← Book details Rufaidah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 29

Sashe 6

Rufaidah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shidai jambros Motar Maryam yawuce ya shiga suka tafi shima yayan bayan sunsaka kayansu a boot din car din ya zagayo yashiga gaban Motar zee zata shiga baya Rufaida tarike ta ina zaki kekuma ciki mana tunda Motar ta ubanki CE koh?? Matsa dallah malama ,Yaya yasaki baki ganin abinda ke faruwa,baiji dadin abinda yafaru bah amma yasan bazai iya yiwa Rufaida magana akan tadaina ba,da kyar ya lallabata suka kaita gd inda suka yi da ita amma tace Sam ita bazata shiga ba,Yayan ne yarakata har cikin gidan suka gaisa da MAMAN tayaba da hankalinshi sannan ta kudurce a ranta tasan mezatayi.

*** suna zuwa parking kawai tayi ta shige ciki ba tare da bita kansa bah,shikuwa dakinsa direct yawuce ya rage kayan jikinshi ya watsa ruwa yafito ya shirya ya zira wata jallabiya Mara nauyi yafito parlour,baiyi mamakin rashin ganinta a parlourn ba yazuba abinci yagama cike da tunanin yadda yake Dada jin son Rufaida a ransa yasan soyayar su daga Allah ne, a Bari daya kuma yana tunanin yanda yabari har zee itama ta shiga ranshi kodayake Ai ba abin mamaki bane duba da halayen yarinyar masu kyau.

*** washegari da safe mummyn zee takirawo wayar kawarta tasanar mata tazo dan Allah ta aiketa gurin malam tanaso yamata wani aiki,,,,,ba a dauki lokacin HAJIA majidda ta iso ta tarar da zee a parlour ahaah mutum canada saukar yaushe ??? Jia muka dawo toh sannunmu dazuwa ,hajian Tana cikine ??eh bata Dade da shiga ba,toh bari nasameta.
Zauna Haj.maijidda kinsan me nakeso dake akwai wani yaro dayazo jiya yana son zee zee shi ne nakeson kije gurin malam mai gani har hanji dan Allah asan yanda zaayi ya karkato da hankalinsa duka akan yarinyar nan sunyi aure kawai ,ita zee din kinsanar mata HAJIA?? Aa ko kusa bana so tasani kinsan ita Ai ustaziya ce inda sanin ta zaayi Ai bazai yiwuba,toh kinsan irin wannan aikin yafi kudi HAJIA nasani GA dubu hamsin nan inbata isaba sai kiyi min magana kinji,yanzu dai kije yau HAJIA kinsan bazan samu zuwa ba tunda Abbansu yana gari, toh shikenan karki damu yanzu haka can zan wuce( wa iya zubillah).

**** sunje sun gaisa da HAJIA ,inda wata soyayya mai karfi takara shiga tsakanin Rufaida da Yaya da kuma Aliyu (Jambros) da Maryam .

** bayan kwana uku ne hajia maijidda tasanar da HAJIA komai yakammala zasu iya tunkarar shi da zancen aure tamata godia kwarai.

Toh a barinsu zee da Yaya suna gaisawa ba laifi sai dai Sam baya bari yakirata a gaban RUFEEY.

*** wata yammaci ne suna zaune a parlour suna hira a parlour yaji wani matsanancin ciwon kai yabukaci bari yaje daki ya huta dama lokacin islamiyyarsu yayi tayimasa sannu suka wuce itada Maryam inda shima yawuce nashi dakin.

Yana kwanciya da niyyar bacci ne yaji wayarsa na ringing da baiyi niyyar daukaba sai kuma yajanyo wayar zee zee yagani akan screen din yadauka tareda da kara wayar a kunne shi yana fadin" hello".

💞taku har kullum Rufaida Yusuf.. Kukasance dani domin jin yadda zata Kaya.
Domin tsokaci katuntubeni akan email dina [email protected]
💘💃🏽🌹RUFAIDAH🌹💃🏽💘

Written by Rufaida Yusuf.

6⃣2⃣ - 6⃣4⃣

I Dedicate dis page to my luvly friend Hauwa Bashir Karaye( Mr's Mahmoud).

***** am so sorry readers 4 d short typings it happens under some circumstances and eyn sha Allah by next week everything will be OK!!

.............Tayi Ku kanta mai isarta ta godewa Allah amma duk da haka tanajin zuciyarta na tukuki,tashi tayi ta dauko hijab ta sanya dama da alwalar ta tayi sallah rakaa biyu tayi adduar Allah ya dai dai ta tsakaninsu da Yaya yakuma rage mata sonshi.bayan tashafa adduar ne takishigida a wurin Tana tunanin laifin datayimasa haka,ita dai tasan koma wane irin laifi ne haka babba ne domin tun tasowarta ita dai tasan koh umman tace tamata tsawa sai yaji haushi bare wani bare kuma ace yau da kanshi yakamata haka, ajjiyar zuciya ta sauke.
Ganin ba inda tunanin zai kaita kuma takasa runtsawa yasata tajanyo Qur'an ninta Tana karantawa har bacci ya dauketa,bata farka ba sai da asuba ganin ta tayi akan sallaya,taje tayo Alwala ta tashi Yaya Maryam sallah.

Bayan ta idar da sallar ne tayi azkar din safia tadanyi karatu shafi 3 kasancewar wani bacci datake ji,tana kai ayat tahaye gado sai bacci .

**** toh Tana farkawa taga har Maryam ta tashi ta shirya itama wanka tayi ta shirya da summer gown Mara nauyi da daura hula akanta,tanufi sama.

Tana isa taga umma saman gado ta durkusa tareda cewa UMMA ina kwana? Lafia lao Rufeey antashi lafia? Lafia kalao.toh madallah dazu Ai na leka dakin naku naga Maryam ce kadai ta tashi,eh nazatama Tana saman,Aa dazu tashigo,amma yanzu Tana kitchen ita.

Zoki samu guri ki zauna inaso muyi magana kinji,toh UMMA .

Kinsan kowanne bawa da Abnd Allah yatsara masa zakiga kina taki Allah shikuma yana nasa ,ba abinda kakeso ne zaiyi takansancewa bah.nikaina lokacin da naji zancen hakika abin ya girmame min sosai sai dai Dana tsaya nayi tunani nabar abin akan cewa kaddarar kici hakan,Ni kaina dabani akaiwa abin ba banji dadi ba bare ke yanzu abinda nakeso dake shi ne koda kinji zancen Indai kin haifu kinuna ba komai bane kuma Inason yafi ruwa gudu dan wucewa domin banason kidamu kanki akan abinda bazai damu dakeba kokuma damuwar bazata kara miki komai ba,,,,,,UMMA wai menene Niki fadamin Yaya ne yamutu kome???? Koh daya Rufaida yayanki jiya yasamu babanki akan zaiyi aure da wata Zainab zaa hada dana Jambros wata daya maizuwa sabo...... Harta karasa zancen sannan takalli barin da Rufaidan take ganin mutum tayi a kwance babu ko numfashi ,Innanillahi wa inna ilahir rajuun !!! Maryam!!Maryam!!!!! Tana karasowa suka dauketa suka sakata a mota umma da kanta tayi driving motan.

Basu tsaya ko ina ba sai nearest hospital HALL MARK CLINIC nandanan aka turata sai emergency aka bata taimakon gaggawa Tana farfadowa suka yamata Allurar bacci aka saka mata drip,sai a sannan aka bar su umma suka shiga ,takira Baba tasanar mishi da kuma mama Zainab.

*** bata farkaba sai gefin maghriba,Tana farkawa da salati a dakinta a lokacin umma taje gida ta dawo ,da sauri Maryam da mama Zainab suka karaso gefenta sannu meyake miki ciwo,keeh?!!!!!! Jiki kira likita maza maza ............

Bayan komai yalafa umma da mama Zainab suka karayimata nasiha suna mas tausayamata tayi musu alkawarin eyn sha Allahu zan manta dashi umma zanyi kokarin maida komai ba komai ba,su Kansu sunyi ganin yanda tayi tawakkali da wuri .toh shikenan mu bari muwuce Ku zauna da sassafe zamu dawo.

Sis Maryam ta taimakamata tayi alwala tafara sallah , karar wayar Rufaida tadawo da hankalin maryam daga chatting din dtakeyi,ganin sunan besty yasata dauka hello HABIBA maryam ce ...................................

Salamu alaikum,kai besty amma kunyi sauri kai Mara lafia ce take surutu haka. Nidai ince naga zakuzo islamiyya ba akwai dalili( habeeba da ummy kenan friends dinsu na islamiyya) bayan sungama gaisa wa UMMY tace bari Nidai bari nawuce kan mama tadawo kefa habeebah???ai Ni muna 2gether anan zan kwana Aa toh bari muraki ki UMMY toh sai kun dawo.

Bayan sun dawo ne sukabawa habeeba labari ita dai Rufaida hawaye kezuba a idonta ke malama yi kukan ki dan ammiki abin kukan.

***😞kunsan me abinda yake sani tunani shi ne Wai shi yayan bayajin yadda nakeji ne hmmm ,sis wallahi yanaji anfi karfinsane kawai amma addua ita tamu ynz.

Kinsan me besty cewar Beebah,nasan yadda kikeji a ranki amma abinda nakeso dake ki dake karki nuna kin damu kinji!!! Owk sis .....a haka harsuka shiga shirye shiryen bikin sis Mar� .................

Taku har kullum Rufaida Yusuf. Domin taokaci Ku tuntubeni akan email dina [email protected]

. ina gayyatar kowa da kowa zuwa bikin yayata Wanda zaayi a OANO ranar asabar a st.Louis secondary school by 3:30pm promt.sai kunzo
💘🌹💃🏽 *RUFAIDAH*💃🏽🌹💘

Written by Rufaida Yusuf.

6⃣1⃣

❤am sorry lovers 4 d short typings plxx its due to some reasons and everything will be settled soon eyn sha Allah. I dedicate dis whole page 2 my beloved sister Mar�am Muha��ad San� I appreciate 4 ol d luv and cares u show .Allah yabar zumunci (ameen).

****** Yana daukan wayar tareda sallama yasaka ta a kunnenshi ta amsa sallamar suka gaisa cikin mutinta junansu sannan tayi �unkurin fada masa sakon mahaifiyarta gareshi " am dama Ismail mommy ce tace nafada maka Indai da gaske kake katuro magabatanka Afara zancen auren mu",tsintar kansa yayi da Kasa yimata musu yace mata karki damu Indai wannan ne ba matsala gobe inna fita zanyiwa Alhajinmu magana sukayi sallama yako�a ya kwanta.

** ba�an sun dawo daga islamiyya ta tarar da Yayan a parlour yana kallon news tasameshi bayan sun gaisa basu dau lokaciba yacemata zaije ya kwanta ganin ba fuska bata cemasa komai ba,saida safe.
Allah yatashemu lafia,ameen.

****** washegari bayan duk sun shirya da niyyar yau a cikin gari zasu kwana,taje ta sameshi a daki yagama shiryawa yana feshe turare a jikinsa,Yaya kazo ka kaimu Unguwa kaji yacemata kuje driver ya kaiku da akwai inda zanje kafa tafara bubbugawa da alamun zatayi Kuka,tsawar daya dakamata ne yasata nitsuwa tareda da kallon anya wannan yayantane kuwa " leave my room now" .juyawa tayi sai dakinta tafada kan gado tarusa wani uban ihu tafara kuka .
Ita kuwa Maryam ganin shirun yayi yawa yasata tayo dakin Tana kiran sunan ta Ai da gudu ta karasa ciki Tana tambayar meya faru sisto fadamin mana umma ce koh Yayan ba lafia dakyar tasamu tafada mata meyafaru inda tabata shawarar tabari inya sakko ko zuwa darene sai taje har daki tabashi hakurin.

Bayan yafita bai zame ko ina ba sai gdn su yana zuwa suka hadu da Jambros a parlourn tareda Alhajin nasu,yawwa YAYA yanzu dan uwanka yaxomin da labarin yanaso Ayi zancen aurensu shida Maryam,dafatan kaima sun shirya da ita Rufaidan kaga sai a hada lokaci guda.

Gabansa ne yayi mumunar faduwa jin Alhajin nasu ya ambaci wannan matar,,dakai FHA nake ina sauraronka dama Alhaji akwai wata Zainab wadda muka daidaita da ita da niyya ta itakuma Rufaida takarasaa degree dinta.

Tabbb!!! Amma baka da hankali kasan mekace kuwa,ohhh Ni zamanin nan 😞dakyar da sidin goshi ya yarda amma da sharadin Indai ita Rufaida ta yarda a auro wata.
Chapter 6 · 0% Book details