Sashe 27
Rufaidah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ALHAMDULILLAH bane. Idan kika yi abinda ya dace ma kin nuna godiyarki. Fadila kina sabawa mijinki yana hakuri baki gode ba, kin kullawa matar abubuwa da dama wanda �a kai a saki a tsakaninku �ar sau biyu tana sawa ya yafe miki baki gode ba, Allah Ya baki rai da lafiya, gidan aure da zuria nan ma baki gode ba. Mijinki da abokiyar �amanki basu taba tunanin tona miki asiri ba sai gashi rashin godiyarki ya janyo naki asirin ne ya tonu. Me kike nema ne a rayuwa Fadila? Babanta cikin kunan rai yace me take nema kuwa Yaya banda ta jawo mana zagi da bacin suna. Babu abinda Allah bai baki ba na jindadin rayuwa Fadila sai dai zuciyarki bata da godiyar Allah. Duk macen da zata kasa sauke nauyin mijinta kuma ta nuna kishin banza don zaiyi aure bata da maraba da jaka. Fadila ta�i saurin kallon mahaifinta yace kwarai kuwa. Baki da maraba da jaka mana. Kina zaune wata can tana koya miki yadda zaki zauna da mijinki. Ke kuma kamar mara hankali duk abinda ta fada ya zauna miki a ka. har ki fasa kayan dakin kishiya dangin miji su biya ba tareda an neme mu ba. Haba Fadila! Indai hakan r�ba ne yau idonki ya gane miki ai. Umma ta ce Fadila yau kinga sabanin abinda kika so ya faru. Da yanzu wannan baiwar Allah zamu saka a gaba da fada da zagi. Ki sani zaman gidan miji iyawa ne. Kissa da kike ji ana fada ba hauka bace. A yadda kika iya kulla abubuwa haka da kinyi amfani da basirarki wurin kyautatawa miji da tuni bamu zo ga yau ba. Ni shaida ce auta ya so ki sosai sai gashi abin mamaki aure bai rufa shekara biyar ba ya kara wata. Zamanin daga ni sai mijina ya wuce. Yanzu fatanmu kawai idan tazo a zauna lafiya idan kuma ita muka tarar ma dai a zauna lafiya. Rayuwar har nawa take da zamu batawa kanmu lokaci da neman ganin bayan wasu. Shawarata ta karshe gareki shine kiji tsoron Allah ki gyara halinki. Su Yaya shukriya duk suna da abin fada a bakinsu amma tarbiyar umma ta hanasu magana idan manya nayi. Dole dukkaninsu suka yi shiru. Huzaifa ya dubi iyayen fadila...Baba ku yi hakuri ku yafe min amma bazan kara iya zama da ita ba. Ina tsoron abinda zaije ya dawo nan gaba ne. Baban gandu yayi ajiyar zuciya Huzaifa kayi hakuri gaskiya kuma bazan goyi bayan ka zauna da ita a wannan yanayin ba. Duk macen da zata iya shiga hotel da mutumin da ba muharraminta ba har daki dole aji tsoron zama da ita. Huzaifa ya kalli Aishatu wadda tun zamansu bata yi magana ba. Kawar da kai tayi gefe alamun yau babu ruwanta sai kawai ya tashi ya dora wa Fadila takardar da tun bayan da ya baro wurin fahad ya rubuta. Kukan da take yi ya bawa mutanen wurin tausayi sai dai duk bawan da bai godewa rahmar Allah ba,wata rana bazai ki godewa azabarSa ba. Haka iyayenta suka saka ta a gaba tana hawaye suka tafi gida. Umma ta sake yiwa su Aishatu nasiha suka tafi. RASHIN GODIYA ✂ 52 Kafin Fadila ta karasa gida Fahad ya tura mata text akan cewa kada tayi masa text ko waya saboda Aishatu tana dakin. Hankalinta kwance ta yi masa reply akan za ta kiyaye. Sai bayan rabin awa da komawar Fadila gida sannan Huzaifa ya dauko Aishatu suka taho. Da ya iso a waje yayi parking din motar suka shigo ciki sai Aishatu ta tsaya a falonsa na waje. Shi kuma yayi sallama ya shiga ciki. Ciki da nishadi ya shiga gidan yana ta faraa. ba shiri ya tsaya da yaga Fadila da Wasila a tsakar falo suna ta kai kawo. Ya sake maimaita sallama Fadila ta amsa da kyar, muryarta har rawa take yi. Huzaifa ya kallesu kamar mai mamaki yace lafiyarku kuwa ko yayar taki ta mutu ne wasila? Ta ja dogon numfashi jikinta da sauki. Gidanka ne dai a cikin matsala. Fadila ta share hawayen munafurci kinga ki iya bakinki kawai idonsa ya gane masa. A can waje kuma motoci biyu ne suke horn a bakin gate. Mal Habu ya bude musu suka shigo. Daya Yaya Kubra ce tare da Umma. Dayar kuma dreban yaya zainab ne ya daukosu ita da Yaya shukriya da Saddiqa. Aishatu ta leka ta window ta gansu hankalinta ya kara tashi me ya kawosu gidan a lokaci daya ta tambayi kanta. Su dinma a cikin tashin hankali suka shiga gidan. Huzaifa da yake tsaye a falo yana jiran amsar su Fadila ya juyo a tsorace yana tambayarsu ko lafiya. Saddiqa tace kai zamuyi wa wannan tambayar auta. Fadila ta kira dukkanmu tace muzo gidan nan akwai matsala. Yace nima shigowata kenan bata fada min komai ba. Umma ta kalleta ke Fadila ko dai yaran ne? Wasila tace yara Laure ta rakasu islamiya. Za ta sake magana sai ga sallamar baban Fadila da yayansa Baban Gandu. A take cikin Fadila ya bada wani mugun sauti tace Baba daga ina kuke haka? Baban gandu yace kaniyarki, ba amsa sallama ba gaisuwa sai daga ina muke? To daga inda kika aikemu muke mara kunya. Huzaifa da sauran suka gaisa dasu. Umma tace ni ku fada min abinda ke faruwa fadila ce ta kira mu. Baban gandu yace mu kuma Huzaifan ne ya kiramu da kansa. Yace lallai yana bukatarmu a gidan nan saboda wani abu mai matukar mahimmanci. Yaya Zainab tace wai ni ina Aishatu ne. Fadila ta durkusa gabansu dama dalilin nawa kiran kenan. Nasan duk abinda zan fada zaku ga kamar kishi ne yasa na fada shiyasa na kiraku ku zama shaida. Ban dade da dawowa gida ba munje duba yar wasila sai nake jin kamar maganar mutum sama da daya a dakin Aishatu. Da nayi zaton baki ne da ita sai kuma naji muryar ta namiji ce. Duk da haka nace ko kannenta ne. Ta kalli Huzaifa nasan dai ka hana maza wuce falon nan amma sai nace kila wani abin ne daban. Baban gandu yace ke kuma uwar shisshigi sai kika dorawa kanki damuwar da ba taki ba ko? Umma tace haba Alh kyaleta ta gama bayaninta. Fadila ta sake sauke murya tace to daga nan nace da wasila tazo muje mu gaisa sai naji kofar a kulle ta ciki. kuma na tabbatar da mutane a ciki. Na buga baa bude ba shine hankalina ya tashi na zaga tagarta ta baya. Wayyo Allah sai kuka ya kwace mata Abban Aliya ha'intarka Aishatu take yi. Ta window din tagar na hangota ita da wani suna.....Baban Fadila ya daka mata tsawa bana son zancen banza. Su Umma kuwa sai salati suke. Wannan wane irin tashin hankali ne. Jinkin kowa a mace suna kallon Huzaifa wanda ya dafe kai yana hawaye. Kowa ya tausaya masa basu san kukan tsabar bacin rai bane na irin halayyar Fadila. Falon yayi tsit can Huzaifa ya ce Fadila kin tabbata kin gansu tare. Tace wallahi na gansu a mugun yanayi. Ai wasila ma na wurin, ban bari sun ganni ba dai. Kasan yau baka dawowa da wuri kuma na mata waya cewa na fita. Kila shiyasa ta kirawo shi. Yayyan Huzaifa suna ta juyayin zancen. Kawai suka ga ya tashi. Waje ya fita har umma na cewa a bishi kada yayi wani wurin. Bai dade ba sai gashi ya dawo rike da hannun Aishatu. Fadila ta tashi da sauri jikinta na bari. RASHIN GODIYA ✂ 53 Kowa na binsu da ido ya kaita gaban mahaifiyarsa ya zaunar da ita sannan yace mata Aish bani key din dakinki. Ba musu ta dauko ta mika masa, yace guda nawa ne mukullan? Ta ce hudu ne biyu suna jakata biyu kuma suna wurinka. Huzaifa ya shiga daki ya fito da su. Ya hada ya ce da Baban gandu ai sun cika hudu ko? Yace hudu ne zahiri. Wai ni kadai ne kaina ya kulle a wurin nan? Umma tace nima jira nake su yi min bayani. Idanun fadila kamar zasu fado kasa. Ta riga ta gama tsurewa tunda taga ya shigo da Aishatu tasan abinda zai biyo baya bazai mata kyau ba. Huzaifa ya tashi yaje ya bude dakin Aishatu sai ga Fahad ya fito. Nan fa kowa ya tashi tsaye ana kallon kallo. Umma tace auta don girman Allah me yake faruwa? Huzaifa yace su zauna yanzu zaiyi musu bayani. Suna zama yace Fahad bismillah. Nan da nan fahad ya fara bayanin abinda ya faru tun daga wayar Wasila ta farko. Kowa da abinda yake fada game da Fadila da kawarta. Aishatu kuwa sai kuka take yi. A wurin Huzaifa ya fadi wasu daga abubuwan da fadila tayi masa a baya tun kafin aurensa da Aishatu. Fadila ta soma kuka Huzaifa sharri zaka yi min ko har ka iya hada baki da tsohon mijin matarka don kawai baka so na. Baban fadila ya tashi ya hau dukanta. Fadila ke wace irin yarinya ce yanzu da ke zaa hada baki a kawo namiji dakin wata don miji ya saketa. Kuma da yake baki da tsoron Allah har ki kirawo dangin mijinki su zo kallo ko. To gashi ramin da kika gina kin fada ciki. Tana kuka tace Abba wallahi sharri ne. Tunda yarinyar nan tazo take kulla min sharri. Huzaifa kawai sai ya jefa mata hotunansu ita da Fahad a mota da hotel. Wannan karon Baban gandu ne ya kai mata duka. Kin cucemu kin cuci kanki Fadila. Umma ta ce Aishatu iyayenki sun san abinda ke faruwa...ta girgiza kai a'a Umma. Tace Allah Yayi miki albarka da kika rufa sirrin gidanki. Fahad ya tashi zai tafi suka yi masa godiya da bai biyewa son zuciya ya fada ga halaka ba. Ana ta yiwa Fadila fada tana rusa kuka wasila ta sabi jakarta zata gudu Huzaifa yace dawo nan. Ki jira mijinki zai zo daukarki. Wasila ta soma matsar kwalla tana bada hakuri. Babu wanda ya saurareta har Kamilu ya iso bai tsaya gama jin bayani ba ya ce ta tafi ya saketa saki uku. Nan kuma manya suka soma yi masa fada yayi aika aika. Shi dai murna yake yau ya sami kwarin gwiwar rabuwa da matar da ta zame masa karfen