← Book details Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 38

Sashe 14

Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin kakkausar murya ya ce, "shiga muje, wallahi na kuma jin tarin ki saina tsaya na zubar dake anan ba abunda ya daman"

Aguje na fad'a motar ina kerma, ya ce "fito dalla shiga Gaba uban waye driver ki anan?"

Jikina tsuma kurin yake na zaga na shiga,sannan yaja motar muka cigaba da tafiya,mai makon gudun da yake yi da farko sai ya koma yin tafiyar kamar wanda ba shi da lfy,sikiyarin ma daker yake sarrafa shi,ni dai kamar ruwa ya cini nama kasa kallon fuskar sa,mugun tsoron sa ya dirar min tare da tsanar sa mai yawan gaske.

Abun kamar wasa tafiyar ta nemi gagararsa,wani irin burki yaja yana dafe kirjinsa,da fari na dauka ko na d'an lokaci ne amma naga mutum ya bud'e murfin mota ya zube k'asa ba numfashi,wata razananniyar k'ara na fasa na fito jikina kerma kurin nake,wace irin masifa ce wanan na shiga ukuna.

Jijjigashi nake ina kiran sunan sa ba alamun zai tashi,ko ina rawa yake jikina sosai kuka kurin nake,don gani nake ya mutu kawai kuma ban san wane irin bayani zan yima yan gida ba,banda waya ban ma fito da ko hanky ba ga hanyar ko kare babu,gashi rana tatafi zata fad'i la'asar tataho duk da ban duba time ba,tsabar tashin hankali fitsari naji yai mugun matsata, na fara lalubar aljihun sa naji wayar sa yar karama nai saurin daukota na saka no. Din Abbanmu,bugun farko ya dauka "ke Roohe ina kuka tsaya haka,inata neman ku ban samu lafiya kuwa.........kuka na rushe dashi sosai "Abba ya mutu,gashi nan ya zube a titi ban San Miya samai ba,kawai......kawai naga ya fad'i"

"Innalillahi wa inna ilaihir raju'un,bar kuka kuna ina maza gaya mun"

Na soma waige waigen inda muke,na samu wata alama na gaya mashi wajen,yace gasunan zuwa yanzu na zauna gefen sa ina kukan,, "ni banga abun da ya faru ba,ko dama baka lafiya?na shiga uku ban tab'a ganin an mutu gabana ba,Allah kasa ba mutuwa yai ba.

Mom Muhseen &Asaad

_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_

*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*

By
Mom muhsen&
Asaad.

Wattpad name
Humaira3461.

🅿️.....10

Cikin d'an k'ank'anin lokaci su Abba suka iso shida Abba Habibun,sai naji hankalina ya sake tashi ainun ganin yadda aka kin keme shi kamar gawa aka sa amota,su duka hankalin su a tashe yake jinake kamar zan zauce tunda nake ban tab'a ganin an mutu gabana ba,hawaye kurin nake don ba batun wani abuba ina cikin kid'ima da tashin hankali.

Driver akai ma waya yazo ya dauki motar ya maida ta gida, dani suka wuce asibitin da ake kwantar damu in wani bai da lafiya anan gida,gefe guda na tsayaa inata hawaye su Abba ne keta shege da fice har aka anshe shi aka shiga dashi emergency,su ka dawo inda nake suka tsaya Abba Habibu yai shiru kanshi k'asa,duk sai naji ya ban tausayi don kuwa kowa yasan duk cikin zuriar sa ba wanda yake so kamar yah Ramadan,amma yana kokarin dannewa bai nuna ba.

"Miya faru a hanyar taku har haka ta kasance?"

Abbanmu ya jefeni da tambayar ina cikin wannan halin,kan in bada ansa Abba Habibu Yace "haba Taheer,tana cikin kid'ima har tuhumar ta zakai?taya zata san wani abu?"

"Tare fa suke Yaya,kaga kau ai dole tana da masaniyar wani abu"

Sai yai shiru bai sake cewa komi ba,Abbanmu ya sake kallona da son karin bayani,hawayena suka k'aru na soma cewa "wallahi ban san komi ba,lafiya lau muka isa airport ya sauke Yah Rafeeq,muka kamo hanya muka taho,to.....to....to......shine sai kawai naji ya taka burki,ya dafe kirji da cikinsa,sai......sai.....kurin naga ya bud'e k'ofa ya fad'i k'asa,wallahi Abba iyakar abunda ya faru kenan"

Ina ta sharb'en majina,shiru bai ce mun komi ba zuwa can, sai ga Abba Nura ya iso shima cikin tashin hankalin,

"Mike faruwa ne Yaya? Taheer lafiya?Hajja ta kirani tana kuka wai Ramadan yai hatsari,meeting muke dole na dauki excuse nataho"

Ajiyar zuciya Abbanmu ya sauke, Abba Habibu yace "ka kwantar da hankalin ka insha Allah ba matsala"

"Allah yasa"

Ya fad'a yana zama bisa kujerun dake wajen, Abbanmu yake gaya mun bayanin da nai masa,inaji suna tattauna maganar da tunanin ko yana da wani ciwo ba wanda ya sani,shine ya tashi farat d'aya haka.

An dauki tsawon lokaci likitan dake kanshi da nurse basu fito ba,har na gaji da tsayuwa na zauna inata masa addua bakin iyawata har raina banaa son ya mutu,koba komi d'an uwana ne na jini akwai kauna ta jini tsakanin mu,duk da ba jituwa muke ba.

Cikin taimakon Allah sai gasu sun fito su Abba suka tare shi da neman ba'asin jikin nashi, yace su isa office hadda ni aka bishi don son jin meke damunsa da ya sashi wannan halin,

"Karku tashi hankalin ku ya samu,yana bacci ne a halin yanzu amma ulcer yai mishi mugun kamu sosai,don gaskiya sai ankula da abincin sa yana zama da yunwa,kuma itace babbar illa ga mai irin wannan ciwon,in aka kiyaye komi zai zama lfiya lau,in sha Allah zuwa gobe kila na sallameshi in naga yana yin jikin nashi,"

Hankalina ya kwanta na dawo hayyacina,duk da banga gamsuwa ba afuskar iyayen nawa,bama kamar Abba Habibun duk da bai furta ba amma ga damuwa nan sosai akan fuskar sa, shiga mukai inda yake muka duba shi yana ta bacci ga drip na shiga jikinsa,lokaci d'aya har ya rame a fuska.

Nan muka bar Abbanmu nida Abba Habibu da Abba muka koma gida,da ace da kara da zumunci Ummanmu ko mami wani xai zo ya zauna dashi,ba dole sai Mama ba to babu kod'aya shiyasa dubiyar ma saida su Abba sukai masu jan ido sannan suka zo,shima a ginshire sukai masa yajiki,da yake shima gwanine uffan bai tofa musu ba.

Inaji maman na mishi magana, "Ramadan ana maka sannu baka ansawa?"

Saima ya rufe idanun sa kamar baiji ba,aiko suka kama surfa masifa da muka dawo gida,nidai uffan bance ba tunda bai mutu ba ai da sauk'i, na cigaba da hidimata.

Ammin kausar sun sauka Abuja kwatsam,watau Anti Rahma wadda Yah Ramadan ke bima wa,duk halin ko inkular da muke da ita bai hana tayo mana tsaraba ba,mu duka yan matan har su Anti Rafeeq da Anti Sha'awa,sannan tabi uwayen mu har d'akunan su ta gaidasu,bata damu da shan murr da ko inkular da suke da ita ba,mace ce mai kirki duk abuna dole na fad'i gaskiya,ta biyo halin uwarta duk abunda zakai mata na sharri bata tab'a maida maka da sharrin nan,saidai Alkairi,kuma indai zata zo to hidima take yoma su Abbanmu sosai,dankalin turawa ne doyace manja ne da su fruits,jibgi guda haka take kawowa.

Indai tazo to kowa sai ya gane,mace ce mai alkairi ga kowa don a wajena tafiye mun Yah Ramadan da sauran yan uwansa,su kam ai yan iska ne miskilan banza da wofi.

Ita dasu kausar d'in suka zo kasancewar sun samu hutu acan kebbi inda take aure,ba laifi mijin nata yana samu d'an kasuwa ne ita kuma tana aiki da wata makaranta secondary dake cikin garin kebbin,Ammin kausar duk gidanmu ba mace mai kirkinta,duk hassadarka dole zaka yaba mata da irin son zumuncinta,don zan iya cewa halin su Abbanmu ta dauko na son zumunci da yan uwa,duk safiya in har tazo to har falon Abba zataje su gaisa susha fira duk yadda umma ke had'e rai tana shan kunu bai dame ta ba,haka Mami ma duk shak'a shak'enta bai damu Ammin kausar ba,su gama firar su tatashi abunta.

Saidai bata daukar raini ko kad'an,zata sake maka sosai amma bata yadda da raini ba ko iskanci,tsaf zata ci ubanka a zauna lafiya,shiyasa muke shayinta ainun bata daukar wargi,har gara Yah Ramadan zai nuna baisan kana yi ba,amma ita kam nan take zata gurjeka.

Wannan kenan..........

An sallami Yah Ramadan daga Asibiti wanda saida ya kwana uku sab'anin dayan da Dr yace zaiyyi,ya warware kamar bai ba haka nan nima na share komi ya wuce kamar ba ayin ba,ba ruwan sa da sabgar kowa haka muma ba ruwan mu da sabgarsa da ta yan uwansa,in baa Abba Nura daya sanya doka ba don dole kowa yaje sashen Abba Habibu ya gaida su mama in gari ya waye,to inba hakan ba babu mai shiga huld'arsu,sai fa Kausar da ummi da suka jone kamar wasu k'awaye,duk fad'an ummanmu da zage-zagen ta ta saka musu ido,saboda ummin taki bata hadin kai hadda kukanta cewa zata gaya ma Abba,umma ranta ya b'aci sosai ta ce "watau har wuyanki yayi gwab'in hakan ko ummi?saboda wad'ancan matsiyatan zakice zaki had'ani da ubanki?to Allah ya baki sa'a"

Daga nan bata sake mata magana ko hanata huld'a da Kausar ba,nida Anty Rafeea dai kadaran kadahan,har gara ma ita don ni gaskiya bazan b'oye ba bana yinsu haushin su nakeji,yadda sun hana ummanmu da Abba zaman lafiya inhar suka samu sab'ani to akan su Mama da Abba Habibu ne taya zanji ina son su?

Bangarena da Yah Rafeeq kuwa ba a magana don kamar yadda yace in dauka yana gida hakan ce take faruwa,always muna tare a waya wadda Abba ya siya mana nida Rukee,tare da kwakkwaran warning,ranar ban iya bacci ba kusan raba dare mukai muna magana dashi,jina nake cikin wata sabuwar duniya wadda ban tab'a shigarta ba,wata irin Soyayya ce mai ratsa dukkan zuciya da gangar jiki muke ma juna,son juna muke kamar Allah don juna ya halicce mu,kulawa muke da juna ainun walwalata tak'aru sosai hakaa fara'ata da maganata,ya zamana inhar ina gida to bakin kowa ma bazai huta ba,wani irin farin ciki nake samu dagaa Yah Rafeeq a yadda muke ji da juna ko k'uda bama so ya shiga tsakanin mu,a hankali a hankali gida aka fara fahimtar halin da muke ciki,wanda wannan abun ba wanda yakai su Ummanmu da Mami jin dad'in shi,har Rannan Anti Rafeea ta ce ma ummanmu.

"Umma na dauka fad'a zaki ma Roohe akan turb'ar da take son d'ora kanta tun yanzu,ko ni da nake cikin shekara ta biyu a jami'a Abba bai bani damar yin saurayi ba balle Roohe da ke zana weac,a ganina ki dakatar da ita kafin abun ya shafeki in Abba yaji"

Ina gefe ina karatun neco da muka kusa gama wa,time to time ina chat da Yah Rafeeq, raina ya sosu sosai da maganarta ina jiran Umma tace wani abu kafin ni ince,
Chapter 14 · 0% Book details