← Book details Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 38

Sashe 24

Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna fita kamar jira sai ga Yah Rafeeq ya kirani,duk yadda na kai ga jin d'okin dauka sai naji na kasa daukar,komi yasa oho saida yai kira biyu a na ukun dole na dauka saboda zai damu, murya k'asa-k'asa na ce "Hello love"

"Rooh na ykk"

"I'm fine,saida kuma I'm so much missing u love"

Murmushi yai mai sanyi ya ce, "me too,naki na fila ne Rooh ko yau na kira Abba na rokesa yabarni ko bikin ayi dani in dawo ko ranar monday ne,amma yaki ya Rooh ina nan saboda damuwa har zazzabi naji ya sauko mun,shiyasa na kiraki kozan samu saukin halin da nake ciki,"

Tausayin sa ya kamani nama mance inda nake, na ce "kaya kuri love shekara guda kamar gobe ne in sha Allah,inda ina da yadda zanyi wallahi da nayi,saboda ni ji nake nafika son in ganka,Amma tunda Abba ya hana kayakuri kaji ko karka saka damuwa ni ma tana iya shafata,saboda duk abunda da ya dameka to lallai ya dameni............karar buga k'ofar motar yasa nai saurin dubawa,sai sannan na fahimci da wa nake tare,kuma shine ya fita ya bango murfin mota kamar ana yak'i,hango su Mufeey da nai sun fito sai nace masa, "sorry love munzo ansar dinki in na koma gida muyi waya pls"

"Ohk karki manta dani,inaso yau inta jin muryarki zai karfafa mun zuciyata"

Nai masa murmushin da yakeso nace, "dont mind love"

Mom muhseen&Asaad
_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_

*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*

By
Mom muhsen&
Asaad.

Wattpad name
Humaira3461.

🅿️.....16

Fitowa nayi daga cikin motar dai-dai sun iso inda muke jikin motar,shidai wayarsa yake dannawa Mufeey ta shagwab'e Fuska, "favorite"

D'ago kai yayi yana kallon ta, kafin ya ce "kun gama?"

Ta sake narkewa, "Aa,"

Idanun sa suna lullumshewa ya ce, "why?"

"Ba cewa yai bazai bada ba saboda bamu kawo kudi ba,kuma fa sun san ba guduwa zamuyi ba"

Rukee ta ce, "duk Abba ne yaja mana,da yana nan duk haka ba zata faru ba..........aljihu yasa hannun sa ya ciro ATM yaba mufeey, "su cire naki dana Ruk'ayya ku anso mu tafi akwai inda zani"

Wani tsalle ta daka da yar k'ara, "thank you so much favorite I really appreciate it"

Har ta ruga zata koma sai ta dawo,nidai kallon su kurin nake ta tsaya gaban sa bayan ta dubeni fuska ba walwala yanzu, tace "Yah Rohee fa?"

Bud'e motar yai ya shige yana cewa, "ban da ita"

Duk sai sukai hucking suna kallona,ni kaina abun ya dakeni na farko har yaushe yake da wannan kud'in da zai iya biyan har na mutum biyu?kafin wannan mamakin sai na maganar sa ta karshe ya sake kama ni,Rukee ta ce "ko kin masa wani abunne bayan shigarmu ciki"

Wani abune yazo mun wuyana ya tsaya mun,saboda bak'in ciki nama rasa mi zance don ina bud'e baki hawaye zasu zubo mun, na juyar da kaina kurin ban tanka ba, mufeey ta ce "karki kuka please..........Allah ya kyauta kukan me zan?shi har yana da kud'in da xai iya mun abu aduniyar nan ne?karki sake cemun haka"

Duk yadda naso sarrafa b'acin raina abun ya faskara,iyakar k'ulewa nayi watau dole saiya nuna cewar nid'in ba komi bace a wajen sa,Rukee ta rik'o hannuna "come down pls,kiyi hkr danne bacin ranki"

Fizge wa nai daga rik'on da tai mun,na shiga motar ji nake kamar zan banka mata wuta,su kuma suka koma shagon don kwaso kayan,kuma da gaske suka hana nawan saboda teloli basu da kirki,nai alkawarin nida sake kai musu dinki har abadan,bayan sun shigo motar ne shi kuma ya tada ta zamu tafi, naja wani dak'ik'in tsaki ni kadai nasan yadda zuciyata take tafasa,maganganun dake kai kawo a kirjina suna da zafi,saidai nasan fad'insu zai jawo mun matsalar da ban san karshen ta ba..........fitowa yai daga motar saidai kawai naji ya bude inda nake zaune, idanun sa jajir daker yake budesu muryar sa ta sake zama cool ya ce, "fito"

Da idanuna da suka tun batsa da bacin rai sun firfito waje nake kallon sa, kirjina har wani d'agawa yake don b'acin rai na ce da rawar murya kuka na son kwace mun, "mizan yi?"

"Idan kin fito saiki san ke zaki"

Fitowar nayi ina jiran ganin ikon Allah,sai kawai naga ya rufe kofar ya juya zai koma motar, hawayen da bake rik'ewa suka silalo mun ban shirya ba muryata da kuka na ce, "Kana nufin anan zaka barni?"

Wani kallo ya jefa mun ya bude murfin motar ya shiga, "duk abunda kakeji dashi inaji nima,saidai ka sani baka isa ka tsayar da numfashina ba,kuma yadda kakejin tsanata a ranka ni wadda bakeji akanka da zaka ganta saika tsorata"

Ya jima bai tada motar ba,kansa a bisa sikiyarin motar tsawon lokaci yana a haka,zuwa can ya dago ya tada motar suka tafi,kuka na durkushe a wajen inayi mai cin rai,saboda irin yadda bakejin haushi da bakin cikin abunda ya faru,ban san iyakar lokacin dana bata ba naji dai ankira magriba, na tari taxi nahau na taho gida.

Ranar kwana nayi cikin k'unci da bakin ciki,nama kad'aice ni kadai a daki na juyama kofa baya,duk iyakar hikimar su Rukee da Mufeey sun kasa shawo kaina,ko wayata kasheta nayi don ko ya kira bazai sameni yadda yake so ba,wajen eleven thirty na dare Mufeey ta dawo daga firar ta ita da Rukee ni kuma sannan nai sallar isha'i ta na gama ina linke sallayar Rukee ta jawo ledar data shigo da ita ta ce, "ga kayanki"

Kallon ledar nayi na kalleta na ce, "kaya na?na ina?"

"Ankon ki mana"

Nai mata wani kallo kafin na ce, "waya biya kudin?"

"Abba Habibu ya biya,mufeey tai masa magana"

Bance komi ba na haye gadon nai kwanciyata,inajin su suna shirin fara gogesu nidai daga haka bacci ya dauke ni.

*******

An shiga hidimar biki ka'in da na'in amare sunsha kyau kamar basu ba,mai gyara ta musamman aka dauko tai aikin kwana goma aka biyata,ita dai Anti sha'awa saidai Anty Rafeea ta biya kudin gyaranta angon bai bada ba,hakan ya sosa ran Mami sosai taita fad'a cikin jama'a daker Umma ta shawo kanta tai shiru.

Ko hidimar event ba wasu kudi ya bata ba duk su Anty Rafeea ne keyin komi da kudin da Angota ya bayar,shi kam ai kamar ana masa ruwan su haka yake barar dasu,abu kadan da tai masa magana zai turo dubu dari kaza,mu kam ai gaba ta kaimu muna jikinta muna kwasar rabon bu,ranar alhamis za'ai kamu juma'a ayi Arabian sai asabar dinner za'ai,duk mun shirya tsaf sauran tsararrakin mu yan uwa na bangaren uwa duk muna tare dasu kodayaushe,mufeey ce zamu nema mu rasa tana can wajen wannan mutumin,don sunan da na koma ce masa kenan,inhar zan fadi sunan sa wani kullutun bakin ciki ne yake cika mun zuciyata.

Duk inda zan shiga wayata nake da Yah rafeeq ina bashi labarin komi dake wakana a bikin,Bluetooth nasa ga kunnena sai anji ina magana ake gane waya nake.

Alhamis tazo aka tafi kamu wani rantstsetsen hall da yagaji da had'uwa,an shirya shi yadda ya kama ta,an kuma tsara komi bisa ka'ida yadda zai tafi ba matsala,in zaka shiga saida get pass in babu KO waye kai saidai kaja baya.

Irin wankan da mukai dole ma kace munyi kyau,namiji duk taurin kan sa sai munja hankalin sa akanmu,saboda duk inda muka wuce saidai ace Masha Allah tubarakallah,ankonmu mu uku iri d'aya ne less ne mai sunan less d'an kasar chana haka Abba yabiya kud'in oder sa nida Rukee da Mufeey kudi masu tsadar gaske,baida nauyi shawal yake kamar material red ne da golden sai ratsin light purple a jikinsa,gashi mai d'inkin ya zuba fasahar sa anan wajen,dukan mu gown ce akai mana an ratsa wani abun kwalliyar d'inki tun daga kafadar dama ya ratso ta tsakiya har k'asa,gaskiya munyi kyau sosai kamar wasu triple😂

Saida duk aka tafi ina can ina video call da Yah Rafeeq,na lalace wajen sa sai santin kwalliyata yake duk ya susuce ya hanani tafiya,ni kuma na biye masa muna ta shan kaunar mu,tun Rukee na magiyar in fito mutafi har ta gaji tatafi ita da Mufeey,daker muka rabu da niyyar dana dawo kamu zamu dasa.

Sadda na fito naga gidan duk ba yawa,hankalina ya tashi za ayi babu ni na fito compound ba kowa ba alamar ma wata mota,wajen umma na koma "Umma ki kira Yah Fahad yazo ya daukan pls"

"To ke miya tsayar dake har kamar yanzu,ai da hakuri kikai tunda ankusa tashi"

Kwalla ta cika idona ina diddira kafafu, "please Umma ki kirashi inaso inje in aka tashi banje ba wallahi bakin ciki kamani zai"

Dariya take ita da wata yayarta,tace "kin san halin Fahad dai ko?"

"Ki jaraba Umma kila adace ya dauka"

Nan ta soma kiransa har five missed call bai dauka ba,har na soma hawaye na fito na dawo compound din gidan, ba kowa kamar anyi shara na jingina da bango hawaye na silalo mun kan make up din da aka kashe kudi kanta, can saiga Abba Habibu ya dawo Sallar isha,na kauda kai na dauka wani ne cikin samarin da suka zo biki, "Rohee lafiyarki kike nan tsaye?ba kije partyn ba"

Sai hawaye sharrrr suka zubo mun, na ce "Abba duk tafiya sukai suka barni,na rasa mai kaini kowa bai nan"

"To daina kukan karki b'ata kwalliyar ki,ai zakije ko?"

Nai saurin d'aga kai ya ciro wayarsa ya ce, "Ramadan na gidan nan baije ko ina ba,bari yazo ya kaiki motar tana waje"

Wani sanyi ya ratsani,duk da haushin sa bar barni ha har yau amma indai zai kaini banjin komi, wallahi na ce "to Abba nagode"

Ya shiga kiran sa a waya bugun farko ya dauka naji yana cewa, "fito ina nan farfajiyar gida ina neman ka"

Ya sauke wayar yana cewa, "kwantar da hankalin ki yanzu zaki ganki kunje"

Minty biyar sai gashi ya fito,wallahi ban dauka shi bane saboda tunda bake ban tab'a ganin sa cikin shiga mai kyau irin wannan ba,shadda ce mai mutukar tsada a jikinsa kalar golden dinkin zamani rigar iyakar guiwar sa take hannun mai links,tasha aikin computer ya zauna d'as jikin rigar kanshi ba hula sai lallausan gashin sa irin na Yah Rafeeq,ya sha gyara sai daukar ido yake kafarsa cikin cover bakake,.........."gani Abba"
Chapter 24 · 0% Book details