Sashe 15
Rufaidah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a ta tafi. Ga dukkan alamu ma akwai wani abu mai tsami a dust bin din falon don ana shigowa zai daki hancin mutum.. kusa da ita ya zauna kinci abinci kuwa? Tace cikin tsiwa bana son gulma don nasan cin nawa ba damunka zaiyi ba. Yaji zafin abinda ta fada sai ya share. Ki tashi ki zo falo an kawo abinci daga gidan umma. Idan kin gama kizo dakina ina son magana dake. Bai jira amsarta ba ya tashi. Ya rasa wannan tura baki na Aishatu tun asuba da ta tashi. Tayi wanka babu kayan sawa saboda nata suna kulle a side dinta. Ya zauna a kusa da ita a kan gado sai yaga ta dan matsa. Yayi dan murmushi A haka zamuyi kawancen kina zumbura min baki Aish, Ko dai nayi laifi ne ban sani ba? Eh .....subhanallah me nayi miki. Ta sake turo baki, hakan yana bashi shaawa game da ita. Tace kana kyamata ko? Tambayar yaji ta wani iri yace me kika gani? Sai ta dukar da kanta saboda ya kafe ta da ido...gani nayi ka kwanta a kasa. Sai tayi tunanin kada ya fassarata kuma da wata manufa. Uhmm ina nufin da ka barni a kasan ko...ba komai dai abar zancen. Hancinta ya ja har ta danyi kara. Ki dena irin wannan tunanin Aish. Ko har kin manta maganarmu ta jiya? naga duk kin ruda kanki ,tambayar ma kin kasa yinta sosai. Kina son sanin ko ina kyamarki ne ko amma kina tsoron kada nace kina son kwana kusa da mijinki. Murmushi ne ya kufce mata ta kasa dago kanta. Bana son takura miki shiyasa amma da ina kyamarki ai bazan aureki ba. Amma yau haka zamu kwana ya nuna mata yatsunsa guda biyu a hade. Ba shiri ta tashi ni ba nufina kenan ba. Ni kuma nufina kenan my dear best friend. Amma seriously ya kike jin jikinki yanzu? Babu kurajen sai kaikayi wani lokacin. Yace discharge fa? Akwai amma bai kai na da ba. To Alhamdulillah sauki ya fara samuwa. Irin wannan infection din naci gare shi ki cigaba da shan magani. Kuma tsaftar nan kada ki sassauta mata. Anjima zan siyo miki wani ma. Godiya sosai tayi masa yana dariya yace kinga fa bana son godiya malama kawai ki kawo kudin consultation. An fada miki ana ganin Dr kyauta ne? Aishatu tace to da me zan biya Dr Rano? Bugo kofar dakinsa kamar zaa balleta yasa ya fasa magana. Fadila ce ta shigo da alama har yanzu batayi wanka ba. Ganinsu da tayi zaune kusa da juna yasa ta harari tace Aishatu to jarababbu da sanyin safiyar ma. Huzaifa ya daka mata tsawa kina hauka ne zaki shigo min ba sallama..kuma ki kiyaye abinda ke fita bakinki kada ranki ya baci. Samu wuri ki zauna mana kin tsaya min a ka. Aishatu tace ina kwana? Fadila ta yatsina fuska a hankali tace yana wurin uwarki. Sarai tasan sunji. Huzaifa ya yunkura zai tashi cikin fushi Aishatu ta rike masa hannu. Baby dan karasa shafa min man a bayana mana. Dama wata jallabiyarsa ta saka Fadila tana ganin ya mika hannu ta tashi wannan karuwancin ba dai a gabana ba. Dama kiran na wulakanci ne? Ya ce ga wanda ya wulakanta kansa ba. Bayan yan mintuna dakin yayi shiru Huzaifa yayi musu nasihar zaman lafiya sannan yace idan Aishatu ta gama kwana ukunta a matsayinta na bazawara zasu raba kwana two-two days. Sannan ya gargadi Fadila akan rufe kofar side din aishatu. Zansa a saka sabun handle yanzu amma Allah kika sake a gidanku zaki kwana. Itama tayi dana sanin yin hakan don gashi dakin da take jimawa bata gyara ba ta zage ta gyara wata daban ta kwana a kai. RASHIN GODIYA ✂ 30 Huzaifa na rufe kofar gaban Aishatu ya fadi. Wani tsoro ya saukar mata ta kasa karasa shiga dakin. Irin kallon da Huzaifa ke yi mata yasa taji kunyar kayan jikinta ta mika hannu zata karbi mayafinta da ta bashi. Boye shi yayi a bayansa tace don Allah ka bani...kwaikwayonta yayi yace don Allah naki. A hankali ya matso kusa da ita... har suna jin sautin numfashin juna yace ba don ni kika yi wannan kwalliyar ba. Tayi dan murmushi tare da sunkuyar da kanta kasa. Hannunta ya rike ya ja ta har bakin gado sannan ya zaunar da ita. Ya zauna a daidai saitin kafafunta daga kasa. Ya kallonta yace Aish you always amaze me. Nayi mamakin yadda mijinki na fari ya kasa fahimtar ki har ya rabu dake. Maganar Huzaifa tasa hawaye ya cika mata ido....muryarta tana rawa ta soma magana. Shekarata 17 aka yi min aure. Kuma kamar yadda na fada maka Fahad mugun mutum ne. Bazaka fahimce shi ba sai zama ya hadaku. Sau tari mutum baya gane ni'imar da Allah Yayi masa sai ya rasa ta. Duk musulmin kwarai yana da kyau yayi godiya ga Allah a halin samu ko rashi domin duk abinda Ya bamu yana tafe da alkhairi. Rashin godiya ga Allah akan kyautarSa garemu yana jawo mana asara mai yawa. Kaga dai yadda Fadila ta gigice akan auren nan wanda ita ta jawowa kanta. Shima Fahad har yau bai fidda ran sake aurena ba. Kaga a da basu nuna damuwarsu yadda ya kamata ba sai yanzu da suka ga zasu rasa abinda da basa bashi mahimmanci. A shekaru ashirin da hudu nayi aure uku, ina fata ka zama mijina na karshe...ta dan numfasa, nasan cewa ours is not a love marriage amma ina fata zaka rikeni amana ka zama mijina na karshe. Maganganun Aishatu sun shige shi sosai amma kalmarta ta karshe ta dan daga masa hankali har yayi saurin rufe mata baki da hannunsa. Murmushi ta sake yi masa....Dr nasan kana matukar son Fadila kuma kana son ku zauna lafiya da ita. Nima ina so maka hakan shiyasa zan taimaka maka har ta gane rashin dacewar abinda take yi. Amma ina rokonka alfarma daya....ya kura mata ido yana jiran yaji abinda zata ce. Nasan ina tare da ciwo don Allah kada ka bari kowa ya sani. Sirrina ne wanda bana son ya zama sanadin da za'ayi min gori watarana. I just want a home to call my own. Zuciyar Huzaifa ba karamin karyewa tayi ba. Sai yau ya kara yadda Aishatu mace ce mai hankalin. Hawayen da yaga tana shirin yi ne yasa ya janyota jikinsa ya rungume. Sun jima a haka yana shafar gashin kanta wanda yasha gyara. Kanta a kasa ta fara kokarin tashi ya ce tsaya mana ai nima ina da abin fada. daga yau you are my best friend, my sister and.......shiru tana jiran taji me zai ce har ta gaji ta dago kanta. Kissing dinta yayi a baki kafin yace my wife yana mata murmushi. Har ya tashi ya shiga wanka bata iya tashi ba saboda yanayin da ta sami kanta. Anya Aish ko dai son Dr H.M Rano kike yi? wasu riga da wando na bacci ya bata ta dauka ta shiga toilet. Wanka tayi da alwala ta fito suka yi nafila. Ya fita samo plate da zai zuba musu naman da Saddiqa ta gasa masa. Yana dawowa ya tarar ta jingina da gado tana bacci. Tausayinta yaji ya kara kamashi ya dauketa a dora ta akan gado. Sai da ya gama abinda yake yi ya kashe fitila ya kwanta shima. Fadila dake zaune a kofar dakin tun bayan ya fita dauko plate tana ganin duhu ta karkashin kofar taji kamar zuciyarta zata buga saboda kishi. Tana kuka tace na shiga uku. Nan ta zauna tana ta rusa kukanta har asuba babu wanda yasan ta�a yi. RASHIN GODIYA ✂ 32 Huzaifa ya kira mai gyaran kofa kamar yadda ya fada an gyarawa Aishatu kofarta. Bangarenta akwai kitchen, parlour da dakuna biyu. Daya an saka mata gado mai tsada irin na zamani har kuka sai da tayi. Iyayenta suna iya kokarinsu wurin kyautata mata. Daya dakin kuwa kayan turare ne da �adadden kafet da pillows. Ga shi akwai wadatar iska a wurin. Sai ta mayar dashi wurin shan iska kawai. Falonta ma ya hadu ga kitchen wanda Huzaifa ya wadata store din cikinsa da dukkan kayan abinci. Ya kuma sanar dasu kowa zatayi nata abincin ne wadda take da girki ranar ta hada dashi. Hakan yayiwa Aishatu dadi don tana gudun abinda zai hadata da Fadila. A kwanaki ukun da Aishatu tayi sun kara sabawa da Huzaifa. Banda masallaci babu inda yake zuwa. Idan ya dawo kuwa hira suke yi da bawa juna labarai akan rayuwarsu. Lokacin bacci kuwa a kasa yake kwanciyarsa tana daga kan gado. Haka zasu cigaba da �ira har suyi bacci. Abinci kuwa kullum zaa kawo safe ,rana da dare daga gidan umma. Aishatu tace wannan wahala ce zata rinka dafawa da kanta. Yaya kubra da ta ji sakonta ta kira ta a waya...ke dan kwana ukun nan ai lokaci na baki ki kara sace zuciyar mijinki. Duk abinda nake dafawa irin wanda yake so ne so kada ki damu. Kullum aka kawo sai Aishatu ta buga waya tayi godiya. Ita kuwa Fadila an ga bulus itama dena girkin tayi. Wani lokacin ma kafin Aishatu ta debarwa Huzaifa ita zata fara diba duk ta tsince naman ta bar musu kada. Ana gobe Aishatu zata fita girki Huzaifa yana aiki akan computer a dakinta tana zaune daga gefensa tace yaushe zamu je gidan Umma ne da Rano? Wani murmushi yayi wanda ya nuna yaji dadin abinda ta fada sosai. Aish harda Rano zaki je? Tace eh mana. Ba garinku bane kuma akwai yan uwanka a can. Ni kazo ka fada min su waye closest to you ma a can tun wuri. yace mai yasa? Murmushi tayi tace sirri ne. Lumshe idanunsa yayi cike da nishadi. Yan kwanakin da suka yi tare damuwarsa da yawa ta ragu sosai. Ya dan jima a haka yana jindadin kamshin falon nata sannan yace ki bari sai kin sake karbar girki. Ta bata fuska har gidan Umman? Kinga yanzu aiki nake dan dubawa kuma gobe ba ke ce da girki ba. Kema bazaki so ranar girkinki na fita da Fadila ba. Aishatu tayi dariya bazan hana ba amma ka tabbatar idan kuka dawo sai dai ka koma dakinta don ban san abinda zan maka ba. Dariya sosai