← Book details Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 38

Sashe 6

Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai hawaye sharrrrr na rik'e hannunta muka zauna bakin gado ina hawayen na ke cewa, "Yah Rafeeq zai zo nan,ni kuma bana son na ganshi Anti,pls kice karya zo don Allah ga wayata ki kirashi kice komi zai fad'a mun ya fad'a miki saiki fad'a mun"............tausayi ya kama Rafeea cikin lallashi ta ce "ya isa haka minene na tashin hankali a ciki Roohee?Yah Rafeeq ne fa ba wani ba,babu abunda zai Faru kinji ko,shima nasan babban dalili ne zai sashi neman magana dake a keb'ance,ki kara daurewa komi zai wuce"

Kasa magana nayi na dora kaina a cinyarta ina shashshekar kukan har na samu ya tsaya, "in sha Allahu Roohee wata rana zaki bada labarin wannan yana yin da kike ciki,zai wuce har sai kinyi mamakin wucewar sa"

Nidai bance komi ba ta sake cewa, "bari naje na idasa shirya musu falon bayan sallar isha'i zasu zo"

Na tashi daga bisa cinyarta na koma bisa filo na kwanta idona rufe ban san wane irin kalar tunani zan ba,
Na shafe a kalla minty talatin a haka kafin Iklas babbar yar Antin ta shigo ta ce "Ammi Roohee Anna ta ce kizo uncle Rafeeq yazo yana karamin falonta"

Kaina na d'aga mata kawai har ta fita na kasa tashi daga inda nake, saida Antin ta shigo ta ce "wai miye haka kike yi,haba Rooheen umma tashi kinji ko"

Tashin nayi na dauk'i gyalena madaidaici na yafa ga kafad'ana guda kurin na dauki wayana na fito, ina tafiyar kamar iska zata kayar dani tsabar bana da wani nauyi da kuzari jikina,da siririyar sallama na shiga falon wanda har k'amshin sa ya isko ni wanda ke sake samun son kasancewa dashi a kullim,

Ban yadda na ciro kaina na kallai ba na dai zauna cikin kujerar farko dana isko kaina k'asa na ce a sanyaye,

"Ina yini Yah"

Shiru na wani d'an lokaci banji ya amsa ba mafarin naa d'an ciro kaina na kalli inda yake kyakkyawan four eye's mukai da juna ya tsareni da kallo,idona yai k'wal-k'wal zan kuka na ce "shine zaka k'i ansawa"

Sauke wani gauron numfashi yayi yana cewa, "naga ko kallonaa bakya son yi shiyasa,ammaa yanzu sake gaidani zan ansa"

Ban san sadda idanuna suka maka masa harara ba na kawar da kaina, naji ya ce, "kai kai kai,ni kike harara ko?uhm kin kara ma kanki hukunci akan wanda ke jiranki,"

Na sake watsa masa wata na ce, "ni zan tafi"

"Kin san fa bana son ana hararata,tau gara ma ki daina yarinya,"

Sai kurin na saka masa kukan dake ta kai kawo a cikin kirjina, kuka sosai wanda daman jiran abun da zanyi sa nakeyi,ai ko a rikice ya dawo kusada ni a k'asa yana magana cikin kid'ima,don a rayuwar sa babu abunda ke saurin nuna weakness d'insa irin kukana........"Rooh pls stopped,kin sani bana so don Allah ki daina, karki sa na kamu da rashin lafiya,in dan nine kiyi hkr ki fad'a mun me na miki amma pls stopped kinji"

A rayuwata babu abunda da nake so sama da a lallasheni idan ina kuka, ya sani sarai shiyasa yanzu ma nad'an sauko na fara rage kukan ina cewa, "gashi nan hankalin ka a kwance shirin aure kake,ga dukkan alamu baka damu da halin da nake ciki ba,watau kama amunce da wacce aka baka kenan"

Ina shashshekar kukana kasa-kasa,ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi ya ce "Rooh kece fa kike guduna,duk hanyar da zan ganki kinbi kin toshe ya kike so inyi, sannan koda na tashi hankali na kamar a farko Rooh ba abunda zai canza k'addarar mu,a riga ta faru babu yadda zamuyi da abunda Allah ya shirya a tsakanin mu,daman ba zan zama mijinki ba kema ba zaki zama matata ba,wanin junan zamu aura pls and pls Rooh ki cire komi ya fawwalama Allah kinji ko,"

Hawayen sunk'i tsayawa nake cewa, "taya zan iya cireka a raina da sunan wanda nake kauna nake burin Aure,taya zan canza wannan mafarkin nawa na sanya wani akai?wallahi bazan iya ba,koda anyi wannan auren sunan anyi ne amma bazan tab'a zama matar wannan k'azamin kuma kucakin ba har abada.............RAFEEQ KABAR PHONE NAKA ANA TA KIRA"

maganar kurin mukaji ba tare da munji sallama ko motsin da zai aankarar damu shigowar sa ba, kallon wulakanci na watsa masa na kawar da kaina ina goge hawayena, ko a jikina ban damu dana yaji kalamin da na fad'a ba,sab'anin Yaj Rafeeq da yaketa jin kunya yake kame-kame, "Ayya na shafa'a ne, na barka kana ta jira to ka shigo ka zauna sai mu wuce,har ma kun gaisa da Wife d'in taka to be ko?..........Allah ma ya sawak.........zan sab'a miki idan na sake jin wata magana marar dad'in ji anan LAYLA"

Yah Rafeeq ya fad'a cikin fushi sosai da na dad'e bangan shi a ciki ba,fuskar sa ta d'aure ta mau ainun kamar bai san dariya da murmushi ba, Yah Ramadan ya ce "sai ka fito ina jira"

Ya fice ya barmu anan zan cigaba da kukana ya ce, "tun da baki san lallashi da banbaki ba zan tattaraki na fita harkar ki,rashin kunya da fitsara ba halinki bane karki sake ki aro su ki yafa ma kanki saboda kina k'insa, don nasan watarana zaki nadama,nasiha nazo inyi miki matsayina na yayanki kuma wanda kika fi shak'uwa dashi a duk cikin yayyenki maza,Aure babu fashi Rooh sannnan masifarki da rashin kunyarki da duk wani kalar wulakancin da kika tana da don shi bazai fasa komi ba,saima dai ke ki jefa kanki cikin wani hali,don nayi imanin RAMADAN ko sama da k'asa zata had'e bazai tab'a SAKIN ki ba,don kuwa shi d'in mai biyayya ne ga umurnin iyayensa,da duk wani na gaba dashi nai masa wanna shaidar,don haka shiyasa muka muka daura d'amarar koyi dashi nida Fahad,zamu zauna da matanmu cikin amana da kwanciyar hankali har Allah ya kawo ranar da zamuji muna son su,tunda zuciyoyin mu ba a hannun mu suke ba suna hannun Allah,a duk sadda yaso yana iya canza komi,don haka don Allah Rooh don girman Allah ki zauna bil amana da RAMADAN, wallahi summa tallahi zakiji dad'in zama dashi baida fitina,baida hayaniya baida mugun nufi akan ki akan kowa ma,in kikai hakan zanji dad'i kinji nasiha ta kuma kin girmama maganata, ina miki fatan alkairi Allah ya canza abunda yake zuciyarki"

Sosai nake kuka wanda har bakajin muryata saboda yadda nakeyin sa cikin fidda zallar bakin cikina,

Har ya juya zai tafi ya tsaya bai waigo ba saboda kukan yana tsananin ratsa shi,wani yana yi dake cinsa yana neman galaba akansa ya ce, cikin raunanniyar murya "bazan tab'a juya miki baya ba Rooh,duk sadda kike da matsala karki tun kari kowa kizo gareni,duk girman ta ina fatan Allah ya bani ikon warware miki ita, Bissalam"

Mom muhseen&Asaad

_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_

*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*

By
Mom muhsen&
Asaad.

Wattpad name
Humaira3461.

🅿️.....5

Saboda halin dana kasance a ciki yasa saidai a gidan Anti Rafeea na kwana,don kuwa kuka nasha na koshi wanda har sai da ya haddasa mun ciwon kai da zazzab'i, na kuma hana ta sanar da Ummanmu kowa ma hana ta nai ta gaya mashi, saboda bana son wannan taron dangin akaina.

Raba dare mukai tana lallashina da bani hakuri tana nuna mun shi namiji ma ya hakura ya kauda komi saini ce zan nace inyita damun kaina da rashin zaman lafiya? Da nasiha da ban baki har dai na samu nai shiru, ta kawo mun meatpie naci da tea mai kauri nasha magani sannan nayi isha'i,na dora da shafa'q da wutri, na jima a sujjadata ina kuka saboda adduar da zanyi nauyi take mun, daker na iya ambatar "Allah ka samun sauk'i da salama a cikin zuciyata,ka sassauta mun zafin kishin yah rafeeq ka sassauta mun kaunarsa ya Allah"
Da wannan na samu nai bacci wanda na jima banyi irin sa ba.

********

Tun daga wannan rana na koma yin rayuwata kada ran-kada han,ni bana cikin farin ciki haka zalika bana cikin k'unci,yadda nake da magana amma yanzu wuya take mun ainun,ummanmu duk juyin da zatai inyi fira da ita bana iya wa Abba kanshi duk ya damu da yadda na sauya masa,iya kata dashi ina wuni ko ina kwana,sannan in an had'u cin abincin dare nice farkon gama wa in tashi kuma in na saddar da kaina k'asa bana d'agowa har sai na gama,saboda kowa ma ni bana son had'a ido dashi.

Bikin ba fashi an sanya shi wata hud'u anan gaba,don tuni har anfara shirye shirye, daga b'angaren iyayen mu duk yadda basa son bikin amma bai hana sun fara shiri ba baji ba gani, ni kam nuna wa nake kamar ban san me ake ciki ba,nafi zaman gidan Anti Rafeea don can ne kurin nake iya fira sosai,Rukee kanta tasan na canza amma ba yadda ta iya dani dole ta samun ido.

Rannan ina kwance uwar dakar ummanmu naji suna wata magana ita da Mami akan aurena da YAH RAMADAN, wadda nan take shawarar bata shigan ba,

Ummanmu ce ke cewa Mami, "Safiya wallahi auren Roohe da yaron can neman d'ora mun hawan jini yake, dana zauna ban da wani tunani sai na neman hanyar dazan lalata abun,wallahi ni rayuwata ma ban jin akwai abunda na tsana irin auren nan nasu,duk hanyar da nake tunanin zanbi sai maganar Abban su tai mun tsaye a rai,ban san ya zan ba"

Mami ta ce, "Maijidda kenan, ke yanxu har sai hanyar raba wannan auren ta gagareki?ni nan jira kawai nake inji kince mun kin shirya kawai mun nntaya tare,"

Umma ta ce cikin rashin Fahinta, "Bangane ba?wace hanya ce wannan haka da ban san da ita ba,kimun yadda zan gane"

Dariya mamin tayi tana cewa tare da rage murya, "hajiya Huda k'awar nan tawa take bani labarin wani malami wallahi ya kware da aikin sa, tun da taje wajen sa ta samu kan d'anta isah da matar ta rabata dashi, to shine tun da taji halin da muke ciki tace wallahi zata raka mu cikin kwana uku maganar auren zata lalace na Roohe da Rafeeq, don wallahi da ya auri d'iyar mak'iyyata gara ya dawwama babu aure"
Chapter 6 · 0% Book details