Sashe 13
Wukar Fidar Giwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai na d'aga mishi,ya tashi yai ma umma saida safe, na sauke ajiyar zuciya na tashi na ansa oat din na fara sha,saida taga nasha maganin sannan tatashi tatafi,su Anti Rafeea suka shigo da Anti sha'awa suna mun sannu,sai ga Mami ita ma da Rukee jinai kamar zan tsere don kunya, daker nake ansa mata maganar har tatafi.
Daga wannan ranar komi ya soma.!
Mom Muhseen&Asaad
_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_
*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*
By
Mom muhsen&
Asaad.
Wattpad name
Humaira3461.
🅿️.....9
A cikin kwana kin da sukai mashi saura ya koma makaranta wata irin kulawa yake bani,gashi inhar yana cikin sabon feeling to fa kowa gane mashi yake,don haka yanzun ma gidan ba wanda bai san sabuwar alak'ar mu ta kirki ba,kowa sai da yai mamaki ainun da ganin yadda Yah Rafeeq yake mun,yini yake agida duk abokan sa dake sintirin neman sa,daya fita bai jima wa yake dawowa,har na soma rikicewa ta fannin karatun mu,gashi mun kusa fara weac.
a wajena abun bak'one don na kasa sakin jiki dashi, zai ta mun magana yana jana da fira daker nake bashi ansa,duk inda zanje yana biye damu har na gaji da magiyar ya daina binmu,makaranta ma in bacin baiga fuska ba shi zai kaimu,to wanda ke kaimun baiga fuskar tun karar sa da wata magana ba,amma kullin safiya saiya rakoni har bakin mota ba zai tafi ba har sai yaga tafiyar mu sannan.
Rannan Rukee ta ce "da alamun fa kin susuta mun yayana,irin wannan rawar k'afa haka?"
Murmushi kawai nayi don ban san me zan ce mata ba,ummi da Najeeba dai ba wanda yace k'ala balle kuma uban yan fad'in ran duniya.
Mun soma weac da kwana d'aya yah rafeeq ya tafi,ban san cewa na soma kamu wa da irin halin daya ke ciki ba sai wannan ranar, duk yadda nake basarwa abun ya ci tura,nashige toilet d'in dakin mu na kama kukan da ban sa dame xan kira shi ba,na dauka ya tafi na fito kenan sai gashi ya shigo.
"Shine Kika b'oye don kawai kar ki rakani"
Idonsa yai rau rau kamar zai kukan shima,na gama gane akaina Yah Rafeeq baida wata jarumta irinta namiji, ban yadda na kallai ba na ce "Aa ba haka bane"
Jingina yayi da kofa yana crossing legs dinsa yana kallona,jinai wasu hawayen sun sake tahowa nai saurin juya baya ina gogewa, nama rasa abun da zanyi, jinai yace "kibar goge hawayen ki a b'oye,ki jiyo ki fuskan ceni nine ya dace na share miki su"
Makale kafad'a na nayi inajin kukan zai k'wace mun, ya tako zuwa bayana ya riko hannuna cikin wata irin murya marar amo, "zo muje kimun rakiya airport,mu sake yin bankwanan sosai"
(Na manta ban Sanar daku inda yake karatun ba, yana india wata scholarship Abbanmu ya samar mashi)
Kasa mashi musu nayi,na dauki hijab d'ina muka fito,anan main falon gidan gaba d'aya kowa na nan har su Abbanmu,kasancewar weekend ne ba aiki ba school, Mami tana ganin mu tayi murmushi don zan iya cewa tafi kowa shiga farin cikin alakarmu dashi, Abba Nura ya ce "saida ka fiddo ta kenan,"
Kaina k'asa shi kuma ya sosa kai ya ce "Abba ai bazan tafi bamuyi bankwana ba"
Murmushi kawai yayi Anti Rafeea ta ce "duk bankwanan da akai dazun da sauran kwanaki bai yi ba kenan"
Harara ya sakar mata,yana cewa "kewai miye naki aciki?"
Anti sha'awa ta ce, "ai kai baka son gaskiya,ni wai mike tsakanin ku ne farat d'aya ka zama haka..........."mami ki shiga tsakanin mu da wannan yarinyar,nidai ai ba sa'anta bane da zata ringa gaya mun haka"
Dariya duk aka kama yi mashi,saboda angane dai borin kunya yake bai son a gane miyake boyewa,
"Bari muje muyi ma Hajja sallama"
Yajani muka tafi nidai na kasa cewa uffan,jikina duk amace yake ainun,bamu jima sosai ba wajen Hajja muka fito Abbanmu ya ce muje bangaren Abba Habibu yai masu bankwana,Yah Ramadan xai kaishi Airport d'in.
Nida shi duk bamuji dad'in maganar ba,amma bamu isa muce aa ba,koda muka je bangaren nasu Fuska ba annuri yake musu sallama,su kam basu damu ba saima nuna jin dad'in su suke yazo musu sallama, Mama tatashi ta shiga ciki ta fito da wata leda tana cewa, "ga wannan Rafeeq,kila yai maka amfani Rahma ta sani nayi mata shi zasu zo jibi", donuts ne sutu-sutu mai wata madara-madara a ciki,sai dambun kifi mai yawa.
Hakan bai sa ya saki ransa ba ya ansa yana cewa, "Angode"
Bata damu da yadda ya ansa ba karsashi da nuna jin dad'i ba,ta rakomu har wajen mota inda sauran yan gidan ke tsaye,Abba Habibu yana ta mishi nasiha ya kula da kanshi ya rik'e ibada ya kuma tsaya yayi karatun sa hankali kwance, "karatun ka na son natsuwa da kwanciyar hankali,Allah ya taimakeka kaji yarona"
"Amin" kawai yace ni har na soma jin kunya ma,don ba dad'i irin abunda yake musu.
Daga ni sai shi sai Yah Ramadan,duk baya muka zauna shi kuma yana tuk'i,muka dauki hanya sai Airport,tunda muka tafi munyi shiru yak'i sakin hannuna kamar zan b'ace mashi, saida mukai nisa da gida sannan cikin sanyin murya ya ke cewa kamar mai baya son aji,
"Wane irin alk'awari zaki mun kafin in dawo?"
Kaina k'asa na kasa cewa komi,ya sake matsoni yana cewa "kinji Rooh"
Har raina sunan daya kira ni dashi ya mun dad'i, daker na iya cewa cikin siririyar muryata "ni ban san wane irin alk'awari kake nufi ba"
Iska ya busar yana cewa, "badan tafiyar nan ta zamar mun dole ba,wallahi Rooh ba inda zani inbarki,ji nake kamar zam bar duka rayuwata anan"
Saurin kallon sa nayi yajin jina mun kai, "sosai ma"
Na rausayar da kaina cikin rashin abun cewa, ya katseni da fad'in "in so ki kasance tare dani a zuciyarki har inje in dawo,sannan inaso ki nisanci ko wane namiji don duk duniya ba wanda zan iya barma ke,nasan kin gane mi nake nufi please Rooh,kimun wannan alfamar zan jima ban dawo ba amma saboda ke zan ringa zuwa duk bayan shekara daya da rabi in ganki in koma,karki ba wani dama akanki koda kun gama weac kima Abba magana kina son nursing,kinga ni dr ke kuma nurse ko had'in bai miki ba?"
Murmushin na saki ina kaudar da fuskata,watau duk kewaye kewayen sa dai so yake yace sona yake kuma duniyar nan baida burin auren kowa saini, "yes ban da wani buri a rayuwata illa na mallake ki,ban san taya zan sanar dake ba amma cikin raina kece kawai muradina,duk wani abu da nake miki a baya ba har raina bake yi ba,kawai inayi ne donki maido hankalinki kaina,ganin zan tafka kuskuren da har Abada bazan iya gyarawa ba yasa na dawo hanya, ina fatan babu wani abu da zai mun katanga da cikar burina kinji my Rooh"
B'oye fuskata nayi saboda wata irin kunyar sa nakeji matsananciya, ga wata irin kewa da nakejin tana ratsani ko ya zan kasance babu shi a cikin gidan?har muka iso airport ban iya ce masa komi ba,shine yake ta kokarin ganin ya fayyace mun abunda ke cikin ransa,koda yai parking saiya ki fita ya dai bud'e kofar inda yake zaune ya fidda kafarsa guda yana danna wayarsa.
Dogon tsaki Yah Rafeeq yaja ganin abunda Yah Ramadan d'in yayi,ya ce mun "kar ki dauka bana nan,ki dauka always ina gida kuma zaki ganni,zan ma Mami magana a siya miki waya I promise u zamu ringa video call at least twice par day, yayi miki hakan?"
Na d'aga kaina kurin saboda jinake zan kuka, har na kasa controlling hawayen suka ringa silalowa, muryar na rawa na ce "ka ce zaka ringa zuwa after one year"
Murmushi ya saki mai cike da tsananin bege da soyayya, ya rik'e hannuna sosai ya ce "in sha Allah,kodan farin cikin ki zan takura Abba har sai nazo"
Ya shiga goge mun hawayen da Hanky d'insa, yana cewa "oya inhar ba kina so na tafi cikin damuwa ba give me smile"
Ban san sadda na sakar mashi murmushin ba,yaja iska yana cewa "u are very beautiful Rooh,ban tab'a fad'a miki ba yau na fad'a,kina da kyau mai rud'a duk wani namiji,saidai wanda yasan daman bazai same ki ba,ki kula mun da kanki kinji ko"
Daker muka rabu saida yaji ana sanarwar neman su sannan ya bud'e motar ya fita yana d'aga mun hannu,kuka ya kwace mun don alokacin ji nake duk wani jin dad'i na ya kare tunda bai nan,haka muka kamo hanya nida shi kamar sabbin kurame,har gara ni inata shashshekar kukana,shi kam banda tuk'i ba abunda yake kamar daman tukin aka halliceshi yazo duniya yayi,ni ban tab'a ganin mutum irin sa ba kwata-kwata rayuwar sa babu armashi,ba walwala babu farin ciki sai fad'in rai da girman kan tsiya, da tsabar k'azanta wannan dalilin ke sake samun jin tsanar sa araina,bana son namiji babu gayu babu kula dakai,.........ban san sadda naja wani dogon tsaki ba,ai ban idasa jaan shi ba naji wani uban burki ya taka,har kaina na bugar kujerar gaba,a mutuk'ar fusace naga ya bud'e bayan motar inda nake cikin zafin nama ya finciko ni, muryar sa ta wani irin disashe cike da b'acin rai matsananci ya ce "uban wa kike ma tsaki?"
Jinai zan saki fitsari a inda nake,tunda nake rayuwata a gidan magana tafatar baki bata tab'a had'amu ba in banda gaisuwa sai yau,cikin tsananin tashin hankalin dana ganshi a ciki yasa na rud'e don ban tab'a jin tsawar data gigita tunanina ba irin yau,idon sa har tsoro ya bani kamar yai shaye-shaye ya bugu,sun wani rikid'e sun juye ban san ina cewa "Aa....Aa ni.....ni banyi tsaki.....banyi maka tsaki b...........mahaukaci kika d'aukan komi?ashe zaki kwana nan"
Muryata kerma kurin take na soma girgiza kai, cikin tashin hankali "ka yarda dani ba dakai nake ba,ban san nayi ba don girman Allah ka maidani gida,wallahi bazan sake maka tsaki ba,kuma ba dakai nake ba kubce mun yayi na rantse da Allah Yah Ramadan"
Babu sassauci ko k'adan a fuskar sa,ban tab'a ganin tashin hankali irin wannan ba,inhar ya barni a dajin nan shikenan bani ba sauran wata rayuwar jin dad'i,yadda ake kidnapping d'inan ana kashe mutane,aini tawa ta k'are.