← Book details Uncle Justice Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 49

Sashe 49

Uncle Justice Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Wanda duk takaranta ta nishadantu Kuma takaru idan yanada Hali kibiyani Hafsat Abubakar sadeeq first bank 3195366407

Aims and objective of this novel are

*UNCLE JUSTICE*

Salam inna yima kowa fatar Alheri, makasudin
Labarin "Uncle justice" nagina sa ne akan manu fofi kamar haka.

1. Riko da Amana da wanzuwarta da kuma aiki da ita. A tsakanin Al'umma.
Alh muktar ya Auri Haj Aseeya yayi zama da ita na Amana haka kuma Ummu salma tashigo cikin rayuwarsu itama din sukayi zama da juna da Amana.
Haka kuma Rayuwar Raheema da Fareeda akwai yarda da Amana. Sai kuma yanda rashin Amana da cin Amana yanxu yayima zukatan mu mummunan illah Arayuwa. Wanda hakan yasa naketa kambama Amfanin Amana a cikin labarin.

2. Sai Abu na biyu Alheri! Wato wanzuwar Alheri a tsakanin zaman takewa koda dayaran gidanku ne to ko shakka babu Alherin zai dawo agareku

3. Sai Abu na ukku shine rashin haihuwa nakuma duba duk wani, ko wata da Allah bai bama haihuwa ba, to tabbas bama iyya basu haihuwa! Toh Amma kuma mudin munada rawar da zamu taka. Al'umma wane tai mako muke basu, inda hakan yasa nashigo da lamarin Maman fareeda, da yar gidan Aseeya. Mubasu wuri, mubasu fuska, mubasu izzini, mubasu dama, suyi iko da ya yanmu. yazama ya'yanmu nasu ne, suma suyi iko dasu.dan Allah ko kishiyarki ce, ko makociyarki ce, ko ya'yarki ko kanwarki toh kibata wannan damar idan har tanada zuciyar musulunci.

4. Sai Abu naga ba shine mutun tun tawa da girma ma juna wanda hakan nada matukar muhimmanci arayuwa mu tayau da kullum,

5. Sai kuma nisha dantarwa wanda shine abu nakarshe acikin labarin.

Inna da wannan labari inna da wananna kudirin rubuta labarin kusan shekara biyu dasuka wuce, bansamu dama bane sai yanxu.

Komai a rayuwa munayinsa ne domin karuwa ko cigaban mu.
Nikam a yau inna ga insha Allahu zai daina rubuta littafin Uncle justice, komai Anayinsa ne domin karuwa nikam gaskiya ba riba.bazai yi yu nace kowa sai ya siye littafina ba, ah ah.

Ba zai yiyu nace wanda yasiya ya turama wani naiyi masa Allah ya isa ba, sam domin indai ita din mai Adalci kuma mai Amana ce tasan meya kamata.

Bazan yima dan kowa mugun furuciba bakuma zanyiwa dan kowa mugun kalamiba
Haka kuma bazan yima dan kowa Allah ya isaba innah. Bazanyi ba.

Domin nima inna da yara ukku aduniya bazanso daya daga cikin hakan tafaru dasuba.

Haka kuma nima mai laifice fatar nake Allah ya yafe mana laifukkanmu.

Haka kuma da akwai matan malam Audu da muke lallaba rayuwa irina wanda su idan dahali idan nasan suma da kaina zan rika binsu daya bayan daya natura masu, saboda nasan yanda halin rayuwa irin wadda suke ciki ake fama Allah Alhamdulillah.

Yanxu dama ga yara sun koma makaranta hiddimar kaisu da daukowar ga homework kula da uniform socks da dai sauran hidimar gida, ba zai yiyu kuma duk dahaka narika cracking brain dina ba just to motive you kuma abun ba riba.

Yan paid group littafin "Uncle justice" yanxu akazo kan rabi saboda haka wadda tabiya 300 tanada chanjin 150 zan mayar mata sai kuma wadanda suka biya 200 sukuma sunada changin dari hannunah Dan soyayyarku da Annabi muhammadu kubani Account nuber dinku na maida maku hakkinkune domin yanxu akayi rabi acikin labarin.

*Dukkanmu masu laifine Allah yayi mana afuwa 🤲🤲🤲*

*Na barku lafiya Allah yabamu Alheri🤲*
Chapter 49 · 0% Book details