Sashe 25
Rufaidah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Huzaifa yace kaine mijin Haj Sauda ko? Babban su Islam yace eh nine lafiya dai? Huzaifa yayi masa bayanin abinda ya gani. Yace to ni bana son aiki da zargi, nasan halin mutuminan amma ina neman izini muyi magana da Saudan ta fada min gaskiyar abinda ya faru. Alh Adam yace kayi tunani mai kyau Dr. Allah Ya tsare mana iyali daga sharrin shaidan. Muje gidan..Huzaifa yayi masa godiya yace haba har daurin aurenka fa nazo. Rashin zamana yasa bama haduwa sosai. RASHIN GODIYA ✂ 49 A falon gidan suka zauna Anti Sauda tayi musu gamsasshen bayani game da zuwan Fahad. Ta kare da cewa wallahi Dr matarka tana sonka kuma tana da rikon amana. Bai kamata zargi ya shiga tsakaninku akan abinda ka gani kawai baka bincika ba. Idan da tana son komawa gareshi ai bazata aureka ba. Huzaifa ya dafe kai ya kasa magana. Garin yaya ya nuna bacin rai sosai ga matarsa wadda take yiwa mai lafi uzuri. Alh Adam yace Sauda kibar kishi, babu abinda baya sawa. Tace hakane kaga ko ba komai nasan kanwata tana da babban gurbi a zuciyar Dr. Murmushi Huzaifa yayi yace nagode sosai da yadda kike kula da Aish, Allah Ya saka da alkhairi. Ya tashi zan tafi don Allah idan ya sake contacting dinku sai ki sanar dani tunda kince ya fada muku akwai abinda ya kawo shi. Har bakin motarsa Alh Adam ya rako shi. Sai da ya fita sannan maigadin ya biyo Alh Adam. Uhmm Alh ga wannan takardar. Wani mutum ne dazu ya bani yace na bawa Hajiya sai na manta yanzu na tuna da na sake gani bako. Alh Adam yace kuma bai fadk suna ba? Maigadi yace na tamba�a yace idan na bata zata gane. Alh Adam ya bude takarda ya karanta. (Nasan ba lallai ku yarda dani amma akwai bayanin da nake son �i Aisha ko mijinta. Ga numbar wayata pls contact me. Fahad) Alh Adam yayi tsaki kuma shine sai yanzu zaka bani? Gashi wanda abin ya shafa yanzu ya tafi. Gida ya shiga ya nunawa Anti Sauda ta�� ta salati ta kira Aishatu wayarta a kashe, ita kuma bata da numbar Dr Rano. Dole suka hakura sai washegari. Huzaifa bai koma gida ba sai da ya nemo wata kaza da Aish ke so. Duk ranar da rigimarta ta tashi ta rinka nacin sai ya siyo mata ga layi da akeyi a wurin. Haka ya zauna yana ta tunanin halin da take ciki. Fatansa da�a ba kuka take yi ba. Gashi ta �ashe waya ya kasa samunta. Hudu �a siya ya wuce gida. A falonta ya ajiye nata ya wuce dakin Fadila ya kai mata biyu. Nata daya na yara daya, ta karba cike da �ur�a, ita dai ta ga kayan kwada�i kawai. Har zai fita tace Abban Aliya ina na kanwata? Yana jin yadda tayi maganar yasan gulma ce kawai. Yace ban siyo ba ki kyale ta kawai. Ta ce gaskiya irin haka ba dadi ai sai ya zama rashin adalci. Ya dan kalleta to ko zaki dibar mata ne. Tuni ta hade rai kai ne hakkin ciyar da ita ke wuyanka ai. Kuma nasan idan ka koma kila ya tashi mai naman ko? Ba komai amma dai ka rinka adalci. Yace naji kije ki kwanta ki kular min da baby. Ta sake jindadi ta rufe kofa tana tsalle da murna. Aiki ya fara kyau saura na gobe ma. Huzaifa yana mamakin hali irin na Fadila, ya tabbatar da ita ce a wannan yanayin Aish bazata nuna farinciki haka ba. Da sallama ya shiga dakinta ya tarar bata ciki. Allah sarki Aish yasan dakinsa ta tafi duk don kada ta nunawa mutan gidan halin da suke ciki. Can gefen gado ya hangota tana bacci akan abin sallah. Zuciyarsa tayi masa zafi ya kara jin tausayinta. Shiyasa Annabi SAW ya hanemu da daukar mataki cikin fushi. Ya ajiye ledar naman ya zauna a gefenta tare da dora kanta a cinyarsa. Motsinsa ne ya tasheta tayi saurin mikewa tana murza ido. Tana ganinsa ta soma kuka wallahi ban san shine yazo ba. Cewa akayi nazo kana jirana wayarka ba chaji kuma. Kamshin turaren da take yini ana yi mata ya doki hancinsa....bakinsa yasa ya hanata magana. Sun jima a haka hawayenta bai dena zubowa ba. Ya dago habarta da hannu biyu yana kallonta...kiyi hakuri nayi kuskure da ban tsaya sauraron hanzarinki ba. Kishi ne ya rufe min ido tare da mamakin abinda ya kawo shi har nan. Wani kukan yaga zata fara yayi saurin rungumeta, gaba daya ya zaunar da ita akan cinyarsa yace Aish I love you so much, bana son tuna kin taba auren Fahad bare na ganshi. Ya cutar min da ke sosai kokari nake na mantar dake duk wannan mugun experience din. Tana kukan tace kai kadai na taba so a rayuwata baby. Idan ka kasa amincewa dani bansan yadda zanyi ba. Duk wani farincikina ya danganta da kai. Haka suka yi ta kara jaddadawa juna so. Can yace wai kinyi wanka yau kuwa? Tsami nake ji. Dundu tayi masa a baya ba kaine ka sani kuka ba. Kuma wallahi bana tsami duk turaren nan da nake yini a ciki. Yayi dariya to kauri kike yi no wonder naji dakin kamar ana girki da itace. Hawaye ta soma tana kukan shagwaba ta tashi tana tura baki haka ma zaka ce ko? Duk gyaran nan da nakeyi saboda kai, to na dena kuma wankan ma na dena gaba daya. Yana mata dariya yace ashe haka kike da nauyi cinyata kamar ba a jikina take ba. Yana murza wurin da ta zauna daga yanzu idan zan rarrasheki daga nesa nesa zanyi. Kara shan kunu tayi tana masa mita nima bazan kara zuwa kusa da kai ba. Ta dauki mayafinta sai da safe na dena zuwa dakin nan. Ya dago ledar kaza ga wannan bari na cinye sai kisa a shara. Yadda tayi murmushi ya burge shi ta dawo da sauri wasa fa nake yi. Ai duk macen kirki a dakin mijinta take kwana. Yayi dariya sosai sannan suka zauna suka ci abinsu. Bayan sun gama suka yi wanka ya janyota jikinsa suka kwanta. Aish taji ya kirata a hankali. Naam babyn Aish ta amsa masa. Wai sai yaushe za'a gama gyara jikin nan? Naga ya gyaru sosai tun yanzu. Tayi murmushi sai nan da sati uku. Dan murmushin fuskarsa ya dauke ki manta da wani sati uku don bazan bari ba. Wai baki san medically bai kamata a rinka yawan shakar hayaki ba. Shi kanshi turaren da kuke yi ba'a so yayi yawa saboda kada yayi wa jiki illa. Aishatu ta gane abinda yake nufi tace to ai kaga ba laifina bane. Wato shi irin wannan gyaran idan ba'a jira an gama ba to baci zaiyi. Jinsa kawai tayi ya kara matseta cikin kunnenta taji yace wannan dai yau zai baci gobe sai a sake wani. Tace to ai Anti Sauda tace........maganar da bata sami damar karasawa ba kenan sai da asuba. Washegari tana kitchen wayarta ta rinka ringing. Huzaifa da ke shirin fita asibiti ya dauka yaga ko waye. Sunan Anti Sauda ya gani ya duba time bakwai da yan mintuna. Sai kawai ya dauka. Tana jin muryarsa ta gaishe shi sannan tayi masa bayanin sakon Fahad. Yayi mata godiya sosai ya fita kitchen wurin Aish ya sanar da ita. Suna maganar text ya shigo da numbar da ya rubuta musu. Huzaifa ya kwafa a tasa wayar ya kira. RASHIN GODIYA ✂ 50 Yanayin canjin fuskar mijinta yasa ta fara tsorata ta kagu ya gama ya sanar da ita abinda ya fada masa. Bayan sun gama yace mata ta zai je wurin Fahad a hotel din da yayi masauki. Aishatu ta ce kada ka je idan don nasan karshe ranmu ne zai baci. Huzaifa ya shafi fuskarta kada ki damu duk wanda ransa ya baci shi yaso. Tace ban gane ba. Zaki gane bari nayi sauri. Kafin ya fita ya kira wani abokin aikinsa ya nemi alfarmar ya kama masa aiki kafin ya zo. Fuskarsa a hade ya bi bayan Fahad ya shiga dakin. A jikin kofa ya tsaya ya rungume hannuwansa a kirji. Fahad tace don Allah ka zauna Dr. Magana nake so muyi ta hankali. Huzaifa yace nan ma ya isa. Fahad yace suit yourself. Fahad yace nasan ka sanni ka san wasu abubuwa da dama akaina. Bayan rabuwata da Aisha na so ta kamar inyi hauka. Kuma har yanzu ina sonta. Huzaifa ya daure fuska abinda ka kirani ka sanar dani kenan? No bashi bane amma ka sani son da nake mata ne yasa zan sanar da kai. A shekaru uku da nayi da matata ta yanzu naso haihuwa sosai. Duk lokacin da naje asibiti sai likitoci suce lafiyarmu kalau lokaci ne kawai baiyi ba. A lokacin na rinka tunanin yadda zanyi na rabaka da Aisha. Sai watarana naji waazi da ya tayar min da hankali. Ga tsananin mamakin Huzaifa hawaye ya gani a idon Fahad. Nayi nadamar zama sanadin zubewar cikin Aisha har sau biyu. Nayi roki iyalina, iyayena da sauran yan uwana gafara game da irin zamanmu da su. Aisha kadai ta rage min da hakkin rai biyu. Huzaifa abin ya fara isarsa. Kaga malam ni fa ba tarihin rayuwarka nazo ji ba. Fahad yayi murmushi ni kuma sai kaji tarihin zaka fahimci inda na sa gaba. A halin yanzu dai na shiryu daga munanan halaye na. Sai dai kwatsam wata rana wata mata mai suna wasila ta kirani a waya. Suna neman hadin kaina ne a rabaka da Aisha ni na aura tunda sun sami labarin ina sonta. Sai a lokacin Huzaifa ya zauna. Fahad ya cigaba tun lokacin na amsa mata amma banyi niyar yin komai ba sai da matarka Fadila ta kirani a waya da wannan bukatar dai. Naji tsoron idan ban amsa ba zata iya neman wata watar ko wani mutumin shiyasa nazo. Tare da sannin matata don ita ta bani shawarar yadda zanyi. Huzaifa ya tashi tsaye kana son kace min fadila ta sanka ne,wato sharri kake son kulla mata. Dama nasan zuwa wurinka will be a complete waste of time. Hotuna Fahad ya baza masa akan table din gabansu. Wasu shi da fadila ne a wajen makarantarsu Aliya. Sai wasu