← Book details Uncle Justice Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 49

Sashe 14

Uncle Justice Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saboda tsabar gauraya dasukayi, kai naga tasku awannan ranar. ahaka munsamu kusan awa daya ahaka tukunna naji yasauke wata sanyayar ajiyar zuciya! duk nauyin jikinshi yasakarmun shi, har na tsawon mintuna shabiyar, kafin yatashi yazauna yajiyo yana kallona. Irin kallon dayakemun yasa sai yanxu nagane wato yasanma dawa yake tare, yasaka hannunshi agashin kaina, da duk ya hargitse innadai jinsa amma banbude idanuna ba.haka kuma hawayen basu daina zuba ba, ya sunkuyo yaimun light kiss asaman kwarmin idona, nakara runtse idona ga gam, yadan tsaya yana kallona. lumfashi mu sarke cikin najuna.

Araina nace shima yanaganin rashin dacewar abun da yayin yatsa ya yana kallona,
kafin yatashi ya kwabe kayan sa yasaka towel din Aunty Raheema tsoho, tukunnah yashiga wanka.

Dakin dayake kullum sai anshiga anshareshi an wanke toilet, tareda chanza zanin gado, abi shi da turaren wuta yasa bakataba cewa ba a amfani da dakin ba sam, komai nadakin tab yake.

Aranshi shima yana tunanin wai meyake shirin faruwa dashi ne, shidai yasani sam baishirya yin rayuwar aure da wannan yarinyar ba sam, haka kuma yakudurta sai in idan angama komai kura talafa dole yanaimo wadda yake tunanin zata iya daukar lalurarsa, kamar wadda ashekaru dai duka bai wuchi yabata shekara ukku ba ko hudu amma inna jinta ajikinsa sai yaji kamar wani fitina nan maganadisune yake jansa da bazai iya hakuraba, wallahi kuma duk da dai bawai yafitar da abunda kedamun san bane amma kuma wani Karin abun mamakin wata irin natsuwa sosai yakeji ataredashi, harwata iska iska yakeji tana ratsashi, idan yantuno da alherin yarinyar kuma agaresu siayaji tasamu wani muhalli azuciyarsa, amma baisan kowane iri bane.

Ahaka dai har yagama wanka yafito, nibanma san kalar tunanin da zanyiba, dama nasani sanda ummu salma tace saina kirasa awaya danayi zamana, ban zoba konace nakirasa yace karnaje, ban maji fitowarsaba sai dai kawai naji, cikin murya mai masifar sanyi naji yayimun magana, ko zakiyi wankan ne, jin hakan yasa nadawo cikin haiyachina nadawo cikin duniyar da muke.

Duniyar mu tagaskiya nabaro duniyar taurari nayi maza nadiro daga gadon dirowata.daniyar nagudu nabar dakin, amma sai naganshi, tsaye gaban gadona. dagashi sai towel, ganin haka yasa nayi sauri komawa gadon nafada tabaya tareda runtse idanuna.har inna bugewa ahannu. nakuma hanzartawa natashi nahada hannu duka biyu inna rokonsa kaina sadde akasa muryata na rawa duk jikina rawa yake bandagoba nake cewa pls kayimun rai gefe daya yakoma yachi gaba dashirin sa baidai cedani komaiba, har saida yagama yadauko jalla biya yasaka yashafa turarukka. tukunna yajiyo cikin natsuwa atake yafito a "uncle justice" dinsa na ainihi! yace kobazakiyi wankaba kishiga ki kama ruwa, kiwanke fuskarki
nasan hali ban tankaba nawuce nakama ruwan nakuma wanko fukatan, jina nake duk wani bakon yanayi yasameni, tamkar bani ba hakanake jina lebunana sun dan kumbura, duk suncika mun baki nakeji, sunyi dan jaja sai zugi suke, nazama duk banida kuzari sosai.

Saidana fito yataka har inda nake yakama hannuna yatunkari kofa dani sai lokacin nafahimci nufinsa fita zamuyi ahaka ai bansan sanda nakira sunansa ba ban kalleshiba ammashi yajiyo niyake kallo, hannun namu nasarkafe dole tasa nima saboda tsoron tunanin idanunsa yasa nayi shiru!

Ahaka mukafito dakin yajani zuwa har cikin pallown Fulani babba pallon kuwa na acike hatta suduka amaren suna ciki, ai tuni bansan sanda wani karfi yazomun ba nakubce hannuna, shima din baice komaiba yawuce zauwa dakin mahaifiyar sa,
Haba wa yana wuce wa wuri yadauki ihun, su zeena dadina da yayana yamaseefar sanin kan luv, tamkar wanda yayi dagree da masters akansa.cewar shukura aifa "uncle justice" ba bayaba inji zeena, to amma dasaiki gayama su ummu salma cewar kefa kina wurin mijin ki👀 kar ma su wahalar dakansu gurin naimanki, duk gidan nan yau basashen daba adubaki ba, baki balabarinki, saida Allah yasa asabe mai aikin fulani babba tace taga shigarki dakin marigayiyah, kuma yarima jawad ma yana ciki.haba jinna yi kkamar nakurma ihu! hawaye suka dingayimun zarya, oh Allah haba ganin hawayena yakara basu dariya yarinya aikin tonama kanki asiri, ba irin kiran wayarki da maman fareeda batayi ba, amma yar nan kikaki dagawa, kedadi miji koh! cewar small aunty khausar,

Zeenah ce tazo tazauna dani daga mutuwar tsayen danayi, tace haba zauna mana yar uwa damaku masu cika baki to sam baku iya shiga hannuba, fitowar Fulni babba tareda "uncle justice" yasaka su yin shiru.

*IDAN KINADA HALI DAN ALLAH KIBIYANI TYPING AKWAI WAHALA*

*xxii*

D'ariya naji ankwasheda ita ashe mama habiba ce kaanwar Fulani babba, shakiyay da ai sai kuchi gaba mana, hhhh tajiyo takalli "uncle justice" tace toh ai saika kai fareeda gida tunda annnai meta ba agnata ba, ni alokacin inna durkushe iina gaida Fulani babba so, nake nace aska driver yakaini amma bahali saboda kunya yace ai munatare tundazu, jinhaka yasa wata uwar zufa tarufeni, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, har wani zazabi zazabi nakeji, najima da sanin cewar "uncle justice" shi sam bakunya acikin al amuransa, amma wallahi sam bansan cewar abun nashi yakai hakaba, sai yau 😰

Ya illahi nidai gani nan dai ne kawai
Baba Fulani tadafani tanamun murmushi, ita kamar nalura ka san cewar mu taren dadi yaimata sosai yar gidan aseeya kozakiyi kwanciyar ki anan, sai agayama mamanki cewar kina nan din! da sauri na girgiza mata kai inna kara sadda kaina kasa, bandaiyi maga naba to ai naga dare yayi,

Muryata chan kasa dama kuma ga kunyar danasha ga nauyin da lebena keyimani, yatai maka gaya nasakawa muryata takarayin kasa nace mata ah ah innada fita asibiti gobe tace toh! bakomai Allah yayi albarka.

Acikin ranta tana hamdala da Allah yasa yaronta yau yadan samu sawaba, domin hardan cikowa taga yayi ga fara arsa yau takaru, yau shine har yanacewa ga abunda zaichi a shirya masa bakamar sauran kwanakin bayaba da kullum cikin azumi yake, duk yayi wata rama gashi idan yasha ruwanma yayi bude baki bawani abincin kirki yakeciba sosai wani lokachin har saita tsaresa tana matsa masa, amma duk dahaka da kyar takesa mu yadan tsikara, yatashi kai kasan abunda zaisaka jawad yaguji abinci to tabbas yafi abincin amfani, domin tun tashinsa tasaan shi da son abinci da cin abincin amma yau kadai gashi har shine dakanshi yake naiman abincin!

To kutafi auta dare yana karayi tasamu takanta tahuta tace gobe sunada fita, na dukusa har kasa nayimata bankwana, muka fito a yayinda shukurah da zeenah suka mike domin yimana rakiya.hararasu "uncle justice" yayi yace kukuma fa inna zaku tuni ko waccensu tayi u turn shikuma yariko hannunah muka wuce,

Bayanda ban yiba yasake mun hannu amma yaki ko kallona ballan tana yasan menakeyi mutum komotsi bayayi tamkar gini, dole tasa nahakura iya kunya yau kam nashata araina nace nida gidan mai martaba kam sai illa masha Allahu!.

Kasan cewar dare yasomayi kuma akaidar gidan mai martaba karfe goma akesakin wasu mahau katan police dogs amma kasan cewar yau anyi hidima gidan baisan da fitowar muba kwai yabude cage din suka fito kodayake saida ya hura usur domin tabbatarma mutan nen gida cewar zaibudesun amma ganin cewar yau anyi hidima yasa yabarsu har zuwa shadaya suka fito a 360, tareda gurnani da haushi haba aiban san sanda na karbe hannuna awurin uncle justice ba, naruga da gudu wata wawuyar chakuma "uncle justice" yayimun bansanma lokacin dana maleshiba abunku ga kakarfan mutum kuma mai tsawo tuni yarikeni da hannu daya kuma irin daukar da akayima yara, kafin yatsaya yaima karnukan wani yare mai kamada yaren Chinese, sai kuwa naga duk suntsu gunna, gabanshi, sun daina haushi, shima kuma tsugunawar yayi dani a hanunsa, ganin yana kokarin saukeni yasa nakara kankameshi jikina ko innah bari yake!

Waini meyake shirin faruwa danine, juyowar da zanyi nagansu gabdamu nikuma dai dai wurin kunnesa nace masa "uncle justice" plsssss muryata cikin kuka kuma in a low turn, a kokarin danake gudun kar sujini.
wani mugun waha lalen lumfashi domin tamugun tabo adakarsa, yanayin yanda tayi magan hucin iskar maganar yana sauka cikin kunnanen sa.

Yashafa kaina tareda mannamun light kiss saman kwarmin idona, da asaman lebuna na, "it's just going to be an introduction noting else" wayyo yau naga takaina duk narude yajuya wurinsu yakarachi yarensa sai dayagama bayani sukuma sunyi sshiru tamkar masu amsar darrussa, da yagama dasu sannan yajiyo tareda mayarda hankalinsa kaina, yace zaki gaisa dasu tayanda duk sanda kuka koma haduwa bazasuyi miki haushiba. kokuma yunkurin biyoki cikin kaduwar jiki da tsananin tsoro yau Allah yakawoni wai nagaisa da kare nadai cemussu sannunku batareda nakkallesuba.😜 kuma har alokacin inna makale jikin "uncle jsutice" cikin dan daga murya yake cemun bahaka zakiyiba hannu zakibasu kuyi musa biha yaufa naga takaina, nafadi araina ban ankaraba kawai naji yariko hannunah saidai naji abu mai laushi laushi ahannu naah wanni ihu nayi maidan sauti nace wayyo "uncle justice" baimabi takainaba yachi gaba da mimmi kamusu hannuna muna gaisawa, tamkar yanda maza sukanyi musabiha da junansu idan sun hadu.
har muka shigo mota tukunna yafiatrda senitizer muka shafa ahannu duka yahada hannu wanmu yana murzawa, jikina baidaina bariba sai wata ajiyar zuciya danake, saukewa lokaci bayan lokachi.

Mun isa gida wurin shadaya bamu samu kowa a pallow ba, saidai nadanji motsi acikin kitchen, inna lekawa sainaga ummu salama a kokarinta na hadama abba rowan bunu da yakesha duk dare! banma tsammanin taganiba saidai naji tace kekuma kedawa murya ciki ciki inna faman sadda kai kamar wadda tayima sarki karya nace mata tare mukeda "uncle justice" yana pallow ummu salma tafito cikin girmamawa suka gaisa tacemasa maiyasa yabiyemani yataso cikin daren nan ai dakabari saida safe tunda munan bawani abun zatayi manaba.
Chapter 14 · 0% Book details