Sashe 22
Rufaidah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
akayi Fadila sai tayi ta shagube idan taga Aishatu. Abin ya rinka damunta sosai, dan sakin jikin da take tare da Huzaifa ya fara ja baya. Ana haka wata jumaa Huzaifa ya sanar dasu zasu je Rano gaba dayansu. Fadila har tace bazata ba sai ta tuno maganar wasila tace zata bisu. Ranar asabar kafin karfe tara sun kama hanya. A mota suna ta hira Aishatu da Fadila kamar wasu yan uwa. Hirar ma Fadila ke kawo ta. Gidan kowa murna anga iyalin Huzaifa. Fadila dai ta kasa sakin jiki sosai dasu. Ita kuwa Aishatu da yaran kamar wadanda suka saba. A falon wan baban Huzaifa duk yawancin matan yan uwa da 'ya'yansu suka taru ana ta tsokanar juna. Wata abokiyar wasan Huzaifa ta dubi Aishatu...anti amarya ina fata mun kusa zuwa suna ko. Murmushi tayi cike da kunya don akwai manya a wurin Huzaifa yace kin tanadi shanun suna ko, baki ji an hana yanka rago ba sai shanu. Duk aka yi dariya Fadila tace rabu dasu kanwata ke ina kika ga lafiyar yin cikin yanzu. Duk kuyi ku gama sai nan gaba. Aishatu da Huzaifa suka yi saurin kallon Fadila ita kuwa ta basar. Matan wurin sai suka mayar da maganar wasa. Har suka dawo gida Aishatu bata da nutsuwa. Ba jimawa da faruwar haka kuma Nurain yazo gidan kanin Aishatu na biyu. Tayi murnar ganinsa sosai, da yake yana da saukin kai har kasa ya gaishe da Fadila. Da taimakon Habu maigadi ya kinkinmo kwandon tumatir masu kyau ya shigo dashi main falo. yace baba ne ya dawo daga getso jiya gonarsa tayi albarka. Aishatu ta kira babanta tayi masa godiya. Da ta gama tana durkushe da ledoji a hannunta tana rabon tumatir din har da yan uwan Huzaifa saboda manya ne sosai masu kyau. Tace Baba yasan ina son tumatir shiyasa yayi min wannan babbar kyautar. Fadila ta yatsina fuska sai ta ce ai da yake ance ana son irinku su rinka shan tumatir sosai yana da sinadarin kariya daga kamuwa da cancer. Aishatu da Nurain suka kalleta cikin rashin fahimta. Aishatu tace ban fahimci maganarki ba. Fadila ta dafa mata kafada ba wani abu nake nufi ba. Kinsan shi tumatir yana da sirruka masu tarin yawa. Zai miki amfani sosai lokacin da kika warke. Ta tashi ta shige daki. Nurain yace anya Yaya matar nan kalau take kuwa. Ni duk zancen nata na kasa ganewa. Aishatu bata ma jinsa sosai hankalinta ya tafi ga tunanin da take. Wai yan kwanakin nan meye yake damun Fadila take mata irin maganganun nan. Banda iyayenta da Anti Sauda, Huzaifa ne kadai yasan lalurarta. Gabanta ya fadi....Allah Yasa ba fadawa Fadila yayi ba. Sai tayi saurin kwabar kanta. Dr Rano is a good man bazai taba tozarta rayuwarki ba. RASHIN GODIYA ✂ 43 Aishatu ta tambayi Huzaifa zuwa gidan Anti Sauda ta yini ya amince. Tace nagode Allah Ya saka da alkairi. Cikin mamaki ya kalleta don na baki izinin fita kawai kike min wannan godiyar? Ta na bude masa maballan rigarsa tace ai ya wuce kawai. Ya rike hannuwanta biyu yanzu idan nace bazaki ba zaki hanu? Sosai ma kuwa. Haram ne mace ta fita ba tare da izinin mijinta ba. Huzaifa ya rungume ta sosai na sani Aish amma banyi tsammanin akwai macen da fitarta ta dogara da izinin mijinta ba. Allah na gode maKa da Ka bani Aishatu a matsayin mata. A hankali itama tace Alhamdulillah. Yace kinsan kin kusa dena shan magani ko. Idan kika shanye dose din da na siyo jiya zamuje ayi miki pap smear. Yana dakina idan kin shigo anjima zan baki. Ya daga gira... Hopefully zuwa time din kin gama warkewa sai ki zama amaryar gaske. Murmushi suka yiwa juna Ya saita bakinsa a kunnenta did I tell you how much I love you? Tana dariya tace noooo. Wani irin kallo yake mata tana ja da baya yace zo na fada miki....suka ji an bude kofar dakin. Fadila ta yi saurin ja da baya kuyi hakuri wallahi ban san kuna ciki ba. Huzaifa ya daka mata tsawa wane irin iskanci ne wannan Fadila. Ta dan nuna alamun rikicewa to ai bansan ka dawo ba ne. Kuma naga nan dakinta ne. Yace shi dakin nata bazaki iya yin sallama ba. Fadila tana bashi hakuri Aishatu na bashi. Yayi tsaki ya cewa Aishatu idan kun gama ki sameni a daki. Kuma kiyi sauri. Har ya rufo kofar Aishatu tana murmushi....tana son mijinta fiye da tunaninta. Ta dubi Fadila da ta tsaya jikin kofa ki zauna mana ko mu koma falo ne. Fadila ta sunkuyar da kai kasa sai ga hawaye yana zuba. Aishatu na gani ta dawo kusa da ita. Subhanallah me ya faru? Fadila ta shaki hanci nasan Huzaifa ba karamin fushi yake dani ba akan abubuwan da nayi masa a baya shiyasa baya min uzuri yanzu. Haba ki dena kuka tunda mune a karkashinsa hakuri zaki sake bashi. Fadila ta goge ido to nagode sosai Aishatu Allah Ya barmu tare. Dama jiya ne da ya dawo lokacin kin kwanta ya bani wadannan maganin na kawo miki sai bacci ya dauke ni. Zuciyar Aishatu sai harbawa take da sauri da sauri don bakincikin da ke cin ranta. Fadila tana kallon yanayin Aishatu tace ga maganin ki taimake ni kisha yanzu kuma don Allah ki rufa min asiri kice tun a jiya na baki. Kinsan lalurar shan magani kullum babu dadi. Amma yace daga wannan kin gama ai. Shiru Aishatu bakin magana. Fadila tayi alamun tausayi da fuskarta baki ga yadda ya damu da lalurar nan taki ba. Nima duk na damu bayan ya fada min. Ta tashi tsaye bari naje daki...af! Ai kuwa ina da kawa mai gyaran jiki idan kin warke sai muje. Tana fita Aishatu ta fashe da kuka ita kuwa Fadila ta kwashe da dariya. Kadan kika soma gani yarinya. Huzaifa har ya gaji da jiran Aishatu yace ko dai Fadila ta ja ta da zance ko kuma bacci ya dauke ta. Yayi ta kiran wayarta a kashe. Yaje dakin kuma tana sallah. Haka ya zauna yana jiran ta idar har kusan minti talatin taki idarwa. Ta sallame raka'a ta takwas a kirgensa yayi saurin tsayawa gabanta. Muryarta har rawa take ta daga hannuwa sama zata yi kabbara ya rike su. Haba Aish tun dazu nake jiranki. Ki duba time har daya saura baki bani abinci ba. Kukan da take rikewa ya kwace mata. Ya rungume ta yana rarrashi me aka yi miki. Fadila ce ko? Cikin kuka tace bani da lafiya ne. Sai tauyinta ya kara kamashi kuma shine zaki yi shiru tun dazu. Ita dai kukanta take yi. Sai da tayi shiru yace Aish yaushe kika koyi karya ne. Ki fada min gaskiya me aka yi miki. Tace tausayin kaina nake ji. Huzaifa ya riketa sosai Aish this is so unlike you. Ki fada min gaskiya. Sai ya fita kawai yana kiran Fadila. Aishatu ta na riko shi yaki sauraronta. Duk da dare ne Fadila ta jima tana kasa kunne taji lokacin tashin bomb. RASHIN GODIYA ✂ 44 Kafin ya shiga dakinta Fadila ta shige cikin bargo tana baccin karya. Da karfi ya buga kofar ya bude. Ta tashi tana murza ido ita ga mai bacci me ya faru Abban Aliya? Yace ki taso ki biyoni daki yanzun nan sannan ya koma. Da bin bango ta shiga a dan tsorace ta ga Aishatu ta takure a kasa tana kuka. Tayi kwafa a ranta lallai tarkonta yayi kamu. Huzaifa sai kai kawo yake a dakin yace kinga samu wuri ki zauna zaki wani tsayawa mutane a ka. Sai da ta zauna shima ya zauna akan kujera Fadila ki fada min gaskiya me ya hadaki da Aishatu. Ai itama sai kukan Aishatu ba dai kin masa zancen maganin ba, ke da na rokeki ki rufa min asiri kada yasan yau na baki. Tuni Aishatu ta karasa yarda da cewa Huzaifa ne ya fadawa Fadila tunda gashi bata ji tsoron maimaita zancen a gabansa ba. Dan zaman da tayi daga gefensa a kasa ta tashi ta canja wuri gaba daya. Shi kuwa ya kasa gane inda su biyun suka dosa yace Fadila wane maganin. Ta kalli Aishatu ina ledar? Aishatu ta nuna mata tana kan bedside drawer. Fadila ta dauko ta durkusa a gabanshi ta mika masa. Yana gani yayi saurin tashi Fadila a ina kika dauko ledar nan? Dan kukanta ta cigaba kayi hakuri Abban Aliya nasan tun daren jiya kace na bata shine na manta sai dazu da na shiga dakinta. Dama ni nace ta sha na yau yadda bazaka gane ba. Ta kalli Aishatu nasan ba fada masa kika yi ba, ganewa yayi na kwana daya ne ko. Huzaifa yace ke ni ban fahimce ki ba. Aish yi min bayanin abinda ya faru. Fadila tace ni dai na fuskanci kamar baki so ya sanar dani ba ko? Shima ai ba son ransa bane. Shimfida na gani a kasa na tambayeshi shine yayi min bayanin infection dinki. Yace saboda karnin discharge ma shiyasa ba kya rabo da turaren wuta da air freshner. Nasan ba dadi miji ya nuna kyamar matarsa shiyasa na bashi shawarar ya daure ya kwana tare dake. Ta dan masa kallon tuhuma dont tell me baka dauki shawara ba. A lokaci Huzaifa ya tabbatar Fadila makira ce ajin farko. Yana kallo ta tashi ta rungume Aishatu kiyi hakuri kinji kanwata. Nasan da ciwo amma kamar yau ne komai zai daidaita tsakaninki da mijinki. Duk mace ai tana so� ganin danta bayan aure. Burina ki warke yadda zaki iya samun ciki ki cika gidan nan da yara. Aishatu fus�ar Huzaifa take �allo yadda �a saduda cewa ta gama dashi. Har gumi yake saboda yadda hankalinsa ya tashi. Aishatu duk fushinta a take ya sauka. Idan Huzaifa yana son tona mata asiri ko kyamarta bazai aureta ba. Kuma tun yaushe suka fara kwana wuri daya ma. Tuntuni baiji kyamar ba sai yanzu? Ta yaba da kyaun halin Huzaifa da na yan gidansu. Hakika kullin Fadi�a ne wanda ta jefa mata shakku a zuciyarta game da mijinta. Tana tunaninta taji yace Fadila abin har ya kai ga ki yi min sharri haka. Aish wallahi karya take min. Yadda yayi maganar ya kara bata tausayi sosai. Hawaye ya zubo