Sashe 5
Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Acikin compound d'in gidan can cikin rumfa inda ake parking motoci,shimfid'a akai isassa da darduma babba Abban na tsakiya su suna gewaye dashi, Rafeeq da Fahad sune karshen isowa on ready RAMADAN yana wajen zaune, da alama sun jima suna magana da Abban, Fahad yaba Yah Ramanda hannu sukai musabaha sannan ya zauna gefensa, amma Rafeeq yai mirsisi kamar bai san da akwai mutum a wajen ba, Abban suka gaisar sannan suka natsu don jin dalilin kiran, "RAMADAN bude mana taron da addua"
Ba busu cikin daddad'an lafazee nashi da cikekken tajweed cikin karatun ya kammala tare da bukatar a karanta salatin Annabi aka shafa,sannan Abban ya fara da Rafeeq.
"Rafeeq banga ka ba d'an uwanka hannu kun gaisa ba kamar yadda Fahad yayi"
Sunkuyar da kai yayi kunya na kama shi ainun,Abban ya juya ga Yah Ramadan "Kai ma maimakon ka bashi hannun tunda shi bai hakan ba sai ka share shi, ashe abunda ake gaya mun akanku da gaske ne cewa gabar kuke?.........Abba ni bana gaba dashi wallhi"
Yah Ramadan ya katse Abban da fad'ar haka.........Aa kar ku maida ni sakarai mana,ba gashi kun nuna a gabana ba,ashe ku da zaku ga yara k'annan ku naayi ku tsawaatar ku dai-daita su shine ku ke aikata hakan,to ku gaya mun yadda za ku iya sasanci ko gyara b'araka irin wannan cikin k'ananku?"
Duk sukai shiru bamai magana saboda sun san basu da gaskiya,Abban bai saurari jin tsakanin su ba ta ci gaba da cewa, "kune manya ku zaku gyara zumuncin dake k'ok'arin lalacewa a cikin gidan nan,koma minene yasa bakwa ga maciji da juna bana son inji, abunda nake so shine daga raina irin ta yau inason naga canji a cikin mu'amalarku,inaso ku zama yan uwan da ake kwatance daku,inaso ku had'a kanku ku ukun nan ku yak'i rikicin dake cikin gidan nan,saboda watarana kune iyayen mu bama nan ta Allah ta kasance damu kasa ta rufe idonmu,idan har akace tun yanzu bakwaa shiri da juna ta yaya kenan saura zasu so yan uwansu,?"
Kowa yai shiru yana nazarin maganarsa wanda kowa yasan haka maganar take,don ba shakka zumuncin gidan nan na neman tab'arb'arewa,......."Don haka yanzu ba sai anjima ba kuyi musabaha da juna, tare da niyyar kun yafi juna kuma komi idan ya taso zaku zauna ku tattauna a a Fahimci juna,Ban da Matsala da Ramadan nasan duk abunda na d'ora shi akai bazai tab'a bijirewa ba,to inaso kuyi koyi dashi,Bismilla kuba juna hannu tare da Sallama"
Jikin su yai sanyi sosai karma ace Rafeeq daya dauki abun da zafi fiye da Ramadan d'in, cikin sanyin jiki Rafeeq yaba Ramadan Hannu yana masa sallama,shima ya bashi nashi suna gaisawa tare da amsa masa sallamar.
Fahad yai murmushi yace, "That's my brothers i like"
Abba ma yai murmushin suma duk sukai, Rafeeq yace "Abba kai masa fad'a akan rashin sake fuska,yana d'aya daga cikin abunda ke had'ani dashi"
Fahad yai dariya Shidai Ramadan murmushin kurin yake, Abban ya ce "to kaji Yah Ramadan,ko yaya ne a ringa ma y'an k'annan nan naka fara'a"
Shafa kanshi yake cikin muryarsa irin ta y'an gayu kuma silently calmly ya ce, "Shikenan,daga yau zan fara salan kuma ace tayi yawa"
Duk sukai dariya abun da yai ma Abba dad'i kenan, sannan ya gyara zama ya ce "Alhamdulillah Allah ya kawar da shaid'an tsakanin ku,magana ta gaba itace akan AURENKU ne,nasan kowa baya jin son wacce aka had'a shi da ita,bama kamar kai Rafeeq duba da yadda lamarinku yazo shi ya sake damalmala komi,inaso na baku hakuri kuma na rok'eku alfarma ku ba marad'a kunya,don Allah Ramadan,RafeeqFahad ku zama masu nuna biyayya ga abunda muka d'oraku akai,wannan auren yana daga cikin babban abu da zai kawo lalacewar zumuncin gidan nan,haka kuma shine abu mafi girma da zai kawo cigaba da sake d'orewar zumuncin,don haka ina jan hankalin ku da cewar duk ruwa duk iska karkuyi sake da matanku,kar kuyi abunda zai kawo cikas da yan tsugunne tsugunne,bance mutum in yaga wata yana so nan gaba karya k'ara ba,amma ya zama banda wulakanci banda tozarci inhar aka samu d'aya to ni bazan bada goyon baya ba,don Allah ku nuna mun cewar ni d'in na isa daku"
"In sha Allahu Abba ba zamu baka kunya ba,zamu yi bakin iyawar mu"
Cewar fahad kenan,Rafeeq ya ce "zamu kiyaye in sha Allahu"
Ramadan ma ya ce, "zamu yi duk yadda kace Abba in sha Allah"
Abban ya ce, "Allah ya yarda,sannan Rafeeq inaso ka zaunar da qanwar ka Roohee kai mata nasiha matsayin yayanta,sannan ka nuna mata yadda kai ka hakura ka amshi Kyautar da akai maka itama tayi hkr ta amshi k'addarata da hannu biyu,kila ta d'an sauko daga yana yin da take ciki"
Kanshi k'asa yace a sanyaye, "zanyi mata magana Abba In. sha Allah"
Sun jima yana nusar dasu abubuwa da dama da kuma kara haska musu rayuwa,saida aka soma kiran sallar magriba sannan suka tafi masallaci tare, har cikin ran Abba yaji dad'i sosai.
*Bayan kwana biyu*
Yanayin jikina ya sauya sosai na samu sauk'i don ina yin sabgogina yadda na saba,na kuma koma wajen aikina da nake service bautar k'asa wadda bamu jima da farawa ba, anyi jajena sosai friends d'ina suna ta fad'ar ramata alamun nayi ciwo ban gaya ma kowa ba azo a aganni,yak'e kurin nake musu saboda dai bazan iya musawa ba,saidai na basu hakuri akan cewar zan gyara next time,abubuwa da dama na daina tun dana dawo natsuwata sune bana zuwa b'angaren Hajja kwata-kwata,sannan bana fira da kowa duk nacin mutum,inma ta kama maganata da Rukee kawai nakeyi,sai ummanmu suma d'in daga uhm sai Aa sai tayi wuyar gaske inyi sentence da bai gaza kalma goma ba,sannan na daina zuwa b'angaren Mami in ta shigo wajen Ummanmu zan gaidata,tayi k'orafin har ta gaji kuma sun san dalilina nayin hakan,ba komi bane face bana son koda hanya ta had'ani da Yaj Rafeeq,muddin ina ganin sa ciwon dake cikin raina ba zai tab'a warkewa ba,Abba kuwa yasha jinin jikinsa daga yadda na koma tsani na dashi,iya kata gaisuwa da safe in ya fito zai breakfast ya tafi wajen aiki,daga haka bana sake cewa dashi k'anzil,bana tambayarsa ko biyar bana wata huld'd'a dashi bayan wannan.
Kowa dai yaga canji sosai tattare dani wanda ya kara ma gidan zama silent sosai da sosai,kowa baiji dad'in yana yin da nake ciki ba amma kuma ba su da wani abu da zasuyi mun da zan iya dawowa LAYLA ROOHEE ta ainahi, wani lokacin idan na tashi daga wajen aikin mu zan wuce gidan Anti Rafeea inyi zama na sai dare nake koma wa gidan,don da anga ma ban dawo da wuri ba to ansan inda naje, itace kad'ai bata gajiya da lallashina akan in saki raina,babu wani tsanani da Allah ke d'orama bawa don baya son shi,jarabawa ce yake maka don ya auna girman imanin ka,sannan a duk sadda Allah zai daukaka darajarka tofa sai kasha wahala kafin wannan daukakar tazo..........."Auren Yah Ramadan d'in shine d'aukaka Anti?"
Abunda nake gaya mata kenan,saidai tayi murmushi tace "shin kin san abunda Allah ya b'oye a cikin Auren nashi?bana so kiyi abunda zaki ciji yatsa nan gaba Roohee,.............Anti idan kin san irin wad'anan maganganun zaki ringa mun zan yafe zuwa gidanki na har abada,taya zan zo don na ringa samun sassauci anan amma ki isheni da wadannan maganganun,bana so gaskiya ki daina"
"Allah ya baki hakuri in Allah ya yarda ba zan sake miki magana akan Abunda ya shafi Yah Ramadan ba,in har bake kika mun ita ba"
Dajin kalamin taji haushi ammaa bata nuna mun ba, nace "Allah ma ya tsareni da maganarsa,yo wannan Allah na tuba har abun ai magana akansa ne"
Girgiza kai kurin tayi ta rabu dani,daga ranar bata sake yi mun mgnr auren bama gaba d'aya saidai shawarwari da suka shafi rayuwata.
B'angare guda shirye shiryen Auren ake don an siyo kayan saka rana na kowane b'angare,ana jiran lokaci an sanar da dangi da abokan arxiki da zasu anshi kaya,duk da dai agida d'aya muke amma baza'a fasa al'ada ba,Goggo habi na tafe ita dasu Mufee abunda ya d'an sanya na saki raina amma ba dariya nake ba,don rabona da ita har na manta ma gaba d'aya koba komi zamu had'u da Mufee jinin mu yazo d'aya ainun,acikin sa'anin mu Najiba ce kad'a a ware kuma itama dalilin iyayen mu mata yasa muka wareta,duba da cewar ba a shiri da uwarta da uwayen mu mata,duk da mun san cewa ba dai-dai bane hakan amma mun kasa jawota cikin mu,itama kuma sai ta janye daga garemu inba dole ba bata shiga duk abunda zai shafi sabgarmu.
Ana gobe ansar kayan saka ranar mu na tashi aiki na wuce gidan Anti Rafeea nai zama na, aiki ma na d'an taya ta mijinta zai bak'i da daddare zasuyi meeting shine akai masu meat pie da samosa da cake,sai kaji da aka soya tun rana ake aikin sai magrib muka kammala,mukai wanka ta bani wasu daga cikin kayanta na saka kasancewar jikin mu guda,saidai nafita Boob's don rigar ta kamani sosai,ina sallame sallar magariba kira ya shigi wayata,haske na gaani tana yi yasa na gane kirane don bana barin wayata da ringtone, wanda banyi tunanin kiransa ba ne ya kirani YAH RAFEEQ........wani irin fad'uwar gaba naji ras ras ras,har saida na rufe idona ban ankara ba ta tsinke ba jima wa kuma ta sake shigowa, ni kad'ai nasan irin bugun da zuciyata ke mun,kamar nayi gudun kilometer dari da hamsin tsabar yadda take bugawa, ban san hannuna ya d'aga kiran ba,ahankali kamar wacce hannunta baya aiki sosai na saka a kunnena nakasa cewa komi.
"Kina gidan Rafeea ne?"
Abun da ya fad'a mun kenan, kaina na d'aga masa nama mance ba ganina yake ba,daker na dai-daita kaina na iya fad'a "Eh,amma yanzu zan tafi gida"
"OK,wait for me"
Ya kashe wayar ya barni da zullumi har wata zufa nakejin tana karyo mun tsabar shiga zullumi,to mi zai kawoshi wajena?har cikin raina bana son ganin sa don kuwa ganin nashi maaiface a rayuwata,
"Roohe lafiya kuwa?"