Sashe 21
Rufaidah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
can gefe. Kusan awa daya da kwanciyarsu amma babu wanda yayi bacci. Juye juye kawai yake tsakanin hannunsa na hagu da dama baccin yaki zuwa. Duk da duhun dakin ya san itama ba baccin take ba shiru kawai tayi ta kasa juyawa ma kada su fuskanci juna. Bargon da ya rufa dashi ya yaye duk a banza yayi tsaki kawai yasa hannu ya janyo Aishatu jikinsa. Ta fara kokarin zillewa yayi mata rada a kunne lets stop pretending ko Aish. This is what we want. Yayi ajiyar zuciya sweetdreams my Aish. Amma kiyi addua kinji ko. Daga haka bai sake magana ba sai kankameta da yayi ta kwanta kan kirjin shi. A haka suka yi bacci...... Daga ranar suka kara shakuwa da juna sosai. Idan ya fita aiki sun rinka waya da text kenan. Sabon jere su Yaya zainab suka yi mata wanda dole yafi na da kyau da tsari saboda tsadar kayan. Ana aikin jeren Fadila ta shigo suka gaisa karshe ma dai da ita aka karasa aikin. Su Saddiqa sunyu mamakinta sosai. Aka gama Aishatu ta koma side dinta. Bayan kwana biyu Anti Sauda tazo da su Islam suka yini a gidan. Suns�a hira sosai don Aishatu da kyar ta bari suka tafi. ita dai Anti Sauda shawar zaman lafiya da rike gaskiya ta bawa Aishatu. Kuma ki dage da yawan godiya ga Allah bisa niimar da Yayi miki sai kiga Ya kara miki. Kuma ki kasance harshenki baya rabo da azkar. Da zasu tafi kayan kwal�iya ta hadawa yaran suka tafi cike da murna. Tsakanin Fadila da Hu�aifa ma zaman ya dan daidaita tunda yaga ta dena abubuwan da take masa. Hatta bangarenta ma tana gyara shi sama sama. Main fa�on gidan kuwa Huzaifa ya kafa dokar duk mai girki ita zata gyara shi. Ana haka mai aikin Fadila ta dawo. Ba karamar murna tayi ba don dan gyaran da take yi ji take kamar ta shekara tana abu daya. RASHIN GODIYA ✂ 41 Aliya da Aliyu sun dawo gida Huzaifa ya kaisu dakin Aishatu da kansa. Aliya sai rabe rabe take a jikin bango don tafi Aliyu wayo. Huza�fa yace musu wannan itama mamanku ce kunji ko. Daga yau nan ne gidanta kada na sake jin kun kirata da wani suna mara dadi sai na zane ku. Aishatu ta�i murmushi ta mika musu hannu ku zo mu gaisa. A dan tsorace suka karasa gabanta suka mika mata han�u. Ta basu sweets harda ice cream.. daga nan suka saki jiki har da cin abinci. Tana ta musu wasa Aliya tace �u�my tace mu rinka kiranki Maama. Abin yayi wa Aishatu da Huzaifa dadi suna cin abincin Aliyu yace maama abincinki yafi na mummy dadi, zaki dawo dani nan dakin? Huzaifa yace kana son dawowa ko. Yace eh Abba ita Aliya sai ta zama yar mummy ni kuma ga maama na. Ya koma cinyarta ya zauna. Huzaifa ya rada mata maaman Aliyu yaushe zaki masa kani ne? Kai ta sunkuyar tace ba rana bare wata. Yayi dariya kin kusa gama shan magani dai. Saboda haka ku fara saka rana. Fadila ke ta kai kawo a daki tun rana da taji labarin tafiyar Aishatu da Huzaifa Umra ta nuna bacin ranta a fili. Ba Umrar bace ta dameta kamar tafiyar da zasuyi tare. Duk inda Huzaifa zaije tare suke zuwa ko bayan ta fara haihuwa baya yarda ya tafi ya barsu a gida. Yau ga tafiyar tana ji tana gani zaiyi da Aishatu. Hawaye mai zafi ya sauko mata ba karamin daurewa take ba da tana gani Aishatu ke shigar mata dakin miji. Huzaifa na daki shiru har shabiyu saura na dare Fadila bata shigo ba. Ya kira wayarta yaji shiru bata dauka ba har sau uku sai ya tafi dakin nata. Bata cikin falo ya duba dakinta har da nasu Aliya bata nan. Hankalinsa ya dan tashi ya tafi dakin Aishatu. Da sallama ya shiga ya ganta tsakiyar yara suna bacci. Dadi da son Aishatu ya karu a zuciyarsa. Cikin kankanin lokaci ta siye zukatan yaran. Rufe musu kofa yayi ya koma. A tsakar falo ya ganta ta bude baki ganin daga ina ya fito ta fara halin. Kuka take yanzu Huzaifa ranar girkina ma sai ka shiga dakin Aishatu? Ya ce Fadila kenan, dakinki na duba ban ganki ba. Suma yaran basa nan shiyasa nazo dubawa. Tayi gaba kawai ta shiga dakinsa yabi bayanta wai meye yake damunki ne Fadila. Dole kace meye yake damuna mana. Don cin amana sai ka biya muku zuwa Umra ku kadai. Idan adalcin zaka yi ai dani zaka fara zuwa sannan wani lokacin kaje da ita. Huzaifa yayi ajiyar zuciya Fadila rigima to ai bani na biya ba. Alh Sabiu ne ya biya mijin Yaya Zainab. Kuma idan baki manta ba munje hajji da umra dake. Wace kasa na taba zuwa batare dake ba ma. Harararsa tayi kafin tace karyar banza yanzu ka fara aure da bai taba biya maka ba sai yanzu. Kunje kun gama kulla munafurcinku shine zaka fada min son ranka. To dole kasan yadda zaka yi dani wallahi don bazan zauna gadi ba. Zancenta ya fara kular dashi ya dai daure yaki magana. Wuri ya samu ya kwanta ta fita tare da bugu kofa. Bata jima ba ta dawo da sauri Huzaifa ina 'ya'yana? Na duba basa dakinsu. Yana daga kwance yace suna dakin Aishatu. Fita tayi da gudu wallahi bazasu kwana a can ba. Haka kawai kai din na hakura kuma yaran ma namu ne yanzu mu biyu? ta haifi nata mana tunda ta ita zuwa dakin miji. Huzaifa yace na rantse miki idan kika fita daga dakin nan sai ranki ya baci. Sai ki rinka abu kamar wata jahila. Ki fitan na gani. Dole ta hakura ta kwanta tana bambami. Can yaji ta dan matso kusa dashi Abban Aliya kayi bacci ne? Uhmm Abban Aliya kayi hakurk da abinda nayi. Ji yayi ta rike masa hannu yayi dan murmushi ya sake rintse ido. Shiru yayi mata yar rainin hankali kawai...ta iya shafawa idonta toka sai tata ta kawota ta shiga kwantar da kai. Kafin ya dawo daga massalaci da asuba Fadila ta bude wata drawer �ata dauki dan kudi yadda Wasila ta bata shawara. Wai idan bata dauka ba Aishatu zata kwashe. Tana cikin nema ne tayi karo da kwalayen magungunan Aishatu. Ta dauka tana jujjuya su a hankali ta rasa gane ko na meye. A iya saninta Huzaifa baya shan wani magani wadannan kuma an sha da yawa a ciki. Tana ta juyayin abin a ranta sai ta bude takardar cikin daya tana karantawa taga ance kada mai ciki tasha. Sannan an ce idan an dena ganin dischage sai mace ta dena sha. Hannunta har yana rawa ta kwafe sunan maganin a wayarta don ta tabbatar na A�shatu ne tunda mace ake ta a�bata. Haka Huzaifa ya dawo ya sameta akan gado tana browsing. Bakinta bude ciki da mamaki da fargaba. �anzu Aishatu na fama da mugun ciwo irin wannan shine ya aurota. Kuma dole yasan da ciwon tunda haka kawa� Aishatu bazata bar magani a dakinsa ba. Huzaifa na dawowa tayi saurin jifa da wayar ta mike da sauri. Yace �na zaki tace alwala. Yanzu bakiyi sallah ba kika zauna duba waya da asuba. Allah Ya shiryeki. Tace amin amin dai, a ranta kuwa murna tayi don wannan sirrin kamar ta baza shi ta gama. Kai anya kuwa Huzaifa zai kusanci Aishatu da ciwo........no wonder ta taba shigowa taga pillow da abin rufa a kasa. Kai wannan abu yayi dadi wasila zata sha labari. RASHIN GODIYA ✂ 42 Wasila a kashingide kan gadon Fadila tace ai ko kadan kada ki tona mata asiri ta hanyar baza zancen nan. Komai a hankali ake binsa. Ni yanzu kirawo min ita mu gaisa kiga yadda zanyi sai ki dau course. Koda yake gara naje da kaina sai taga kamar an bata mahimmanci. Wasila tayi sallama a kofar falon Aishatu Aliyu ya amsa. Fadila tace kinga yadda ta raba ni yarana ko. Wasila tace su Aliyu manya har ka iya amsa sallama haka kamar babban mutum. Ya durkusa Anti ina wuni, maama na ce ta koya min. Su ka sake hada ido lallai da sake. Aisha ce ta fito daga daki sanye da dogon skirt baki sai wata farar sleeveless riga. Gashinta ta daushe shi da ribbon daga gefe sai kamshi take, hannunta duk kumfa. Tace bismillah ku zauna mana baki ne damu. Daga ciki suka ji muryar Aliya tana cewa Maama in goge jikina kafin kizo. Aishatu tace eh ga towel nan ki dauka. Fadila ta dan wayance wanka tace kiyi mata ko? Tsifa na turata wurin Laure fa. Aishatu tace lauren ce ta yanke a hannu shine na karasa mata tsifar aka wanke kan. Nan da nan Fadila ta hade rai har sai da wasila ta dan take mata yatsa alamun ta saki fuska. Aishatu ta mayar da hankalinta ga wasila sannu da zuwa ina wuni. Wasila ciki da faraa tace lafiya kalau amarya ya gida da kiriniyar yara? Ai basu da kiriniya Aishatu ta amsa tana shafa kan Aliyu yaran albarka ne. Wasila tace sannu Aishatu kin sha aiki ga jiki kina fama dashi. Cak Aishatu ta tsaya a jikin fridge da take shirin daukowa wasila lemo. A sanyaye ta waigo jiki kuma? Wasila tace kinsan masu lalura irin taku suna bukatar hutu sosai. Kuma dai a rinka hankali kada wasu su dauka. Cup din hannun Aishatu a take ya fado bakinta har yana rawa tace wane ciwo? Sai Fadila tace rabu da ita kinji kanwata wai ta dauka ciki gareki kada nima na samu. Na fada mata ai ke da ciki ba yanzu ba sai nan gaba. Aishatu zancensu yana kara kidimata ta danyi yake ta zauna. Fadila tayi murmushi ina nufin sai kin gama cin amarci. Aure wata biyu ai baki fara komai ba a amarcinki. daga nan suka tashi suka fita har tana jin dariyarsu. Gaba daya sai ta rasa nutsuwa. Ta kasa gane hasashe suke na cikin ko kuwa dai zancen lalurarta ne ya fito fili. Haka ta gaji da tunani ta hakura. A daki wasila tace to kawata kinga yadda ake yi dai. Daga mata hankali zakiyi ta yi daga baya sai ki fasa kwan kowa yaji. Haka kuwa