← Book details Uncle Justice Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 49

Sashe 41

Uncle Justice Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

M'unje w'urin meeting Koda aka kirasa da yaganatar da jawabin godiya, bayanin yake Amma idonsa nakaina.

K"unya kamar me takamani ganin kamar hatta shida kansa Mai martabar yalura da hakan.

Amma abun da yayima kowa Dadi da bai wuce yanda naazage sosai lokacin cin abinci w'urin kula nahada Masa Abinci ba,

k'usan komai da aka gabatar w'urin Saida nadibar Masa namatsa sosai kusa dashi naganartar Masa ganin h'aka kowa abun tayimasa Dadi yanda nake kula dashi wanna yanuna ma kowa cewar sosai nasamu kwanciyar h'ankali danatsuwa a Auren.

S'ai bayan da muka dawo dakine m'una dakine mungabatar da sallah magariba su Zeena ketayimun tsiyar wai wane irin dafine "Uncle justice" yazubamun haka da nazama Bata ido bana kunyar kowa anake ciyar da miji.

Khoolsum tace kusanfa itace farkon tashi tabama miji Abinci nihar tajamun zayyan yanata cemani Naga yanda ake Dan nayi course

Y'arinya kinji taraining cewar small Aunty khausar kenan Allah kuwa kowa sai mamakin yake ke Kinga kallon da kowa kemaki

Fulani babbab wallahi tamkar zata mayar dake ciki Dan so.

Ai kuwa Nima Sai alokacin da sukayi magana tukunnah natuna irin tabarar da nayin.

H'abawa ai idan dai "Uncle justice" ne yarinya ke bakyamasan lokacin dazaki Zama Yar hannuba duk mukasaka darya.

*Idan kinada Hali kibiyani Hafsat Abubakar Sadiq first bank 3195433607*

*LXIV*

Y'au bayan sallah da kenan da kimanin sati biyu kenan,

W'anda hakan yayi dai dai da bukin khoolsum saura kwana Ukku afara,

Kuma y'au kusan sati daya kenan m'una fama Nida "Uncle Justice" domin tafiya aiki yaka masa zuwa Abuja ajibin da za,afara bukin khoolsum din.

Shirye shiryen tafiya yake ta shiryamana domin a'take yasaka cewar aje sawake sabon fenting gidansa dake Abj

K'uma a tabbatar da wutar lantarkin gidan lafiya kalau take da Kuma ruwa Suma duk atabbata suna zuwa ko innna tunda anjima ba,ayi amfani da gidan ba to ba,arasa Yan gyare gyareba Nan da Chan.

S'hifa tafiya sosai yake shiryamana a i'nda nikuma nadage cewar bazaniba.

W'annan yayi dalilin dayasa duk Yan kwanakin nan sama sama muke da juna nidashi,

W'anda hakan niyamun Dadi nakan Sami issahen lokacin magana da khoolsum m'una ta shiryen shiryen buki,

Kuma zuciyata nakara karfafamun gyuwar cewa nakyalesa kawai shin yama za ace n'i din ban hallarci bukin khoolsum ba.
Idan badon rigimar Uncle justice ba haba.

W'adda ko a lokacinda m'una school of nursing idan suka samu sabani da zayyan to nice Mai sasanta su

Kaf adangina ba Wanda bai Santaba h'aka itama nata dancing ba Wanda baisanniba.

Kai takaima har Yan gidansu zayyan ma sun San dazamana.

T'unda dukkasu din sun hallarci bukina Amma Kuma duk dahaka sai y'anxu ido ba kwalli ace wai Kuma bazanjeba.

A'nna gobene tafiyar jibi Kuma afara bukin khoolsum n'idai kallonsa kawai nake Yana shirya kayanmu tsab cikin travelling bag.

Duk. Irin shigar dayake masifar son yaga nayi to duk irin kayan yadibar Mani .harda wadanda bantaba sakawaba

Yana hada kayan Yana Yar wakar sa,adu bori ta Ashe mata wayyo sukemana.

N'i gaskiyarma yawa yayimun wani lokacin idan nakallesa nakan karyata cewar Anya kuwa wai wannan din "Uncle justice" ne kuwa.

M'utumen da da maganama wahalar Yi takemasa to ballantana waka.

Yanata shirinsa Nima Kuma munata shirinmu da su samie domin ko yauma Saida natura khairat ta karbomun dinkuna.

H'aka ma y'au dazai fitazuwa gidan Mai martabar da dadare yayi masu bankwana Inna zaune parlor ban nuna alamun zuwaba charting muke damasu snacks da decorations dazasu yimana jibi.

Wuf naji yadagani sama yachafe ya kurreni da kallo f'uskarsa dauke da murmushi yace mutafi muyi masu bankwana gobe I war h'aka m'una Abuja insha Allahu a cikin kunnaina yake radamun idan m'unje mezan samu, nakshe Masa ido daya nace Masa komai kakeso kasamu my dear "Uncle justice" Mai gudun miji.

Gaskiya sai nakada maki gangar wakar mace maigudun miji,

M'ace har mace mace ko ta Inna Masha Allah Amma sai gudun miji.

L'umce Idona kawai nayi nasaka hannu na nadama innashafa sajensa.

N'ace kaina fa kagane "Uncle justice" haba haba ace irin yanda mukeda khoolsum harfa shiiiiiiii yacemai bai Bari nakarasa ba.

G'obefa sa Abuja baby achan nakeson musama little Kani ko kanwa bugun Abuja. 😅

Yana dauke Dani mukaje daki yadaukomun farar After dress, yadiro mun saman doguwar rigar roba matterial sky blue dake jikina.

M'una m'una dakin Fulani babbab m'una fira, tanata hadamana kayan kwalam da makulashe "Uncle justice" tunda shina Auta har gobe kallon karami take Masa.

N'i har dariyar abun nake cikin Raina, nayanda Fulani babbab ta hakikance dauko wannan dakuwa dauko chinchin, dauko loga, illoka,
balla kwabo, mune dai harda dabino tarkacefa sosai saikace wadanda zasu boarding school.

M'una Shirin tafiya Maman fareeda tashigo naruga da gudu narungumata, farin cikin ganinta duk yamamayeni .

Rabona dasu tun sallah damukaje yimasu barka da Shan ruwa, naji dadin ganinki Yar gidan Asiya nakara langabar dakai nace Nima h'aka.

Saida muka koma akadan Taba fira da Maman fareeda tukunnah "Uncle justice" yaduba agogon hanunsa yace yakamata mutafi domin mukwanta da wuri gobe insha Allahu akwai tafiya agabanmu.

M'aman fareeda ce ta magantu ta cetafiya Kuma wace irin tafiya,

A'mma badai da Yar gidan Asiya a koh! dan kallonta yayi rahamar dake f'uskarsa na faukewa.

Y'ace uhum menene matsalar hakan Shiru tayimasa batayi nagana ba sai dai mukaji Tana gayar da Mai martaba a waya atake ta tagaba tar Masa da Tana naiman alfarmane da ayima jawada magana dayabar fareeda datayi bukin kwarata kwaya daya kachal.

H'aba kodon s'aboda hallacin mutanen, kadibafa tayanda kawanchen su yake tun suna Yara, Amma Kuma ace dare daya Jawad dawata akida tasa yahanata zuwa bukin.

A'take kuwa Mai martaba yakira "Uncle justice" a waya Wanda tun sanda mama fareeda tafara waya kansa yake sadde akasa yanana jujjuya wayarsa.

A ringing daya yadauka bayan salama hadda Dan rusunawa yakai gaisuwa tukunnah yayi Dan Jim nawani lokaci.

Mai martaba yace Jawad kayi hakuri kabar iyalin naka data hallacci hiddimar bukin Aminiyarta.

n'i shaidane uban yarinyar Mai mutumci ne sosai,da son karamchi

N'ikuma Inna zaune tamkar wadda ruwa yacini kuri nakuresa da kallo, Inna son ya jalleni Naga awane mizani ya ajiyeni ni Mai laifi ko akasin haka

B'aiyi maganaba saidai Adam Apple dinsa dakeyin sama Yana kasa, Allah yataimakekah yanda duk kace h'aka za,ayi.

Addu a sosai Mai martaba yayi Masa tareda fatar Allah yasa ayi tafiyar cikin nasara da sa,a.

Y'ana ajiye wayar yayi shiru duk mukayi shiru Yana kokarin boye damuwar da fushinsa Amma abun yafaskara.

Damuwa tafito karara afuskar fulani ce taketa kokarin kwanatar Masa da hankalinsa,

T'ana Kuma jadda Masa dayatabbatar cewar yanaimo cook din Mai martaba na Abuja kar yace zaici abincin waje.

M'aman fareeda ce takarbe zamchen tace kamar yaune ai wuyarta dai afara bukin kwana Ukku zuwa hudu angama, insha Allahu idan yasotana iyya samunka d'aga baya.

Kokuma duka duka sati biyu i'nda rayuwa...... Baima Bari takarasa zancentaba yaje ya durkusa gaban fulani yacire hukar kansa, tareda dukar dakansa gabanta,

W'adda Naga alamar itama duk tashiga damuwa yace fulani zan wuce tashafa kansa tareda yimasa Addu'a tace Allah yayi maka jagora jawad, yakaddara saduwarmu yace Amin.

M'ikewa ka wai yayi batareda yako kallo gefen danakeba, yanatafiya yanayima Maman fareeda bankwana.

D'a hanzarina Nima natashi nabisa

Koda nafito har yayi nisa a harabar gidan tun ayanayin tafiyarsa nagane cewar bakaramin konuwa ransa yayiba.

G'udu gudu sauri sauri nakarasa har yashiga mota a motar gudun karyatafi yabarni

*Idan kinada Hali kibiyani Hafsat Abubakar sadeeq first bank 3195433607*

*LXV*

D'a wani irin gudu yafigi motar har Saida na runtse i'danuwana, domin ganin nayi tamkar zaitashi da get din gidan Mai martaba.

K'uma tun amota kamaninsa suka chanza d'aga romantic "Uncle Justice" Dina bayanxu zuwa ainihin "Uncle justice" din Aunty Raheema shine sak agabana.

Da wani irin mugun gudu muka shiga .gida har Saida yabuge wata pillar ta flower vase dake gefen da zai hadaka da sashen baba mairo.

H'ar ban San sanda na riko hannnunsaba, s'aboda tsoro ba yakuwa yarfe hannun nawa yayi da maseefar karfi ya yarfe baijira komaiba yabude motar yafita.

D'asauri yashige cikin gida nabisa dakinsa ya wuce direct yadauki akwatin daya gama hadamana Kaya dazu yajefar da sauri naxo nayi huggin dinsaa tabaya tuni Hawayen sunfara zuba a Idona.

D'a karfi ya fincikeni tsugunnawa nayi gabansa inna bada hakuri.

J'uyawa kawai yayi yashige toilet, nikuma har alokacin bantashiba har yagama wanka yafito baikula niba,

Y'acigaba da Shirin barcinsa Wanda idan da ace gari lafiyane da a tare zamuyi wankan, ko Kuma shiyayimani koni. Nayimasa.

B'insa kawai nake da kallo har yagama shirinsa ya kwanta tukunnah nahakura Nima natashi nayi nawa wankan nashiraya.

K'oda nazo nasamu ya kwanta yajuya yabani baya da sanyin jiki na matsa jikinsa na rungumesa tabaya nafara shafar kirjinsa ahankali nakeyimasa magana "Uncle justice" please kayi hakuri Dan wallahi nibani nace ma Maman fareeda takira wayaba,

W'allahi niba kararka nakaiba bansan zata jiraba da banbariba.

S'hiru dai bai tankaniba, ranar ko dabinon da yakecin karshen kafin ya kwanta da ruwan zamzam baishaba.

H'aka muka kwana ba Wanda yayi barci kirki cikinmu sai juyi muke.

Da Aduba bayan nayi sallah nagama karatun qurani tun wurin six nashiga kitchen duk dacewar jiya innaji Yana fadima orderly cewar sai w'urin karfe komane tafiyar Amma Madai tunda Inna son nagama komai da wuri.

N'ahada masa Kari Mai kyau na lafiyayen fataen doya da wake da stock fish aciki, sai hadin mix macaroni and fish salad.

N'ahada Masa. Chunchin cake, donut da dambun Naman kaza dazai tafi dasu naje da sauri sauri nayi wanka ganin Tara tayi nashirya cikin yellow atampha, Mai Dan jefi jefin Adon red flower aciki atamfar Golding ce s'aboda h'aka nayi amfanida gold Yan kunne da sarka, sarkar tasauko mani har tsakanin mamuna na lokutta dayawa idan nasaka sarka Mai irin wannan zubin "Uncle justice" zaifita kallon kirjin nawa Yana yabawa.

N'a nufi dakin Saidai me innashiga dakin nasamu suna waya da Fulani babbab, Tana yimasa korafin da yatabatar da karya karyasake yakama hanya batareda yaci komaiba.

A'msar dayabata itace tamugun bani shock cemata yayi shi yatashi da Azumi ne s'aboda h'aka bazaici komai ba.

T'saya nake nakuresa da kallo lack of Understanding nafada araina idan bahaka ba "Uncle justice" bai kamata yadauki zafi hakaba.

Yajuyo kaina bayan sungama wayar da fulani ya kureni da kallo shima,, tuni Hawayen suka cikamun ido nafashe da kuka.
Chapter 41 · 0% Book details