← Book details Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 38

Sashe 10

Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Uhm kema kin fad'a ai,ni na rasa wannan k'unata da yake yi da wad'ancan yaran(su Yah Ramadan) tunda sun nuna basa son shigowa cikin mu dole ne?ya barsu suyi sabgarsu muyi tamu mana,to gaskiyani ban yarda da wannan hukuncin ba,hakuri name zasu bashi sai kace sun zagi tsohon sa,wallahi ba zasu bashi wani hakuri ba saidai ya aje tukin...........dai-dai nan ya shigo da Sallama cikin muryar sa mai cike da mazantaka da kwarjini,naja dogon tsaki wanda nasan dole zaiji fuskar nan kamar kodayaushe ya gaida su Mamin,amma ba wacce ta amsa bai damu ba ya isa gaban umma ya aje key d'in motar yana cewa, "kiyi hakuri umma,indai akai wannan ne kibar b'acin rai nima Abba matsamin yayi,inbacin haka bazan anshi aikin daya bani ba,sannan ubana ne bazai sani abu ince bazanyi ba,amma tunda takai ga haka ki bashi mukullin motar sa kice yayi hkr daga yau bazan sake hawa ba balle rayuwaka su b'aci,har takai ga inda bai kamata ba"

Yana gama fad'in haka ya juya zai tafi, Yah Rafeeq ya ce, "wai kai nan zuciya kayi?ai wanda ke zuciya da abu wanda ya mallakin abun amma ba kai..........enough Rafeeq!!!"

Abunda bai tab'a faruwa ba kenan wai kaji Yah Ramadan ya d'aga murya da sunan fad'a ko b'acin rai,kowa yasan wannan..........

"Kar ka soma,ka tsaya iya matsayin ka zai fiye maka alkairi,kuma ni koda ban da abun to nafi karfin a wulakanta ni saboda shi,wannan shine"

Ya wuce kamar zai tashi sama,duk shiru mukai muka kasa magana,yah rafeeq ransa ya b'aci sosai duk da kuwa shine baida gaskiya, yace mun "ke kuma dalla can ki mana shiru da wannan kukan banzai,duk don zaki rasa mark dinki ne kike wannan kukan zanje nai muku submit,idan Abban ya dawo zanje na bashi hkr ya huce"

Har raina naji dad'in maganar, sai na tsaya da kukan, ya dalla mun harara ya wuce yabar falon,Mami tace "lallai yaron can wuyan sa ya isa yanka,shi nan har wata zuciya ce dashi...........yo ta banza da wofi inhar da gaske akwai zuciyar ya tattara tsaffinsa subar mana gida shine kawai"

Nan muka barsu suna tattauna maganar,muka koma d'aki muna cire kayanmu cikin sanyin jiki,duk da kuwa muna murnar dole Abba zai samar mana driver tunda burinmu ya cika.

Mom Muhseen&Asaad

_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_

*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*

By
Mom muhsen&
Asaad.

Wattpad name
Humaira3461.

🅿️.....7

Kwana kin da suka biyo baya Yah rafeeq ke kai mu makaranta,Abba yayi tafiya kwatsam shiyasa ba asake maganar ba Abba Nura kuma ba kasafai ya cika lura da abubuwa ba,kawai dai matsalar fad'an mu da Yah Rafeeq har muje sch muna fad'a dashi,in ya kaini bango inyita kuka dana fara kukan zai fashe da dariya,alamun yayi nasara.

Rannan har Rukee tace "ke kam dai to,har yau kin kasa Fahimtar Yah Rafeeq kukan ki fa shine alamun nasarar shi, da zaki burgeni ki ringa shanye komi zai miki,ni na rasa gane wannan kyara da tsokana tashi akanki,miyasa bai ma kowa ba sai ke?"

Alokacin ina cikin fushi ban bata ansa ba, amma nima abun yana mintsini na a rai miyasa bai tsokanar kowa saini?miyasa baya fad'a da kowa saini?rashin sanin dalilin yasa dole na bar a bun a raina.

Tunda wanan abun ya faru bamu sake ganin Najiba ba, daman kuma ko a sch ba had'uwa muke ba, ita tana B class mu kuma muna A kuma akwai tazara, daman kuma ba magana muke da ita ba itama kuma bata yi damu,don zan iya cewa tama fi yayanta iya b'agarar da mutum,ko iskar data kwasomu bata kallo balle ta tanka mana,inhar ta iske mu waje sallama kurin take bata kama sunan ko d'aya acikin mu,abun yana kara mana jin zafinta ainun,Rukee tace "kyale banza jin zafi ne kurin da Hassada"

To nasan akan Abunda ya faru ne yasa ta daina binmu,bamu san wanda ke kaita ba kila kuma taxi take hawa,.

Muna bangaren Hajja nida Rukee muna taya ta kwalemar bangaren Yah Rafeeq ya shigo cikin shigar sa ta gayu kamar ko yaushe, yai masifar kyau har fiye da kullin, brown shadda ce d'inkin zamani na matasa anyi masa harf jamfer ta d'an kamashi kad'an,ya saka hula milk da brown sai sawu ciki suma brown,kamshi kam kamar kamfanin turare ne a wajen,duk yadda nake zillewa kallon sa saida ya gane kallon sa nake, Hajja ta ce "kai Rafequ,wannan turare kamar na yan bori sai hawan kai yake,kaaji tsoron Allah ka rage sashi da yawa haka,ai saika dauki alhakina"

Me zamuyi ba dariya ba shima ya murmusa yace, "Hajja kawai dai kice nayi kyau ne baki iyawa, saiki b'ige da la'antar turarena"

"Haba dai,miye abun kyau anan Allah yajikan kakanku Alh matawalle in yayi gayu saboda kyan da yake har idon mutum disashewa yake,kaga kuwa ai baka kamo shi a komi ba,...........muka tintsire da dariya ganin yadda yake yamutsa fuska, na ce "gaya masa dai Hajja,"

Ya dalla mun wani banzan kallo, "ki fita idona kafin nai k'asa k'asa dake anan wajen,waya sanya dake iye"

Haushin ankushe masa gayun sa yake,dariya ta kamani Rukee dai tai gefe ta kame baki,don jibga takesha in ta shigar mun in muna abun mu, na ce "yo Yaj Rafeeq sai in k'i magana,ai gaskiya Hajja ta fad'a mu dai nan ba muga wani gayu na azo a gani ba wallahi.......a fusace yayo kaina na ruga bayan Hajja ina ihu.

"Kar ka kuskura Rafequ,akan me zaka daketa don ta fad' gaskiya komi?"

Huci kurin yake yace "wallahi Saina b'ata miki fuska,tun da na shigo na kasa dake?wajenki na zo,Hajjaa ki fita tsakanin mu kawai"

Dariya kawai nake masa Na ce "ashe babu dad'i kushen da kake ma wani,aiko wallahi daga yau na soma rama wa kodan kaji yadda nakeji nima........ban aune ba naji kauuuuu ga bakina,wani zogi ya ziyarce ni cikin azaba na fasa kara ina dafe wajen,dan danan har jini ya fito a lips dina Hajja ta ce "kai kai kai!Amma dai Rafequ anyi mugun mutun Ashe baka da mutunci ban sani ba,daga yarinya ta fad'i gaskiya shine kake son zubar mata da hakora saboda kana bakin ciki da kyawun da Allah yai mata?"

"Allah ya kyauta nayi bakin ciki da wannan yarinyar Hajja, ni kawai bana son rai ni ne kawai ba komi ba,kinga daga yau ba zata sake tsoma mun bakinta ba"

Ya juya ya fice ya barni inata kukana, Rukee keta ban hkr Abba Nura ne ya shigo ya nemi ba'asin kukana Hajja ta soma zayyane masa komi,hadda k'ari saboda itama abun ya bata haushi,cikin fushi ya sa waya ya kirasa "komi kake kazo nan wajen Hajja ka sameni"

Lallashina ya ringa yi yana ban hakuri tare da cin alwashin saiya sab'a ma shi,har sadda ya iso inata shashshekar kukana don ba kad'an ba bakin yake mun zogi ba,tun kafin ma ya zauna Hajja ta soma surfa masa masifa, "watau kai mai karfin duk duniyar nan shine zaka saki k'wanjin ka ka nausar mata baki,to wallahi ba zan lamunta ba ko ubanka ya rama mata ko ni in rama mata,"

Kanshi k'asa jijiyoyi sun fito sosai abunka ga farin fata,idon nan yai jaa sosai alamun bacin rai tsantsa tatare dashi, "watau ba zaka iya bud'e baki ka bata hakuri ba kenan,duk fad'an da zatai taje tai tayi bai dame ka ba ko Rafeeq?"

"Kuyi hakuri kuskure ne............karyar banza da wofi ba wani kuskure ai har shiga tsakanin ku nayi amma hakan bai saka ka fasa abunda kai niyya ba,yo Allah na tuba in bacin tsufa wallahi huncewa zan mu daku nida kai,bazan lamunci abunda zai takura mun takwarata ba eheee".........duk yadda naki cikin kunci saida nai dariya amma na duk'e ban yadda ta Gani ba,Rukee ce saida ta dara Abba kanshi murmushi ya saki,gogan ne kurin kamar ba ai komi ba fuskar nan murtik,nida aka zalinta ma ban kaishi fushi ba...........kalleni nan Rafeeq"

Ya d'ago yana kallon Abban, "sau nawa xan shata maka layi da Roohe?sau nawa xan maka magana akan tsokanarta da kake,watau ni ban isa in baka doka kabita ba ko?.........kayi hakuri"

Rafeeq ya fad'a kanshi k'asa yana kokowa da bacin ranshi, "yo to daman in ba hakurin ba me xaka bada,?ai ka riga ka cuceta kawai saidai Allah yai kata sakayya"

Hajja ta fad'a tana banka masa harara,Abban ya cigaba da cewa "wanan shine karo na karshe dazan ja maka kunne game da Roohe,inhar ka sake take dokata wallahi ni kadai nasan kalar hukuncin da zan maka, tashi ka bani waje"

Haka ya tashi a mutukar fusace,amma sai wanda ya sanshi sosai ciki da bai zai gane yana yin da yake ciki, Hajja taja tsaki bata ce komi ba illa dai nasan hukuncin bai mata ba, yajiyo kaina yana cewa "ki yi nesa dashi,bance kuyi gaba ba amma wannan tsokane tsokanen bana son shi,inkin san kina masa ki daina shi zai kawo rikici tsakanin ku,inkun had'u ki gaidashi da girmamawa yadda kike ma sauran yayunki,kinajina?"

"Naji Abba Zan kiyaye"

"Allah yasa,ku bani waje zan magana da Hajja"

Tashi mukai muka fito saida muka isa Dakin mu sannan rukee ta zube tana ta dariya kamar ba gobe, tun bata ban haushi ha har ta bani cikin fusata na ce, "wai miye ne?"

Tana rik'e cikinta take cewa cikin dariyar, "wai kina nufin Hajja bata baki dariya ba,wai in bacin tsufa huncewa zatai su daku..........murmushi na saki sosai ina cewa, "uhm Hajja ce fa,fiye da haka ma zata aika"

Ta zauna tana nishin dariyar ta, ta ce "kin san miya hasala mutuminki?"

"Aa saikin fad'a"

"Uhm kushe shin da kikai ne fa?baki san bai son ka kushe shi ba koda wasa?ba abunda ke saurin hasala shi irin kushe"

Jinjina kai nayi ina Cewa, "ohhh ashe ba dad'i,ai ke gabanki ake komi wace rana ce bai kushe ni?ni abunda yake mun ma ai bana masa irin sa,sai yau daga na d'ana?kuma fa cikin wasa nai maganar"

Rukee ta ce "uhmm har yau baki gane waye Yah Rafeeq ba,toshi cikin wasan ma yafijin haushin maganarka,ke dai kawai yanzu kiyi nesa dashi don wallahi a tunzure yake,kuma abu kad'an zai saka ya karya dokar Abba,zuciya ce dashi kamar ta mutanan farko,amma kuma abu k'alilan na iya sawa ya huce nan take ya mance"

"Hum shidai ya sani"
Chapter 10 · 0% Book details