Sashe 17
Rufaidah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya iya cewa to kai ka ganshi ne Mal Habu....ehhh, to na dai ga kamar giftawar inuwa dana leqa ta taga. Ba don girmansa ba da babu abinda zai hana Huzaifa dauke shi da mari. Amma sai yace runda baka da tabbas ina ganin gara a hakura da aikin nan naka idanunka sun fara samun matsala. Mal Habu yace a'a yallabai banga komai ba. Amma ita Haj a gabanta abin ya faru. Huzaifa bai tsaya sauraronta ba ya koma dakin Aishatu. Tana nan inda ya barta a tsaye tana zubar da hawaye. Dakinta ya shiga ya rinka fito da akwatunanta yana kwashe kayan wardrobe din yana zubawa a ciki. Sai da ya kwashi wanda zai iya sannan ya fara kaisu dakinsa daya bayan daya. Fadila tana falo tana dariyar mugunta. Ba don shigowar habu maigadi ba har dakin sai ta lalata. Ganin Huzaifa da akwatuna ta ce lafiya ina kuma zaka kai kayan? Shiru ma magana ce. Sai da ya gama kwashesu tsaf Aishatu dai bata iya cewa komai. Ya koma ya rufe kofar gidan sannan ya sake shiga dakin Aishatu. Ji tayi Huzaifa ya daga ta cak kamar jaririya yazo ya wuce Fadila dake matsar kwallar karya a falo. Bai ajiyeta ko ina ba sai akan gadonsa. Ruwa mai zafi sosai ya tara mata a toilet ya sake daukarta ya kaita sannan ya rufo mata kofa. Kofar dakinsa kowa key yasa ta waje ya rufeta sannan ya tafi dakin Fadila. Waya ya tarar da ita tana yi. Jin alamun da mutum a bayanta yasa ta koma muryar kuka. Ai wasila na auna arziki da yau kunji mummunan labari. Wani kato ne.....wayar ya fizge kafin ta tashi ya fara zabga mata belt dinsa. Sai da yayi mata lilis ya kyaleta tana ta kwarma ihu. Mal Habu har ya gaji da buga kofar gidan. Itama Aishatu ihun Fadila yasa tayi saurin fitowa daga toilet taji kofar dakin kam a rufe. Bugu take iya karfinta ta kasa budewa. Huzaifa ya kalli Fadila da jikinta yayi rudu rudu. Cikin fushi yace baki fi karfina ba Fadila, kina cin darajar aure ne kawai nake raga miki. Amma tunda kin zabi haka mu zuba ni da ke shege ka fasa. Kuma wallahi baki da girki har sai na gama gyarawa Aishatu dakinta. Idan zaki gyara halinki ki gyara otherwise ki kama hanyar gidanku. Haba na gaji da masifarki. Tun kafin nayi aure kike hura min wuta. Nayi auren ma ban tsira ba. Ki guji ranar da zaki kaini bango sai na miki fiye da wannan. Wai ni zaki rainawa hankali. Ki yi min barna a gida kice wani ne. Da gaske ne ai so zanyi ya hada dake a fashe fashen. Fadila cikin kuka take masa Allah Ya isa. Yayi gaba abinsa zuciyarsa ba dadi. Yana bude kofar dakin ya tarar da Aishatu zaune a bakin kofa tana rusa kuka. Tana ganinsa tace me yasa ka dake ta? Yace kinga ki sami wuri ki kwanta raina a bace yake i dont want to talk now. Bata sake tanka masa ba ganin ya dau zafi sosai kamar ba yanzu suka shigo gidan cikin nishadi ba. A haka ya kwanta wurin da ya saba a kasa yana ta adduar neman sassauci a zuciyarsa har bacci ya dauke shi. Washegari da sassafe ya kira Yaya Zainab yace suzo gidansa ita da sauran yan uwansa. Aishatu tunda ta tashi take rakube a gefe. Fushin Huzaifa yana neman shafarta duk da ita aka yiwa laifi. Kafin tara na safe dukkan ninsu sun iso harda Yaya kubra da tayiwa umma karya ta fito. A gigice suke saboda kiran yayi wuri. Basu kara gigicewa ba sai da suka ga dakin Aishatu. Saddiqa tace ko baka fada ba auta nasan Fadila ce da wannan aikin. Wallahi sai naci ubanta a gidan nan. Yaya zainab dama halin umma suka yo ita da Huzaifa wurin hakuri tace ba haka zaayi ba saddiqa. Ina Fadilan take? Yaya kubra tace Allah Yaya indai zata fito babu abinda zai hanani dukanta. Ya take so ayi mata ne....fadila na jin muryarsu ta kama kofar dakinta ta rufe da key. Wurin Aishatu ya kaisu wadda tunda ta tashi take kuka. Tana ganinsu ta fada jikin Yaya kubra tana ta kuka. Gaba dayansu ta basu tausayi. Yaya Zainab tace to yan uwa lokacin zumunci yayi. Ya kamata duk mu hadu mu gyarawa Aishatu daki ba tare da sanin Umma ko su Mama ba. Itama Fadilan ka barni da ita zan bata last warning. Ta koma ga Aishatu kiyi hakuri kanwata don Allah kada ki daga maganar nan. Kai kuma na yarda ka hukunta ta duk yadda kake so amma banda saki please. Da fadila taki bude kofa daga waje tayi mata fada da nasiha. Huzaifa duk haushi ya ishe shi har wani lallaba ta ake. Ai bata ga komai ba a gashin kumar da zai mata. Aishatu kuwa ta rasa bakin yi musu godiya. Yaya shukriya tace ai yiwa kai ne. Yaya Zainab na tafiya gida ta fadawa mijinta. Managing director ne a wani travel agency ya ce gaskiya yarinyar nan bata kyauta ba. Amma nasan maganinta....ya kira waya yayi wa wani magana sannan yace da Yaya zainab ki fada ma Huzaifa yayi wa amarya passport next week zasu tafi Umra. Yaya zainab ta washe baki lallai Aishatu yar gata ce. RASHIN GODIYA ✂ 34 Ranar har dare Aishatu bata ga fara'ar Huzaifa ba. Gaba daya hankalinsa ya koma kan gyaran dakin ta. Samarin unguwar ya samu su biyu suka share dakin aka fitar da duk abinda bazai moro ba. Ganin shima ya zage ana aikin dashi Aishatu ta gaji da zaman dakin ta shigo wurinsu harda dan murmushinta. Da me zan tayaku ko in kawo muku ruwan sanyi? Hannu kawai ya nuna mata alamar ta tafi. Haushinsa ya kara kamata, wai meye laifinta ne da zai tsiri sha mata kunu. Daki ta koma ta kunna tv tana kallo sai gashi ya shigo. Dauke kanta ma tayi don kada su hada ido. Ya dawo gefenta zai zauna ta matsa tare da kawar da kai da�a gefen. Sai ya koma gaban tv ya tsaya ita kuwa ta runtse ido a dole bazata kalle shi ba. Yayi �urmushi ya shiga toilet yayi wanka. Kafin ya fito ta tashi ta tafi dakinta. Kayan da ya debo ta duba babu undies a ciki shine ta tafi nema. Yana ganin bai ganta ba ya fita daga shi sai dogon wando. Bazai wuce ta koma dakinta ba, sai taje wani abin ya ji mata ciwo. Kawai sai yabi bayanta. A durkushe ya ganta tana kuka sosai. Jikinsa a sanyaye ya karasa inda take. Ji tayi ya rungumeta ta ba�a, duk yadda taso ta kwace ta kasa. Shima kansa haushinsa take ji. Allah kadai Yasan da yadda Baba ya siya mata wannan kayan. Huzaifa ya juyo ta ita lokacin ta dena fizge fizgen don tasan yafi karfinta ko motsi ya hanata yi. Sake rungumeta yayi yana shafa mata baya..a hankali taji yana cewa Aish ki kara hakuri. Tun haduwarmu dake kike fuskantar matsaloli amma you always find a way to make things better. Wannan karon fadila ta wuce gona da iri amma i promise you bazan barta haka ba. Aishatu ta dago kanta a hankali suka hada ido....wani irin abu da bazata iya fasaltawa ba taji a wannan lokacin. Ga dukkan alamu Huzaifa ma yaji don wani irin murmushi ya sakar mata da ya kara narkar mata da zuciya. Hannunta ya rike suka koma dakinsa. Aishatu tace Dr...harararta yayi wai sai kinga fadila zaki kirani baby, ni nayi fushi. Ya bata dariya tace to yi hakuri baby. Amma seriosly magana zamuyi. Banga dalilinka na cewa fadila bata da girki ba har sai an gama gyaran dakina. Zaiyi magana tayi saurin cigaba Wallahi hakan daukar hakki ne. Abinda ya faru zargi ne muke tunda ido bai gani ba. Huzaifa yace Aish ya wuce zargi fa. Ke kinsan babu wanda zai miki haka sai ita. Aishatu tace ni dai ka je ka fada mata zata karbi girki ni bazan yi ba. Huzaifa ya ce Aish har zaki fara musu dani? Ta zauna bakin gado ba haka bane...lahirarmu nake dubawa. Me zamu ce idan Allah Ya tambayemu hujjar mu ta hukunta bisa zargi? Nasan kana mata uzuri amma please ka kara. Haka tayi ta bashi baki ko kadan bai so ba amma yasan gaskiya take fada masa. Rai a bace yaje ya sanar da Fadila ta shirya karbar girki da daddare. Shawarar Wasila ta karba ta bashi hakuri sosai tana kuka. Ya dai ji amma bai sakar mata fuska ba. Kafin ya fita ya dawo ta gyara dakinta da falo. Yau harda wankin toilet. Sai da yayiwa Aishatu sai da safe ya fita...abin haushi hawaye taji ya sauko mata. Meye na kuka Aish ta tambayi kanta. Its not like kuna soyayya da angon naki. Sauran abincin da Yaya Kubra ta aiko mata taci. Shi kuwa Huzaifa yana ta cika da batsewa ya shiga falon Fadila. Ba yabo ba fallasa ta gyara dakin. Rigar jikinta kuwa iyakarta cinya. Tayi kyau sosai don ta iya kwalliya. Indomie ta dafa masa ya kalli abincin a wulakance amma dole yaci don yunwa yake ji. A hankali Fadila ta rinka jan hankalinsa har ya sakar mata jiki. Ranar zuciyarta fes ta kara tabbatarwa tana son mijinta kuma shima yana sonta. Dole ta yi gaba da Aishatu don bata ga matar da ta isa suyi sharing miji ba. Fahad yana zaune gaban likita yana kara karanta report din test din da aka yi masa. Ya dago kai yanzu dr ka tabbatar ni da yahanasu duk bamu da problem? Dr ya gyara zaman glass dinsa yace kwarai kuwa Fahad. Komai lafiya hakuri kawai zaku kara. Kasan haihuwa lokaci ne. Amma na rubuta maka magani da zakuyi trying. Fahad ya daki table din dr din ya mike cikin fushi. Magani! Magani ! Magani! Na gaji. Ka bar maganinka kawai ba yau na fara zuwa test ba akan fertility ana bani. Ransa a bace ya fita....ya gaji da trying result yake son gani. Ba abinda yake so kamar haihuwa yanzu ido rufe. Idanunsa yaji suna masa zafi alamun hawaye na shirin zuba. A hankali yace Aisha I miss you. RASHIN GODIYA ✂ 35 Haka Aishatu ta cigaba da zaman hakuri