← Book details Rufaidah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 29

Sashe 19

Rufaidah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

babu Aishatu a ciki. Ta soma bacci yaga tasa kafa tana ture bargon. Gumi take sosai hakan ya tabbatar masa zazzabin ya sauka. Haka yayi ta kallonta har bacci ta dauke shi. RASHIN GODIYA ✂ 38 Tuni Huzaifa ya tattaro dukkan nutsuwarsa. Idanunsa sun kasa barin Aishatu. Ita kuwa ba don kada Fadila tayi saurin gano ta ba da ko kadan bazata iya jurar kallonsa ba. Ya juga ga Fadila wadda kuka yaci karfinta sosai, bari na gama na dawo zan kira Baban gandu na sanar dashi abinda yake faruwa. Ko sakin da Huzaifa yayi mata bai kada mata ciki kamar sunan Baban gandu da huzaifa ya fada ba. Wan mahaifinta ne wanda tun suna yara suke tsoronsa. Mutum ne mai tsayar da gaskiya amma yana da fada sosai. Idan laifin mutum ya tsananta ba bakon abu bane a gareshi ya dake shi. Aishatu ta dauki mayafinta ta yafa tare da bin bayan mijinta. Falon Huzaifa na waje wanda yake tarbar baki suka shiga. Bata ma san dashi ba sai ranar. Mal Habu yayi wa Baba da Mahmoud kaninta jagora ya shiga. Murnar a wurinta ta kasa buya, ta durkusa su gaisa sai kuka. Baba yayi saurin yiwa Huzaifa kallon tuhuma. Har abada bazai kara bari wani namiji ya wulakanta masa 'ya ba. Yana son abarsa sosai. Huzaifa ya wayance kinga dai Mahmoud yana kallonki kina hawaye. Baba ya dubi dan autansa kai fita waje kafin ka sami labarin kaiwa gida. Duk suka yi dariya harda ita mai kukan. Huzaifa yace Baba ai tunda aka ce kazo ta fara kwallah wai bata taba tsammanin ganinka ba a gidanta. Mal Said yayi yar dariya yau ma hanya ce ta biyo dani kuma dai kaninki dana aiko ya nace sai munzo. Huzaifa ma ya durkusa Baba ya taro shi da hannu ya bashi hannu suyi musabaha. Haba Huzaifa ai kai dana ne. Dana da ya kira shi yasa yaji dadi. Wani karamin buhun da Mahmoud ya ajiye Baba ya nuna musu. Ga tsarabarku daga Getso. G Juma ce tace ki raba har su Hajiya kwan zabi ne. Bakar Ledar kuwa na yar uwarki ne. Aishatu tace wacce Baba? Yace yayarki mana, ya dan kalli Huzaifa sunan ne ya dan kwanta min. Huzaifa da Aishatu suka yi shiru sai can tace mungode Baba. Da ganinsu yasan akwai matsala yace Aishatu kada kiyi kuskuren yi min karya menene? Naga kuna yiwa juna kallon kallo ko zuwan nawa ne bai kamata ba. Huzaifa yace Subhanallah Baba ba haka bane. Sallamar Fadila ce tasa hankalinsu ya koma ga kofar falon. Bayan fitarsu ta kira wasila a firgice tana kuka tana fada mata abinda ya faru. Wasila na shiga uku Huzaifa ya sake ni. Tace ke kwantar da hankalinki yar uwa. Kije ki bashi hakuri sosai a gaban Aishatun. Itama ki bata ni kuma ki bar sauran a hannuna zam nemo mana Fahad dinnan duk inda yake. Nayi miki alqawari ta inda ta shigo zata fita. Fadila taji dadin zancen wasila tace bari su dawo baban shegiyar ne yazo. Wasila tace to zama bai kamaki ki ba. Kije ki bada hakurin a gabansa. Ki tabbatar yasa baki Huzaifa ya mayar dake. Fadila ta karaso cikin falon lullubinta har ka. Gaban Aishatu ta fara durkusawa ki yafe ni Aisha. Nabi son zuciya �a cutar dake. Wallahi ina son mijina bazan iya rayuwa babu shi ba. Ta koma kan Huzaifa ka �afe min Abban Aliya nayi maka alqawarin ganin sauyi a halayena. Huzaifa duk kunya ta kamashi a gaban suriki. Ta tashi ta koma gaban Baba. Ka yafe min abinda nayi maka kwanaki kuma ka ta��akeni ka sa baki ya mayar dani. Saki da�a yayi min dazu. Ta kuma rushewa da kuka kamar wata zautacciya. Huzaifa ya harzuka me ya hadaki da Baba kuma? Duk suka yi shiru ya sake maimaita tambayarsa da tsawa ga Fadila a tsorace tace kwata na watsa masa kuma na gargade shi kada ya bari ayi auren ku. Huzaifa ya �o kanta zai doketa da kafa. Tashi ki fitar min daga gida. Baba �ace ashe zamana anan bai kara komai ba dana? Ina gabanka kana korar mace. Wata rana Aishatu zaka koro min kenan. Cike da kunya da takaic� Huzaifa ya labartawa baba irin cin kashin da take yiwa Aishatu. Kwarai ran baba ya sosu saidai yana tsoron Allah Ya kamashi da �aifin kin bada shawara tagari. Na yarda kaddara ce ta kawo ni gidanka a yau. Indai ina da mutumci komai kankantarsa a idonka ka mayar da ita yanzu. Huzaifa yace haba baba kafi karfin �aka ma. Aishatu taji dadin yadda ta kasance. Bata da burin zama sanadin fitar wata mace daga gidan mijinta. Baba ya yi musu nasiha sosai akan hakuri da juna. Shi da yazo ya da niyar su gaisa sai gashi sun kusa awa daya. Huzaifa ya harari Fadila bayan tafiyar baba kinci sa'a yau. Amma next time you won't be so lucky. Ta tashi a sanyaye kamar gaske...babu next time Huzaifa. Aishatu duk da taji dadi amma a tsorace take, ta tabbatar mutum baya canja hali lokaci daya. Sai dai zata yi mata uzuri da adduar su sami zaman lafiya mai dorewa. RASHIN GODIYA ✂ 37 Ita ta fara tashi da asuba jikinta yayi mata nauyi amma zazzabin da ciwon idon duk yayi sauki. Sai idanunta da suka kankance ita da kanta taji hakan. Tana juyawa ta ga Huzaifa yana bacci....kasa dauke ido tayi daga kansa ta fara tunanin me ya kawo shi gadon. A hankali ta tuna abinda ya faru a daren sai kunya ta kamata. Rufe ido tayi da hannuwanta kamar yana kallonta. Sai kuma ta cigaba da kallon fuskarsa....Huzaifa irin mutanen nan ne masu kwarjini da daukar hankali. Kyakkyawan sajensa ya zagaye habarsa zuwa saman bakinsa. Ji tayi sonsa yana karuwa a zuciyarta sosai. Ta shagala da kallonsa kamar daga sama taji yace nayi miki kyau ne cikin sanyin murya. Dama gadon ya tsage ta fada ciki haka taji don kunya. Zata gudu yayi saurin riko ta. Zama yayi suna fuskantar juna amma ta runtse idanunta yace ki bude ido mana Aish. Ta girgiza kai da sauri. Yayi murmushi to bari nima na kare miki kallo yadda kika yi min. Kokarin noke kai yaga tana yi sai ya tashi bari nayi alwala kada kisa mu makara sallah. Ko da ya dawo daga masallaci bata dakin. Ya zauna karatu ita kuwa tana kitchen. Sauce tayi da mince meat wanda yasha albasa, attaruhu, koren tattasai, da caras. Sai ta kwaba flawa da ruwa da kwai daya sai dan gishiri. Haka ta rinka soyawa da mai. Yayi fari kuma yayi kyau sai ta dama kunun gyada ta kai masa dining table. takwas ta kusa lokacin da ta gama ta same shi yana bacci. Bandaki ta shiga tayi wanka ta shirya. Har ta gama yana bacci ta dan kwanta itama don jikinta babu kwari sai. Basu tashi ba sai shadaya da rabi. Ta rinka salati wai ta makara. Yace to aikin me zaki yi? Tace to tashi kayi wanka kazo kaci abinci. Wai yaushe rabon duniya...tun Fadila na amarya ma sai ta gama bacci take dora abinci. Yace ki kawo min daki kawai I am feeling lazy. Tayi dariya ta fita main falon gidan inda ta ajiye abincin. Aliya ta gani akan kujera shi kuwa Aliyu akan dinning table din suna cin abinci. Wurin kaca kaca sun zubar da miya. Kuma abin takaicin ma ba'a plate suke ci ba. Flask din suka bude suna tsoma hannuwansu. Yau da ita ta haifesu kila sai tayi musu duka. Hawayen ma sunki zuwa. A hankali ta karasa gaban table kafin tayi magana Aliya ta sauka da gudu tana kiran mummy. Shi kuwa Aliyu akan table ya kasa sauka sai ihu yake wayyo Abba ga Anti Mayya. A tsaye yake yana ihu sauran kadan ya fado Aishatu tayi saurin daukansa. Kafin ta ajiye shi sai dukanta yake da hannuwansa. Fadila da Huzaifa kusan a tare suka fito. Yaro kuwa ihu yake kamar ya shide. Fadila ta karbe danta kaga ni ko Huzaifa ka dauko matar da zata kashe min yara. Huzaifa yayi mata tsawa shut up fadila! . Aishatu kujera kawai ta dafe don kada ta fadi. Bazata iya kwatanta bacin ranta ba. Huzaifa yace Aish me ya faru Aish? Cikin rawar murya tace na fito daukar abincinka na tarar suna ci. Walla�i banyi �usu magana ba ma. Aliyu naga yana ihu shine na sauke shi fa. Fadila ta kalli wurin da suka bata ta rinka dariya. Aliya tace Mummy ce ta bude mana tace muci. waya Huzaifa ya kira dreban Umma yace yazo gidansa yana jiransa. Duk a falon suka zauna wurin shiru banda kukan Aliyu. Kusan minti ashirin sai ga dreban ya iso. Hannun Aliyu da Aliya ya kama ya kaisu mota..ka kaisu wurin umma ka fada �ata zanzo anjima. Fadila tana ta masifa a bata yaranta ko sauraronta baiyi ba. yana shigowa ya sami takarda da biro ya zauna kan kujera ya fara rubutu Ais�atu tazo ta karbi biron. Gwiwarta a kasa tace don Allah Dr kada kayi haka. Ya dagota a hankali Aish mutuwa ce kawai zata hanani abinda nayi niya. Fadila kije na sakeki saki daya. Huzaifa me kace? Cikin fada da kuka ta�e maganar. Yace ki fice min daga gida Fadila na gaji. Ta cigaba ni zaka saka saboda wannan karuwar? Har dame ta fini? Matar da ta gagara zaman gidan miji. Kaine mijinta na uku fa. Aishatu dama ta gama kulewa sosai tace Fadila kinsan da me na fiki? Fadila ta jefa mata harara. Aishatu ta rinka tafiya a hankali tana juya jiki. Jikin da yake tada hankalin Huzaifa. Yana ganin ta fara tafiya yace a ransa abin yazo. Bata tsaya ko ina ba sai gabansa ta kashe masa ido. A hankali take magana amma yadda fadila zata ji. Da irin wannan karuwancin na fiki sai ta hura masa iska a fuska, ya lumshe ido har yaso ya manta a gaban Fadila suke ta sake hura masa a kunne. A hankali tace I love you baby...sai ta karasa rage tsazarar dake tsakaninsu ta hanyar hada bakinta da nasa. Wani shock yaji har kafarsa ya biye mata. Ita kanta ta manta a inda take. shima kamar mai rada yace I love you too Aish. Kiris ya rage zuciyar
Chapter 19 · 0% Book details