← Book details Uncle Justice Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 49

Sashe 24

Uncle Justice Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

S'ai na karshen su shine na kurkur da kwababen manshanu sai wasu sassake ita tuwa data hada tasaka akasko kafin tadauko bargo tarufa mun hayakin itatuwan yana shiga jikina nidai nawa kallo ne, kawai, ba halin yin musu, Allah ne kadai yasan irin halin dana shiga, banajin soyayyar "Uncle justice" haka kuma banajin kiyayyar sa sai dai kuma har zuwa yanxu banajin sam zan iya rayuwar aure da shi. Amma kuma wai meya sa kowa yakasa fahimtar hakane.

K'usan awadaya nayi har saida itatuwan suka karasa mutuwa tukunna aka budeni aka umurtan danaje na yiwanka kamar jiya yauma da rowan sansamin lalle da akajika da jan kajiji farin goro da magarya nayi wankan, da sabuluna na avacado da kiwi.

S'ai tafasas shen ruwan magarya da aka sakani zama acikin su bayan yasha iska maganine sosai dake hana duk wani iska ko namijin dare shiga jikinka mace.

Z'uwa yau kam gidan mu yagama cika dankam kota inna hayaniya ce tajama,a mutane dayawa sun halara tabangarora da dama kowa yana son yima maman fareeda gwaninta ne dakara, wanda hakan yayi mata matukar dadi sosai tanajin kanta yanayimata girma.

D'aga waje tun wurin karfe goma nasafe masu decoration suketa aikin kawata gidan, wuraren karfe biyu masu make up sukazo ba bata lokaci su kafara yimun, kwalliya suka zubamun sosai bawata yar batsau ba but I look down classy and matured.

S'hiri sosai akayimun da wani ratsentsen yellow swiss less da ratsin red, sai wani nauyeyen zubaben set na zinari hannun wuya kunai harda zobuna guda ukku sai azurfa kwara daya sai kuma agogo wanda shima na azurfarne akasaka mun sai jan abunrufa wanda yasauka har kasa dasukayi amfanidashi, duk wannan shirin su Aunty baby da Aunty uwani sai yaya sa,a ne mukadaine adakin maman fareeda suke shirya ni

H'udu da mintuna talatin dai dai sukariko hannuna zuwa cikin filin family get together akayi wanda kusan nace duka gidan maimarta ba yau suna gidan mu hiddima akeyi sosai, gambon sirajo yayi wasa sosai aranar kowa nakalla sai nagan sa cikin nishadi da anna shuwa, anyi picture sosai munyi na family, munyina family ummu salma, mun kuma yina familyn maman fareeda sai bayan magariba taron yatashi.

W'ashe gari tun danatashi da safe nake kwalla sam hawaye sunki yankewa afuskata maman fareeda tashiga damuwa ta kulle dani adaki dagani sai ita, tanata faman tambaya ta ko auren ne banaso sai dai na girgiza mata kai dole dai haka ta kyaleni yinin ranar banci wani abun kirkiba ita kuwa baba mairo mitar ta daya da damuwarta shine rashin zama naci abinci mai nauyi acewarta iyama lalurar jawad jama,a saida koshifa.😃

Y'aya mariya kuwa ita damuwar ta daya kofin tsimi 😰 duk inda nake sai tanemoni duk bayan awa daya tabani nasha ko kuma damammiyar furar dataji magani ko gumba.

Tun wurin karfe ukku mai make up tazo tafara light make up akayimun maman fareeda da kanta tashirya ni cikin wata super wax ligt ash da ratsin baki sai akasaka mun wata datsetsiyar alkyabba dark ash, da adon silver duk yanda akaso da na tsaida hawaye na kasawa nayi, duk inda tashin hankali yake da fargaba ranarnan akaina ya kare, ganin cewar kowa yakasa fahimtar illar wannan rayuwar da suke sonayi da "Uncle justice".

A nacewa nafito na rungume maman fareeda ga gam jinake lumfashina tamkar zao yanke, da kyar aka baban bareni jikinta yaya mariya tajani zuwa dakin ummu salma, zuwa nayi na dora kaina saman jikinta atunanina kozata turemun kaine, amma ga mamaki na first time in history naji tafara shafa kaina tace kiyi biyayayy yar gidan Asiya, maman ki mai kirkice, tashi kuje Allah yayi muku albarka.

Wani kukan nake mai narka zuciya, haka yaya mariya tajani bamuje wurin Abba ba sanin cewar yana tareda dayan uwansa suna gidansu samie.

Gidan babansu samie munsa mesa da dukka yan gidansu Abba wa azi sukayim,un sosai akan yanda nayima iyayena biyayyay ban yimusu musuba yace kwarai Abbanki ke alfahari da hakan sannan yamani kyautar set din sarkar zinari duk da bawata maigirma bace sosai, amma tanada kyau da tsari kirar dubai,

Bayan nan kuma sai mukabiya gidan wasu kakan nina haka wasu daga yan uwan su Abba sai kuma fada ba a wuce dani direct ba muka sauka.

*Idan kinada hali kibiyani Wannan littafin nakidine kibiya Hafsat Abu akar sadeeq first bank 3195366407*

*xxxvi*

A cikin fada kuwa munduka munkai gaisuwa wa mai martaba, duk abun nan da ake yaya mariya narike dani. duk mutanen da ke cikin fada kuwa nata saka mun albarka.

A'nbude taro da sallatin annabi, mai martaba shima yasakama auren albarka, tare da yin doguwar Addu'a kuma yace shekaranjiya da jiya da yau, duk yasa anje gidan anyimun saukar karatun alqurani bakwai sau bakwai, har kwana ukku.

D'uk aka dauki kabbara daga nan cikin gida muka wuce muka fara shiga dakin fulani karama, ta tarbemu da dammamiyar fura ta asalin katsinawa da dambun naman sa, karshe mukayi masauki dakin fulani babba.

N'i sai lokcin ma nasan dacewar wai da akwai hidimar daza ayi welcome to the family suma da suka shirya, wan da za,ayi yamxu anan gidan.

A'nan cikin kuryar dakin hajiya mukayi sallar isha,I tukunna aka maidani tsohon dakin Aunty Raheema Aunty Aunty mamie ce tace kiyi hakuri kidaina kukan nan yar gidan yaya Aseeya banida yanda zanyi dole tasa nadaurema raina nahakura da zubar hawayen ba don na daina na zuciba.

Yaya mariya ce tashigo da wani maganin tsugunno, takalli Aunty mamie tace mata suna son garwashi, tuni kuwa Aunty mamie tabugama uwar madafi wata tsohuwar mai aikin gidan da akayiwa sarautar uwar madafin, saboda kula dashige da fichen madafin gargajiya da cimar gargajiyar.

T'afadi mata baifi mintuna huduba sai gashi.

To tashi yar gidan Aseeya kihada da wananna dama barin sa nayi har sai ranar da za,a kaiki tukunnah tundashi sau daya ake turarashi ashekara. Ni wallahi Al amarin Ya'ya mariya zuwa yanxu kam har mamaki da tsoro yake bani, to duk fadan nata kuma inna tunaninta yake haba wannan abubu wanda take inna ma amfanin su haba ba halin nayi gaddama dole nayi yanda tace.

I'nna gama turaren mai make up wata daban ce ba wadda tayimun na gidanmu ba, tashigo. dan juyawa tayi kafin takuma juyowa takalli Aunty uwani tace gadukkan alamu ke kanwar sace Angon ce koh ta Aunty uwanie tace yayarsa dai. maii make up din tace oh sorry dayake basanin sa nayi yiba inna son ne naji yanayin mijin nata domin asan kallar kwalliyar da za a dora mata.

S'hiru dukka sukayi dan murmushi tayi tace baku gane ba kwalliya ranar kai amarya tanada ban banchi data event wannan tambayar damu ke zaibamu dammar sanin abunda zamuyi da zai kara armashin wannan ranar, misali wani zaki ganshi mai sanyi saboda haka zamuyiwa amarya kwalliya maisanyi maras hayaniya.

A'yayin da wani kuma zakigan samai zafi shima kuma mukanyi wa amarya kwalliya mai zafi wato heavy make up!

(to make the night hot)🔥🔥🔥🔥

Munayi ne dai depending on the nature of the groom.period!.💦🫧

Aunty mamie tanachin abinci tace to ayanayin zamansa dai da marigayiyah duk alamu sun nuna cewa mai zafine shidin, saboda haka yimata ita mai zafin, domin kam mijin nata mai zafinne! jawad kam ai dukkan alamu sun nunacewa lafiyaye ne, cewar Aunty baby dukkan su kuma suka kwashe da dariya.

Runtse idona kawai nayi ni yar gidan maman fareeda, a halin yanxu da so samune da ba anbunda nafiso fiye da nagnni gida saman ciyar maman fareeda, oh ni wannan family sam bata ido, idan dai wurin biyan bukatar dan uwansu ne.😢

N'ikuwa bansan sanda kukana yafito filiba sai yanxu wani irin tsoro da fargaba yakamani, tunawa danayi shifa "Uncle justice" yafadimani ya karbi aurena da hannu biyu, barin da. dashima yakejin auren kamar bama zaiyi yiba, so akwai yiyuwar wannan rayuwar kwanciyar aure tashiga tsakanin mu kenan.

F'uskar kowa dakin dauke da murmushi, suka hau rarrarshina.
matar nan ce wadda take yimun gyaran jiki Tazo tatsaya saman kaina tana rarashina har akasamu nayi shiru.

Domin niduk kusan yanxu kowa ma haushi yakeba ni, tayanda kirikiri kowa yaki fahimta ta kuma da gayya sukaki su fahimceni din.

Make up tayimun heavy abunda yake heavy sosai, koomai yafito ram, lip dina sunsha lips glow sosai bayan red lipstick din daya sha, tukunna a
kashirya ni cikin wani tsadeden material purple mai haske wato lilac, fitted gown har ja take a kasa, ko inna nata walwali yake, tagyra gashina tayi parkin dinshi tsakiya, sai wata lafaya silver color, da tasaka mun sai zallar sarkar diamond tacikin lefena maidan fadi round neck da akasaka mun akalla kudinta zasu tasarma million biyar, sai munduwa mai daya hade da agogo dan siriri fari sai kowane yatsan tsakiya da aka sakama dan sirrin zobuna, kowane hannu guda biyu biyu.

Mark 👉you!

Yes you! 🤓ba acikima amarya kayan yari masu yarbatsau dayawa, idan za,a kaita su akasari anfison sirara it looks more sexy then the heavy ones.

Haka kuma wani lokaci suna dan dagula lissafin miji ko surika cizonshi.

Aka daura mun da daurin dankwalin zara buhari gashina tabaya yasauka sosai yana shining, aka turarani gaba da baya dawani mayen turaren rushi mai sanyin gaske, tukunna kowa yafita, aka barni nikadai adakin.inna dai zaune atsakiyar dakin saman kujerar da na zauna akagama daura dan kwalin kaina akasa banji shigo warsa ba kamar yanda nayi zurfi cikin tunani sam banjii fitar suba.

G'anin mutum kawai nayi yatsugunno gabana, aikuwa gabana yayi wata irin tsinkewa, jinayi tamkar zai fado, dole tasa na rintse idona, banyi tsammanin ganinsa ba, nadauka sai dai muhadu achan gidan ne.

Y'ana sanye cikin danyar sahdda dark Purple da takara fitar da hasken fatar sa, sai alkabba dark ash! daya dora, sai rawanin da akayi masa simple but amazing,

Yayi kau sosai dashigar kallarshi tafarar fata tadace da kalar alkabbar sa, kallo daya nayima shi, nadukar da kaina, baiyi magana ba nima kuma banyi ba, ban kuma sake dogowa nakalle saba, kaina n akasa,
Chapter 24 · 0% Book details