Sashe 3
Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Aure tsakanin Roohee da Rafeeq dai an soke har abadan,in kuma kun shirya taka dokar Allah bismilla tunda bani na hana ba,sannan na biyu Kamar yadda na fad'a rannan Ni da nake matsayin kaka wadda ta isa da ubaninku na yanke hukuncin iyayenku maza su had'a Auren ROOHEE DA RAMADAN,SHI KUMA RAFEEQ GA NAJEEBA NAN,RUK'AYYA KUMA GA FAHAD NAN, WALLAHI KO BAYAN RAINA WANI YA CANZA WANNAN WASIYYAR BAN YAFE MASA BA DUNIYA DA LAHIRA, don naga alamar zumuncin neman lalacewa yake,ada vanyi niyyar matsama kowa akan auren wanda bai ra'ayi ba don yana da illa,amma duba da yadda iyayenku mata ke neman tarwatsa mun iyalai yasa na canza wannan shawarar,bazan zuba ido ina kallo ku maida Habibu da matarsa kamar ba kowa ba,bacin sune kominku kuma kune kuke rawa da bazarsu ba wai su ba,kai Nura da kai Taheer ai kune shaidar hakan don haka ku shaida ma matanku da iyalanku cewar HABIBU DA MATAR SA ZEENA ba abun wulakantawa bane ko rainawa ba,sud'in mutanan kirki ne masu daddataku da sanin darajar y'an uwantaka,wallahi koda wasa naji wani yai musu wani abu na rashin kima ko rashin kunya zai gane wacece Hajja,kuma na bada umurnin a tsayar da ranar aure nan da wata guda,wannan itace magana ta in akwai wanda yake da ja sai inji."
Tsiit kakejin falon saboda cikin fusata da hargagi take maganar wanda ya bawa kowa tsoro,don Hajja nada iska insuka tashi to kowa ma ubanshi yake ci,kuma fusatar ta nadaga cikin abunda ke jawo tashin aljannun,tana iya kwana da kwanaki basu sauka ba suna gana mana azaba,shiyasa yanzu kowa ya shiga taitayinsa.
Abba Habibu ne yai karfin halin cewa cikin kwantar da murya da k'ank'an da kanshi, "Hajja ba wanda ya isa ya taka umurnin ki,daga mu har iyalanmu dole mubi abunda kike so,amma alfarma nake nema masu yaran nan mai zai hana abarsu su huce daga yana yin da suke ciki,sannan aba sauran dama su fahimci juna kafin a fara maganar tsayar da ranar aure...........Kai Ramadan kana da jaa akan hukuncin dana yanke?"
Hajja ta katse Abba Habibu da fad'ar hakan ga Yah Ramadan, dagowa yayi cikin yana yinsa na koyaushe watau silently ya ce cikin muryar sa mai sanyi "Aa Hajja banda jaa akai, kuma na karb'a hannu bibbiyu"
"Shin miye baka sani ba akan Qanwarka Roohee?"
"Babu Hajja"
Ta juya ga sauran duk tai masu wannan tambayar,Yah Rafeeq ne yai mata banza tai maganar har ta gaji ta kyalesa, hawaye suka tsinke mun jinake kamar na bar duniyar kozan huta da wannan bakin cikin.
"To Habibu kaji ai ta bakin su,don haka hukuncina na nan inhar ba anaso anuna mun iyakata ba"
"Aa kiyi hkuri ba wanda ya isa,Taheer kaji kaima Nura kaji ko?"
Suka amsa da cewar sunji kuma zasu zartar da dukkan abunda ta buk'ata, tace "na sallami kowa na gama magana"
Mom muhseen&Asaad🥰
_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_
*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*
By
Mom muhsen&
Asaad.
Wattpad name
Humaira3461.
🅿️.....3
Shigowar Mamar dakin nashi yasa yai firgigi daga dogon tunanin daya shiga ya tashi daga kwanciyar da yake tun wayewar garin yau d'in, ida sa shigowa tayi ta zauna a gefen sofer tana kallon sa cikin nazari sosai kafin cikin natsuwa ta ce dashi
"Meke damun ka RAMADAN,?kar kace mun babu komi domin bazan yadda da bakomin ba"
Jujjuya kai yake yana tunanin me zai gaya mata,shi bai cika son fadar damuwar sa ba balle ma ga mahaifiyarsa wadda yasan duk duniya tafi kowa shiga damuwa in yana ciki,to mizai gaya mata akan abunda yasan itama bata da wani abunyi.........
"Aduk duniya babu wandaa zai karanci halinka sama dani RAMADAN,saboda nid'in mahaifiyarka ce wadda ke tsaye don y'ay'anta,kuma take iya bakin k'ok'arinta akan ku,ku hud'u Allah ya bani amma ba wanda ban san halin sa ba,don haka karka b'oye mun nasan duk akan Auren ka da ROOHEE NE,ko ba shi bane???"
Ya kasa cewa komi don bai da abun cewar,ta riga ta sani no need ya sake tisa mata........."koda yaushe ina k'ok'arin ganin na magance maku damuwarku duk sadda kuke ciki,Amma a wannan karon RAMADAN kayi hakuri bazan iya yi maka maganin damuwar ba,don abun yafi karfina ta inda bana iya cewa k'ala akai,ga Najeeba can tana kuka saboda itama abun bai mata ba, tana da wanda suka dai-daita kaima shaida ne,amma na bata hakuri da yi mata adduar in Allah yayarda addua ta akanku ba zata fad'i k'asa banza ba,Abunda na gaya ma Najeeba Kaima shi zan gaya maka KAYI HAKURI RAMADAN,duk wanda yai biyayya gaa abunda iyayensa suka d'ora shi akai bazai tab'a tab'ewa ba,amma sai kayi hakuri hausawa sunce duk wanda yai hakuri baici ribar sa ba,to baiyyi da yawa ba,nasan abunda kake hangowa nima ina hango maka shi,amma duk in kukai hakuri watarana zaku bada labari,nasanka na san waye kai zaka jure duk fitinar ROOHEE DA MAHAIFIYARTA,zan cigaba da maku addua Allah ya baku nasara ya kara maku hakuri,"
Tunda abun yafaru bai samu natsuwar zuciya da kwanciyar hankali ba irin yanzu,tabbas in Allah ya azurtaka da iyaye na gari ya gama maka komi,
"Na gode Mama,Allah ya taya mu hakurin"
"Yawwa ko kaifa,haka nake so naji maza ka fito ka karya yau ba zaka lek'a wajen aikin naku ba?"
Kanshi ya shafa yana duba agogo, "sai gobe yanzu na makara"
"Allah ya kaimu lafiya,kafa fito ka karya"
Ya juya tafita tana ja masa k'ofar, yaja ajiyar zuciya mai nauyi da numfashi sannan ya mik'e ya shiga wanka.
*******
Daren jiya ba muyi bacci ba saboda firgitar da naitayi tsabar zazzabin daya rufeni,in kana kusa dani har hucin zakaji yana dukan ka tsabar fiver,tun Ummanmu na iya jurewa har ta kasa ta kama kuka sosai saboda in kaga yadda nake zabura ina firgita da kakkafewa zaka dauka raina ake zarewa, tun daga kan ummi da Rukee da umma har Abbana ranar bamu runtsa ba,Yah Fahad Abba ya kira muje asibiti sadda zai zo sai gasu tare da Yah Rafeeq,kowa yai mamakin ganin sa don tunda aka fara wannan kitimillin baya mgn karshr ma kamar zautacce haka ya zama amma yau gashi nan Alhamdulillah, "Rafeeq jeka kwanta ai kai ba lafiya gareka ba"
"Abba zan iya bata taimako ne,I'm fine"
Dole suka hkr ya dubani kasancewar medical doctor ne sosai, bai jima ma da fara aikin sa ba ba'a shekara ba, Yah fahad yaje ya nemo duk abunda ya rubuta masa cikin daren yai mun duk abunda ya kamata,allurai da drip dan danan na samu bacci.
"Koda da safe bata tashi ba kar atashe ta sai tatashi da kanta, kafin sannan kila prasure dake kanta ta sauka,itace tai causing wannan fiver"
Abba ya ce, "Allah ya bata lfy,kuje kowa ya kwanta"
Duk suka fito amma shi ya kasa barin ta ya fito,kallon fuskarta kurin yake yana jin abunda ke zuciyarsa kamar zai kashe shi,saida Yah Fahad yazo yajashi sannan suka wuce dakin su, umma ta ce ma Rukee inhar akwai matsala karkiji komi ki kiramu kinji ko"
Ta ce, "in sha umma Ba abunda zai faru ma"
*Dakin su Abba na*
"Maijidda,bari na gaya maki abu na karshe wanda daga shi ba zamu sake maganar Auren nan dake ba, LAYLA KO MUTUWA TAYI SAI AN DAURA AN KAITA GIDAN MIJINTA SANNAN A KAITA KUSHEWA,don haka daga rana mai kamar ta yau karki sake tun karata da maganar auren Roohee inhar ba abunda zai amfani auren bane, na gama magana"
Ya juya yai kwanciyarsa ya bata baya,umma cike da bakin ciki da takaici haka wuce ta shiga toilet don yin wanka.
Washe gari da safe duk yan cikin gida kowa yazo don duba jikina saboda jin halin dana kasance ciki a jiyan zuwa yau da safen,da sauk'i sosai don karfe goma da raabi na safe allurar ta sake ni,ina bud'e idona akan sa asuka sauka na rufe na sake bud'ewaa tunanin ko mafarkin daya aure ni ne nakeyi,amma still shine zaune gabana muna kallon juna......."How are u feeling now?"
Abunda ya fara fad'a min kenan yana ci gabaa da kallona,dan danan idona yaia rau rau zan fara kuka cikin sauri ya ce, "please stop it,kiji tausayina mana kukan baya isarki haka,bana so kinji"
Ga ummana ga mamin sa,ga Rukke da ummi har ma da Anti Rafeea da tayo sammako tazo gani na,ga Yah Fahad duk za gabansu yake maganar,kamar ma ba kowa gaban mu.
Lumshe manyan idanuna nayi masha Allah,sannan na bud'esu ina kalon kowa dake wajen, "Roohee yajikin,?"
Muryata ta sake koma wa yar firitt fiye ma da sadda nake kal'au, na ce "Da sauki Mami,"
Kowa yai mun sannu da jiki na amsa Anti Rafeea ta ce "mi kike son ci"
Na kalle shi wanda har sannan ni yake ta kallo kamar tv, na girgiza kai "Bana son komi Anty..........ki had'a mata tea mai kauri da zafi ta fara dashi,sannan ki soya mata planten da wainar kwai,idan taci sai tasha magunguna"
Abunda ya fad'a kenan,na turo bakina cikin shagwab'ar da na saba masa, "ni bana so"
Ya harareni kad'an ya ce, "ni kuma ina so"
Ummana da Mami suka fita, Yah Fahad ya ce "tunda kin dawo hayyacin ki ni bari na fita to"
D'an murmushi nayi k'adan wanda rabona dashi kafin a fara wannan dambarwar, shima ya fita yabar mu nida Shi da Rukee ummi ma tabi bayan Anty Rafeea,
Mukai shiru mu duka ba mai magana,Rukee dai toilet ta shige don had'a mun ruwan wanka,ita har yanzu banga wani reaction a tattare da ita ba akan batun auren ta da Yah Fahad,kodan bamuyi mgnr bane oho!
"Kizo kiyi wanka kafin ta gama had'a miki break din"
Kallon sa nayi shima idonsa cikin nawa,wani irin lumshe su yayi ya bud'e akaina yana jinjina mun kanshi alamun inje inyi d'in, na shagwab'e fuska kamar zan kuka "to karka tafi pls"
"Ina nan har sai kin karya,kije kiyi"
Hannuna na mik'a masa alamun ya tadani,ba musu ya mik'o mun nashi muka rik'e juna, wani sabon reaction ya shige ni kamar in dawwama ina rike da hannun nashi,dai dai shigowar Abba Habibu da Mama sai y'ay'an su, Oga kucaki da mabiyan sa, zame hannuna yayi yana mik'ewa cikin bada girma ga Abba Habibun ya ce masa "ina kwana Abba"
"Lafiya lau Rafeeq ya karfin jikin naka?"
"Da sauki Alhamdulillah"