Sashe 29
Rufaidah Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
har uku kika haifa. Ya koma ya rungumeta...i love you. Sannu yanzu ki rufe idonki a hankali zanyi miki dinki kinji ko. Ihunta yasa Dr Abida da nurse din fita. Gidan Mama a cike da yan uwa da abokan arziki yan barka don taki yarda Aishatu ta koma gidanta. Huzaifa yayi ta mita har ya hakura. Ranar suna kuwa a gidan Mama akayi saboda yafi fili. Jamaa sun taru sosai harda su Yahanasun Fahad da Anti Maryam matar wansa. Itama Yahanasu da karamin cikinta. Yara sunci sunan Abdulrahman, Abdulrahim da Abdulrashid. Anyi taro lafiya an tashi lafiya. Bayan wata shida Yahanasu ta haifi yarta mace. Bakin fahad kamar gonar auduga. Ya fidda rai da samun haihuwa a da. Aisha ya sawa babyn bisa shawarar Yahanasu. Suna ta zumuncinsu. Itama sunje suna Aliyu ya kankame baby Aisha har yana cewa Maama wannan ce baby Aish dina ko irin yadda Abba yake fada miki. Aka yi dariya ita kuwa sai kunya. A gida tana bawa Huzaifa labari yace ai kyan da ya gaji babansa. Amma dai tun wuri ya sake sunan nan. Huzaifa ne kadai mai Aish. Suka rungume juna tace Babyn Aish....a hankali yace naam. Tace yau na fada maka ina sonka kuwa? Yace eh amma yana da kyau a yawaita maimaitawa. Allah Yasa mu dace. ALHAMDULILLAH Godiya ta musamman gareku yan uwana wadanda suka bani kwarin gwiwar rubutun nan. 💞 Zainab, Shukriya, Rumanatu, Sadiya and Ibtihal. Nagode sosai Allah Yabar zumunci. Sai kuma yan uwana dukkan masu karanta books dina. Wadanda na sani da wanda ban sani ba. Fatan alkhairi garemu baki daya. Kamar su Rufaida Omar's fans, Matan Albarka, Mu kula da addininmu mata, Classic Ladies Novel, home of novels, modern hausa writters da sauran yan uwa da abokan arziki. Allah Ya bamu rayuwa mai albarka. Batul Mamman💖 Copied By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Arewa hausa novels Novels villa Duniyan novels Hayat hausa novels Hausa novels and fashion And Cool novel, makeup and cooking)
WHATSAPP NO:
+2347039625239
WHATSAPP NO:
+2347039625239