← Book details Rufaidah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 29

Sashe 18

Rufaidah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da Fadila don bata fasa halin neman tsokana ba. Tsakaninta da Huzaifa suna hira sosai. Dakinsa kuwa ya bar mata sai dai ya je daukar kaya. Ranar da Aishatu zata karbi girki tun da ya farka da safe ya sami kansa cikin nishadi. Fadila tana kwance gefensa ya dan taba ta...a hankali ta bude �do saboda baccin da take ji. Yace fadila tara da rabi fa...kinsan dai daren jiya cornflakes nasha. Please ki tashi ki bani abinci. Ta juyar da kanta ni ka kyaleni na dan kara kadan, goma ma bata yi ba. Yace idan baki tashi ba zanje wurin Aishatu nasan....kamar an tsikareta ta tashi naji naji bari nayi brush. Ta fita yabi bayanta da dariya. Fadila kishi. Bayan laasar ya tafi dauko �aransa don sati daya ya rage Aliya ta koma makaranta. Sunyi murnar ganin Abbansu sosai suna ta bashi labarai. Har yar kiba yaga sunyi...ba dole ba tunda suna samun abinci ba kame kame ba. Aishatu tun asuba ta hau gyaran daki. Har mamakin kanta take irin wannan zumudi kada ma Huzaifa ya gane. Ita dai tasan ta damu sosai da shi...muryarsa kadai idan taji sai gabanta ya fadi. Garin yaya ta soma sonsa ne? tun a kan fahad ta sallama maza shima bazata bari ya sani ba har sai ta tabbatar da matsayinta a wurinshi. Kamar kullum ya shigo su gaisa bayan ya dawo ya ganta tayi kwalliya sosai kamar mai zuwa biki. Sai dai ya kula bata rabo da mayafi. Tun zuwanta sau daya ya ganta ba mayafi ranar da aka kawota. Toilet take shiga ta shirya kullum ta shirya. Yana ta binta da ido ta fada masa abinda take bukata na cefane don girkin rana washegari. Yace ko in samo miki yar aiki ne Aish? Hankalinsa yana ga kyakkyawar fuskarta kamar bai taba ganinta ba. Ta danyi murmushi bana bukata gaskiya. Ina su Aliyun ne ina ta jiran ganinsu. Yaji dadi sosai ya ce suna dakin Fadila bari na kira su. Tace ka bari zani da kaina muje kayi introducing dina dai. Zan fada musu ke ce maman kannensu 12 masu zuwa nan gaba. Zaro ido tayi tana dariya sai kace wata bera? Yace to wa ya sani ne abu a duhu? Filo ta dauko ta jefa masa sannan suka fita suna dariya. Fadila tana rungume da Aliyu tace kada ku manta sunan da na fada muku dai kunji ko? Aliya tace ai ni Abba zan fadawa ya koreta kada ta sha min jini. Karaf maganarta a kunnen Huzaifa yace wace zata sha jininki kuma Aliya..kinje kin koyo zance a wurin su hidaya ko? Aishatu na shigowa Aliya da Aliyu suka yo kanta har ta fara murmushi sai suka cire takalma suka fara jifanta. Huzaifa ya daka musu tsawa meye haka Aliya? Ta kyabe baki ta soma kuka Anti Mayya ce ta shigo zata shanye mana jini. Huzaifa ya tsaya yana mamakin wannan magana ta yaran shi. Aishatu ta dafe goshi inda takalmin Aliya ya sameta ta juya zata fita su Aliyu suna mata ihun Anti Mayya. Sai da ta fita Huzaifa ya janyo Aliya yar shekara hudu da rabi da Aliyu dan shekara uku. Wa ya fada muku sunanta kenan. Aliyu yace Mummy tace mana itama ta sha mata jini jiya da straw ko Yaya ya tambayi yar uwarsa. Kuma da zafi kamar allura. Fadila ta kwashe da dariyar mugunta. He should have known mai hali baya canjawa. Yaran yayi wa fada sosai yace da Fadila kin kyauta sannan ya fita cikin fushi. A kitchen dinta ya sameta tana kwashe tuwon shinkafa. Yayi saurin zuwa zai karba ta hana shi. Tana gama zuba tuwon a leda ta kulle ta rufe flask din. Sai ta hau gyaran gas cooker din. Yana magana taki kula shi sai aiki take kawai. Miyar agushin da take yi ta zubawa ganyen ugu ta cigaba da aiki. ya gaji da kallom yadda take yi ita a dole bazata karaya ba. Riko ta yayi ta karfi Aish listen to me please. Ta fizge hannunta kaje daki na kusa gamawa kitchen din akwai zafi. Janyo ta yayi ta karfi ya matseta a jikinsa. Kuka mai tsuma zuciya ne ya kwace mata ta rinka yi bai ko yi yunkurin bata hakuri ba. Gara tayi kukan ko zuciyarta ta sassauta. RASHIN GODIYA ✂ 36 Kusan minti biyar tana abu daya bai kosa da ita ba har ta gaji ta dena don kanta. Tana dagowa ta ga gaban farar shirt dinsa duk bakin kwallinta ya bata masa. Idanunta yabi yaga abinda take kallo...ya dan shafi fuskarta stop looking worried indai akan wannan bakin ne za'a wanke. Ta kirkiro murmushi ni kwallin da nayi asara ne ya dameni. Duk ya kare a gaban rigarka. Har zuciyarsa take burge shi, a wannan yanayin take iya wasa dole ya jinjina mata. Sai Fadila tayi dana sanin abinda tayi don bazai kyaleta ba. Amma yanzu burinsa bai wuce yaga farincikin Aish ba. Da taimakonsa suka kai kwanukan abincin falo tunda nasa dakin babu. Ta kawo masa fruit juice wanda ta hada da kwakwa, kankana, dabino da ayaba tayi blending ta tace. Sugar kadan ta kara tasa a fridge yayi sanyi. Komai nata a nutse take yinsa yaji ta kara shiga ransa sosai. Love will find its way tabbas haka ya taba fada mata...ko dai har ya iso ne bai sani ba? Shi kadai yayi murmushi tare da lumshe idanunsa. plate ta dauko zata yi serving dinsa abinci tana kallonsa. Bata gajiya da kallonsa...sai ta tuna abinda Fadila tayi mata....a sannu zan rama ta fada a ranta. Fahad ma ta koya masa hankali bare mace yar uwarta. Yaji dadin abincin sosai yayi ta mata godiya akan yadda ta iya bata lokaci tayi masa girki. Ya so nuna mata godiyarsa fiye da haka don shi da samun abincin kirki dai yaje gidan Umma. Sai dai kuma yanayin da suke yasa bazai iya ba. Fadila tayi nasarar bata musu mood dinsu. Kafin ya gama cin abincin ma tayi tafiyarta daki. Wanka ta sake yi ta tsaftace jikinta ta kwanta. Kanta taji yana mata matsanancin ciwo. Ta kasa tashi ma bare ta nemi Huzaifa ya bata magani. Wasu hawayen ne suka fara zuba...yanzu ita haka rayuwarta zata kare kullum cikin bacin rai. Anti Mayya da 'ya'yan mutumin da sonsa yayi mata mugun kamu suka kirata yafi komai kona mata rai. Tun yanzu kenan ina ga idan suka kara girma Fadila tana musu hudubar tsiya. Huzaifa kuwa da ya gama cin abinci dakin fadila yaje. Yaran sunyi bacci Aliya tayi cuku cuku da rigar shaddar dake jikinta wadda Fadila ta gagara cire mata. Shi kuwa Aliyu duk sanyin AC da fanka daga shi sai pant ta kwantar dashi. Fadila na ganinsa ta ce yau ma dukan nawa kazo yi a gaban 'ya'yana? Bai kulata ba ya saka musu kayan bacci ya gyara musu kwanciya. Ya dubeta da kyau...ki sani Fadila duk mai hankali yana gudun ranar dana sani. Duk abinda kike shukawa da hannunki ba na wani ba zaki girbe wata rana. Auren mace sama da daya ba kaija farau ba so duk wani haukanki bazai sa na saki Aish ba. Na fada miki ina raga miki ne darajar aure to ki sani duk wanda bai godewa ni'imar Allah ba wata rana zai godewa azabarSa. Naso yi miki hukunci mai tsanani sai gashi wadda kika cutar ta nuna min komai a sannu ake binsa. Yanayin da na ganta bayan ta fita dazu ya sa zan barki da halinki. Yana juyawa zai fita ta yi shewa ta tafa hannu Ahayye yaro Ahayye ba yaro ba Iyye nanaye Duniya bata bar kowa ba hatta wanda baa auri uwarsa ba ma jiransa take. Ki ji tsoron Allah Fadila.. tace ina ji Huzaifa, dole kake ganin laifina tunda ka hadu da annoba, ka auri karuwa ragowar mazan titi. Itakar karfinsa yasa ya mareta sai da taga haske ya fita cikin bacin rai. Dakinsa ya shiga yaji zafi don babu abinda ke kunne na sanyaya daki. Hatta windows duk an saki labule. A tsakiyar gado ya ganta ta rufa da bargo. Yayi saurin yaye bargon yana cewa lafiya Aish? Rawar sanyi take yi sosai jikinta ke karkarwa. Ga wani katon hijab ta saka, yana kokarin cirewa tana kara rike abinta. Idanunta sunyi ja sosai da gani ta dade tana kuka. Ba don Umma ba yau Fadila sai dai ta kwana a gidansu a yadda yake ji a ransa. Da kyar ya iya cire hijab din tan masa wani kukan ita sanyi take ji. doguwar rigar bacci ce a jikinta ta cotton. Ya kai hannu kai da wuyanta. Jikinta yayi mugun zafi, Oh my God ya fada yana tashi ya tsaya yiwa wadda bazata dauka ba nasiha ga Aish tana kwance. Ruwan famfo ya debo a wata roba ya hado da karamin towel. Jikinta ya rinka bi yana gogewa tun tana cewa ya bari har ta dena. Shi har mamaki ta bashi a wannan yanayin wai har tasan kunya don rufe jikinta ta rinka yi ita a dole kada ya ga jikinta.sai da ya gama ya zubar da ruwan ya dawo ya bude wata drawer ya dauko first aid box. Idanunta duk sun mata nauyi da kyar take bude su. Amma tana ganin ya fito da syringe ta fara kokarin tashi. Kayi hakuri don Allah Dr bana so...hawayen da ya tsani gani take yi. Yace kema kiyi hakuri nayi miki don ki sami lafiya. A hankali ta fara kokarin gudu yace bazan miki da zafi ba kinji. Tace to tsaya na shirya...a zaune nake ma ya fada. Ganin dai shirin yaki karewa sai kawai ya rungumeta yadda bazata motsa ba har yayi mata. Ai kuwa wata kara ta saki tare da cigaba da kuka mai sauti. Yana sakinta ta soma dukansa. Shima yasan ruwan allurar akwai zafi. Ya tashi ya kawo mata ruwa tasha magani. Sai dai tana sha shima da kyar ta fara kakarin amai. da gudu taje toilet ta amayar da maganin. Duk tausayinta ka kamashi ya gyara mata jiki kuma ya gyara wurin sannan ya sake kwantar da ita. Sai da yayi nafila har ya jefa pillow kasa inda yake kwana sai ya dawo dashi gadon. Gefe dai ya kwanta yana kallonta cike da tausayi da tsantsar so. Ya tabbatar bazai taba jindadin rayuwarsa ba idan
Chapter 18 · 0% Book details