← Book details Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 38

Sashe 33

Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wace yarinyar?kaifa wuyarka kenan kayi mgnr da mutum zai gane ma ka kasa...........Mama inajin Rohee yake nufi ba kowa ba"
Cewar Najeeba dake zaune tana masa sannu, Maman tace "tashi ka isa daki ka cire kayan,bari naje na had'a ma ruwan d'umi kayi wanka,Najee had'o masa tea mai zafi ki dauko masa paracitomal sai yaji saukin jikin"
Maman ta kamashi suka tafi dakin sa,ta kwantar dashi sannan ta hada mai ruwan wanka mai gumi sadda ta fito ya daura towel,tace"kayi wankan sai kaji sauk'i Allah ya sawak'e, kuma zanyi mamakin yadda zaku tsaya ruwa yai muku wannan dukan kamar wasu yara kananu" tafice tabarsa yana shiga bayin,kwamin wankan ya shige ciki yai lub idonsa a rufe Allah kad'ai dashi suka san abunda ke damunsa har ya haifar masa da wannan fitinannen zazzabin,ya jima cikin ruwan nan saida yaji dad'in jikin sannan ya wanke jikin da sabulun wankan yafito,ya iske tea da maganin ya tsane jikinsa ya shafa mai ya saka kayan baccin sa,sannan ya dauki tea d'in da maganin yasha.
Shiru yai na wani lokaci kafin ya duba agogo time yaja sosae tashi yai sallolin sa magriba da isha'i dasuka wucesa, yai shafa'q da wutri yai adduo'in sa ya shafa sannan ya jingina da gado yana kulle idonsa,ya kasa baccin kwata-kwata ya sake duba agogo yaga karfe biyu saura,kawae ya tashi ya fito.

Ai ban san inajin sanyi ba saida na iso dakin mu, Ac nata aikinta karma kawae nake daker na cire kayan jikina hakorana har gamuwa suke,mai makon nayi wanka da ruwan zafi sai na kasa sabda ba karfi jikin,zazzabi sosae ya rufeni na jawo bargo kawae na shige dagani sai towel jikina canza kayan ma na kasa,ga ba waya hannuna balle na kira umma,tunda ummi nacan gidan jegon Ina cikin tasku,sai kawae na kama kuka saboda a halin da nake ciki Ina bukatar agajin wani,Ina cikin wannan halin na ciwo da tsoro don ban saba kwana nid'aya ba gashi yau wani irin tsoro nakeji,har jinake kamar ana kiran sunana ana dariya,abunda ya sake gigitani kenan dai-dai wannan lokacin naji an bud'e kofar dakin nawa,dunkulewa nayi Ina karanto duk adduar da tazo bakina hawaye kamar an kunna famfo,shirun da naji bayan bud'e kofar yasa na ciro kaina cikin bargo a hankali, wazan gani tsaye??

Sai kurin ya kunna glub din dakin haske ya karad'e KO Ina,saurin maida kaina cikin bargo nayi zuciyata kamar zata kece don bugawa, miya kawoshi dakina?banda wannan ansar zuwa can naji ya bud'e toilet d'inmu ya shiga na fiddo kaina ina sake tsorata dashi bai ce mun komi ba dai,ya gama ya fito ya tsaya gaban gadon mu yana kallona, "ki shiga kiyi wanka"
Kamar sakarai nake kallon sa,wani sabon mutum ya koma mun yau wai anya shine kau?Miya canza shi to? "Ko bikiji ba?"

Duk da bargon na sauko kafafuna na rawa haka ma jikina,na shiga bayin Ina shiga ruwan saida nai ajiyar zuciya,nai shiruu kirjina kurin ke ansawa sosae na dad'e cikin ruwan d'umin gwanin dad'i sai naji d'an relief,na manta shaff wa na baro cikin dakin na dauro towel din na fito,yana zaune kan bedside drawer da cup din tea hannun sa yana motsawa a hankali,koda yaji alamun fitowa bai ciro kanshi ya kallan ba,saima ya tashi yana aje cup din bisa drawer silently yace "ga tea nan, sannan ga magni nan kisha,zakiji sauki saiki sallolinki saida safe"
Kamar walkiya ya ficewar sa,ban san iyakar lokacin dana dauka tsaye ba ina kallon hanyar daya fita, ban san ya akai naji maganar a bakina ba nadai ji labbana suna mgnr "daman yana da kirki?ko yau ne ya zama haka?"
Ahankali na isa ga tea d'in sai kamshin coffee yake yasha madara,nai suffing naji ba sugar sosae yadda nakeson sa,nasha rabi sannan na balli maganin ina runtse ido na had'iya,dan danan zufa ta karyo mun don sadda na fito wanka ya kashe Ac din,kayan bacci nasa KO mai ban shafa ba na zauna akan sallaya,nayi sallolina na kasa daina mamakin sa sosae a raina,karshe anan wani baccin ya sace ni,sanyin asubar fari ya maidoni kan gado bayan nayi sallar asubar.

Nice ban tashi ba sai karfe shad'ayan safe,na shiga nai wankan na shirya cikin wata maroon abaya mai adon duwatsu masu kalar pink da blue,fuskata fresh farar powder na saka kurin da kwalli sai lipstick fari mai dank'o,bangaren Abba naje na iske sa kulle da alama ma bai kwana gida ba,na dawo wajen Ummanmu itama bata nan ga dukkan alamu tatafi gidan sunan tunda safe,Mami kuwa nasan tana can da mutanan ta bama zan nufi can ba,sai nace bari na gaido Abba Habibu kodan Darajar Abbanmu, jinai kurin nai karo da mutum nai saurin jaa baya Ina dago kaina idona cikin nashi,k'urii mukai ma juna kamar yau ne haduwar farko wajenmu,hannunsa yasa bisa goshina kawae labbansa na kalla na iya gane miyake fad'a, "yajikin?"

Juyar da kan nayi gefe guda nace nima kasa-kasa, "I'm fine"

"Ina zaki?"

"Abba zan gaido"

"Baya nan ai"

"Ohk"

Na juya da niyyar koma wa d'akinmu naji ya ce, "keeee"

Saurin jiyowa nai da idona warwaje don na tsani ace mun keee, "Sunana Rohee"

Ya wani kalar dage girar sa cikin salon iskanci ya ce, "dagaske?"

Na juyar dakai bance komi ba,har na cigaba da tafiya zuwa dakin mu najisa yana cewa, "tace ba zata zo ba,don haka ki kyaleni na huta Mufeeda"
Wai gowa nayi Ina kallonsa cikin ido shima kuma hakan,ga waya kunnen sa takowa yai yazo ya samu wayar ga kunne naji tace, "Hello sister"

Har sannan idona a kanshi nace "Naam"

"Wai dagaske ba zakizo yinin sunan ba?"

Sai nace mata kawae "ehy"

"Haba dae miyasa?ko jikin ne favorite yace baki lafiya sannu kinji,to in yamma tayi kidaure kizo zai kawo ki aimana pictures"

"Ohk tohm"

Na janye kunne na daga jikin wayar nai gaba na barsa nan,na shige dakinmu duk raina ba dad'i nakeji hadda kari da wayata bata kusa,ga kewar Yah Rafeeq nasan yakira har ya gaji ransa zai masa ba dad'i,naji kwalla kurin ta silalo mun sannan maganarmu ta rannan a waya har mukai fad'a ta dawo mun,sai na cigaba da kukana kawae wallahi a raina ba wanda nakejin haushin sa irin RAMADAN, bana kaunar had'a hanya dashi amma yana shige mun,yanzu da Yah Rafeeq na nan hakan ba zata faru ba nasani,saboda duk inda nasa kafa yana biye dani bazai samu damar da zai iya koda rik'e hannuna ba,amma miya faru jiya?jikina duka ba inda bai shafi nashi ba miya kai wannan van haushi da takaici,na tsanesa wallahi na tsane sa duk da yana mun kirki wani lokacin,amma ban haushin sa yafi kirkin sa yawa,na gaji da kukan nayi shiru dole na fita neman abinci wajen Mami,ita bata san ma ina nan ba nace mata ai nan na kwana banjin dadine shiyasa, naci fankasu na koshi da naman kai na dawo na sake shiryawa cikin sabbin dinkin sunan sa mukai mu uku, less ne marar nauyi sawai yake amma akwai kyau da tsada, golden da White ne ajikin sa ya had'u akai mana riga da siket,na saka golden gyale da takalmina sai white bag dina ko sauraren jiransa banyi ba na wuce na shiga taxi na tafi.

Mom muhseen&Asaad

_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_

*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*

By
Mom muhsen&
Asaad.

Wattpad name
Humaira3461.

🅿️.....24

Anyi suna lafiya an watse lafiya an samu Mustafa inkiya farhan,sbd sunan baban mijin aka saka mashi,an yanka raguna biyu manya ba laifi gaskiya a d'anyi hidima yadda ya kama ta anci ansha,sannan aka rarraba robobi na ayyukan gida,Amman duk da haka Mami k'orafi take wai ya gaza yak'i sakin kudi ayi hidimar yadda ya kamata,inaji tana waya tana ta sababi ita wallahi auren Anti sha'awa bai amfana mata komi ba sai tsiya, don duk yawanci ita aka tatike akan wasu abubuwan,don cewa yake shi bazai kaza ba kaza zai iyayi,akodayaushe mamakin Mami nake idan naji tana fadar wasu abubuwan,to mitake son samu a mijin y'arta?nidae banga aibu a tattare da mijin Anti sha'awa ba,iyakar gwargwado yana hidimar da yaji yana iyawa,kawae dai shi bamai facakar kudi bane kamar mijin Anti Rafeea,kuma kusan halinsu d'aya da Abba Nura don shima d'in baya b'arin kudi in wani abun ya taso,wannan saidai Abbanmu shine bayajin zafin fitar kud'i bayarwa kawae yake ba ruwansa.

Daga ranar sunan Anti magana ta fatar baki bata sake had'ani da Yah Ramadan ba,ganin sa ma yai mun wahala saboda ba zuwa sashen su nake ba sai a kwana uku ma banje na gaido Abba Habibun ba,duk Nacin mufeey akan muje can muyi firar dare bana zuwa,har gara Rukee takan d'an leka suje tare bata jimawa take dawowa,to shiyasa haduwar mu tai wahala balle tunda ba wani waje muke zuwa ba islamiya ce anyi hutun azumi daya gabato bai wuce sati biyu ba haka.

Mufeey wannan zuwan gaba d'aya bata wuni ma cikin bangaren mu,indai akace yana gida bai fita ba to ba shakka tana wajensa,abun yana ban mamaki kwarae da gaske hidima take dashi kamar dae yadda nake ma Yah rafeeq in har yana gida, rannan ina ta danna computer falon ummanmu Rukee nama ummi kalaba ita kuma tana kwance kasan capet tana danna wayarta, ummi ke cewa "wallahi Yaya Rukee kin rage sauri yanzu fa awar mu daya da rabi da fara kalabar nan amma har yanzu bamu gama ba"

Na ce "wai kardae kice mun anyi azhar muna nan zaune?"..........wata irin zabura Mufeey tayi tana cewa "na shiga uku azahar tayi kikace sister?"
Duk kallon ta mukai da mamaki na irin abun da tayi,Rukee tace "kanki d'aya Mufeey?"

"Yaya Mufeey ina zaki to?"
Cewar ummy dake kalonta itama,ni ai kasa mgn nayi ma na cigaba da abunda nake, ta maida wayarta caji tana cewa "wlh cewa nake zuwa yanzu na gama shirya ma favorite lunch d'insa,har wanka nayi jiransa kawae zanyi muci kinga ko d'orawar banba bari na ruwa shaf shaf in had'a mana wani abun..........ta ruga bangaren Mama duk muka bita da kallo mamakinta na kashe mu,ummi tace "Yaya Rukee Any kuwa yaya mufeey kalau take"
Dariya kurin tayi batace komi ba,don bamu cika magana sosae da tashafi waninmu da Ummy ba kanwar muce.
Chapter 33 · 0% Book details