← Book details Rufaidah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 29

Sashe 16

Rufaidah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yayi ya kura mata ido har sai da ta kawar da nata tana murmushi. Aish kina kishina??? Muryarsa can kasa yayi maganar ta tashi da sauri uhmm bari naje na gyara maka daki. Amsar da bata bashi ba kenan. Sai da ya dawo daga masallaci da magriba yace ta shirya su je gidan Umma da gwammaja. Murna a wajen Aishatu baa cewa komai. Yau zata je taga su mama, dama kullum sai sunyi waya har da baba ma. Huzaifa yana kallon yadda take ta shiri cike da doki har yar waka ta rinka yi a gaban madubi. Wani turare ta dauko mai matukar tsada. Anti Sauda ce ta bata kyauta tun kafin tayi aure, tsaraba da mijinta ya dawo daga Dubai. A ledarsa ma yake ta saka a jakarta. Lace tasa mara nauyi riga da zani sai mayafinta babba wanda ta dora a kanta bayan ta kashe dauri. Kallonta kawai yake tana saka takalmi yace Aish kinyi kyau kamar amarya. Ta dan tura baki me kake nufi, ni ba amarya bace? Kinfi kama da.....ta koma gaban mirror tana sake kallon kanta. Da me nayi kama please? Ko dai kayan basuyi ba na canja. To sarkin rikicewa wasa nake. Komai yayi banda abu daya. Ta dago idanuwanta menene baiyi ba? Baki fesa min turare ba. Kinsan idan mutum baby ne babu wanda ya kaishi shagwaba. Ta rasa me yasa Huzaifa yake son sata jin kunya. Tare suka fito duk sunyi kyau kana ganinsu kaga masoya masu kaunar juna. Ya shiga dakin Fadila yace mata sun fita. Naman gabanta ta cigaba da ci hankali kwance. Suna fita ta shiga kitchen ta dauko tabarya sai kofar bangaren Aishatu. Gwammaja suka fara zuwa suka tarar da Baba da abin sallah a waje zai tafi masallaci sallar isha. Huzaifa ya bishi ta shiga ita kadai. Mama da kannenta sunyi murnar ganinta sosai har Huzaifa suka dawo suna ta hira. Baba yayi musu nasihar da ya saba akan rikon amana da kula da addini. Ga mamakinta kaya ya debo daga booth dinsa masu yawa ya basu. Suka yi ta godiya. A mota suna hanyar zuwa gidan umma yace Aish ina son Baba. Yana da kirki ga saukin kai, sai �ake tuna min da nawa mahaifin. Tace Allah Yayi masa Rahma ni na hakura ya zama baba��a daga yau. Shan miya amma. Meye kuma shan miya Aish? Tace dama ranar da na fara ganinka nasan kai dan kau�e ne, ta rike haba ace dan kano bai san shan miya ba. To me ka sani? Ya kashe mata ido nasan yadda ake...in fada? Fadi mana nasan bazai wuce kace ka iya lomar tuwo ba. Sai da maigadi ya rufe gate din gidan �ace mata nasan �adda ake kissing bakin Aish. Duk da sau daya hakan ta taba faruwa tsakaninsu ranar da aka kaita amma babu ranar da bata tunawa. Kafin ya gama kashe motar ta fice ta shiga gidan da gudunta..wannan kunya ta Aish. �a shafi sumarsa yabi bayanta. Umma tayi murnar ganinsu sosai, tace autan umma �ar ka fara kiba. Aishatu tace dama sunanka kenan? To daga yau na samu. Yace haba umma meyasa kika fada a gabanta salon ta raina ni. Yaya kubra tace sai kai dai ka fiye son girma. Aishatu zo muje kici abinci. Aishatu tace ni dai daga yau umma nice autarki kinga ai girmeni. Duk suka yi dariya, ta tambayi su Aliya akace Shukriya ta tafi gidanta dasu. Sunyi hira sosai da zasu tafi ta bawa umma turaren da taho dashi. Tana son kamshinsa duk da yana kwali ana ji. Umma tayi ta sa mata albarka. Yaya Kubra kuwa sai washe baki kanninta ya auro yar arziki irin albarka. Sai goman dare suka koma gida. Sai dai tun daga kofar falo suka ga wurinta a bude. Kusan komai na falon an fasa shi babu wani abin mora hatta kafet da kujeru an tsaga su da wuka. RASHIN GODIYA ✂ 34 Ranar har dare Aishatu bata ga fara'ar Huzaifa ba. Gaba daya hankalinsa ya koma kan gyaran dakin ta. Samarin unguwar ya samu su biyu suka share dakin aka fitar da duk abinda bazai moro ba. Ganin shima ya zage ana aikin dashi Aishatu ta gaji da zaman dakin ta shigo wurinsu harda dan murmushinta. Da me zan tayaku ko in kawo muku ruwan sanyi? Hannu kawai ya nuna mata alamar ta tafi. Haushinsa ya kara kamata, wai meye laifinta ne da zai tsiri sha mata kunu. Daki ta koma ta kunna tv tana kallo sai gashi ya shigo. Dauke kanta ma tayi don kada su hada ido. Ya dawo gefenta zai zauna ta matsa tare da kawar da kai daya gefen. Sai ya koma gaban tv ya tsaya ita kuwa ta runtse ido a dole bazata kalle shi ba. Yayi murmushi ya shiga toilet yayi wanka. Kafin ya fito ta tashi ta tafi dakinta. Kayan da ya debo ta duba babu undies a ciki shine ta tafi nema. Yana ganin bai ganta ba ya fita daga shi sai dogon wando. Bazai wuce ta koma dakinta ba, sai taje wani abin ya ji mata ciwo. Kawai sai yabi bayanta. A durkushe ya ganta tana kuka sosai. Jikinsa a sanyaye ya karasa inda take. Ji tayi ya rungumeta ta baya, duk yadda taso ta kwace ta kasa. Shima kansa haushinsa take ji. Allah kadai Yasan da yadda Baba ya siya mata wannan kayan. Huzaifa ya juyo ta ita lokacin ta dena fizge fizgen don tasan yafi karfinta ko motsi ya hanata yi. Sake rungumeta yayi yana shafa mata baya..a hankali taji yana cewa Aish ki kara hakuri. Tun haduwarmu dake kike fuskantar matsaloli amma you always find a way to make things better. Wannan karon fadila ta wuce gona da iri amma i promise you bazan barta haka ba. Aishatu ta dago kanta a hankali suka hada ido....wani irin abu da bazata iya fasaltawa ba taji a wannan lokacin. Ga dukkan alamu Huzaifa ma yaji don wani irin murmushi ya sakar mata da ya kara narkar mata da zuciya. Hannunta ya rike suka koma dakinsa. Aishatu tace Dr...harararta yayi wai sai kinga fadila zaki kirani baby, ni nayi fushi. Ya bata dariya tace to yi hakuri baby. Amma seriosly magana zamuyi. Banga dalilinka na cewa fadila bata da girki ba har sai an gama gyaran dakina. Zaiyi magana tayi saurin cigaba Wallahi hakan daukar hakki ne. Abinda ya faru zargi ne muke tunda ido bai gani ba. Huzaifa yace Aish ya wuce zargi fa. Ke kinsan babu wanda zai miki haka sai ita. Aishatu tace ni dai ka je ka fada mata zata karbi girki ni bazan yi ba. Huzaifa ya ce Aish har zaki fara musu dani? Ta zauna bakin gado ba haka bane...lahirarmu nake dubawa. Me zamu ce idan Allah Ya tambayemu hujjar mu ta hukunta bisa zargi? Nasan kana mata uzuri amma please ka kara. Haka tayi ta bashi baki ko kadan bai so ba amma yasan gaskiya take fada masa. Rai a bace yaje ya sanar da Fadila ta shirya karbar girki da daddare. Shawarar Wasila ta karba ta bashi hakuri sosai tana kuka. Ya dai ji amma bai sakar mata fuska ba. Kafin ya fita ya dawo ta gyara dakinta da falo. Yau harda wankin toilet. Sai da yayiwa Aishatu sai da safe ya fita...abin haushi hawaye taji ya sauko mata. Meye na kuka Aish ta tambayi kanta. Its not like kuna soyayya da angon naki. Sauran abincin da Yaya Kubra ta aiko mata taci. Shi kuwa Huzaifa yana ta cika da batsewa ya shiga falon Fadila. Ba yabo ba fallasa ta gyara dakin. Rigar jikinta kuwa iyakarta cinya. Tayi kyau sosai don ta iya kwalliya. Indomie ta dafa masa ya kalli abincin a wulakance amma dole yaci don yunwa yake ji. A hankali Fadila ta rinka jan hankalinsa har ya sakar mata jiki. Ranar zuciyarta fes ta kara tabbatarwa tana son mijinta kuma shima yana sonta. Dole ta yi gaba da Aishatu don bata ga matar da ta isa suyi sharing miji ba. Fahad yana zaune gaban likita yana kara karanta report din test din da aka yi masa. Ya dago kai yanzu dr ka tabbatar ni da yahanasu duk bamu da problem? Dr ya gyara zaman glass dinsa yace kwarai kuwa Fahad. Komai lafiya hakuri kawai zaku kara. Kasan haihuwa lokaci ne. Amma na rubuta maka magani da zakuyi trying. Fahad ya daki table din dr din ya mike cikin fushi. Magani! Magani ! Magani! Na gaji. Ka bar maganinka kawai ba yau na fara zuwa test ba akan fertility ana bani. Ransa a bace ya fita....ya gaji da trying result yake son gani. Ba abinda yake so kamar haihuwa yanzu ido rufe. Idanunsa yaji suna masa zafi alamun hawaye na shirin zuba. A hankali yace Aisha I miss you. RASHIN GODIYA ✂ 33 Saboda tsabar tashin hankali Aishatu ta kasa cewa komai. Kofar dakinta ta kalla an rotsa ta duk da katakon mai kwari ne. Da sanyin jiki ta karasa ciki abin mamaki baa taba komai ba. Karamin falonta kuwa cike yake da kamshi saboda komai na show glass dinta ya fashe rugu rugu. Bakinta ta toshe saboda kukan da yake neman fin karfinta. Sai hawaye kamar famfo. Huzaifa kuwa jingina yayi da abinda yayi saura na kofar falon ya runtse idonsa. bazai iya kwatanta yadda ransa ya baci ba. A hankali ya bude idonsa yana kallon Aishatu...mayafin da tasa ta toshe bakinta ne ya hana kukanta yayi karfi. Tausayinta yaji sosai kukanta yana kara daga masa hankali. Zuciyarsa kamar ta fashe don tsananin bakinciki. Fita yayi yana kwalawa Fadila kira cikin daga murya. Ko ita Aishatu da take daki sai da ta tsorata. Tare ya sun shigo da Habu maigadi. Mal Habu yace yallabai kaga barnar da ta faru ko? Fadila ta ruga da gudu ta rungume Huzaifa tana shesshekar kuka. Abban Aliya kaga girman mutumin kuwa? Allah ne ya rufa min asiri da kila ma yanka ni zaiyi. Iyakar karfinsa ya tureta don bai shirya jin karyar da zata yi masa ba. Mal Habu yace na zaga bayi kenan na rinka jin kamar ana buga wani abu. Ina zuwa naga Hajiya tana ihu tana kuka tace wani ne ya hauro yake fasa kayan hajiya amarya. Rainin hankali Huzaifa ya fada a zuci. Da kyar
Chapter 16 · 0% Book details