hankali tace"Ki natsu ba fa wani abu bane,irin haka na faruwa sosai koni nasha yin irin wanan mafarkin sai kaga kamar gaske,karki damu kanki kinji ko ki dauka mafarkin kikai, kuma Rohee kina wasa da adduar bacci tunda yah Rafeeq ya dawo, ba dole ki ringa munanan mafarkai ba. "

Shiru kurin nayi ina jinta ban sake cewa komi ba,nidai nasan ba wani mafarki danai abunda ya faru zahirin gaskiya ne bakomi ba,abunda ke rikitani shine waye ya maidoni dakin?

Wannan ya wuce.
********

Bayan kwana biyu nayi kokarin ganin abun bai dameni ba,duk da idan na zauna ni daya abun yana dawo mun tsoro matsananci ya cika zuciyata,hakan saiya haifar mun da zazzabi mai zafi shiyasa nai iyakar k'ok'arina wajen ganin na cire ma raina abun,na zama Busy a makaranta indai ina ni kad'ai to zaka sameni ina karatu ko research,a d'an tsukin na rage kara kaina sosai,duk na zama sukuku dani Yah Rafeeq Yafi kowa damuwa da hakan,sbd na kasa sake wa kamar yadda muke,ya gaji da min tsogumi har ya gaji,Ummanmu kanta ta damu matuk'a rannan ta zaunar dani take tambayata, "Rohee mike damunki?,kusan sati biyu duk kin rage walwala,abinci ma bakyaci sosai kin faye zaman daki sai a yini ba ajiyo muryarki ba,ni mahaifiyarki ce sanar dani kinji ko"

Shiru nayi kwalla suka cika idona kafin nai aune sun silalo kan kuncina, cikin sanyin murya na ce, "Umma kwana biyu mafarkai nake marasa dad'i,abun yana damuna shiyasa.........daidai lokacin Mami ta shigo falon ta zauna,ganin ina kuka take tambayar mike faruwa, umman cikin jimami ta ce " wai mafarkai take na ban tsoro shiyasa duk kwana biyun nan gatanan sukuku"
Mamin ta kalleni cikin rashin jin dad'i ta ce

"Shiyasa Rafeeq ya dameni akan Rohee kamar bata lfy kwana biyu,kuma nima naga alamar rashin sakewa tattare da ita,Y'ata zonan inji"

Na matsa jikinta na dora kaina bisa cinyarta, ta dafa kaina cikin kulawa take mun mgn, "kin rage Azhkar ko?na sani kin rage don haka ki cigaba karki daina,shi daman shaid'an ai inda ake wasa da ibada yake zuwa,ki ringa alwalla in zaki kwanta kinji"

Kaina kurin na iya D'aga mata,sai suka cigaba da firar su ita da Umman,har bacci ya daukeni kan cinyar Mamin.

*******

A hankali a hankali sai na fara da ya yewa daga yana yin dana ke ciki na rud'u da damuwa,na dawo kamar komi bai faru ba,ban sake ganin matar ba balle wani abu makamancin irin na ranar ya faru, muka cigaba da soyayyar mu da Yah Rafeeq,kamar ma yanzu ne muka farata saboda shauk'in juna, kuma har zuwa wannan lokacin alak'armu dasu Mama su Yah Ramdan bata canza daga yadda take ba,saima abunda yai gaba.
Chapter 29 · 0% Book details