Sashe 22
Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rukee ta daukar mata wata jikka ita kuma taja akwatin ta,har suka fice ban da niyyar tashi,sai nakejin ba dad'i sosai a raina bamu tab'a irin wannan rabuwar da Mufeey ba,duk sadda tazo mana hutu da kuka muke rabuwa,farkon zuwanta kuwa kodayaushe cikin raha da wasa muke mu ukun nan,amma wannan zuwan yazo da sabbin abubuwa,sai naji can kasan raina babu dad'i kwarai,inata dannewa kar raunina ya bayyana in bada kaina har dai na kasa,na mik'e na isa ga tagar ina lek'ensu amma ban hangota ba,wayata Abba ya kira na dauka ya ce mun "me kike baki fito rakiyar su goggo ba,maza ki fito ki rakasu kibiya Bangaren Yaya kice da Ramadan su ake jira"
Bai saurari abunda zan ce ba ya kashe wayarsa,nai tsaye sororo da wayar a hannu har saida ya sake kirana,na dauka nace gashinan na fito,har na iso kofar bangaren nasu inata tunani wanda ban san ma wane kalar tunani bane,Mama ce kawai falon na gaidata sama-sama ta ansa itama kadaran-kadahan, "Daman Abba ya ce ace masa yafito lokaci na k'urewa"
Hanyar bangaren su shida Yah najeb ta nuna mun,ta cigaba da abunda take na gama tsayuwata na wuce can,cikin raina ina mamakin yadda itama ta canxa ai da ba haka take mun ba,naja tsaki kurin ina tura k'ofar falon su...........kyakkyawan gani nai musu Mufeey ce rungume dashi ajikinsa,ta zagaya da hannuwanta bayansa,shi kuma yana tallabe da kanta dashi mukai four eye's saboda ita tabada baya,wani mugun fad'uwar gaba naji wadda ban tab'ajin irin ta ba a rayuwata,kallon-kallo muke ma juna nama rasa me zanyi kawai mamaki ne,?al'ajabine ko ko minene ban sani ba,kawai dai ganin su a haka ya dakeni sosai,kuka take tayi masa shi kuma yana lallashin ta,dauke idon sa yai daga barin kallona yana d'ago kanta yana goge mata hawayen,sai kawai na juya da sauri na fice daga dakin,koda na iso farfajiyar gidan duk su Abba na nan sai Mama data fito da Rukee da ummi,sai su Anti Rafeea sai ni har na tsaya gefe guda ban fita daga cikin shock din ganinsu haka ba,Abba ya ce mun "ina suke ne wai?"
Nama kasa cewa komi,sai na nuna hanya da hannuna bance komi ba,goggo ta ce "miya sameki ne?"
Girgixa kai na nayi kurin kamar wata sakarai,dai-dai nan suka fito suke rik'e da hannun Juna,kallon su nai tayi ban san miyasa al'amarin su yaban mamaki ba,gashi ba magana muke da Rukee ba balle in labarta mata,kai ko muna magana ba bana iya fadar wannan abun,ban kuma san dalilina ba.
Ban kwana aka shigayi dasu goggo ta rungume mama tana cewa, "sai Allah ya sadamu kuma Mama,mungode da karamci Allah yabar zumunci"
"Haba ba komi Habi,ai anzama d'aya komi mukai muku ai kanmu mukai mawa,sai Biki kuma in Allah ya kaimu da rai da lafiya"
Tai ma su Abba sallama on ready sun sallameta da duk abunda zasu bata,ta shiga bayan motar da Yah Ramadan zai tuk'a Rukee ma ta shiga,Mufeey ta shiga baya ana d'aga musu hannu Abbanmu ya ce "Rohee bazaki ma Yar uwar taki rakiya ba,ba haka kuka saba rabuwa ba ko kunyi fad'a"
Na sadda kaina k'asa bance komi ba,goggon ta taga tace mun "bud'e kishigo kinji ko,karku biye ma shaid'an ya raba kanku"
Ina dago kaina muka hada ido dashi,wani kallo da ban san ma'anar sa ba ya jefan dashi,na kauda kaina gefe Mufeeyn ta ce cikin muryar datasha kuka "please Rohee"
Sai na bud'e inda Rukee ke zauna na shiga,Abbanmu ya ce "in kun dawo keda Rukayya ina son ganin ku"
Kai muka daga sannan yaja motar muka tafi,tunda aka fara tafiya goggo keta mana nasiha mai shiga jiki,tana nuna mana muhimmancin zumunci da nuna ma d'an uwanka kulawa da soyayya,ta bamu takaitaccen tarihin su ita dasu Abbanmu da Abba Habibu,da dalilin da yasa suke jin duk duniya basu da kamar Abba Habibu bayan Hajja,yai d'awainiya dasu da aljihun sa da karfinsa,sadda suna kananu babansu ya rasu,har kaskare da jan ruwa a baro ya siyar yayi don suci abunci,shine baci shine walda shine gini shine duk wata sana'a mafi kask'anci ga mutum yayi don ya samu suci suyi karatu,shiyasa suke tsaye akan duk wanda yace zai raina shi to sai ida karfinsu ya k'are,"don haka kuyi hakuri da juna kar ku biye ma zuciyar ku ta kaiku ga kogin dana sani,inkuka rik'e zumunci kun tsira a duniyar nan baku da kamar juna,don Allah Rohee akula a gyara wasu d'abi'un kunji Rukayya?"
Rukeen ta ce, "in sha Allahu Goggo zamu gyara muna kan gyarawar"
"Allah yasa ya baku ikon hakan"
Har muka iso tashar jirgin k'asan bamai cewa komi,muka fito shi kuma yaje yai musu duk abunda zai ya fiddo musu kayan su aka kaisu inda ake killacewa,ya dawo inda muke muka zauna don lokacin ya idasa, suna zaune kusa da juna kuma rik'e da hannun juna bamai cewa komi,ni kam idona a sace yana kansu,dana ga zamu had'a ido dashi zan maza in canza direction din fuskata,har aka soma neman su mutane suka fara shiga,mukai ma Goggon sallama ta shiga Mufeey tana ta hawaye sukai sallama da Rukeen,sai ta iso inda nake ta rungumeni tsam tana kukan, "ki yafeni sister in akwai abunda nai kika k'ullaceni,sai watarana"
Wasu kwalla masu zafi suka zubo mun nai saurin rungumeta nima muryata tai sanyin sosai na ce, "baki mun komi ba sister na yafe miki,nima ki yafeni karki kullaceni please I'm very sorry"
Daker muka rabu da ita ta koma gareshi ta rungumeshi tana kuka shiya kaita har sit d'inta,sannan ya fito muka shiga mota mukai gida,har muka iso kamar masu ciwon hakori ba mai uhm balle uhm uhm,yana yin parking muka fito tuni Rukee kamar walkiya har ta shige gida,banga alamun sassauci a fuskar ta ba dangane dani,sai na tuna inhar tai fushi to saukowar ta abune mai wahala,nima na nufi hanyar part din mu nasan ma Abbanmu ya fita saidai zuwa dare..........."Ba kiji ba"
Cak na tsaya saboda dai nasan dani yake duk wajen ba kowa sai ni dashi, "Bakiji ba....?na nanata maganar,to bai san sunana ba kome?juyowa nayi ina kallon sa shima ni yake kallo da idanun sa masu wata irin kala ni banma tab'a lura da yana yin kwayar idonsa ba sai yau,saurin kawar da kaina nayi daga barin kallon cikin idonsa, isowa yai gabana ya sa hannu aljihun wandon jeans din sa ya ciro wani chan din dan hannu,waro idona nai saboda nasan nau ne kuma ko dana tashi a yau yana sanye a hannuna,na kalli hannuna na sake kallon wanda ke hannun sa,mamaki ya kamani na sake kallon fuskar sa har sannan kallona yake,inaso ince ina ka samai?ya akai yazo hannun ka?bakina yai nauyi,sai ya mik'o mun "wajen kallonmu d'axun kika yar"
Ya mutsa fuska nayi, "Ban gane ba?"
Juyawa yayi yana tafiyar sa ta isa da yakeyi ya ce, "Ai bazaki tab'a ganewar ba"
Ya barni nan kamar sakarai, taya d'an hannu na d'aure damtsen hannuna kuma ya zare ban sani ba?tafiya nake zuwa cikin gida ina duba chan d'in,dana lura sosai ya tsinke ba kuncewa yai ba,sai na tuna sadda na juya zan fita lokacin danaje kiran sa dakinsu,naji kamar abu ya rik'eni na fizge hannun nai gaba,to why?
*"Ai ba zaki tab'a ganewa ba"*
Maganar ta sake dawo mun,tab'e baki nayi na wuce dakin Ummanmu,
_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_
*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*
By
Mom muhsen&
Asaad.
Wattpad name
Humaira3461.
🅿️.....15
Bamu je ga Abbanmu ba sai washe gari monday zamu je sch,munje gaidashi kamar yadda muka saba ya bamu kudin breakfast sannan yace damu,
"Kafin kubar nan inaso inji miya had'aku?ban son jin bakomi kun sani ban son musu ko gardama don haka ina sauraren ku"
Mukai shiru na wani lokaci,kafin zuwa can Rukee ta fara magana, "Abba ka gafarcemu,shaid'an ne yaso dagula komi kuma muka biye masa,duk da ni akan gaskiyata nake itace take son nabita akan rashin gaskiya"
Ta zayyane masa komi ba rage ba k'ari game da abunda ya hada mu,kaina na soke k'asa don tun kafin yace komi naji kunya ta kamani, saida ta gama naji ya ce mata "Allah yai miki albarka Rukayya,Allah ya baki miji nagari kinji ko,tashi kije karki makara"
Ta sadda kai tana ansawa kasa-kasa,sannan tatashi tai ficewar ta bata tanka mun ba,shima sai ya tashi zai barni anan hankalina naji yai mugun tashi,nai saurin rik'o k'afarsa cikin nadama na ce, "Abba na tuba,nabi Allah nabika karkai fushi dani don Allah,fushin ka masifa ce a gareni wallahi zan gyara Abbanmu"
Cikin rawar murya nake maganar,saboda inhar ya tafi yana wannan fushi dani na shiga uku,bazai sake shiga sabgata ba balle ma akan wanda yafi dauka da muhimmanci ne,ahalin Abba Habibu yana son su fiye da son da yake ma nashi ahalin.
Tsaya wa yayi bai jiyo ya kallan ba,hakan ya sake bani damar rik'esa gam na fara hawaye,don ba abunda ke saurin karyar masa da zuciya irin ganin hawayena,......"Abba ka yadda dani zan gyara wallahi zan gyara nayi alkawarin irin haka ba zata sake faruwa ba,zan yi duk abunda kake so Abba ka yafe mun don Allah"
Sai lokacin ya jiyo yana fuskanta ta, fuskar sa da damuwa sosai ya ce, "zan iya yafeki a cikin ahalina LAYLA saboda iyalin Yaya Habibu dashi kanshi,ina masa kallon mahaifina ba yayana ba,idan akwai wani da zai tsine mun bayan Hajja da Alhaji ta binito Yaya ne,don haka zan iya komi akan sa in kina son zaman lafiya dani to karki kuskura a hada baki dake wajen muzguna musu,ina sonki sosai amma son bazai hanani yi miki hukunci mai tsanani ba Rohee"
Hawaye nake tayi jikina yai mugun sanyi, na ce "ka yafe mun Abba,zan kiyaye zan gyara zanyi duk abunda kake so"
Yai shiru na wani lokaci kafin ya dago yana kallona inata sharbar majina,ya sa hannu ya dagoni ya zaunar dani gefensa,ya shiga yimun nasiha cikin kwantar da hankali da kulawa,jikina yai la'asar ya kare da cewa, "ki tayani mu idasa wannan zumuncin,uwarku ta kasa kuma tana kokarin ta hanaku kubini,karki yadda ki shiga cikin jerin wadanda zan hukunta su"
"Bazan shigaba Abba in sha Allah,alfarma daya nake nema wajenka itace, karka tilastani dole mu zama cloth da YAH RAMADAN Abba bamu jituwa,muna yawan fad'a amma zanyi kokari in ringa gaidashi in bashi girman sa,ba sai na zama cloth dasu ba"