Sashe 23
Rufaidah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mata ta share da bayan hannunta, gabanta ya�o ya tsaya a sanyaye zai sake magana tasa hannu ta rufe �asa baki. Cike da tsantsar so tace Babyna did I tell you how much I love you? Yayi murmushi mai cike da takaici saboda Fadila ta masa wulakanci sosai. Yace No. Ta rungume shi ta baya to muje muyi wanka sa� na fada maka. Huzaifa da Fadila gaba dayansu sunyi matukar mama��� abinda Aishatu ta�i. Tamkar Fadila bata dakin ta dawo gabansa ta tsaya tana masa shagwaba ni ka zuge min zip din na kasa. Bai iya cewa komai ba ya zuge zip din doguwar rigar atamfar dake jikinta. Ta ja hannunsa suka shige toilet suka bar Fadila a tsaya baki bude. Bata san lokacin da tace kan uba anya yarinyar nan mutum ce kuwa? Ta fita ta bugu musu kofa da karfi. Bata kula da lokaci ba ta kira wasila tana kuka, dama itama jiran feedback take bata kwanta ba..tsam ta tashi daga daki ta koma wani dakin ta amsa wayar. Ni na rasa yadda zanyi da yarinyar nan. Ta bata labarin duk yadda suka yi Wasila tace kwantar da hankakinki next week Fahad zai zo. Su Aishatu kuwa suna jin ta fita suka fito. Huzaifa zaiyi magana ta ce kada kace komai. I trust you. Kissing dinta yayi tare da godiya ga Allah. RASHIN GODIYA ✂ 46 Fadila ta aikawa Fahad text tana son su hadu ranar litinin da safe a kofar makarantar su Aliya. kamar yadda ta sani wannan litinin Huzaifa yana da call wato aikin kwana a asibiti. Da wuri ta tashi ta shirya Aliya harda yi mata girki ita da duk ranar girkinta sai dai ta bata biscuit da lemo. Ta shiga dakin Aishatu ga yarki zata tafi school tace bata ga Maama ba. Aishatu ta gyarawa Aliyu kwanciya ta dauko homework din Aliya ta saka mata a jaka. Sai kun dawo Aliya Allah Ya bada saa. Fadila tace amin maaman yara. Lokacin sati uku kenan da faruwar rikicin da ya jawowa Fadila saki na biyu. Tun lokacin take neman shiri da Aishatu. Tana dai kokari su zauna lafiyan amma ta gagara sake mata. Mutum kamar Fadila ba haka kawai ake sakewa dashi ba. Kamar maciji take mai jiran sara da ya sami dama. Aliya na fita daga motar ta fara neman numbar Fahad zata kira shi. Seat din gaba taji an bude sai ta ga mutum ya zauna a gefenta. Bude baki tayi zata yi ihu yace shut up and drive. Kamar tasan muryar amma bata tantance ba jiki na bari tace tare muke da mijina. Yayi yar dariya irin wadda ta taba ji a waya. Sai yanzu ta gane shi...Fahad? Yace eh. Bata sake magana ba ta rinka bin hanyar da ya nuna mata sai da suka je gate din central hotel yace ta shiga. Jikinta ya danyi sanyi kana hauka ne? Hotel ne fa sai wani ya gan mu. Fahad ya bata rai sosai idan kin fasa ne shikenan. Aikin banza kai, ki neme ni sannan ki nuna tsoro. Ai na zata mijin naki dan gwal ne zaki iya komai dominsa. A harzuke tace kada ka gaya min magana mana. Mijina yafi karfin ka zage shi. Fahad yace eyye kaga mai miji...yana magana yana tafa hannu. Fadila a tsorace take da shi tace muje amma kayi sauri kada ya koma gida bana nan. Har dakin da yayi masauki ya kaita duk da ta san hakan bai dace ba amma tana ji a ranta babu abinda bazata yi ba akan raba Huzaifa da Aishatu. Mijinta ne ita kada�. Sun hada plan din duk �adda zasu bullowa la�arin yace to sai naji daga gareki. Fadila tace shikenan. Tana fita ya koma kan gadonsa ya zauna. Yahanasu ya kira a waya tace ya aikin kayi breakfast kuwa? Ya gyara kwanciya banyi ba na dan soma abinda ya kawo ni ne. Tace to Al�ah Ya dubi niyya my dear. Yace amin Yaha....yana jin ihunta tana cewa Allah bana so, wane irin Yaha kamar a �auye. To ba yar kau�en bace ya amsa yana dariya. Huzaifa daga wurin aiki gidan Umma ya wuce. Yaya kubra tace to meye kuma kayi mana sammako yau kamar wani gwauro? Yayi murmushi yau a waliyinki nazo. Ta jefa mishi dankali Umma kinga autanki zai min rashin kunya �o? Umma tace rashin kunya ko gaskiya kaga shigo daga ciki autan umma muyi magana. Yaya kubra ta tsaya daga jikin kofa tana jin bayanin Huzaifa akan �adda suka yi da mijinta. Yayi alqawarin raba musu gida da mahaifiyarsa tunda ya tabbatar zaman tare ne yasa Hajiyar ta koyi sa wa iyalinsa ido. Gobe �asu je Rano tare ya biya sadaki. Yaya kubra ta ce duk yaushe aka gama wannan shawarar ina cikin gidan nan. Nifa ba cewa nayi ya rabu da Haj ba. Kawai abinda take yi ne bana so. Umma tace ya rage naku ni dai wannan zaman naki ya isheni a koma ayi bautar aure. Daga nan Huzaifa ya wuce gida. Sai da ya shiga dakin Aish suka gaisa sannan ya tafi dakinsa. Fadila yanzu kwantar da kai take sosai shi dai yana zaune da ita ne kawai saboda Allah amma duk ta fice masa a rai. Aishatu kuwa gyaran jiki suke zuwa da Anti Sauda sauki ya samu. Anti Sauda har tsokanarta take wai tana sheki saboda zata fara amarci. Tace kai antiña ni kunya nake ji. Ta kai mata duka a baya kyaji da gulmarki bayan nasan kwana bakwai dinnan sunyi miki nisa. Aishatu ta sake dariya. Wayarta ce tayi ringing gashi duk jikinta an shafe shi da wani abu an rufeta da bargo ga garwashi da turaren wuta mai matukar kamshi. Ta kalli wayar da kalar tausayi alamun anti sauda ta saka mata. Anti Sauda tace kaji min yarinya fa. Tun dazu yake bugowa ku gaisa kamar na sato ki. Aishatu tace na karshe ne Anti daga wannan zan fada masa yayi hakuri sai an goge min yadda zan dauka da kaina. Anti Sauda da mai gyaran jikin suna ta dariya. Daga lokacin da suka fara Huzaifa ya kira sau hudu duk Antin ke saka mata wayar a kunne. Wannan karon tana dora mata tace baby kaji Anti Sauda ko.....muryarta da yaji tayi masa dadi. Yaushe rabon da yaji wannan muryar mai taba masa zuciya. Shiru taji tace baby ko baka ji na ne. Yace ina jinki Aisha....Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun. Da karfi tace FAHAD? Anti Sauda ta yar da wayar ba shiri. RASHIN GODIYA ✂ 45 Kasa bacci Huzaifa yayi a daren saboda bacin rai. Hakika ba don Allah Ya taimake shi Aishatu mace ce mai fahimta da yin uzuri ba bai san da yadda zai fitar da kansa ba. Zama da Fadila bala'i ne, sai yanzu ma ya kara tabbatar da hakan. In Allah Ya yarda sai ya toshe duk wata kofa da zata sake kawo musu matsala. Yana dawowa daga sallar asuba ya tafi dakinta. kwance tace hankali kwance tana bacci. Lallai bata da kunya duk abinda tayi har ta iya bacci haka. Takardar da ya rubuto tun kafin ya shigo gida ya ajiye a karkashin wayarta ya fita. sai yanzu yaji wani dadi kamar an sauke masa katon dutse. Yaransa yasan ko bashi da rai Aishatu zata rike su amana. Ya koma daki suka koma bacci bayan sunyi karatu don bacci bai ishesu ba a gidan. Wurin karfe takwas suka ji wani gigitaccen kuka. Aishatu ta farka a tsorace baby waye wannan? Kaji wani irin ihu kuwa. shi kuwa ko yunkurin tashi baiyi ba tunda yasan mai kukan da dalilin kukan. Aishatu ta dan jijjiga shi don Allah ka tashi ka duba. Yayi murmushi na duba wato idan dodo ne ya cinyeni ni kadai ko? To anki wayon. Tace to ni bari naje ya cinyeni tunda haka kake so. Ya janyo hannunta dawo ki kwanta kinji Aish. Fadila ce take yi. Ai tuni ta mike shine kake kwance bayan kasan mai yi. Idan wani abin ne ya faru a gidan fa. Huzaifa ya juya baya ya gyara kwanciya sai ya cinyeta ita kadai. Ganin da gaske bazai fita ba sai ta tashi ta tafi dakin fadilan. Kuka take sosai tana fizge fizge. Aishatu dai sai taki karasawa ciki don tsoro ta bata. Fadila me ya sameki? Da katon zaginta ta juyo zata fara sai ta tuna yadda suka yi da uwarta wasila. Ta rarrafa ta rike kafar Aishatu ki min rai Aishatu kingani. Abban Aliya ya sakeni, na biyu kenan. Duk abinda nayi jiya sharri ne da karya. Ni kadai nayi bincike na batare da ya sani ba. Daga yau na dena na hakura na tabbatar aurenku babu mai iya raba shi. Wannan masifaffen kishi ta fada tana dafe kirji ki tayani addua Allah Ya yaye min. Dama tsoro nake kada ki rabani da mijina to gashi da kaina nake sawa ya nisance ni saboda halaye na. Kayya na cuci kaina na biyewa kishin banza. Tausayi sosai ta bawa Aishatu tace nawa yayi miki. Fadila a ranta tace ji kamar ba ita ta zuga shi ba. Daya ne ta fada tana ta matsar kwalla. Ki rufa min asiri yadda Allah Ya rufa miki. Tare suka juya zasu dakinsa suka ganshi a tsaye. Yace Aish zo ki wuce daki. Kin zauna tana fada miki karya da gaskiya kina ji. Zuwa yanzu ya kamata kisan halin Fadila. Tafiyarta ita ce alkhairi garemu. Fadila ta fara bashi hakuri kawai sai ta fadi kasa. Huzaifa yayi dariya yana kallonta. Yace kin gani ko Aish, idan bata yi abin kallo ba bata jindadi. Idan kin farfado ki kira mutanen gidanku suzo daukarki don wallahi bazaki min idda a nan ba. Zan baki ci da sha duk inda zaki. Aishatu ta sake kallon Fadila wadda taki motsi duk da yadda kanta ya soma kaikayi kamar mai kwarkwata. Tace babyna kayi mata afuwa for the last time. Nasan dacin saki da rayuwar da ke biyo bayansa ga wanda ya zalumci dan uwansa. Ta dan shafa mata ruwa a fuska sai gashi ta farfado huzaifa yace ai na zata kin tafi kenan. Fadila cikin kuka tace ku taimake ni ko albarkacin cikin dake jikina. Duk sunyi mamaki sai dai Huzaifa yasan bazata masa karyar ciki ba. Don tasan zai iya dubawa