← Book details Rufaidah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 29

Sashe 26

Rufaidah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a gate din hotel din,wasu kuma a kofar dakin. Jikin Huzaifa ya soma rawa a sanyaye yace Fahad ka nemi matata ne? Fahad yace ka kwantar da hankalinka ko a da ni ba mazinaci bane. Magana tazo muyi akan yadda zamu bata tsakaninka da matarka. Ta yaya nasan gidan da Aisha take jiya? Huzaifa gumi ne ya jika shi lokaci guda. Wane irin tashin hankali ne wannan. Ina Fadila zata kai mugun halinta. Bata laakari da kullum tayi sai asirinta ya tonu. Wannan yafi komai kure shi tunda har zata iya kebewa a dakin hotel da mutumin da ba muharraminta ba. Ya ce da Fahad to meye next plan dinku. Fahad ya dauko waya a gabansa ya kira Fadila yasa a speaker. Tana dauka tace ,yauwa tun dazu nake jiran wayarka, ya fita itan ma dreban gidan uwarsa yazo ya dauketa. Huzaifa ya rike baki wai uwarsa. Fahad yace to yanzu ya zaayi? Ta cigaba na gano gyaran jiki take zuwa. Na riga na yanki key din dakin nata. Fahad da Huzaifa suka hada ido. Jin anyi shiru yace Fahad kana ji na? Eh ina jinki yanzu ya zaayi na shiga dakin yadda wannan mijin naku zai ganni. Fadila tayi dariya kada ka damu. Kazo bayan laasar sai na bude maka dakin. Zan tabbatar yau ni na daukota ba shi ba. Daga nan sai ka buya kada ka kuskura ka fito sai kaji muryarsa. Idan da hali ka rungumeta ma komai ihunta. Tana dariya fahad ya biye mata suka yi tare. Huzaifa kirjinsa ya dafe zuciyarsa kamar ana hura wuta. Fadila ta fi karfinsa yanzu mace me irin halinta zaman aure ba nata bane sai dai idan hali ya dace da na mijin. Huzaifa yace Fahad meyasa ka zabi ka fada min gaskiya? Fahad yace baka ji lokacin da na ce maka nayi nadama ba? Da ban amince ba Fadila zata iya neman wani. Dukkansu suka ajiye kishinsu a gefe suka tsara plan din yadda zasu bullowa Fadila. Ita wadda ake yi dominta bata san me sukeyi ba. Tana can cike da farinciki tana karasa gyara jikinta domin neman yardar Allah da ta mijinta. RASHIN GODIYA ✂ 51 Huzaifa ko aiki ya kasa zuwa saboda yanayin da yake ciki. Duk cikin 'yan uwansa babu wadda zai iya fadawa tayi shiru ba tare da ta sanar da umma ba. Shi kuwa yafi son sai ya kashe gobarar ma sannan za ta san abinda yake faruwa. irin wannan sirrin kuwa ba abu bane da zai iya fadawa aboki. Ciki ba don abinci kawai aka yi shi ba, wani idan ya sani ma dariya zai masa ace ya kasa rike mace. Daga karshe dai office ya wuce amma ya sanar yau bazai iya ganin marasa lafiya ba. Maaikatan asibitin sunyi mamaki domin hakan ba halinsa bane. Bai dade da zama ba sai ga wayar Fadila. Gabansa har faduwa yayi ya dauka ya kuma yi kokarin nuna mata komai lafiya yake. Sai da ta gama yi masa hira tace Abban Aliya kaga wasila ce tazo nan aka bugo waya yayarta ta karye a kafa. Na fita rakata muka ga tayarta daya tayi paci. Naga hankalinta duk ya tashi shine nake son in kaita. Hmmm kawai ya ce, yanzu ba don yasan gaskiya ba haka zata raina masa hankali. A fili kuwa cewa yayi mal Habu ya cire ya daura mata spare mana. Kukan wasilar yaji fadila ni na tafi kawai don bansan halin da take ciki ba. Fadila tace kaji ta ko duk a rude take. Huzaifa yace to ba komai ki kaita. Allah Ya kiyaye gaba. Fadila ta ajiye wayar suka tafa da Wasila. Tace kai amma fadila mijin nan naki akwai matsi sosai. Ni Kamilu bai isa na tambayeshi fita ba. Fadila ta ce uhmm nima da bana tambaya, zuwan shegiyar nan ne naga tanayi shiyasa na fara. Sake tafawa suka yi sannan ta kira Fahad tace yazo yanzu. Basu dade ba kuwa sai gashi kamar yadda ta fada masa kada yazo da mota bai zo da ita ba. Ya kira ya sanar da ita yana bakin gate. Sai ta fito ta ce Mal Habu ya duba mata baya tana jin kamar motsi, kafin ya dawo ta shige da Fahad. Wasila ta kare masa kallo tace gaskiya Fadila na kyasa. Ko kadan bata ji kunyar yana jin abinda ta fada ba. Fadila ta ce ke duk namijin duniya ai yayi miki. Fahad yana jinsu dai bai kula ba. Wasila ta sake cewa ita kuma Aishatu duk mazan da ke sonta haka suke kyawawa in dai bazaka damu ba Fahad ina son zama friend dinka. Yadda take masa kwarkwasa ya bata masa rai. Wasu matan basu san darajar da Allah Yayi musu ba. Fadila dai ta dauki key din mota ta rike mayafi a hannu. To zamu tafi zan tabbatar ni na dauko ta. Ga dakin ka shiga na hada maka da keys din falo da na daki. Yace to nagode amma kuyi sauri. Wasila dai kamar kada ta fita. Ta dade tana son Huzaifa ma amma saboda Fadila take hadiye wa. Ana yin laasar ta sake kiran Huzaifa ta sanar dashi zata koma gida amma taga wurin yayi kusa da inda Aishatu take zuwa za ta biya ta dauko ta. Yace ai yau da wuri ta gama ta tafi. Ina jin ta isa gidan ma. Amma dai nagode da kike wannan kokarin na ganin kun daidaita. Fadila dadi ya isheta dama bukatarta Aishatu ta riga Huzaifa zuwa gida. Hu�aifa �a ajiye wayar �a kalli Aishatu da ke zaune a gabansa tana sharbar hawaye. Idanunta sunyi ja sun kumbura sai ajiyar zuciya take yi. Yau bata gama gyaran jikin ba �aje ya daukota. Ya gama yi mata bayanin yadda suka yi da Fahad kenan Fadila ta kira. Kallonta kawai Huzaifa yake yi yace Aish menene abin kuka kuma? Bayan Allah SWT Ya fitar dake ba tareda anyi nasara akanki ba. Tace hakane amma me na tsarewa Fadila haka? Idan da Allah bai kaddari zamanmu ba da tuni mun rabu. Tashi ya�� ya rungumeta yana ta rarrashi ni bana son zancen rabuwa kinji ko. Duk bawan da ya dogara da Allah kuma yake gode Masa a kowane hali bazai tabe ba. Allah bazai dora mana jarabawar da tafi karfin imani�mu ba. Shiryuwar Fa�ad ai ba kokarinmu bane. Ina so ki kara inganta imaninki ki kasance mai hakuri da juriya sai kiga rahmar Allah tana bibiyarki. Aishatu ta kalli Huzaifa tana murmushi tace Alhamdulillah. Ya rike hannunta ko ke fa. Tashi mu tafi gida. RASHIN GODIYA ✂ 53 Kowa na binsu da ido �a kaita gaban mahaifiyarsa ya zaunar da ita sannan yace mata Aish bani key din dakinki. Ba musu ta dauko ta mika masa, yace guda nawa ne mukullan? Ta ce hudu ne biyu suna jakata biyu kuma suna wurinka. Huzaifa ya shiga daki ya fito da su. Ya hada ya ce da Baban ga�du ai sun cika hudu ko? Yace hudu ne zahiri. Wai ni kadai ne kaina ya kulle a wurin nan? Umma tace nima jira nake su yi min bayani. Idanun fadila kamar zasu fado kasa. Ta riga ta gama tsurewa tunda taga ya shigo da Aishatu tasan abinda zai biyo baya bazai mata kyau ba. Huzaifa ya tashi yaje ya bude dakin Aishatu sai ga Fahad ya fito. Nan fa kowa ya tashi tsaye ana kallon kallo. Umma tace auta don girman Allah me yake faruwa? Huzaifa yace su zauna yanzu zaiyi musu bayani. Suna zama yace Fahad bismillah. Nan da nan fahad ya fara bayanin abinda ya faru tun daga wayar Wasila ta farko. Kowa da abinda yake fada game da Fadila da kawarta. Aishatu kuwa sai kuka take yi. A wurin Huzaifa ya fadi wasu daga abubuwan da fadila tayi masa a baya tun kafin aurensa da Aishatu. Fadila ta soma kuka Huzaifa sharri zaka yi min ko har ka iya hada baki da tsohon mijin matarka don kawai baka so na. Baban fadila ya tashi ya hau dukanta. Fadila ke wace irin yarinya ce yanzu da ke zaa hada baki a kawo namiji dakin wata don miji ya saketa. Kuma da yake baki da tsoron Allah har ki kirawo dangin mijinki su zo kallo ko. To gashi ramin da kika gina kin fada ciki. Tana kuka tace Abba wallahi sharri ne. Tunda yarinyar nan tazo take kulla min sharri. Huzaifa kawai sai ya jefa mata hotunansu ita da Fahad a mota da hotel. Wannan karon Baban gandu ne ya kai mata duka. Kin cucemu kin cuci kanki Fadila. Umma ta ce Aishatu iyayenki sun san abinda ke faruwa...ta girgiza kai a'a Umma. Tace Allah Yayi miki albarka da kika rufa sirrin gidanki. Fahad ya tashi zai tafi suka yi masa godiya da bai biyewa son zuciya ya fada ga halaka ba. Ana ta yiwa Fadila fada tana rusa kuka wasila ta sabi jakarta zata gudu Huzaifa yace dawo nan. Ki jira mijinki zai zo daukarki. Wasila ta soma matsar kwalla tana bada hakuri. Babu wanda ya saurareta har Kamilu ya iso bai tsaya gama jin bayani ba ya ce ta tafi ya saketa saki uku. Nan kuma manya suka soma yi masa fada yayi aika aika. Shi dai murna yake yau ya sami kwarin gwiwar rabuwa da matar da ta zame masa karfen kafa. Dama iyayensa basa son auren. Haka wasilq tabi bayansa tana ta kuka har waje ana jin muryarta. Hankali ya dawo ga Fadila, Huzaifa yace Baba dama na kiraku ne don ku zama shaida saboda kada magana ta fito ta karyata. Ku gafarceni amma bazan iya sake zama da Fadila ba. Fadila ta taso tana ihu don Allah kada ka karasa sakina Huzaifa. Igiya daya ce ta rage min. Wayyo na shiga uku Aishatu kice kin yafe kada ya karasa sakina. Huzaifa ya dauko takarda ta tashi ta fizge wallahi baka isa ka sakeni ba. Kayi kadan Huzaifa dama nasan duk bakwa sona ta nuna su Yaya Zainab. Wallahi zama daram a gidan nan babu inda zani. Baban gandu ya kwada mata wani mari ba shiri ta nutsu. Yace bazan hanaka sakinta ba Huzaifa. Fadila kin zalunci kanki don Ubangijinmu sark� ne mai adalci. Kin zama daga cikin mutanen da basa iya godewa Allah. Godiya ga Allah fa ba ta tsaya a cewa
Chapter 26 · 0% Book details