← Book details Rufaidah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 29

Sashe 28

Rufaidah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kafa. Dama iyayensa basa son auren. Haka wasilq tabi bayansa tana ta kuka har waje ana jin muryarta. Hankali ya dawo ga Fadila, Huzaifa yace Baba dama na kiraku ne don ku zama shaida saboda kada magana ta fito ta karyata. Ku gafarceni amma bazan iya sake zama da Fadila ba. Fadila ta taso tana ihu don Allah kada ka karasa sakina Huzaifa. Igiya daya ce ta rage min. Wayyo na shiga uku Aishatu kice kin yafe kada ya karasa sakina. Huzaifa ya dauko takarda ta tashi ta fizge wallahi baka isa ka sakeni ba. Kayi kadan Huzaifa dama nasan duk bakwa sona ta nuna su Yaya Zainab. Wallahi zama daram a gidan nan babu inda zani. Baban gandu ya kwada mata wani mari ba shiri ta nutsu. Yace bazan hanaka sakinta ba Huzaifa. Fadila kin zalunci kanki don Ubangijinmu sarki ne mai adalci. Kin zama daga cikin mutanen da basa iya godewa Allah. Godiya ga Allah fa ba ta tsaya a cewa ALHAMDULILLAH bane. Idan kika yi abinda ya dace ma kin nuna godiyarki. Fadila kina sabawa mijinki yana hakuri baki gode ba, kin kullawa matar abubuwa da dama wanda ya kai a saki a tsakaninku har sau biyu tana sawa ya yafe miki baki gode ba, Allah Ya baki rai da lafiya, gidan aure da zuria nan ma baki gode ba. Mijinki da abokiyar zamanki basu taba tunanin tona miki asiri ba sai gashi rashin godiyarki ya janyo naki asirin ne ya tonu. Me kike nema ne a rayuwa Fadila? Babanta cikin kunan rai yace me take nema kuwa Yaya banda ta jawo mana zagi da bacin suna. Babu abinda Allah bai baki ba na jindadin rayuwa Fadila sai dai zuciyarki bata da godiyar Allah. Duk macen da zata kasa sauke nauyin mijinta kuma ta nuna kishin banza don zaiyi aure bata da maraba da jaka. Fadila tayi saurin kallon mahaifinta yace kwarai kuwa. Baki da maraba da jaka mana. Kina zaune wata can tana koya miki yadda zaki zauna da mijinki. Ke kuma kamar mara hankali duk abinda ta fada ya zauna miki a ka. har ki fasa kayan dakin kishiya dangin miji su biya ba tareda an neme mu ba. Haba Fadila! Indai hakan riba ne yau idonki ya gane miki ai. Umma ta ce Fadila yau kinga sabanin abinda kika so ya faru. Da yanzu wannan baiwar Allah zamu saka a gaba da fada da zagi. Ki sani zaman gidan miji iyawa ne. Kissa da kike ji ana fada ba hauka bace. A yadda kika iya kulla abubuwa haka da kinyi amfani da basirarki wurin kyautatawa miji da tuni bamu zo ga yau ba. Ni shaida ce auta ya so ki sosai sai gashi abin mamaki aure bai rufa shekara biyar ba ya kara wata. Zamanin daga ni sai mijina ya wuce. Yanzu fatanmu kawai idan tazo a zauna lafiya idan kuma ita muka tarar ma dai a zauna lafiya. Rayuwar har nawa take da zamu batawa kanmu lokaci da neman ganin bayan wasu. Shawarata ta karshe gareki shine kiji tsoron Allah ki gyara halinki. Su Yaya shukriya duk suna da abin fada a bakinsu amma tarbiyar umma ta hanasu magana idan manya nayi. Dole dukkaninsu suka yi shiru. Huzaifa ya dubi iyayen fadila...Baba ku yi hakuri ku yafe min amma bazan kara iya zama da ita ba. Ina tsoron abinda zaije ya dawo nan gaba ne. Baban gandu yayi ajiyar zuciya Huzaifa kayi hakuri gaskiya kuma ba�an goyi bayan ka zauna da ita a wannan yanayin ba. Duk macen da zata iya shiga hotel da mutumin da ba muharraminta ba har daki dole aji tsoron zama da ita. Huzaifa �a kalli Aishatu wadda tun zamansu bata yi magana ba. Kawar da kai tayi gefe alamun yau babu ruwanta sai kawai ya tashi ya dora wa Fadila takardar da tun bayan da ya baro wurin fahad ya rubuta. Kukan da take yi ya bawa mutanen wurin tausayi sai dai duk bawan da bai godewa rahmar Allah ba,wata rana ba�ai ki godewa azabarSa ba. Haka iyayenta suka saka ta a gaba tana hawaye suka tafi gida. Umma ta sake yiwa su Aishatu nasiha suka tafi. RASHIN GODIYA ✂ 54 Kwana biyu da faruwar wannan al'amari aka kira Huzaifa daga gidansu Fadi�a kan cewa tayi bari cikin dare. Ko da ta fice masa a rai yaso kwarai ta haihu don yana son yara. Ranar da yaje dubata ta bashi tausayi sosai kuma ta bashi hakuri. Har ta roki ya tayata bawa Aishatu ma hakuri. Bayan sati biyu Aishatu da Huzaifa suka tafi Umra. Bakinta ya kasa rufuwa lokacin da ta ga Ka'abar Allah. Daga inda ta ganta ta durkusa tayi sujjada ta kara godewa ALLAH SWT bisa ga niimoninsa gareta. Sunyi sati biyu banda ibada babu suke yi. Sai soyayyarsu da shakuwa da suke karuwa kullum. Basu da burin da ya wuce kyautatawa juna. Nan suka yi azuminsu har sallah. Ranar da zasu dawo tun safe Aishatu tace jikinta ba dadi tana ta narkewa. Huzaifa ya ce nasan ciwon bakya son komawa gida ne. Tayi murmushi wa yake son yin nisa da kasa mai tsarki? Ya ja hancinta babu. Suna jirgi ta dan kwanta jikinsa ta tashi ba shiri saboda amai da yake damunta. Kafin jirginsu ya sauka tayi sau biyar. Duk ta bashi tausayi haka suka tafi gida jikinta ba kwari. Su Aliya sun sha tsaraba ta dame shi sai an dauko mata su a daren yaki amincewa. Ke kin fiye rigima Aish. Kina fama da kanki kina kiran yara. Ki bari gobe na dauko su. Yau naga alama kwanan jinya zanyi. Ta dan turo baki please baby. Nayi missing din su sosai. Ya janyota jikinsa ni bakiyi missing dina ba ko. Ta gyara kwanciya ba ina ganinka ba kullum. Yace su ma yaran ai kullum kina waya dasu. Gobe zanyi musu albishir mai dadi. Tayi kara riko shi don Allah ka fara yi min kaji. Ya noke kafada haba babyn Aish. Huzaifa ya kura mata ido yana kare mata kallo....shi dai yana sonta. Ta hura masa isa a fuska me kake kallo ne baby? Yadda kika ciko mana 'yan kwanakin nan. Gobe zanyi miki pregnancy test. Naga alama yarinyar nan ciki gareki. Kunya tasa ta kara shigewa jikinsa taki yarda su hada ido. Yayi yayi taki dagowa haba Aish meye na jin kunya kuma. Ko kunyar karyar ce ta motsa. Ta na dariya tace ta gasken ce baby.....shima dariyar yake yace indai ita ce to bari nayi maganinta. Bayan wata hudu kowa yasan Aishatu tana da ciki don ya fito ya fi watanninsa girma ma. Kulawa take samu sosai daga iyayenta da umma. Su Yaya Zainab ma duk sun gama yankewa yan biyu ne a cikin yadda yayi girma shiyasa suke kara shagwabata. Duk da haka ita ke yiwa mijinta girki kullum. Tun yana hanawa har ya hakura, yace da kanta zata dena idan jikin ya kara nauyi. Rayuwarsu abin shaawa suna kula da su Aliyu sosai. Yaya Kubra ma ta koma gidanta sun dena fada da uwar mijinta. Wata talata Huzaifa na asibiti ya gama duba patient an kira next one sai yaga Fahad tare da wata mata ta sha katon mayafi. Tun ranar da aka tona Fadila basu sake haduwa ba. Huzaifa ya yi murnar ganinsa don kuwa yayi ta kiran wayarsa baya samu. So yake suyi zumunci saboda taimakon da yayi masa. Shima Fahad din da faraa ya shigo suka gaisa. Fahad yace Dr ga madam fa Yahanasu. Ta sake gaishe shi Fahad yace duk abinda ya faru kwanaki da taimakonta ne. Huzaifa yana ta murmushi yace kawai kace kanwata ce. I hope ba problem dai. Fahad yace akan matsalar haihuwa ne Dr. Ya nuna masa medical reports dinsu na wasu asibitocin. Bayan dogon nazari ya tura su yin wasu gwaje gwajen tare da basu wasu magungunan. Suka rabu cikin mutunta juna. Daren ranar suna kwance da Aish yake bata labarin zuwan Fahad. Tace ikon Allah kenan da �ana gudu yan�u yana nema. Huzaifa yace �aka rayuwa take. Allah Yayi mana jagora. Wai kinsan labarin da na ji yau kuwa? Fadila ta auri mijin Wasila suna ta rigima da wasilan don itama har tayi auren kashe wuta. Aishatu tayi mamaki to Allah Ya kyauta. Ya sake cewa ai akwai wani labarin...Aishatu ta ce yaushe ka zama mai labara� ne. Tun da na auri Indo Aisha �ana...my one and only Aish. Ta rungume shi sosai ai kuwa Aish tana da labari mai dadi da zata baka. Suka ja bargo suna dariya. Ko da Huzaifa yayi mata scanning yan biyu ya gani amma basu fadawa kowa ba. Cikin na da wata bakwai ta dena fita ko'ina saboda girmansa. Mama bata zance sai na tausayin Aishatu har Baba yana mata tsiyar bata jin kunyar yar fari. Wata rana Huzaifa ya dawo daga gidan Umma ya tarar da Aishatu tana ta kai kawo a cikin gida. Dama ya barta da safe tana complain din mararta ta rike. Yana ganinta yasan haihuwa ce ya dauko akwaitin da ya hada mata suka tafi asibiti. An shiga da ita labour room suka hanashi shiga. Ya zauna a waje sai ga su Yaya Kubra dukkanninsu. Mama ma ta�o tare da kanwarta lawisa sai Anti Sauda. Wurin awa uku suna ciki kana kallon Huzaufa sai ya baka tausayi. Da an fito ya rinka tambayar ko lafiya kenan. Karshe har wani fada fada ya koma yi musu. Dr Abida ita ta hana ya shigo ganin yadda Aishatu ke wahala. Da fargaba ta ishe shi a waje ya shiga kawai ana ta kiransa yaki sauraronsu. Aishatu na ganinsa ta soma kuka don ta sha wahala. Dr Abida tace Dr Rano ina jin ko CS zamuyi mata ne cibiya ta nade baby daya. Safar hannu ya saka ya tsaya gaban matarsa. Yana yi yana karfafa mata gwiwa ya yi dabararsu da likitoci ya warware cibin. Kusan rabin awa yana kanta kukan ma ta dena sai ga kan da ya fito. Dr Abida tana gefe tana kallon yadda Dr Rano ke lallaba matarsa. A hankali ya taimaka dan ya fito ya mikawa nurse, sai ga na biyun shima ya fito da taimakon Allah. Yana yi mata sannu ta sake wani nishin sai ga na uku. Bakinsa yaki rufowa cewa yake ku sa musu shaida. Aish
Chapter 28 · 0% Book details