← Book details Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 38

Sashe 18

Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rayuwa ta cigaba da tafiya a cikin gidan kadaran kada han,ba wannan zumuncin sosai haka babu wannan gabar mai tsanani,saidai kuma har yau su Ummanmu basa hulda da mama itama kuma daman bata shiga tasu Huld'ar,tana dai sauke hakkinsu dake kanta ta kuma ja girman ta ba ruwanta dasu,haka aketa tafiya gidan kullin in muka zauna fira falon Abbanmu nasiha ce da jan hankali tsakanin mu dasu Abba Habibu,ya daina fad'anan sosai saidai janmu ajiki da nuna mana hanyar data dace,har muka saki da tsanar da muka kwallafa musu,amma ta Yah Ramadan na nan daram a sak'e a gefe,don bana jin shi zan daina tsanarsa saboda abunda yai mun.

Shikenan muka koma sama-sama dasu Najeeba,Ammi dama ta koma tun tuni ita dasu kausar d'in,yah najeeb ya dawo hutu shi muna gaisawa duk sadda aka had'u,daga ba gaisuwar ba babu wani abu dake sake had'amu,to wannan abun ya kawo farin ciki sosai a fuskokin Abbanninmu,sai suka zage wajen hidinta mana komi muke so duk tsadar sa Abba da Abba Nura zasuyi mana,don daman komi namu sukeyi tunda Abba Habibu bai aiki tun fil azal bamu tashi munga yana wani aiki ba,komi daya shafi iyalinsa da hidimarsu Abbanmu keyi shida Abba Nura,don ma dai Abbanmu yafi Abba Nura samu sosai don shi Abba Nura Babban lauya ne da akeji dashi cikin garin abujar,shi kau Abban mu NNPC yake aiki kuma yana da babban muk'ami sosai,bayan haka suna kasuwanci shida Abba Nuran sai suka sanya Abba Habibu ciki,duk wata alwuns suna shigar ma kowa ta bankin sa,to inba wannan ba Abba Habibu bai komi gaskiya tunda bai karatu ba,primary kawai yayi.

Wannan kenan!

Tsakanina da Yah Rafeeq kuwa sai dai ince Aure ne kawai ba a daura mana ba,amma soyayya tayi nisa wanda zaka dauka an saka mana rana,amma muna kokarin kiyaye duk abunda bai kamata ba,duk kuwa shaid'an yana d'an samu nasara wani lokaci,amma muna baki iyawar mu wajen ganin bamuyi abunda zai jefamu ga dana sani ba,a wannan lokacin bana jin komi sai nishad'i da annashuwa,don Yah Rafeeq yana samar mun da natsuwa fiye da kima,wata irin kauna da soyayya yake mun mai ratsa dukkan jiki da b'argo,idan ina waya dashi bana son koda k'uda ya gifta tsakanin mu,wata natsuwa nake kamar ina daukar wata muhimmiyar lecture,har an gane mun ma in ina waya dashi ba mai mun mgn,don ba ji zan ba shiyasa na rage zaman fira,ina daki abuna muna soyewa salo-salo na daukar hankali ban san na iyaba sai da nafad'a tarkon sa,nida shi bazan iya gane wanda yafi son wani ba,ko fad'a bama yi sai muyi wata bamuyi fad'a ba shiyasa shak'uwar mu tai k'arfi sosai,muna tsananin ji da juna kamar rai sannan muna kishin juna kamar hauka,inhar yaji zan fita zuwa wani waje hankalin sa tashe hake,haka zaita damuna da kira yana bani umurni ga yadda zanyi,kar in sake inyi murmushi har in dawo,sannan dole na ringa saka nik'af da doguwar abaya,doka kala-kala da yake son sa nake bana iya sab'a ko daya daga cikin dokarsa,Rukee har mamaki nake bata tasha ce mun, "ke kam yar wahala ce,yanzu shida ba ganinki zai ba bainan yana can wata uwa duniya shine kike biyesa kike duk wannan abun,lallai ba ayi namijin ba walllahi"

Murmushi kawai nake mata in ce, "ba zaki gane miye so ba sai ranar daya sark'e ki,a sannan zan gane shin Rukee tana da wani ra'ayi ko saina habibinta"

Sai dai ta girgiza kai kurin ta rabu dani,to shima kuma inhar naji muryar wata a kusa dashi ranar bamu wanye wa lafiya, rigima muke sosai saboda zafin kishin sa da nakeji,gani nake kawai k'wace mun shi za'ai balle can akwai yan mata masu sunan yan mata da suka dameni a komi,india fa!ai karshen kyau kenan.

To da muka gane cewar ko wannen mu nada kishi sosai kan d'an uwansa sai muke kiyaye abunda zai motsa mana shi,muke zaman mu lafiya har Allah yasa muka shiga jami'a muma.
Wata private university dake nan cikin Abuja wai ita *BAZE UNIVERSITY* Abbanmu yai mana komi da komi na zuwa makaranta,hadda sabbin d'inku na mukayi Abba Nura yabamu kudi muka shiga kasuwa muka siyo kayan duk da muke buk'ata,jakunkuna da takalmomi,da sauran tarkace na yan mata masu ji da kansu,shigata jami'a ya jawo mun farin jinin samari sosai ma duk da na kasance mai killace surata,bana yadda na bayyana zahirin kyauna kodan kar wani yace yana sona ina kiyaye ma Yah Rafeeq wannan bangaren,Rukee har ta gaji da mamakina yadda na maida kaina wata matar aure wajen kula da rufe duk inda zai bayyana kyawun ta,amma duk da haka ban tsira ba daga samarin cikin makaranta,yanzu driver na musamman Abba ya samar mana yace saboda Yah Ramadan bai da lokacin da zai ringa kaimu da dauko mu,saboda yana zuwa wajen aikin furniture's ranar da naji wannan labarin munyi dariya sosai nida Ruky,lokacin munje yima Abba Nura sannu da dawowa yayi wata tafiya muka same su suna maganar,wai ana biyan sa a sati dubu goma,wanan yasa bamu san sadda dariyar ta kwace mana ba,sosai mukai tayin dariyar aiko ran Abba ya b'aci sosai da sosai saida muka gwammace bamuyi ba,don wayar charger ya dauko ya dunga tsula mana,rabon kau da adake mu har mun manta har kwalla mukai ya kuma ce mu bashi hakuri.

A rayuwata abunda yake kunsa mun bakin ciki kenan,ace in bashi hakuri ina hawaye da shashshekar bakin ciki na ce, "I'm sorry"

Uffan bai ce mana ba har Abba ya kora mu yace ko kudin break ba zai bamu ba yau,ya kuma sanar da Abbanmu abunda mukai,shima yace sai munyi kwana uku ba abami kudin break ba,aiko munji jiki kuma mun sakejin tsanar Yah Ramadan,saboda duk don saboda shi akai mana haka saidai ummanmu ko Mami wani ya bamu,duk da ba zasu kai yawan wanda su Abba ke bamu ba,don mu a rana ma muna iya had'a 30k ba wani abu bane wajen mu,shiyasa ai mukai dariya jin wai har sai anyi kwana bakwai sannan zai samu 10k abun da dariya wallahi,shi karatun ma bai mashi rana ba tunda almost 2years bai ci moriyar sa ba,daman kuma daker aka sha wajen karatun.

***********

"Gafara dai masu wuri,ai mana iznin shigowa da iznin zama,"

Wata mahaukaciyar dariya ce ta karad'e dajin har cikin dodon kunnenta,duk da cewar ba yau ta fara xuwa ba,amma kuma ta kasa sabawa da jin wannan dariya mai sata jin kamar zatai fitsari a wando,zuwa wani lokaci kuma dariyar ta lafa sanna taji sautin maganar bokan daga can saman wata gingimemiyar kuka bama a ganinsa,saboda duhun dajin da kukar.

"Sai yau kika wai waye mu kenan?hajiya kina wasa fa naga kin Fara tsorata da lamarin,karki sake kija baya inba haka ba komi zai lalace,zakisha mamaki nan gaba inhar kika ja baya damu"

Jikinta na rawa take cewa, "wallahi rashin kud'i sukai mun tsaye kwana kin nan,shiyasa kajini shiru,kai kuma ba a zuwa maka saida kud'i shiyasa saida na tara iya tarawa sannan nazo ayi min aikin gafara"

Wani sautin gurnani mai karfi ya karad'e wajen,saida ta dod'e kunnenta sannan ya ce "ga mutumin nan ya bayyana kiyi masa bayanin komi,yau dai kandala bata kusa na aiketa wani tsibiri inkin dawo wani lokacin sai ku gana,amma kin san kafin kiyi bayanin sai kin aje kud'i ko?"

"Na sani nakan tudu,shiyasa ban fito ba saida na shirya"

Ta zage jikkarta ta aje damen kudi sunkai miliyan biyu,sannan wannan dariyar ta sake karad'e dajin na wani lokaci sannan ta tsaya, "kiyi bayanin ki dan duwala yana saurare"

Ta gyara zama tana cewa, "godiya nazo na karayi maka d'an duwala aiki yana tafiya yadda ya kamata,wannan yaro dai har yau ba batun wani aiki sai kame-kame da yake,to haka nake so rayuwar sa tai ta tafiyar har abadan babu wani cigaba kamar dai yadda aka hana shi yayi karatun kirki wanda yayi ma don shine rabon sa,a hana shi duk wani abu da zai kawo masa cigaban rayuwa,sannan a sake cusa ma mazajenmu tsanar taimakon sa duk da kace zai wuya,to nidai a dage kota halin yaya ne a hana su taimakon shi,sannan bamu son yaranmu su sosu a damalmala tsakanin su,in bacin wannan ni banda wata damuwa sai ta uwar mijinmu dake son hanamu zaman lafiya,itama ai mana magninta karta sake uzzirawa mazanmu balle har su takura mana,sai kuma batun mijina asake kama mun shi sosai yadda duk sadda na nemi kud'i ba sai yaja ba zai bani,wannan shine kawai buk'atata"

Dajin ya sake daukar wannan dariyar fiye data farkon,kusan minty biyar har tafara kerma sannan ta tsagaita,amma tana yi kasa-kasa jitai na kan tudu ya ce, "buk'atar ki ta biya hajjaju,saidai d'an duwala yace kin tabbata babu wata matsala a had'in auren da kuke sonyi da y'ay'anku?"

Tayi shiru na wani lokaci kafin tace, "banda matsala da yar uwata,nasan hakan kuma suma yaran basu sa wata matsala,son junan su suke bilhakki da gaskiya ba za'a samu wata matsala ba"

"Ki je ki sake tunani,ki kuma saka ido ga yar uwar taki tunda kin yarda da ita sosai,kiga ba wata muna-muna da take kokarin yi? Sannan wannan yaro da kike ta kokarin a hana rayuwar sa tayi kyau,aikin sa babban aiki ne don nasha gaya miki daga shi har mazajen naku basu zaune haka nan,suna rik'o da azkhar sosai bama kamar shi yaron munsha wuyar aikin sa wancen karon sadda yana karatu,yana daya daga cikin nasarar gama karatun sa wannan azkhar din da yakeyi,gaskiya ki karo kud'i don na gaya miki taurarin sa sunsha banban da duk wani d'a dake cikin gidan nan,ke har mazajen naku taurarin yaron sun fi nasu kyau nesa ba kusa ba,in akai wasa arzikin da zai saiya kusan haukataki.........dakata nakan tudu bana son jin irin wad'anan maganganun,nidai ko nawa ne zan biya kar hakan ta faru,kai ni inba y'ay'ana ba kar wani yai arxikin da zai fisu,indai kudine zan kawo nawa kake bukata"

Wata mahaukaciyar dariya ya saki ya ce, "shegiya marar imani,to kamar wannan zaki karo daga haka komi kike so ki dauka anyi angama"

Ta Saki murmushi, "yawwa yanzu naji bayani,zuwa jibi zan dawo ma dasu"

Tatafi da baya-baya har ta bar wajen, saida tayi tafiya mai nisan gaske kafin ta shigo cikin wani kauye ta samu d'an mashin ya kawota cikin garin abujar.
Chapter 18 · 0% Book details