← Book details Uncle Justice Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 49

Sashe 31

Uncle Justice Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kuma mun dade da maman fareeda sosai harr su little saida mukayi Magana dasu, tukunna mukayi ban kwana haka kumma Abba da ummu salma wadda da nasan ita din kamtabbas idan har aure "Uncle justice" zai kara to tabbas sai ta fadimun tunda kusan ita kullum akan komai yimaka tuni game da al'amarin fadin gaskiya komai dacinta. ko tayimaka hannunka mai sanda ko kuma tunatar da kai kan halin rayuwa.

K'ai ganin kamar zan bama kwakwal wata wahala yasa nayi watsi da batun nabarshi akan wata kila gudun suke kozan daga hankalina ne kozan shiga cikin damuwa ko kuma sunfison shi din yafada mun da kansa,

N'attatara komai na watsar na janyo charbi nafara yiwa annabi sallati, bayan nagama sallah na dade sosai saman sallayar innnata rokarma Aunty Raheema rahama da gafara da duk musulmi, ganin yau nasamu kaina tunda tun fitar "uncle justice" baai dawoba hakan yasa tun da nazauna sallar la asar har magariba ban tashiba.

I'nna nan zaune ban tashiba har baba mairo tazo muka gaisa, take tambayata ko baki za, ayi yau a gidan nace mata bai fadi maniba Amma kam dukkan Alamu sun nunah hakan. Tace toh Allah yasa nace Ameen.

T'ukunna na tashi agabatar da sallar isha I ai kuwa inna gamawa banmagama adduaba naji uncle justice yashiga, direct dakina ya wuto yana shigowa kuwa direct niyan tunkaro nikuma inna ganin haka namike tsaye fuskaata da daan annuri nima ganin yanayin sa cikin tsananin farin ciki yana zuwa baiyi watta wataba kawai ya fincike hijab din dana gama sallah dashi yayi wurgi dashi , tareda daukata in a bridal show, yana juyi dani cikin daki acikin kunnanai yace kitayani murna yau insha Allahu zanshiga wata sabuwar rayuwa.

D'an murmushi nayi nagefen baki cikin sanyi nace Allah yasanya alheri, Uncle jawad, saida yakaima bakina dan light kiss tukunnah yace amin thanks! mumushin fa still afuskar sa tukunna ya ajiyeni tare da cewa bari na watsa ruwa.

H'aka nan araina kuma sai nadan dinga jin ba dadi, tayanda wai ace mijin Aunty raheema ne zai hada kwanciya da wata yau, ba Aunty ra heema ba, duba daa irin son da sukeyima juna,

H'akannan sainaji raina yadan baci amma da yake nafi kowa sannin uncle justice bazai iya zama hakaba ko banza gayanayin halitar sa, yanda yake.

H'aka nima nayi niyar shiga wanka, amma duk jikina badadi amma ni nadan ganta hakan da rashin girki da banyiba yau, domin nidai a rayuwata nariga da saba da hidima, sam bansaba da zaman wuri dayaba, wuni daya zungur bawani motasa jiki amma banma kaiga tube agogon hannun naba naji kiranshi yana naimana ne danazo zamuyi wata Magana adakinsa nace toh nadauki zumbulelen hijab dina nasaka na nufi dakin nasa nasame sa har yayiwanka ya cahanza daga shaddar dazu, yanxu jallabiyace jikinsa milk color mai sulbi sosai mai kuma hade da hula, amma madadin amfani da hular sai ya dora hular tashi kafiya nachi wato asallami dakare itama milk akansa.

S'higowa nayi nasamu nasamu wuri chan kasa kasan capert na zauna, kaina duke akasa tun kallon daya dana yimasa shigowata bansake dagowaba, fuskarsa cikin rashin fara a sosai yace kicire wannan hijab din. ban iya yimasa musuba nacire kuramun ido yayi sosai shiru baiyi maganaba koda bandago ba nasan niyake kallo innajin kaifin sa akaina.

S'hiru ne yabiyo baya sai azabar kallo! Wanda har yar natsuwar danake da ta naimim kubucemun, faduwar kaba tarafar tasarmun,
araina jinake inna son natambayesa maganar auren nasa amma sam bazan iyaba,

D'aganan zaune batareda yayi maganaba kawai alamu yayimun da hannunsa dana matso kusa, matsowar nayi kusa dashi banyi gigin zama kusa dashidinba kamar yanda yabukata madadin nazauna inda yanunamun saman doguwar cup chair din dake dakin dayake zaune ah ah sai dai na zauna kasa gurin kafa fafuwansa

B'ai matsamun ba haka kuma baiyimun magana ba, har na dan tsawon wani lokaci araina nace ran yarima ya dade dan sarki.

J'in shirun har lokacin yasa na dan dago naga kodai wani abun ne yadaukemasa hankali, kokuma yana duba wayarsa ne, to my greatest suprice nidin dai yake nachin kallo👀 ai kuwa cikin dan rudu daya baiyana amuryata nace pls "Uncle justice" yaushe second Aunty na zata tarene ganin kamar yau banga alamar zuwan suba, duba da yanayin lokaci.

B'aikai ga amsamun ba sai dai dawowa dayayi kasa kusa dani yazauna, yariko duka hannaye na, yarike su cikin nasa yana murzawa, shima muryarsa da sanyi sosai kusan maganar ma kamar rada yace zata zo ayau dinnan insha ALLAHU! yasake saka hannuwan nawa duka biyun cikin nasan babban dan yatsansa ya na murza duka saman fatar hannuna,

Yakuma cewa saidai kedai abun da nake so dake da duk abunda kika gani da kiyi hakuri kowa da komai da kika gani arayuwa toh hakan mai samaniya ya tsarama bawa, iyawarka ko wata dubara bazata fasa abunda Arraham Araheem yanufeka dashiba.

D'an murmushi ya kubucemun araina inna cewar wato shi "uncle justice" yana dauka cewa kamar cewar aurensa zai dameni ne bayan kumani harga Allah iyyakar gaskiyata kenan sam badamuwa ataredani, domin nasan yin auren nasa shine samun mafitarsa, dani baki daya, ganin yanayin fuskata yabashi kwarin gyuiwar chigaba da zanchen sa kiyimun addu a adaren yau nasamu baby a bugun farko, domin yau insha Allahu ango nake!

N'i kunyar duniyama ta kamani nakawar da fuskata, muryata chan kasa nace uncle justice inna maka fatar alheri a zuciyata nace inna dai tausayama koma wacece domin yau saidai Allah kenan, kuma araina kamar natambayesa din amma na dai yiahi ai koma wacce gani zanyi.

Y'anaji shiru kuma haryanxu ba akawo amarya ba, amma sai dainayi shiru kawai tunowa da nayi ko wata kila ankaita gidansa dake goruba road inda Auntie Raheema ta zauna. watakila ko chan zasu zauna da Amaryar yanda naga yakafeni da kallo yasanayi saurin tunowa da bafa hijab ajiikina.

B'a arziki na mike tsaye cikin dan hanzari inna cewa bakaci abinciba, duk da cewar yasa karmun hannu amma dan cikin sassarkewa murya ya kecewar mekikechi nabaka nazuba muje ai zancine.

*Saifa mun kula sosai munrika tunowa da yan uwanmu da Allah yayima rasuwa Jama, a munayimasu Addu'a Allah yayima musulmi gafara da rahama*

*Idan kinada hali kibiyani Hafsat Avubakar sadeeq first bank 3195366407*
*xliv*

*Single's should pleace mute this page, a page next to it and a page after!. Ubangijin Rahama kuma yabaku maza nagari*

G'a mamakina saman dinnig din abincine cike, abincine kala kala, duk na kasashen waje ne, tundaga farkon table din har karshensa.

K'usan abinci kaloli goma zuwa sha biyu ne, sai dai komai nau'ikkan abincin kadan kadan ne nakamar chin mutum daya ko biyu.

A'bun mamaki shine yajamun kujera na zauna ta gefen daman sa
kusan abincine kala sha biyu amma kowane saida yadan tsunkura yazubamun.

D'a kansa yake servin komai haka yachika plate ukku aganabana ko nama nau,ika kala ukku ne wurin, ga ferfesun kaza sai danbun naman sa sai gasashen naman rago..

B'achin cups hudu da kowane da nau'in kalar lemun da keciki, banyi wani mamakiba saboda nasan wani lokacin namiji can go to any extend to show concern in terms of bringing a new wife!.so bandamu ba.

H'akan namaida hankalina wurin wani chocolate cake mai dadi, sai wani milk strawberry shake sukadai nake sha! lura da hakan da "Uncle justice" yayi yasa yature nashi abincin tareda dauke plate din dake gabana yamayarda na gas meat dana dominitors chicken meat.

D'a kansa yasaka hannu yadebo naman yana bani, sosai naso na kawar da kaina amma ganin fuskar sa babu alamun wasa yasa ala dole haka nayi hakuri nacigaba da karba, haka nan kuma nima bansan daliliba sai dai kawai naji wata irin yanga nakejinyi mai dauke da launin launin shagwaba haka,

W'anda hakan yasa da kyar nake dan bude round lips dina nakarbi naman, shikuma sai aikin kallona yake a ganina acikin idanun sa sai naga kamar sunatara wasu launin ruwa haka masu stars acikin su,

B'a irin yanda ban yita bata fuskata ba inna tutturo baki, amma inna sam bai kyaleniba harsaida na cinye rabin kazar nan daya da dan wani share daga cikin gas meat din.

S'ai ko milk shake danake ta faman sha domin jinayi duk cikina yayimun wani irin mugun nauyi duk ya hakkame mun yayimun kabe kabe ba dadi.

R'anar nan dai sam baifita sallar isha iba, tunda ba mubar dinnig dinba sai kusan misalin twakas da rabi tukunnah, dakina nawuce domin na watsa ruwa ko zan danji dadin cikina nayi sallah ayayinda shima ya wuce nashi dakin.

W'anda wannan yarda daraba dakin danaga kamar "Uncle justice" yasaki yau munyi bakaramin dadi yayimun ba kobanza yanxu sosai nake sakewa nacire kaya na daura towel bakamar dakinsaba.

S'anin cewar yau batare zamu kwanaba yasa nabude kayyaykin da Ammy ta sissiye mun, tun zuwanmu ummura kafin rasuwar Aunty Raheema wata rigar barci nadauko wadda a wanchen lokacin duk cikin siyayar Ammyn itama red color nighty da ratsin baki, silk ce rigar amma ba transparent ba sosai, sai dai batada tsayi rigar da kuma super getty hand datake da.

B'ude wadan nan kayan yasa sun tunomun abubuwa dada dama game Auty Raheema, wanda hakan ne yasa danagama shiryawa tareda game duk jikina da turarukka kawai sai nakoma saman sallaya ta tareda kallon gabas na dauki charbi na nafara ja inna yima Annabi salati inna nan zaune "Uncle justice" ya turo kofar dakin yashi go, bai cedani komaiba haka kuma bai tsaya sauraren komai ba kawai umurni yabani cewar kisameni daki.

W'anda ganinsa kuwa har saida gabana yafadi ganinsa sanye da kayan barci, tunani nake araina meyasa har ya chanza kaya bazai kama hanya zuwa wurin matarsa ba.

H'aka yana gaba inna binsa har tsakiyar dakin sa inda naga yashimfida carpet na sallah guda biyu, baice dani komai ba kawai naga yahau kan daya dake dan gaba kadan da daya.

N'ima kuma bance dashi komaiba haka kuma banida zabin dayarage nima nahau kan dayan sallayar! yajamu sallah raka a biyu baija wasu dogayen suroriba, saidai kam yajima sosai bayan munsallame wurin jan doguwar addu a.

N'ifa kaina duk adaure yake zuwa yanxu nagama yanke shawa rar dole idan muka gama nakoma daki nakira wayar maman fareeda natambayeta game da auren na "Uncle justice" din.
Chapter 31 · 0% Book details