Sashe 20
Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A wajen filin wasan an zagaye sa da kujerun roba dasu Abba zasu zazzauna sune yan kallo,kowa na gidan ya fito ba wanda ya fita har su mama da Hajja duk sun fito kallo,yan team kuwa kowa ya shirya ya fito,kasancewar Family d'in kowa kyakkyawane sai jessin sukai masu kyau sosai,ni da Rukee kawai akejira tun a daki dana kalli kaina cikin dark pink dan blue Jessy din na Kara gode ma Allah,domin ya kyautata halitta ta sosai,kayan sunyi matukar yimun kyau rigar am less ce ta fiddo Boob's d'in sosai ma sha Allah,daman gasu a ciki ta fitar da shafaffen cikina,sai three quarter wando daya bi cinyoyina ya lafe,na daure dogo cikekken gashina mai sulbin gaske cikin pink ribbon a tsakiyar kaina sai na saka ban dana blue mai rubutun angel, "na rantse da Allah ban tab'a ganin kinyi kyau irin na yau ba, da ace qalbinki na nan wannan wasan ba zai iya buga shi ba saboda susucewa zai........dariya na kama yi nace "wallahi saina fad'a masa,ke dashi ne"
Tare muka fito muna ta dariya muna zaga yowa na hangi Mufeey ita da mutuminta sun sha nasu jessy din suma sunyi kyau sosai, duk kushen ka da hassadar ka dole ka fad'a,Rukee ta ce "ke mutumin can mugun yai kyau ko baki gani ba,shi gara ma yaita saka jessy din anfi ganin kyan sa"
Ban bata ansa ba saboda wani kallo dana hangi yana bina dashi,duk iya hasashena bazan iya gane ma'anar sa ba ya iya kallon munafurci wanda karyar ka ka fahimci manufarsa a kallon, tsaki kawai naja ina kaudar da kaina gefe,wajen su Anty Rafeea muka je kowa sai yaba shigata yake har su Umma da Mami,kar ma ace mami don wani iri ji take dani tunda muka soma dating da d'an gaban goshinta.
Abbanmu yace azo a fara don fita zai baison ruwa ya sauko baije inda zaije ba,don garin hadari keta had'uwa har ya fara baki hadarin, na ce ma Rukee "ina ma ruwan nan ya sauko ana cikin wasan nan,wallahi dana ji dadi ina son wasa cikin ruwa"
"Kedai Bari,amma kuma kinji ajikin ki inya dakeki ba"
"Ai magani zan sha,amma kam bazan wuce shan dad'in ruwan saman nan ba indai ya sauka yanzu"
Cikin kan kanen lokaci aka fara buga wasan,team d'inmu yawan ci duk aka tara k'wararrun amma duk da haka kusan minty shabiyar ba ajefa kwallon ba,karo na biyu ina isa ga inda zan jefa kwallon da jikina da nashi ya gogu zan saketa kawai inja baya raina b'ace,duk yadda na kai ga son jefawa da mun kusanto juna sakinta nake,karshe ta koma hannun su Rukee,tana koma wa zai ansota cikin hikima da wayon sa,haka aketa fafatawa karon farko ya jefata cikin raga,aiko su Umma da su Abba suka hau tafi da shewa,sai kuma naji kishin hakan haushi duk ya isheni,Abbanmu cewa yake "ai daman nasan Ramadan zai fara jefata a raga,keep it up Babban yaya"
Ya saki wani killer smile yana shafa sumar sa kamar ta india ya ce, "thank you Abba"
Kowa dai yaita yaba mishi,su Rukee kuwa suka hangula aka sake koma wa karo na biyu,nan fa su Yah Fahad suka dage baji ba gani muma muka zage,tuni na manta da banson had'a jikina dashi gogayya muke sosai ana son a cimma nasara,Mufeey tai wata irin fad'uwa Allah yaso ta yana baya ya tareta dalilin da yaja kenan muka fad'i, Yah Fahad ya jefa kwallo a raga,sai ihu da shewa aka hauyi na murnar anzo one-one, raina ya b'aci saboda duk iskan cin Mufeey ne shikuma sauna ya biye mata na ce mata "banza ai duk ke kikaja mana,ko ince kukaja mana daga duzgud'ewa zaki wani lauye,mtss sakarci kawai"
"Allah yasa bada favorite kike fadar sakarcin ba,waike miye damuwarki ne iye?"
Na sake hangula da maganarta, "naje nafad'a kiyi maganin abun,koma da wa nake ki dauki mataki........Roohee shot up karna sake jin wata magana anan,kafin na sab'a muku kuduka"
Abba Nura yai maganar,dole mukai shiru da yake rab'oce har ta fara hawaye,ta juya zata fita daga cikin filin ya riko hannun ta ya ce, "miye haka?oya come in"
Dole ta dawo ta tsaya position dinta,tana goge hawaye aka tillo ball muka cigaba daga inda aka tsaya,wasa ya dau zafi ta ko ina kowa so yake yacimma nasara,mun shafe mintoci sosai ana gwabzawa tari ya sark'e anty Sha'awa dole ta fita taje shan ruwa,fitar ba jima wa na anshe ball nai ciki da ita na buga tsalle na jefata a raga,sadda zan dawo na fad'a jikinsa ban ankare ba muka fad'i warwas a tare,can kuma sunata ihun murnar cin da mukai,kunya ce takaici ne haushi ne bazan iya gane me nakeji ba,saboda yadda na hayesa abun inka gani dole zakasan naji wani abu a raina,na saurin tashi cikin rawar jiki haushi ya tirnik'eni na juya kawai ina kakkabe jikina duk da kuwa babu k'ura a wajen,duk na diririce ne ban san dalili ba fita nai daga filin wasan naje na sha ruwa, su Abba suna ta yaba mun don nima nasan nayi kokari sosai,aka huta sannan aka koma round d'in karshe wanda sukai nasara Abba ya dauki nauyin gift mai tsoka a team din,saidai ana koma wa wasan aka soma yayyafi Abba yace shidai ya tafi komi kenan inya dawo yaji labari,ai kan kace me duk yan kallo sun watse saboda ruwan daya soma yawa,zuwa can Anty Rafeeq ta fece itama kafin Anty Sha'awa ta bi bayanta a takaice dai ko wane team ya rage mutum uku,can nasu Rukee daga ita sai jamil da ummi,namu kuma nida shi da Mufeey,a haka mukai ta bugata ruwa na sauka kanmu wani irin nishadi na ratsani,abunda na lura suma suna jin dad'in wasan da ruwan,jik'ewar da nayi yasa gashina ya bi bayana ya kwanta am less din jikina ta lafe sosai inka ganni kamar wata flawer don tsananin kyau,muna cikin wasan muka sake wani irin karo dashi gaba-da gaba kirjina ya dau zafi sosai, bansan nace "wayyo Allah na"
Yai saurin cewa, "I'm sorry"
A tarihin rayuwar mu wannan ce kalma mai taushi tsakanina dashi,sai na juya kurin bance komi ba,Mufeey ta ce "sannu"
Kai na d'aga mata kurin,aka cigaba da wasa danaga zamu sake gamewa zanyi saurin ja baya,kafin su Rukee su sake ankarewa mun sake cinsu,tsalle da ihun dana buga sadda ya jefa kwallon a raga shine dalilin da sulb'in wajen ya dauk'eni ya nanani da k'asa nai wata irin gurd'ewa na fad'i, wata razananniyar kara na fasa mai tada hankali,saboda azabar danaji ga k'uguna da k'afata wajen guiwa,aguje sukayo kaina shine farkon zuwa ba zaka kalleshi kace ya razana ba,amma idonsa kawai zai nuna maka a kid'ime yake,ruwa sosai akeyi kafar ya kama zai murza na fasa kara,rukee ta kamani da mufeey in tashi na kasa,wata irin azaba nakeji ga k'uguna kuka nake ina kiran"nashiga uku K'uguna ya kare,Rukee na bani wayyo umma Abba ka taimakeni na kare k'ugu"
Mufeey sai kuka da yake gwanace a kuka,Rukee ma hawaye take tunanin ta dagasken karewar nayi,ganin halin da nake ciki yasa ya nufoni ina zaune dirshen k'asa ya sak'o hannunsa ta kugun ya saka d'ayan karshin kafafuna sai jinai kurin d'afff ya daukeni yai cikin gida dani,azabar da nake ciki bata hanani mamaki da al'ajabin abun ba,rungume nake jikinsa sosai don zan iyajin bugun zuciyarsa,ruwa nata dukanmu bamu damu ba su Rukee suna bayanmu,wata kwarankwatsi da aka saki bansan na k'wak'ume shi ba na saka kaina tsakanin wuyansa da kirjinsa,Ya salam musallim wani abu naji ya ratsa hancina da kwalwata, *K'AMSHIN TURARE* azabar da k'uguna keyi bai hanani dagowa ina kallon fuskar ba cikin mamaki,kamar bai san me nake ba koda wasa bai kalli fuskata ba,har sadda muka shigo cikin main falo ya wuce dani har dakinmu bisa gado yad'orani,bai kallan ba ni kam kamar na samu tv wajen zare hannun sa daga k'uguna ne na zabura nace "wayyo Allah na"
Ya mik'e yana ce mun, "Allah ya sawake"
Dai-dai Su Rukee sun shigo,shi kuma ya fice sai na saka kuka kurin ina cema Rukke ta kira umma akaini asibiti,mutuwa zanyi duk sun damu sosai Rukee tatafi kiran umma,Mufeey sai sannu take mun.
"Laifina ne Roohee nina jawo wasan nan,da ba ayi ba bazaki samu matsala ba ki yafe mun"
Kukana kurin nake sosai hadda hawaye,don k'ugun yafi mun ciwo sosai, cikin kankanin lokaci na tara mutan gidan,hadda goggo Habi anata mun sannu ita takira Abba Nura aka kaini asibiti,sun duba babu wani mugun rauni buguwace kurin,aka bani magani na shafawa in angasa,su Mama da najeeba duk sunzo dubani har Abba Habibu kowa yazo amma ban ganshi ba,Abbanmu washe gari yace in ina iyawa zai tura ma YAH RAMADAN KUD'I muje shopping mu siyo duk abunda mukeso yan team d'inmu,jin ance shopping nace zan iya duk da kuwa d'angyashi nake sosai.
Na fito wanka ina shafa mai daga ni sai Rukee nace mata, "wani abu yaban mamaki jiya Rukee,ashe guy d'in nan yana saka turare,turaren ma mai aji mai tsada Abbanmu kad'ai nasani da irin sa wallahi Rukee"
Mamaki itama take kafin tace, "ya akai kikaji to"
Shiru nayi kawai bance komi ba,kamar banji ke tace ba dariya naji tana yi na dago ina kallon ta, "miye ne to?"
"Aa mefa,hangoki nai dare-dare a jikinsa,shine nace kunyi kyau..........na jefeta sa robar man da nake shafawa, "Allah ya isa tsakanina dake,ashe kina nan kinyi mun tanaji,dadin abun bance ya daukan ba da ina cikin hayyacina hakan ba zata tab'a faruwa ba"
Dariya kurin take tana cewa,"aa ni kam me zaki cemun kuma"
Aiko na k'ule-k'ule na hayeta naita jibga har sannan bata daina dariyar ba,saida naji ina fama ciwona na sauka daga cikinta, raina a b'ace haka na gama shirin,Mufeey na can b'angaren mama indai yana gida to ita kam tana nanik'e dashi.
_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_
*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*
By
Mom muhsen&
Asaad.
Wattpad name
Humaira3461.
🅿️.....14